← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 115

Sashe 19

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se da Sadik ya shige sannan yace "bana son dinga yi miki faɗa, ko makamancin haka a gaban 'ya'yan ki, saboda ba na son martabata ta zube a idanun su, ba na son farincikin da na kafa a gidana in sa ƙafa in rushe shi, shiyasa nake kawar miki da kai, amma naga kin ɗau abun wani fanni daban, Yakamata ko yaya nima ki dinga kamanta yi min kara akan ahalina, ko ba komai nima zan ji daɗi"

Share hawayenta tai ta riƙe hannunsa tace "insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, kuma zanje in duba sji insha Allah, amma dan Allah ka dena fushin nan dani ba zan iya jurewa ba"

Abba yai murmushi, ya É—an ja hancinta yace "ya wuce"

Tai murmushi tace "to muje part É—ina in rarrasheka"

Abba yace "Ai yanzu ma na rarrasu"

A ɗan shagwaɓe tace "ni ban yadda ba, dan Allah muje, kaci Abinci ka canza wannan wankan da kayi"

"Ke dai ba zaki Girma ba ko? Gashi kin ajiye sirika, wadda a kowane lokaci za'a iya cewa ta haihu amma kin ƙi girma"

"Yaushe zan bari in Girma ka hango min wata, ai gara in ƙi girman"

Murmushi sukai tare, suka nufi part É—in ta.

Rashin zuwan Sadik ba ƙaramin damun Farhan yai ba, ya sata a matuƙar damuwa, kullum direbansa zeje ya maida ita gida, amma yaƙi zuwa, kuma yaƙi ɗaga wayarta ko responding ɗin messages ɗin ta.
Shima a ɓangaren sa hakan da yai yana damunsa, amma a ganinsa hakan shine matakin da ya dace ya ɗauka, dan ya zama gargaɗi kar ta kuma aikata laifin da tai masa.

Mother ta fara noticing kusan kullum direba dai dai lokacin tashin Sadik daga Makaranta seya fita, ita dai ta san ba aikensa take ba, kuma Sadik ya kammala Makaranta, amma ta rasa ina yake zuwa.

Yanzu ma kusan awa guda tana jiransa ta aike shi, amma ba ya nan ta rasa in da ya tafi haka, dan haka tace idan ya dawo ace ta na son ganinsa.

Haka kuwa akayi, bayan ya dawo daga cika umarnin megida Sadik, ya nufi amsa kiran da matar gidan ke masa.

Ya ɗan jira a falo kafin ta fito, cikin takunta na isa ta ƙaraso falon ta zauna, ta kalle shi tace "Yawwa, dama na aika a kiramin kai ne dan inji in da kake tafiya, kusan kullum seka fita, ni ba aiken ka nake ba, kuma dai ga Sadik ya kammala Makaranta, ina kake zuwa haka? Yanzu tun ɗazu fa ina zaune ina zaman jiranka zan aike ka amma baka nan, ina kaje?"

Ɗan Jimm Direban yayi, yana ɗan nazari yana jin kamar ya gayawa Hajiya Hauwa abunda ɗanta ke aikatawa, amma wata zuciyar tace masa 'kul ɗinka, wannan matar da bata son laifin 'ya'yanta kana gaya mata zata iya cewa ƙarya kake, za kaiwa ɗanta sharri, koma shi yaron ya ƙaryata ka, dama dai mahaifinsa ne'

"Ina magana kai shiru ka ƙyaleni" muryar Hajiyan ta dawo da shi daga tunanin da yake.

Yace "Amm Hajiya, dama Sadik ne yake aike na"

"Yake aiken ka ina?" Tai maganar tana tsare shi da ido.

"Yake aike na, wani guri"

"Wani guri ina? Gurin ba shi da suna ne?"

