← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 115

Sashe 25

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Sadik yai yaƙi amsawa.

"Ya kai shiru baka amsa ba, can a gidan naku ma haka kake wannan rashin É—a'ar baka gaida iyayen ka da safe ko?"

Sadik ya sunkuyar da kai yaƙi Magana.

Hakimi yace "a bashi Abincin safe"

Nana ta kawo wani kwano ta ajiye.

Hakimi yace "bismillah, maza É—au Abinci ka ci"

Sadik ya buɗe kwanon nan, tuwon masara ne a ciki da miyar kuɓewa ɗanya.

Sadik ya gyatsine fuska yace "ni bana ci"

Hakimi ya kalli É—aya daga dogaran yace "A sashi yaci Abinci"

Ai ganin da Sadik yai dogarin ya É—aga bulala, ze zumbuÉ—a masa yasa Sadik a gigice yace "zanci dan Allah, a bani cokali"

"Bame baka cokali, sa hannunka kaci da shi"

Haka Sadik Ya janyo kwanon ya runtse ido ya kai loma ɗaya bakinsa, da kyar ya haɗiye saboda warin daddawar da ya addabe shi, sega ƙwalla a idon Sadik ya kai loma ta biyu amma ya kasa haɗiyewa se kakarin amai da yake.

Hakimi yace "idan yai amai, ku zane shi sannan a ƙaro masa wani tuwon, zakaci ƙaniyarka, seka kwan uku kana cin gabza, saboda rashin ta ido har ayi Abinci a baku kace kai ba zaka ci ba ko, za'a ladabtar da kai ai"

Haka A saka Sadik a gaba, seda ya cike gurbin Abincin da be ci na na jiya, seda ya cinye tuwon nan tas.

Sannan aka kai masa ruwa banÉ—aki yai wanka, sedai shi kansa banÉ—akin tsoro ya bawa Sadik, ga wani soson wanka irin na mutan da É—in nan me zafi a jiki, ga ruwan wanka a bucket ko abun zuba ruwa babu, masan dake banÉ—akin ma tsoro ta bashi, kar yaje yana cikin wankan ya faÉ—a ciki.

sabulun kawai ya goga ya watsa ruwa ya fito da sauri, dan tsoro idan ya kalli rufin azarar nan se yaga kamar zega maciji a ciki.

Da ya fito, Aka kawo masa wasu irin kaya over size, wanda ko Abbansa aka bawa kayan nan sun masa yawa, akace ya saka kayan.

Sadik ya dinga kuka, hawaye shaɓe shaɓe yana tunanin wannan wane irin abune se kace zamanin bayi.

Akai masa rawani kamar dagacin ƙauye, aka fita da shi zaman fada.

Shigar da a kai masa tasa Nana ta dinga tuntsura dariya, duk gayun Sadik yau an maida shi ɗan ƙauye typical.

Farhan duk ta damu kanta sosai akan rashin jin Sadik kwana biyu, ta kalli group É—in su Lilly da suke kiran kansu da Sweet fifteen, suna ta shirmen su a ajin, sedai Lilly tayi shiru da alama tana tunanin wani abun ne.

Haseena tace "ke Lilly, wai kwana biyu meke damunki ne, kullum cikin zancen zuci?"

Lilly tai ajiyar zuciya tace "bakomai Normal"

Yasmin tace "Ni sirrin Wannan glowing ɗin da kike zaki bani, kinga yadda kika ƙara ja kuwa, ga kumatunki sun sake girma"

Banza tai musu suka cigaba da surutan su, Haseena tace "Yasmin zoki rakani Clinic in karɓi pad, a kowane lokaci zan iya ganin abun nan, kuna ban zo da pad ba"

Yasmin tace "i thought you are pregnant ai"

"Ke pragnent É—in uban wa, ke kika min cikin dalla tashi muje ki rakani"

Gaban Lilly ne ya faÉ—i jin hirar da sukeyi, cikin hanzari ta tashi ta tafi Office É—in Sir Nazir.

