← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 115

Sashe 87

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan yaje guri ya tarar da cunkoso a hanya, ji yake kamar yaiwa motar fuka fukai ya je in da za shi, saboda Azabar ruÉ—ani da hanzarin son ya ga Farhan.

A ƙofar Gidan su Amin yai parking, gashi ko waya be ɗakko ba, idan ma ya ɗakko wayar ina yaga lambobin 'yan ajin na su yanzu.

Wani irin mahaukacin horn ya dinga yi, wanda se da layin gaba É—aya ya É—auka, a gigice megadin gidan ya fito yana wane mara tunanin wannan?

Sadik ya sauke Glass yana kallonsa, megadin yace "Ahh Yau kaine da kanka, Yaushe rabon duniya da ayyaraye, munyi cigiyarka har mun gaji"

Sadik ransa a haÉ—e yace "yi min magana da Ameen"

"Aminu yana makaranta ai"

"Wace makarantar?"

"Yana Makarantar nan, ta Nijar amma nasan yau zuwa gobe in Allah ya kai rai, ze shigo ko dai a satin nan"

Dukan sitiyari Sadik yai, yana wani irin huci, a hankali ya furta "Why Farhan, meya haÉ—aki da Mubarak, tabbas idan na kama Mubarak da aikata wani abu akan ki da hannun na zan kashe shi"

Ya kuma jan motar nan ya bar unguwar su Amin, kusan duk abokan nasa na ajinsu ya zaga, amma ba wanda ya samu balle ya samu wani information, ya koma unguwar su Farhan, ya aika yaro a kirata amma aka kuma ce masa ba ta nan.

Har ƙarfe biyar na yamma Sadik yana gararamba a gari akan yadda ze samu Farhan, amma abu ya ci tura.

Haka ya koma gida, Mother na ganinsa ta fara faÉ—a "daga ina kake haka? Jiya Usman yace min ya zo ya tarar da kai wani iri, na duba naga kana bacci, yau wayewar gari kan in tashi wai har ka fice daga gidan nan, kalli se yanzu biyar da rabi ka dawo, daga ina kake haka?"

Sadik yace "ba ko ina?"

"Kamar ya ba ko ina?"

"Mother bani da lafiya ne, naje Asibiti ne aka samun ruwa"

"Kuma shine ka kasa kiran kowa a waya ka sanar masa? Ya jikin naka?"

Yace "naji sauƙi Alhamdilillah"

"Sun baka magani ne?"

Sadik ya gaji da tambayoyin Mother ya jinjina mata kai kawai ya shige É—akinsa.

Tea ta sa aka dafa masa, ta kai masa É—aki ta takurashi akan ya sha.

Sam Sadik ya manta da wata yunwa, dan ba ya jinta sam.

Mother ta kalleshi tace "Sadik, ko dai duk akan Yarinyar nan ne kabi ka da mu ka É—aga hankalinka?"

Da sauri Sadik yace "Mother wace Yarinyar?"

"A'a wace Yarinyar ban da matarka? Ko dan sun tafi ƙauye ne kake wannan abun harda rashin lafiya?"

Sadik ya girgiza kai yace"A'a"

Mother tace "ka dai shiga hankalinka ka dena wannan zaƙewar, su mata ba a musu haka, idan ta fuskanci irin wannan son kake mata, wahalar da kai za tai, idan kuma saboda ɗanka ne ai za su dawo, ka sha tea ɗin nan ga doya nan ka ci kan ai sallar magariba, da anyi isha'i se ka kwanta"

Da ƙyar Sadik ya cakali Abincin yaci ya bar shi, dan a ganinsa Mother ba zata gane halin da yake ciki ba.

Sunusi ne keta binciken kayansa, yayin da Haladu ke gefe yana rubutu a jikin allo.
Aƙalla Sunusi ya shafe da mintuna talatin yana zazzage kaya yana mayarwa, amma Haladu be ce masa uffan ba.
Sunusi ya É—ago ya kalli Haladu a fusace yace "Haladu"
Haladu ya É—ago ya kalleshi yace "ya akayi?"

