Sashe 113
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tace "Saboda iyayena, da 'yan uwana na shiga damuwa idan na bugu, shiyasa na zaɓi inje Hotel, in da ba wanda ze ganni in yi shaye shaye na in bugu ba wanda ya ji balle ya gani, amma nai dama sanin yadda na gurɓuta rayuwata, saboda shaye shaye sam ba mafita bane, musamman ga ni mace, duk mazan nan da suke bina, suka kashen kuɗi ne, saboda suna sa ran zan amince da su wataran, amma Wallahi ban taɓa zina ba"
Sadik yace "Shhhh, ni zan bada wannan shedar, ni na fara karatun, kuma na dawo na tisa shi na wanke allon" ya ƙarasa maganar yana kashe mata ido.
Wani irin sanyi ya dinga ratsa zuciyarsu lokaci É—aya.
Can ta nisa tace "Prince, wai dan Allah meye a tsakaninka da Mubarak, da yake ta ƙoƙarin ganin se yai abunda ze ɓata maka, har ya sakoni a ciki?"
Sadik ya ɗanyi shiru sannan yace "Lokacin da aka kawo Mubarak Babba, yana Ss1 ina Jss3, ya zo da zafinsa makarantar, sedai ya tarar gani ƙarami sosai, amma shahararrene ni ana ji da ni, ina da ƙoƙari ina son gayu, kuma ina da sakin hannu sosai.
Se ya fara cewa ina burgeshi yana son yai abota da ni, kasancewar kowa nawane ya sa ban damu ba, muka fara abota da shi, abokina ne shi sosai, sena fuskanci yana shaye shaye, nai ta masa nasiha akan ya dena yana ɓata rayuwarsa ne kawai.
Kwatsam wataran ya zo min da wata mummunar magana, da ba zan taɓa mantawa ba, lokacin daga ni se shi a ajinsu, muna wata game a waya, ba kunya ba tsoron Allah ya gayamin wai sha'wata yake. Da farko ban kawo komai a raina ba, nake masa dariya se daga baya muraran ya nunan buƙatar sa, ashe riƙaƙƙen ɗan Neman maza ne, duk yana da ƙanan shekaru a lokacin, ya sanar min ba wanda ya san sirrinsa se ni, shima wani abokin babansa ne ya koya masa, kuma yake biyansa kuɗaɗe akan hakan, saboda ƙuruciya har sunan mutumin ya gayamin.
Hankalina ya tashi ƙwarai da gaske, saboda mutumin babban mutum ne, ganin ba zan yadda ba yasa Mubarak Babba ya so yai amfani da ƙarfin tsiya, kasancewar ya na da girman jiki sosai, a lokacin muna amfani da ƙararrawa ne ba jiniya ba, dan haka Allah ya temake ni, na ɗau ƙararrawa na buga masa a mararsa, na bar shi a gurin.
Ba wanda na gayawa, amma abun ya tsaye min, na dinga mamaki saboda ni ban taɓa sanin, namiji na ɗan uwansa namji ba, se a wannan ranar.
Mubarak se da yai wata biyu baya zuwa Makaranta, wai ba shi da lafiya, ranar da ya dawo, muka haÉ—u ya dinga min wani irin kallo da ban gane kansa ba, kawai naji zuciyata ta kasa nustuwa ina komawa gida na gayawa Abba komai.
Aikuwa daga Abba har Mother hankalinsu ya tashi sosai da sosai, Abba yace ba ze yuwu ba, ya shigar da ƙorafi gurin 'yan sanda.
Babba be san waye mahaifina ba, dan haka aka kamo shi, da shi da uban gidan nasa gaba da Mahaifinsa.