Sedai baya Office ɗin, ta nemi guri ta zauna tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa da sauri da sauri.

Ta daɗe tana jiransa se ga shi ya dawo, hannunsa riƙe da litattafai da maka.

Yana ganinta ya fara murmushi yace "Baby yaya?"

Ta kalleshi tace "Akwai matsala fa"

Yace "subhanallah, matsalar me kuma Fateena?"

"Am sick wallahi, bani da lafiya fa"

Yace "eyyya sorry, ai baki gayamin bane, muje in rakaki clinic a duba min ke"

Tace "Bafa yadda kake tunani bane"

Yace "to yaya ne?"

"Sir, wata biyu kenan ban period ba fa, kuma fa hakan na nufin ciki ne dani"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Lilly ya a kai kika san ciki ne da ke?"

"Ina karantawa a Novels, kuma ka kanka ka mana lesson, ni gaba É—aya hankalina ya tashi, ina jin tsoro idan babana ya sani ze iya harbeni wallahi"

Cikin dirircewa yace "kinga, kwantar da hankalinki ki nutsu, haryanzu bamu tabattar da abinda kike zargi ba"

Cikin kuka tace "meya rage wanda zamu tabattar ka sani a bala'i, duk wasu signs na ciki su nake ji a jikina, and kana cewa bamu tabattar ba"

Nazir cikin tashin hankali yace "kinga calm down, yanzu bari in baki robar ruwa, kiyi fitsari a ciki, zanje in siyo pt strip dan mu tabattar se mu san abunyi.

Ba tace masa komai ba ta cigaba da kuka.

"Dan Allah Lilly ki nustu kar asirinmu ya tonu ki dena wannan kukan, bari inje yanzu zan dawo"

Ya fita daga Office É—in cikin sauri.

Abba kuwa gani yai be kyautawa Mother ba da ya fita a sabgarta ba, tabbas an mata ba daidai ba amma yadda ya haƙura yai biyayya ita ma dole tayi.

Sashinta ya nufa, bata falo ya wuce bedroom É—in ta, aikuwa ya tarar da ita akan gado a zaune, tayi shiru ta zubawa guri É—aya ido.

Sallamar da yai ne ta dawo da ita hankalin ta daga dogon tunanin da take.

A ciki ta amsa masa sallamar ta É—auke kanta.

Ƙarasowa yai ya zauna a kusa da ita, ya ɗan ƙura mata ido, yaga yadda idanunta su kai ja, da alama ba ta samu isashen bacci ba.

"Barka da safiya" ya faÉ—a yana kallonta.

Tura baki tayi ƙwalla na taruwa a Idonta.

"Hauwa'u, nasan abunda a kai miki ba'a kyauta miki ba, amma tunda naiwa iyayena biyayya ya zama dole kema ki haƙura, nasan ba za su taɓa yi masa abunda zasu cutar da shi ba, dan haka kiyi haƙuri ki dena wannan damuwar, dan ban shirya yin musu ko jayayya da iyayena ba saboda ke"

Ta É—ago ta kalle shi tace "Amma...

Ya katseta ta hanyar É—aga mata hannu tare da cewa "bana son sake jin wata magana akan wannan lamarin, na riga na rufe wannan babin, ki kai min breakfast É—ina part É—ina zan karya in fita"

Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, ya juya ya fita daga ɗakin.

Wasu hawayen baƙin ciki suka shiga zubo mata, da ta san a can za'a baro mata Sadik, da duk yadda za tai seta hana shi zuwa garin, da wani aka bari a cikin yaran ba Sadik ba, da ba zata damu haka ba, amma Sadik tun tasowarsa be taɓa nesa da ita da kwanaki ba, har gara dr. Da Faruk suna zuwa cikin Family, har ƙasashen waje sunje karatu, amma Sadik baya zuwa ko ina ya zauna se in da Mother take, rana ɗaya ta ƙarfin tsiya an ɗauke mata shi.

