← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 115

Sashe 111

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kunya ce ta kamata kamar ta nutse ta sunkuyar da kai, tun da Nana tai masa magana akan Khairat, ya fara jinta a ransa, kuma yana tausayin yadda take son sa.

"Oya, aje a canza kayan nan maza". Tace "to".

Sunusi yana kwace yana fama da kansa, Wani irin matsanancin ciwon ka ne yake damunsa, ya sha magani amma abu kamar turi, baya jin magani, yana kwance a ɗaki ya ga wata inuwa tana shawagi a kansa, ya waiwaya amma be ga komai ba, ya yunƙura ya tashi yana waige waige amma ba kowa, ya koma ya kwanta, amma ya kuma ganin inuwar yana ɗaga kai, yaga Farhan a kansa hannunta riƙe da wata bulala, jikinta duk a ƙoƙƙone.

"Ke Farhan meye haka? Meye ya ƙonaki haka?" Ba tai Magana ba ta shiga zuba masa bulalar hannunta, nan ya dinga kurma ihu kamar wanda ake cirewa ido.

Haladu ne ya shigo a gigice yana faÉ—in "lafiya, menene ya faru?"

Sunusi yace "ita ce, dukana take"

"Ita wa?x

"Farhan ce take dukana da bulala"

Haladu yace "wace irin Farhan kuma?"

Sunusi yace "Wallahi yanzun nan ta bar ɗakin nan" yai maganar cikin ƙaraji.

Da ƙyar Haladu yai tai masa Addu'a, da tunanin ko gamo Sunusi yai.

Duk yadda Sadik yake tunanin lamrin ya wuce tunainsa, dan sosai Farhan ke gudunsa, take nuna masa ba ta sonsa, ita Abbas take so amma ya Aureta, se fama yake da ita, amma babu alamar zata sassauta masa, abun ya bawa Sadik mamaki sosai, Nana kuma tai watsi da su, kamar ba suyi existing ba, idan ya zo in da take shikenan, in be zo ba ba ta damu ba, makarantar ta take tafiya, in aka taso ta tafi gidan Mother ba zata dawo ba se dare.

Ranar da Sadik ze bar ɗakin Farhan, ya ɗaukesu zuwa gidansu, dan su gaida Mother, Nana tana zuwa ta shige bayan mota, ba tare da ta saurare su ba, Farhan ta miƙ hannu ta ɗau Sahal, amma ya dinga ihu ya ƙi yarda, Saboda akwai shi da ƙyuya.

Farhan tai mamakin ganin Nana ta kame a bayan mota, ta basar da su, dan ta Farhan ba ta son Irin wannan zaman da suke da Nana, duk da ita ma Farhan ba me son mutane bace, amma yadda suk zaman kowa da halinsa, ba ta jin daÉ—in hakan sam.

Ko da suka je gida, suna zuwa sabo direba yai murmushi yana kallon Farhan yace "Allah yayi, Amaryar Sadik Allah ya amsa wannan soyayya"

Farhan ta sunkuyar da kai cikin jin kunya, tana gaida Sabo.

A falo suka haÉ—u da Abba yana shirin fita, Nana ce ta fara gaisheshi ya amsa cike da kulawa yana cewa ina abokin nasa wato Sahal.

Sega Sadik sun shigo tare da Farhan da Sahal, suka gaida Abba ya amsa ba yabo ba fallasa, yai musu sallama saboda yana sauri ze shiga taro, sedai Abba ya dinga tantamar abunda aka faÉ—a akan Farhan, saboda a nutse take sosai ba alamar rashin ji a tare da ita.

Mother ce ta fito, ba tare da tasan su Sadik sun zo ba, Nana ta fara gani tsce "ke kuma daga ina haka?" Tana rufe baki ta ga Sadik tare da Farhan.

Turus tai tana bin Farhan da kallo, cikin ladabi Farhan ta gaida Mother, guntun tsaki Mother tai ta cigaba da maganarta.