"A'a Hajiya, amma dai sa da ze fi kyau ki tambaye shi da kan ki"

Ɗan shiru tai sannan tace "shikenan, in kayi sallar azahar kaje gidan Mummy, kace ta baka saƙon ka kawo min"

Yace "to Hajiya, bari in sallar in je"

Daga haka Ya miƙe ya fice daga Falon, yana godewa Allah da ba ta titsiye shi tace lallai se ya gaya mata ba.

Mother na nan zaune a falo, Sega Sadik ya shigo yana 'yan waƙe waƙensa, be kalli in da Mother take ba, ya nufi Kitchen.

"Sadik zo nan" Mother ta kira shi.

Juyowa yai ya dawo in da Mother take, ya nemi guri ya zauna yace "gani"

"Ina kake aiken Malam Ayuba direba, da kusan kullum se ya fita?"

Sadik ya kalli Mother yace "wani abun yace miki ne?"

"A'a be ce min komai ba, na tambaye shi yace in tambayeka, tun É—azu nake jiransa zan aike shi baya nan"

Sadik yace "eh yana É—an min wani aiki ne"

"Wane aikin kenan?"

"Mother, wata yarinya ce nasa yake kaiwa gida"

"Ita yarinyar gidansu babu motar da za'a É—auketa, ko se ubanka ne me arzikin banza na baitil mali?"

Sadik ya É—an tsuke fuska yace "dan Allah Mother ki dena, da suna da motar ai na zan sa a dinga kaita gidan ba, kuma kamar taimako ne, mu baga motocin nan birjik a gidan nan ba, gamu da ma'aikata, ba fa abun damuwa bane".

"Kaga Sadik ka kiyayeni akan batun matan nan, duk makarantar ku babu wanda zaka ce min gidansu babu motar da ba za'a iya zuwa a É—auke shi ba, bana son aikin rashin gaskiya fa"

Haushi ne ya kama Sadik, Mother ba dai faɗa ba akan abun da be taka kara ya karya ba, tai ta mita akan abunda ta riga tafi ƙarfinsa.

Miƙewa Sadik yai ya bar mata falon yana kumbure kumburen baki.

A harabar gidan Sadik ya samu Ayuba direba yace "ka gayawa Mother in da nake aiken ka ne?"

"A'a ban gayamata ba, cewa nai kawai ta tambaye ka"

Sadik yace "ok, shikenan"

Ayuba yace "Yawwa, Yarinyar dama tace min wai kar in ƙara zuwa ɗaukan ta, zata dinga tafiya da kanta"

Sadik yace "saboda me tace hakan?"

"Wallahi nima ban sani ba" ya bawa Sadik amsa.

Sadik yai shiru yace "shikenan, bakomai nagode Sosai"

Ya juya ya nufi BQ.

"Sadik ka dena sona ko? Ka dena zuwa in da nake, ka dena duba saƙona, na baka haƙuri kaƙi haƙura ko? shikenan Nagode sosai"

Message É—in Farhan kenan, da Sadik ya ci karo da shi a wayarsa.

Take se yaji tausayinta, yaga be dace ya wanata haka ba.

Kiran wayarta yai, baiwar Allah ba tai zuciya ba ta É—aga wayar, kasancewar tana makarantar Islamiyya.

Tana É—agawa ta sa masa kuka.

"Wayyo Allah, am sorry my dear, na san ban kyauta ba dan Allah ki min Afuwa, wallahi ni kaina kewar ki ta dameni sosai"

Cikin kuka tace "ba wani nan, ka dena sona wallahi ko Abincin kirki ba na iya ci saboda damuwa, Why are you playing with my emotion?"

"Yi haƙuri am really sorry, kina jina?"

"Ni ba abunda zan ji, ka dena sona na gane" ta katse kiran.

Ajiyar zuciya Sadik yai, dole yaje ya ga Farhan yau, dan yana missing É—in ta sosai da sosai.

A ƙoƙarin kaucewa fushin Abba, yasa da Mother taji Abba da Usman zasu koma ƙauye dubiya, tace zata bisu taje taga jikin Hakimi, ko ta huta da fushin Abba.