Seda suka kwan uku a gurin 'yan sanda Sannan Abba ya ɗauke ni muka je, aka sa na maimaita abunda ya faru, se da aka gayyato har shugaban Makarantar, Abba yace seya rufe makarantar, a kai ta bawa Abba haƙuri, da ƙyar ya haƙura a nan aka sanarwa da Abba cewa, ai dukan da nai masa a mara, baze taɓa haihuwa a rayuwarsa ba, dama duk ya gama lalata kansa, gurin aikata wannan mummunan aiki, yaro ƙarami da shi, amma yana wannan mummunan aiki, babban abunda ya ban mamaki be wuce yadda daga abokin mahaifin har mahaifin ba su damu da abunda Mubarak ɗin yai ba.
Abna yace se ya ɗaure Mubarak, a kaita bawa Abba haƙuri, shine a kai min iyaka da shi, kuma aka nemi in rufa masa asiri, aka kuma ce muddin aka kuma kamashi da irin wannan laifin se an hukunta shi, akai rufa rufa aka binne case ɗin. Kinji in da gabar mu ta samo asali, yai alwashin yadda nai masa illa, shima se yai wani abu da ze min illa, ban taɓa gayawa kowa ba se ke, kuma a binciken da nai da babansa talaka ne, sanadiyyar ba da Mubarak ɗin da yai ne, ake wannan harkar da shi yai wannan arzikin.
Jikin Farhan yai sanyi ƙalau, tace "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah yai mana tsari da mugayen mutane, thank God da Allah ya tsaremin mijina"
Sadik yace "godiya ta tabatta ga Ubangijin da ya tsaremin mata ta, ba tare da wani abu ya sameta ba"
Su kai murmushi a tare, se wajen azahar sannan suka sake wanka, suka sha kwalliya, suka shiga kitchen tare, Farhan ta kalleshi tace "Prince, dan Allah ka É—akko min Sahal mana"
Sadik yace "kai gaskiya bana son motsawa daga nan zuwa can in barki"
"Dan Allah ka É—akko min shi, baka san yadda nake son yaron nan ba ne"
Sadik yace "to kamar yaya kike son babansa?" Yai maganar yana saka fuskarsa a wuyanta.
"Ina son babansa sosai, kuma ina son É—ana ma sosai"
"Ni zakiwa wayo?"
Farhan tace "dan Allah kaje ka ɗakko min shi, Kafin ka dawo na gama girkin" da ƙyar ya iya ƙyale Farhan ya tafi ɗakko Sahal.
Sadik ya tarar Mother ta fita, Faruk ne yake rainon, Sadik yace "kai aka bari da rainon?"
Faruk yace "to rainon Sahal É—in har wani aikin wahala ne?"
Sadik yace "lallai kam, lallai kuna son Abban nan sosai, gaskiya kaima ka yunƙura mana, mu tarawa Mother yara da yawa"
Faruk yai murmushi yace "kan inyi Aure, na san amaryarka ma ta juye ita ma, ƙarami da kai se kasada".
Kwashewa da dariya Sadik yai yace "kaga ni fa Sahal na zo É—auka, Farhan ta dameni in zo in É—akko mata shi".
"To a dinga yi ana tausayawa marainiyar ƙanwarmu, naga akan wannan kake ta rawar kai".
Sadik yace "wai dan Allah waye ya gaya muku bana son Nana? Wallahi ina son ta sosai, kowacce akwai mazaunin da ana ajiye ta, kowacce tana da matsayi na musamman a zuciyata"
Faruk yace "hmmm Allah ya sa, ka san ni tunda Nana ta É—arsa min son Khairat naji kamar ina sonta, na fara jinta a raina sosai"
Sadik yai murmushi yace "kai amma na tayaka murna, Soyayya ai duniya ce, wanda baya Soyaya da me yake more rayuwa, inji wani mawaƙi"
Haka suka taɓa hira, sannan ya ɗau Sahal ya tafi gida.
A falo suka baje sukai salla suka ci Abinci, suna hira Farhan ta haÉ—awa Sahal madara ta na ba shi, Nana ce tai sallama a falon, Nana na shigowa Farhan tai saurin tashi daga jikin Sadik.
Nana ba ta nuna taga wani abu ba, ta zauna tana cire safarta, Sadik yace "Sannu da zuwa besty, ya school É—in?"