Se Nana taji ba taji daÉ—i ba, saboda ta san raÉ—aÉ—in irin wannan abun, Sadik yace "Mother ga Farhan na kawo miki"

Mother tace "naganta ai, se a kai yaya?"

"Ai naga ta gaisheki ba ki amsa ba".

"To in amsa ince mata me? Ba dai Aurene ka dage ka je ka Aureta ba, to ga ka nan gata ai, dama na gaya maka ba ruwana da Aurenka ba hannuna a cikin wannan Auren, dan haka kar ka ƙara kawomin ita wai ka kawota gurina bana buƙata"

Dam dam! Gaban Farhan ya faÉ—i, kenan iyayen Sadik ba sa so amma ya Aureta.

Nana tace "Mother, ai aikin gama ya gama, abu ka ya faru ake ƙinsa, amma ya riga ya faru dan Allah kiyi haƙuri komai ya wu....

"Dalla rufemin baki mara zuciya kawai, ke har abada Mijinki baya laifi komai yai daidai ne, amma hakan be hana yai miki kishiya ba ai, sakarya" Nana ta ja bakinta ta tsuke, Farhan kuwa se murza yatsunta take, amma hawaye ne ya cika mata ido fal, Yanzu da Abbas ta Aura da shikenan ba ruwanta da wannan tashin hankali.

Haka suka wuni a gidan nan, babu daÉ—i sam dan Farhan tai dana sanin zuwa gidan nan, dan ta sha miyagun maganganu a gurin Mother, maganganu na muzantawa, ba tare da la'akari da koma menene É—anta ne sila ba.

Se bayan sallar isha'i sannan suka koma gida, ko Abincin gidan Mother Farhan ba ta ci ba, ita kanta Nana sam ba ta ji daɗin abunda Mother taiwa Farhan ba sam, duk da ba shiga shirgin Farhan take ba, amma Koba komai Allah ya riga ya ƙaddara Auren be kamata tai haka ba.

Suna zuwa gidan Farhan ta wuce É—akinta, ta dinga kuka kamar ranta ze fita, saboda wani irin É—aci da zuciyarta ke mata.

Sadik ya durƙusa a gabanta cikin sigar rarrashi yace "Farhan, nasan abunda mahaiiyata tai miki ba daɗi, amma dan Allah kiyi haƙuri komai ze wuce, watarana se labari".

"Yanzu dan Allah kasan mahaifiyarka ba ta sona amma ka Aureni? Ba ka kyauta min ba ba kai min adalci ba, da ka barni na Auri wani daban da shikenan da duk ba haka ba, amma kana tunanin akwai lokacin da ze zo Mahaifiyarka ta canza ra'ayinta a kaina? Baka kyauta min ba tunda ka shigo rayuwata nake haɗuwa da ƙaddara kala kala, ni haɗuwata da kai ba ta haifarmin komai ba se tsananin nadama da gurɓacewar rayuwa, ina dana sanin haɗuwa da kai, bana son ko ganinka Sadik".

"Farhan, kar ɓacin rai ya sa kiyi kuskure, ina son in gyara laifukana a gareki"

"Ba wani abu da ze gyaru, ka tafi ka bai guri kawai, ni ko san ganinka bana yi, ka cutar dani Sadik da ba saka ba da duk wannan abubuwan ba su faru da ni ba" a sanyaye jiki ba ƙwari, Sadik ya bar ɗakin gaba ɗaya ya rasa abunyi.

Ya daidaita nutsuwarsa Sannan ya nufi É—akin Nana.

Ya tarar tai shirin bacci, tana shan madara a kofi, ta kalleshi tace "ya dai ya na ganka?" Hararta yai yace "saboda kin sallamani har kin manta yau zan dawo gurinki"

"Aini ban zaci zaka dawo ba, ka koma na ƙara maka wata ɗaya kyauta"

Banza yaiwa Nana,yaje gaban mirror ya cire agogon hannunsa ya wuce toilet, ko da ya fito Nana har ta kwanta, bayanta shima yabi ya kwanta, ya rungumeta ta baya, gaba É—aya ransa a cunkushe.