Ko da sukaje garin ƙin sakin jikinta tai, dan a fili ta dinga nuna ƙyamar garin, duk da irin tarin tsafta ta Inna.

Nana kuwa dama tunda suka gaisa, ta fita ta basu guri, dan jininsu baya haÉ—uwa da Mother kwata kwata, dan ba zata manta yadda Mother ta dinga mata ba a É—an zaman da su kai a gidan su ba.

Shi Usman kam dama kamar yadda yake É—abi'arsa, tunda aka gaisa yaiwa Hakimi ya jiki, ya koma gefe ya tsuke bakinsa, se idan Wani ne yai masa Magana se ya amsa.

Abba yace "Alhaji jikin nan naka kamar babu wani cigaba fa, ni dai dan Allah ka bari mu tafi da kai a duba ka yadda yakamata"

Hakimi yace "A'a, Asibitin nan namu baka ga yadda suke ƙoƙarin su ba, sunce hadda shekaru ma da suka ja, ka kalla fa cikin ikon Allah da ƙudurar sa naga Auren jikana namiji, ai Alhamdilillah ko yau muka tafi Allah yai mana ni'ima se fatan dacewa, ina Faruku ne wannan karon ba ka zomin da shi ba"

Abba yace "ai ka san yana ta fama da shirye shiryen tafiyar sa, yaje yin clearance ne, ina ga a satin nan, ze tafi ƙaro karatu Insha Allah"

Hakimi yace "to su haka zasu ƙare a yawon neman boko, baze Aure ba tukuna"

Mother da ba da ita suke hirar ba tai farat tace "Ranka ya daɗe, ai haryanzu yaro ne, kallon dai babba kuke masa amma yarone ƙarami, gara tunda ƙuriciyar su suyi karatun kan nauyi ya hau kansu"

"Eh hakane kam, to shi É—aya abokin nawa fa, da yace wata shekarar zan koma É—aurin Aurensa, kun masa Auren ne?"

Abba yai dariya yace "Allah ya temake ka, yayansa ma be yi ba se shi? Ai shirme ne kawai irin na Sadik, nan da 'yan watanni shima yana Turai ƙaro karatu"

Hakimi yace "ku dai naga kun bawa Boko mahimmanci sosai, ko da yake ai Ilimi abune me mahimmanci, amma Yakamata a dinga sara ana duban bakin gatari, ni karatun ma da ze yuwu suyi shi a gabanku kuna sa ido yafi ka kai yaro turai, baka san me yake ba"

Abba yace "eh hakane, amma jami'oin namu ne na nan, kullum cikin yajin aiki da sauran matsaloli, shiyasa gara a can ƙasashen ƙetaren, nan da nan su gama su huta"

"Hakane, amma ina fatan ze zo ya ganni kan ya tafi turan, dan babu lallai harya dawo ina raye"

Abba yace "insha Allah ze dawo kana raye, ka dena wannan maganar, Ranar Asabar insha Allah, zan zo maka da shi ya duba ka"

Hakimi yai murmushi yace Allah ya kaimu"

Mother kamar a kan ƙaya take, dan Alla Alla take suyi su tafi, aikuwa da yin Azahar suka juya zuwa gida.

Sadik yayi zarya a layin su Farhan dan ya samu ya ganta amma baya ganin wucewar ta, ya je Makaranta amma ya tarar wai kwana biyu ba taje ba, nan da nan hankalinsa ya tashi, ya kira wayarta amma ba ta shiga, ya tura mata messages amma babu reply.

Tun magariba, har kusan ƙarfe tara yana unguwar su Farhan, amma be samu ganinta ba, Jiki a sanyaye ya koma gida, ya tarar da Su Mother sun dawo daga ƙauye.

Sadik yace "wai ina kuka tafi haka, na shigo ba kowa a gidan nan, na kira wayarki ba ta shiga"

Mother tace "hmm ƙauye mukaje duba Kakanku"

"Wai haryanzu be warke bane?".
Chapter 19 · 0% Book details