Lilly na nan zaune Office É—in Nazir, se gashi ya dawo, kamar wanda zaki ya rarako, kallo É—aya za kai masa ka san yana cikin matsanancin tashin hankali da zunzurutun damuwa.

Ya shigo Office ɗin, ya rufe ƙofa ya kalleta yace "kinyi fitsarin?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya karɓi robar, ya saka tsinken gwajin sedai yana zaro tsinken ba tare da jan lokaci ba ya nuna ɓaro ɓaro, Akwai ciki.

Wani irin gumi ya shiga tsatsafowa daga goshinsa, ya ɗaga kai ya kalli in da take zaune ta ƙuro masa ido.

Tace "Yana ga ka canza meyafaru? Me ka gani ne?"

"You Are pregnant!" Ya bata amsa.

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
07063065680.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Saurin toshe bakinta tayi, dan bata son abunda ihun nata ka iya haifarwa a tsohon daren nan ba.

Bedsheet ɗin da take kai, duk ya ɓaci da jini, ga wani irin gigitaccen ciwo da marar ta keyi, se uban gumi take kamar me naƙuda.

A hankali ta ja jikinta zuwa banɗaki, dan gyara jikinta, sedai abu ya gagara  ƙarshe ma ta zube akan gwiwowinta, jini na cigaba da zuba daga jikinta.

Ita kanta ta firgita da jinin da ta zubar daga jikinta, yunƙurawar da tai zata miƙe, cikin ya faɗi gaba ɗaya.

Ta dinga sauke numfashi, idonta har wani lumshewa yake saboda Azabar wahala.

Ta daɗe a durƙushe a banɗakin, kan taji ya ɗan lafa mata, ta miƙe a durƙushe, ta gyara jikinta, ta cire bedsheet ɗin da ta ɓata, da kayan jikinta ta naɗe su ta ajiye su guri ɗaya, sannan ta koma ta kwanta.

Sedai tun ba'aje ko ina ba ta kuma ɓaci da jini, saboda yadda take cigaba da zubda jinin ba ƙaƙƙautsws, haka ta dinga sintiri tsakanin ɗakin da banɗakin tana gyara jikinta, ga ciwon mara da ke cigaba da nuƙirƙusarta.

Da ƙyar ta samu jinin ya tsagaita, sedai yana tsagaitawar kuma ta fara jin wani irin sanyi, ga jiri da ya fara kwasarta, da wani irin matsanancin ciwon kai, haka ta kwanta ta duƙunƙu ne, jikinta na cigaba da rawa.

Sadik ba ƙaramin jin daɗin Alkaki da kilishin da Nana ta jefo masa yai ba, da gari banza ne se yai mata rashin mutunci saboda ta jefe shi da abu, amma da yake nema yake ba ƙorafi ba wani abu haka ya ɗauka ya ci.

Mother ce zaune a gaban Abba, tana kuka wiwi kamar ƙaramar yarinya.

"Dan girman Allah ka koma ka É—akkomin É—ana, kana jin yadda yake min kuka a waya, wallahi yana cikin matsananciyar damuwa, dan Allah ka dawomin da É—a na"

"Wai dan Allah ya kike so nayi ne? Inyi fito na fito da Iyaye na, yau Sadik ko mutuwa yai a hannunsu na san ba zasu kashe shi da gangan ba, ko tunda kike haihuwa an taɓa ɗaukar ɗa ɗaya yaje garin ya zauna, meyasa kike hakane, kamar fa kina nuna sena nunawa iyayena basu isa bane ba fa"

"Ni ba haka nake nufi ba, amma dan Allah ka basu haƙuri koma me yayi su barshi ya dawo gida, dan Allah ba danni ba"

Abba ya kalli Mother yace "yanzu da yaron nan mutuwa yai fa? Ko kuma aka sace shi ya za kiyi?"
Chapter 25 · 0% Book details