Nana tai ajiyar zuciya tace "kamar wani abu na damunka?"

"To Besty ya zanyi? Kowa ya ƙi fuskanta ta, duk yadda nake da Mother ta juyamin baya, kun ƙi yadda Auren nan nawa ƙaddara ce, rabona da ke a shimfiɗa ta watanni uku da wani abu, amma yau in dawo gareki kice wai kin ban wata ɗaya, ya kuke so inyi ne? Da wace kalma zan miki amfani wadda zata tabattar miki da ina sonki?" Ya ƙarasa Maganar cikin tsantsar damuwa.

Nana ta juyo tare da fuskantar Sadik sosai tace "Besty ya zanyi, ka auri wadda kake so dole in ja jikina, kar in fiye maka shishshigi, amma ni kaina bana son abunda Mother tai, amma nasan lokaci ne, tunda Mother ta ƙaunace ni, to tabbas ita ma watarana zata so ta".

"To amma meyasa kuke zama kamar na gaba, ina kallo fa wataran se tai miki Magana ki shareta, bana jin daɗi, kin san in ita ce ba zan taɓa bari ta wulaƙanta ki ba, ke meyasa kike mata haka?"

"Saboda ina so da kishin mijina, ins ganin ta rage min wani jin daÉ—i na rayuwata, amma ina tausar zuciyata za dena insha Allah, ba zan sake ba hakan yai maka?"

Sadik ya janye jikinsa daga nata yace "Ni rabu dani, idan na mutu ai duk kun huta"

Ta rungumo shi tace "haba Besty, am sorry ba zamu so ka mutu ka barmu ba, dan Allah kayi haƙuri Bestyna, i miss You sosai"

Yace "serious?"

Ta jinjina masa kai alamar eh, murmushi yai ya sake rungumeta a jikinsa, daga nan suka sha soyayyarsu, hakan ya ragewa Sadik damuwar da yake ciki, dan da gaske yai kewarta.

Farhan kuwa seda ta tabattar yau ba tare zasu kwana da Sadik ba, sannan ta shiga hankalinta, wani irin kishi ya dinga damunta, tare da kewar Sadik É—in.

Da safe yau Nana tai girki, Sadik ya ƙi zuwa su gaisa da Farhan, ya shareta ya cigaba al'amuransa.
Gaba É—aya se abun ya dameta, ranar da ze dawo gurinta da safe, ya shigo É—akinta amma ta ganshi da travelling bag, kallonsa tai saroro tace "ya naga haka?"

"Zan tafi Zariya ne"

"Zariya kuma, me za kai a Zariya?"

Sadik yace "makaranta zan koma, tun kan ai bikinmu nake ƙoƙarin komawa can, Alhamdilillah na samu zan tafi"

Kamar za tai kuka tace "amma meyasa ba ka gayamin ba?"

"Ni da ba kya so, idan na tafi kika dena ganina maybe ki dena jin haushina" be jira me za tace ba, yai waje abunsa, binsa tai da kallo ta kasa furta komai. Can kuma seta bi bayansa da sauri, amma tana leƙawa har ya kunna mota, Nana tana tsaye da Sahal tana ɗaga masa hannu.

Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, gaba ɗaya taji abubuwan da tai ba ta kyautawa Sadik ba sam, shiru tai ta rasa abunda yake mata daɗi, gashi sam ba ta ƙawaye ko wata wadda zasu tattauna akan matsalar tare.

Nana na falo tana son ta ci Abinci, amma Sahal ya hanata, se ƙoƙarin zubar da Abincin yake, yana kai hannu cikin kwanon, Farhan ta fito daga ɗakinta, ta kalli Nana tace "barka da rana"

Nana tace "yawwa barka" daga haka ta cigaba da kokawa da Sahal.

Can Nana tace "Ya salam da wannan Yaron, kai ga babarka can tafi ka bani guri" tai maganar tana nuna masa Farhan, murmushi Farhan tai tana miƙawa Sahal hannu.
Chapter 111 · 0% Book details