"Alhamdilillah" shine kawai ta faÉ—a, ta cigaba da abunda take.
Farhan tace "Sannu da zuwa"
"Yawwa Sannu da gida, É—akko Sahal ku kai kenan, Allah ya sa be takura miki ba"
Farhan tace "A'a ai uwa ba ta gajiya da É—anta".
Nana tai murmushi tace "lallai kam"
Sahal kuwa ƙoƙarin rarrafawa yake ya tafi gurin Nana.
Nana ta miƙe tsaye tace "kai daga daowowata zaka fara wani kuka a ina ka sanni".
Kuka Sahal yake, a lallai se yaje in da Nana take.
"Kai lallai ma yaron nan, ga madara nan an baka ka sha ka ƙoshi, amma se ka zo ka addabamin, aikuwa ba ka isa ba" tai maganar kamar ta na yi da sa'anta.
Sadik yai murmushi yace "Allah ya shiryeki Besty, ya nunan lokacin da zaki girma"
Sahal ya biyota da rarafe, ta É—au jakar makarantar ta da gudu, tai part É—inta.
Ba Sadik ba Farhan kanta abun dariya ya bata, ta tashi ta É—akko Sahal tana rarrashinsa.
Abunda yake bawa Farhan mamaki, Sahal ma Besty yake ƙoƙarin kiran Sadik da Nana, a gwarancimsa na yara.
Farhan tace "wannan sunan shi Daddy kaji ko" tai maganar tana nuna masa Sadik.
Sadik yace "ai yaron nan ba yadda ban ba yace Daddy ya ƙi se besty yake so shima ya dinga cemin".
Farhan tai dariya tace "to ai ku É—in ne kamar yayyansa ba iyayensa ba" Sadik yace "Lallai kin ci mu wasa".
Rayuwar gidan Sadik ta cigaba da tafiya, yana iya ƙoƙarin sa gurin ganin kowacce ya kula da ita daidai da buƙatar ta, Farhan ma ta koma Makaranta, dan ita har taje Ss3, Nana kuma na Ss1, shi kuma yana zuwa ABU zariya, duk ƙarshen wata yake zuwar musu, sedai sam haryanzu Mother ba ta maraba da Farhan.
Soyayyar da Farhan ke nunawa Sahal, da kuma zuwan da Inna tai, tai musu nasiha sosai yasa Nana fara sakkowa daga kishin da take, Inna ta nuna musu su haÉ—a kansu su zama kamar 'yan uwa, se rayuwa ta fi yi musu daÉ—i ganin hakan ya sa ita ma Farhan ta sassauta na ta kishin.
Sadik baya nan yana makaranta, Farhan ta na ta rashin lafiya, Nana ce ta lura da hakan tace "Nikam Mummyn Sahal lafiyarki kuwa, duk kin rame haka".
Farhan tace "Wallahi besty zazzaɓin dare nake, ga ciwon ciki na rasa abunda yake min daɗi".
Nana tace "Ai ba kya zauna da ciwo ba, bari in wa Sabo direba waya, ya zo muje in rakaki Asibiti" Farhan ba tai musu ba, sedai suna zuwa Asibiti, gwajin farko aka ce ciki ne da ita, har watanni biyu.
Ita Farhan ma kunya ce ta kamata, Nana kuwa tausayi Farhan É—in ta bata, Saboda ta san É—awainiyar ciki akwai wahal, tun da suka dawo gida kuma laulayi ya saka ta a gaba, koma a ci se amai, Nana ce keta É—awainiyar kula da Farhan, har mamaki abun ya dinga bawa Farhan, Nana ba dai tausayi ba.
Nana ca ta sanarwa Sadik halin da ake ciki, murna Kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha.
Ranar da ze dawo, Nana tace "Princess be kamata ya dawo ya ganki a haka ba, duk kinyi wani iri, ki wanke gashin ki, se in miki stretching.
Haka kuwa aka yi, ta gyarawa Farhan kai, ta sakata a gaba akan Lallai ta ci Abinci, ba ta son a haifo musu yaro ramamme.