"Ka taɓa min kaya da bana nan"

"Ban fahimci me kake faɗa ba, Kamar ya ina taɓa maka kaya, ƙaddara ma ina taɓa maka yau na fara taɓa kayanka ko kai ka taɓa nawa, ka taɓa ganin na maka sata ne, ko ba ka nan na ɗau abu ka dawo ina gaya maka"

Sunusi yace "kar ka rainamin hankali mana, ba yau ka saba ta;a kayana ba amma tun É—azu nake neman abu ko ka tambayi me nake nema?"

"Meyasa zan tambaye ka bayan nasan ban É—aukar maka komai ba"

Sunusi yai shiru can yace "kai wallahi Haladu kai ne, in ba kai ba ba wanda ze É—au abunda nake nema"

"To wai me kake nema ne?"

Sunusi yace "jakar da nake ajiye ajiyen aikin da nakewa mutune aka taɓa min, na nemi wasu laƙanai da nayi ban gani ba, kuma ni gani nake kamar an sauya min layoyin nan da wasu"

"Kuma shikenan sekace nine na ɗauka, meye haɗina da aikin da kakewa mutane da ze sa in ɗaukar maka, na taɓa yi maka hakane?"

Sunusi ya dawo gaban Haladu ya tsuguna yace "Haladu, naga take takenka ne a 'yan kwanakin nan, ka damu da lamarin Yarinyar nan, matar da zan Aura, wallahi ka sake ka shiga hurumin da ba naka ba, ko kuma na gano kai ka É—au abinda nake nema, zaka ga abunda ze biyo biya"

Seda cikin Haladu yai wata irin ƙara saboda yasan Sunusi ze iya, amma ya dake yace "ba ka isa kai min abunda Allah be min ba, kuma Yarinyar da kake iƙrarin zaka Aura, ba sonta kake ba wallahi, kuma ba zaka taɓa mallakar ta ba tunda Allah ba ya barin zalunci sam"

Malam Labaran ne yai gyaran murya yace "wai meke faruwa ne, hatsaniyar me kuke ne?x

Sunusi yai saurin cewa "bakomai Malam, saɓanin fahimta ne kuma Komai ya wuce"

"Ku dinga ƙoƙarin kai zuciyarku nesa, ku dena irin wannan hatsaniyar yaran nan da ku suke koyi, ku dena aikata rashin ɗa'a suna jinku"

Sunusi yace "to malam, insha Allah"

Malam na barin gurin, Sunusi yaiwa Haladu wani Mugun kallo irin na zan haÉ—u da kai ne, sannan ya fice.

Haladu kuwa ajiyar zuciya yai yana fatan Allah ya tsare shi daga Sharrin Sunusi, dan Sunusi ba shi da imani sam.

Kwana uku kenan, Sadik yana sintiri a tsakanin gidan su Farhan da na su Amin, har gidan su Nas yaje, amma akace shima baya nan yana dutse, baya so ya tunkari in da Mubarak babba yake ba tare da ya san in da Farhan take ba.

Abun duniya ya damu Sadik, ya rasa in da ze sa ransa, gaba ɗaya Mother ta kasa gane kan Sadik gaba ɗaya, baya wuni a gida baya cin abinci, tun tana mitar har ta gaji ta ƙyaleshi, ta zata kawai kewar matarsa yake da ɗan sa, dama kuma tun da suka dawo Nigeria ba wani fita yake ba, dan haka kawai ta zaci se yanzu yake zaga abokansa.

Wanka ma se yayi dagaske yake iyayi, salla kawai yake cikin kwanciyar hankali, raba dare yake ido biyu, haryanzu ya kasa gane dalilin da yasa ya manta da Farhan a duniyarsa, babban abunda yake É—aga masa hankali be wuce batun Ganin Farhan da Mubarak da akace anyi ba, ya rasa in da ze sa kansa ya ji daÉ—i ba shi da wani burin da ya wuce ya saka Farhan a idonsa.

