← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 115

Sashe 60

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farhan ba ta gane a zahiri take ko a mafarki, Sadik take gani kwance a kusa da ita yana mata murmushi yace "Princess, kin rame Sosai meyasa?"

"Ba tafiya kai ka bar ni ba, bayan kace ba zaka bari a Auramin Sunusi ba, meyasa ka tafi ba ka dawo ba?"

"Ai na dawo ba gani ba"

Ta matsa ku sa da shi, ta rungume shi,  tana shaƙar ƙamshin turarensa, yayin da a zahiri kuwa pillow ne take gani kamar Sadik yana mata Magana, ta ƙanƙame pillown ta na cigaba da surutai, ta na jin Tamkar Sadik ta rungume.

Ba Adda Maryam ba, hatta Umma abun ya bata mamaki, yadda Farhan ke wani irin bacci na rashin kan gado, har sha biyun rana bacci take taƙi tashi, ko sallar Asuba ba tai ba, anyi anyi ta tashi amma Abu ya gagara.

Da ƙyar ta iya tashi, ta haɗa sallar Asuba da ta Azahar, sedai gaba ɗaya jikinta a mace yake, ko Abinci ba ta ci.

Seda Adda Maryam tai ta mata masifa, sannan ta sata gab ta sha kunun tsamiya daga haka ta ƙi cin komai.

Adda Maryam zaton ta kawai miskilancin Farhan ne, da kuma rashin lafiya dan haka ta ƙyale Farhan ɗin.

Tana nan kwance akan katifar ta, ta ƙurawa fankar sama dake ɗakinta ido, tamkar za taga Sadik a jiki, tana tuna irin rayuwar da sukai, me cike da kulawa da Soyayya, ko da wasa ba ta taɓa kawo Sadik ze iya Auren wata ya barta ba.

"Assalamu alaikum" taji anyi sallama a É—akin.

A hankali ta juya ƙwayar idonta, dan ganin me yin sallamar, Hajiyar Abbas ta gani, nan da nan ta yunƙura ta tashi zaune, kanta kuwa ya sara seda ta ɗan rintse ido.

"Hajiya ina wuni" ta faÉ—a a hankali.

Hajiya ta ɗan tsura mata ido tace "Lafiya ƙalau Farhan, ohh ni Maimuna, Amare na ƙyalli ke kina baƙi, fatar duk tai duhu kin rame se idanuwa haka, anya Farhan, wace irin rashin lafiya ke damunki haka?"

Farhan tace "bakomai Hajiya"

"A'a fa, ban yadda bakomai ba, kimga daga ni seke a É—akin nan, gayamin menene?"

"Dagaske nake Hajiya bakomai"

"Hmm, ko dai Auren ne ba kya so?"

Farhan ta girgiza kai tace "A'a"

Ba ta san Abbas ya riga ya gayawa Hajiya, ba ta so Auren ba, nan Hajiyar ta sake jinjina zurfin ciki irin na Farhan.

"Farhan, shi lamarin rayuwa haƙuri ake da shi, ƙaddara duk a yadda ta zowa bawa haƙuri yake ya karɓeta, dama nace nasan iyayenki ba lallai su damu da yi miki wani abu ba, ga Aure zaki yi, kuma shi Aure mace duk in da take se da gyara, ana zaunar da ke ai miki faɗa akan yadda zaman Aure yake?" Farhan ta girgiza kai alamar a'a.

Hajiya a ranta tace 'se aukin siyan kwanuka kawai suka sani, ba a san a gayawa yaro wace irin rayuwa ze fuskanta ba'

Hajiya ta kalli Farhan tace "idan kinje kama ruwa, kina ganin farin Ruwa, ko ƙaiƙayi a al'aurar ki alamu na sanyi?"

Farhan ta ɗanyi jimm, ta ƙi Magana.

Hajiya tace "ke kalle ni nan, ni ba wadda zaki ji kunya bace, na haifa nima 'ya ki ke agurina, ki gayamin"

Nan ma Farhan ta girgizawa Hajiya kai, alamar a'a.

Tace "to shikenan, duk da haka dai na sa a haÉ—amin magungunan sanyi, akwai saiwar zogale da jar kanwa, zan dafa in aiko miki da shi, maganin sanyi ne sosai, in ma akwai a jikinki ze temaka miki".

Farhan dai tai shiru ba tace komai ba.

Hajiya ta numfasa tace "Abbas ya takuramin akan lallai yana son Magana da ke, bari in kirashi in haÉ—aki da shi"

Tai maganar tana danna wayar hannunta.

Tai ringing na seconds, sannaan ya É—aga Tare da yin Sallama.

Hajiya ta amsa sannan tace "Ga Farhan ɗin" ta miƙawa Farhan wayar tace "in kin gama, ki bawa ko su Amir ne su kai min Wayar"

Farhan ta jinjina kai sannan ta karɓi wayar ta saka a kunnenta.

"Assalam Alaikum" yai mata sallama.

A hankali ta amsa sa da "wa'alaikum salam"

"Daughter, jikin ne dai kokuwa, naji muryarki a ƙasa ƙasa?"

"A'a, lafiyata ƙalau"

Yai ajiyar zuciya yace "jikina ya bani ba lafiya ƙalau kike ba, duk da muryarki a haka take, Amma tana ɗauke da damuwa meyafaru ne?"

Kamar ya na ganinta ta girgiza kai tace "bakomai"

Yace "Shikenan, Hajiya tace min an kawo lefenki an saka wata É—aya ko?"

"Mmmm" shine abun da ta iya cewa.

"Farhan" ya kira sunanta.

"Na'am"

"Kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki irin taki jarrabawar kenan, Allah ya baku zaman lafiya, Allah ze baki ladan biyayyar da ki kaiwa iyaye"
Se da ya kai aya, sannan yaji ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya, Kamar duk surutun da yai hankalinta ba ya kansa.

"Me kike tunani ne?"

"He's gone" ta faÉ—a a Sanyaye.

"Who?"

"Sadik, he replaced me with another girl"

Abbas yace "subhanallah, and how do you know that?"

"Gayamin a kai, na yadda da maganar ka, Sadik baze dawo ba, Dole se na Auri Sunusi, amma ka gayamin ta ya zan dena tunaninsa?" Tai maganar tana hawaye.

"You still love him?"

"Yes i do"

"Ki sawa zuciyarki ke Yanzu mallakin wani ce, ki nesanta kanki da duk wani abu da ze sa ki dinga tuna shi, Sannan kiyi haƙuri, ki miƙa lamarinki ga Allah"

Ta É—an ja numfashi tace "shikenan, Nagode sosai doctor nagode"

"Karki kuma yi min godiya, Allah ya sanya Alkhairi"

Ba ta amsa ba ta cire wayar da ga kunnenta.

Haka kurum se ta tsinci kanta da saka lambar Sadik da ta haddace, a cikin wayar ta gwada kira amma wayar a kashe.

"Meyasa ba ki da zuciya ne Farhan?" Wata zuciyar ta tunasar da ita.

Ta ajiye wayar a gefe, ta kuma bin guri ta kwanta.

Yau unexpected, Steve ya kawowa su Nana ziyara, Nana tai murna sosai suka karɓe shi cikin girmamawa, Weekends ne dan haka Sadik ma ya na gida.

Nan yake sanar da Nana cewa, Ranar Litinin ze zo ya kaita sabuwar makarantar da zata cigaba da zuwa, Nana tai murna sosai dan dama zaman gidan duk ya isheta, ga wanda take zaune da shi ba shiga sabgarta yake ba.

Steve ya É—akko wayarsa yace, bari in kira babanki yace in haÉ—aki da shi idan na zo"

Ta kalli Sadik da yake zaune yana kallo, ko uffan be ce musu ba.

Tace "kuma wallahi se na gayawa Abba duk abunda kakeyi, da yawon dare da kake da tara abokai da taɓa mata duk se na gaya masa".

Sadik a ransa yace 'wannan mahaukaciyar Yarinyar tsaf za ta kuma jamin wata damuwar fa' amma a fili kallo É—aya yai mata ya maida idonsa kan tv ya cigaba da kallonsa.