"Nana ba zaki sha kunun nan ba se ya huce, se fama kike da waya a hannu tun É—azu"

Nana ta ɗan ɓata fuska tace "Inna, Besty yau kusan kwana Biyar be kira mu ba, kuma ni na kira wayarsa amma ba ta shiga"

Inna tace "waye kuma haka?"

Nana ce "baban Sahal mana, kullum fa se ya kirani a waya, yace in kara wayar a jikin Sahal yaji numfashinsa amma kwana biyar be neme mu ba"

Inna tace "to jiki da jink, ai dole wataran ze gaji ko?"

"Inna yau fa kwana biyar, Allah ya sa Lafiya yake hankalina ya fara tashi"

"Ban da abunki ai Lafiya ita ke ɓuya, yana nan lafiya insha Allah"

"To Inna Allah yasa, amma yana da kula sosai in lafiya baze kasa kiranmu tsawon wannan lokacin ba"

Inna tace "to ai se kiyi, tun da akan ku ze ƙare" Nana ta ja bakinta tai shiru, amma dai jikinta na bata akwai wani abu a ƙasa.

Yauma da safiyar Allah Sadik yana hanya gari ya ƙarasa wayewa, hanyar makarantar su Amir ƙanin Farhan yaje ya tsaya, da Amir yaga Sadik se da abun ya bashi mamaki ba ze iya faɗin sau nawa yaga Sadik ba, ba yau ba gobe cikin sintiri yake, gashi kamar Farhan ta san da zuwansa taƙi zaman gida sam.

Sadik ya nufo Amir, Amira ya gaisheshi ya amsa sannan yace "Ameer dan Allah ko lambar Farhan ka bani mana"

Ameer yace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba ta nan, dan Allah in wani abun tai maka kayi haƙuri, ka barta ta ji da halin da take ciki"

Sadik yace "a wani halin take dan Allah, ka gayamin"

Shiru Amir yai, se ga ƙwalla ta taru a idonsa zeyi kuka.

Sadik ya dafa kafaÉ—un Amir yace "dan Allah ka gayamin halin da take ciki, da kuma in da zan sameta"

'gaskiya ko É—aya ba zan iya gaya maka ba, amma kaje gobe in Allah ya kaimu zan nemo lambar ta ka zo in baka"

Daga haka Amira ya zame kafaÉ—arsa yai gaba abunsa.

Sadik ya koma cikin mota ya kifa kansa a kan sitiyari, yana sauke numfashi da kyar, ga cikinsa har wani ciwo yake, saboda Azabar yunwa har wata ramar dole yayi.

Wasa wasa Har ta gaji da kiran layin Sadik amma kullum a kashe, dan harta fara kuka a ɓoye dan kar Inna ta gane tai ta mata faɗa.

Amir har mamakin nacin Sadik yake, dan a ƙofar Gidan ya tarar da Sadik da uwar sassafiya.
Ya koma gida ya É—akkowa Sadik lambar Farhan a jikin takadda.

Wata irin ajiyar zuciya Sadik yai, ji yake tamkar yaga Farhan, dubu biyar ya bawa Amir, amma fafur yaƙi karɓa.

Se dai Sadik be fito da waya ba, dan haka ya nufi gida, kawai ya ratse hanya ya koma gidansu Amin.

Megadin su Amin na ganinsa yai murmushi yace "a wannan karon kayi sa'a, ya shigo jiya da daddare, bari in masa Magana.

Kusan mintuna biyar da shigar megadin, se gasu tare da Amin, shima ya ƙara girma yai fresh, ya fito fuskar sa cike da fara'a yana "Takawarka lafiya Prince namu, ba amana wallahi"

A Wani irin fusace Sadik ya buɗe murfin motar ya fito, fuskar sa babu walwala ya ƙure Amin da ido, cikin huci yace "Aminu ina Farhan take?"

Amin yace "wacw irin tambaya ce wannan? Ai kai zan wa wannan tambayar"
Chapter 87 · 0% Book details