Steve ya miƙawa Nana waya, se da wani murmushi ya kufce mata tace "Abba ina wuni"

"Lafiya ƙalau daughter na, ya kike ya gidan?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya su Yaya Faruk da Mother?"

"Suna lafiya, Faruk ya tafi karatu shime"

Nana tace "Allah sarki, Allah ya bads sa'a"

"Ameen ya Allah, Steve ya gaya miki ranar monday in Allah ya kaimu ze kaiki Makaranta da zaki cigaba da zuwa ko?"

"Eh ya gayamin Abba, ita ma boarding ce?"

"A'a ga mijinki Yaushe za'a kuma kaiki boarding, day ce, ko kin fi son boarding É—in?"

"Eh Abba na fi son boarding"

Abba yace "Yana miki wani abun da ba kya so ko?"

"A'a ba ya min Komai"

"Ki gayamin gaskiya Nana, me yake miki na rashin kyautawa?"

"Allah Abba dagaske nake, ba abunda yake min na rashin kyautawa" Sadik ya É—ago yana kallonta, ya san koma mene akansa ake Magana.

Abba yace"in dai yai miki wani abu na rashin daidai, ko kika ga yana aikata wani abu na rashin kyautawa ki bugo ki gayamin"

Tace "to Abba"

"Yawwa, Allah yai miki Albarka, kina da buƙatar wani abu ne?"

"Eh Abba, ammm. Ina son siyan mayukan shafawa, wanda na zo da su daga school sun ƙare, kuma garin akwai sanyi sosai"

Abba yace "Ai Sadik zaki gayawa, na saka masa kuɗi a account ɗin sa, duk abunda kike buƙata ki gaya masa, in yaƙi yi kuma shima ki sanar da ni, bari in haɗaki da Hajiya, gani na zo garin"

Miƙewa tsaye Nana tayi, cike da murna.

"Salamu Alaikum"

"Inna ta ke ce?"

Inna tace "ji wani shirme, to da wace in ba ni ba"

"Wayyo Allah, Yaushe rabon da inji muryarki Innata? Dan Allah ba ki kewata ba?"

"Kice haryanzu dai Nutsuwar da sauƙi ba ta ratsa ki ba"

Nana ta É—an tura baki tace "haba Inna, in ban kewarku ba kewar wa zanyi, ina Kakana? Ya jikinsa?"

"Jiki da sauƙi sosai Alhamdilillah, sunje gangare ɗaurin Aure, ai yanzun nan baban naki ya zo, yace takanas ya zo dan ya haɗamu a waya"

"Allah sarki, wallahi Inna ina kewar gida sosai"

Inna tace "kin dena koke koken kenan? Ina mijin naki?"

Nana ta kalli inda Sadik yake, ta harare shi tace "Allah ya kiyaye ni ba mijina bane"

Inna tace "Meki ka ce?"

"Ni Inna dan Allah a dena wani ce masa mijina, haba dan Allah wannan ɗan yaron ai abun kunya ne ace mijina ne, nan gaba idan na ƙara tsawo fa sena kamo shi a tsawo, Ni babba zan aura me hankali, kawai ku dinga min Addu'a Allah ya bani miji nagari, se ki ga ma na kawo miki bature a matsayin sirikinki"

Inna tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ke baki da hankali ko, dan ubanki Aure abun wasa ne? Wato nan É—in ma zuwa ku kai kuka cigaba da raba abun faÉ—a ko Nana, duk nasihar da nai miki ba ki ji ba kenan?"

"Ni wallahi Inna ba na son shi, Auren dole fa akai min, wannan yaron ban da hantara da masifa meya iya, a gabanki fa har dukana ya dinga yi, ni dai kawai ki min fatan Allah ya bani miji nagari"

Inna tace "na shige su, a nan É—in ma dukanki yake?"

"A'a ni be dakeni ba, amma dai wallahi ba na son shi, shima kuma ba ya sona, dan Allah ba se ya sakeni ba, in Auri wanda nake so".
Chapter 60 · 0% Book details