Sashe 41
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai duk yadda Inna take dakewa se kuka, tace "kiyi haƙuri Nana, Allah ya baku zaman lafiya, ki bi mijinki ki samu aljannar ki, na so in samu isashen lokaci tare da ke, amma baze yuwu ba, kiyi haƙuri kiyi karatu da kyau Allah yai miki Albarka, ki kula da tarbiyyar da muka ɗoraki a kai"
Nana tana turjewa tana kuka, aka kaita Mota, se kuka take kamar wadda aka gayawa ranar mutuwarta.
Hakimi ya ƙarewa Nana kallo yace "zanyi kewarki jikata, ko a 'ya'yan da na haifa, babu wanda nakewa son da nake miki, sedai ba yadda na iya".
Ya kalli Sadik yace "ga ta nan, Amana a hannunka, Nana Yarinya ce me tarbiyya, da muka raina nasan wa na aura maka, nasan na maka laifi, amma nan gaba zaka gane gata nai maka, ka kula da Amana, idan kaci Amana Allah yana kallonka, Abdullahi kar a bari inji wani abu mara daÉ—i game da Amanata, kuje Allah ya sauke ku lafiya"
Nana tana kuka, haka aka ja motar nan suka tafi, yayinda zuciyar Sadik kamar wutar ƙira, saboda wata irin wuta dake ruruwa a cikin zuciyarsa, jin Hakimi kawai yake, amma wannan Amanar kam ba abar karɓa bace a gurinsa.
Ganin kukan na Nana a ta da niyyar denawa yasa Abba yace "haba Nana, kukan ya isa haka, kar kanki yai ciwo kinji, ki dena kukan nan haka ya isa"
Faruk yace "hakane, ki dena kukan nan kar kanki yai kafin muje can gida" ya ƙarasa maganar tare da miƙa mata hankici, dan ta goge hawayenta.
Wani uban tsaki Sadik ya ja, dan ko motsin Nana baya ƙaunar ji, duk da yau ce kusan zece ranar 'yanci a gareshi, bayan takure shi da akai tsawon lokaci, aka hanashi walwala kamar wanda ya karya dokar ƙasa, sedai sam baya farinciki da hakan, dan da ya tuna yadda aka katse masa hanzari aka aura masa baƙauyiya, se yaji wani marurun takaici ya tokare masa zuciya.
Nana ba ta sake tsinkewa da al'amarin ba, se da suka shigo gari Sosai, wata fargaba ta lulluɓeta, dan bata san wace irin karɓa Mother za tai mata ba, dan tun ainihi dama Mother ba ƙaunarta take ba, balle yanzu da aka aurawa ɗanta 'yar ƙauye da ta ke ƙyama, kuma ɗan da take ganin be isa Aure ba.
Wajen ƙarfe tara da rabi, Hajiya ta zo Asibitin, tai murna sosai da ganin cigaban da aka samu akan jikin Farhan, dan ta farfaɗo sosai, sedai tayi rama sosai da sosai, ga leɓenta da ya bushe.
Hajiya tace "Sannu Farhan, ya jikin naki?"
Farhan tace "Jiki da sauƙi Alhamdilillah, Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi yasa kifi haka"
"Ameen, bakomai Farhan Allah ya ƙara miki lafiya, Ummanki tace a gaishe ki"
Shiru Farhan tai ta sunkuyar da kai, yanzu idan ma mutuwa tai shikenan, sedai ta mutu ba tare da Umman ta zo ta ga halin da take ciki ba.
Zuwan Hajiya babu daÉ—ewa, sega Anty Uwani, wato babar Huzaifa ta zo.
Nan suka gaisa da Hajiya, ta kalli Farhan tace "Sannu Farhan, gaba ɗaya kin rame lokaci ɗaya, Allah yasa kaffara ne, ya ƙara afuwa".
Kasancewar Anty Uwani mace ce me faran faran, hakan ya sa suka saki jiki da juna ita da Hajiya suke ta hirar su.
Farhan tai farinciki sosai, jin Abbas ya gaya mata ba ta ɗauke da sanƙaran mama (Cancer), wanda ta daɗe a cikin matsananciyar damuwa, da kokwanton ciwon ne ya kamata.
Amma idan har dagaske doctor Abbas yake, da yace idan tai Aure zata dena jin Symptoms ɗin, sannan ta dena damuwa idan har dagaske yake Aure take so, meyasa ba ta farinciki da ɗokin Aurenta da Sunusi? Tabbas ba Aure take buƙata a yanzu ba soyayya da farinciki take buƙata, sedai gashi me samar mata da su ɗin yai nesa da ita, nisan da bata san a wani hali yake ba, balle soyayyarta.
Kenan ta rasa Sadik ne? Kokuwa haryanzu matsalar ƙauyene na rashin network ya hanashi nemanta?
Wata zuciyar tace "ko dai gidansu zanje in tambaya in ji?'
Da sauri ta kauda wannan tunanin, ita a wa, za taje gidan su ta tambayi in da yake?
To ko dai abokansa zata tambaya, su Amin?.
"Ke Farhan, tunanin me kike hakane?"
Firgigit Farhan ta dawo hayyacinta, ta kalli in da Anty Uwani take mata Magana.
Hajiya tace "tunanin me kike haka, ki kai shiru ba ma kya jin abunda ake faÉ—a?"
Farhan tace "bakomai"
"A'a da Komai, akwai abunda yake damunki da alama, wanda ya haddasa miki wannan ciwon naki"
Farhan tace "bakomai fa"
"A'a, to ma naji bakomai amma tunanin me kike haka?"
Tai shiru ba tace Komai ba, nan dai dau kai tai mata faÉ—a akan koma meke damunta, ta cire shi a ranta, ko dan lafiyarta.
Ita dai jinsu kawai take, amma ba ta ji zata iya hakan ba.
Nana na ganin sun shiga layinsu Sadik, ta sake fashewa da kuka, dan ta tabbata shikenan ita da Ƙauyen da ta tashi, nan ta fara saƙawa da warwara akan irin karɓar da zata samu a gidan su Sadik ɗin.
Tana cikin tunanin ne taji an tsaya, Faruk ne ya fito ya buÉ—e murfin motar, da yake tana baya ita da Abba.
Tuni Sadik ya fita daga motar yai cikin gida, ba tare da ya jira kowa ba.
Faruk ya É—akko Akwatin Farhan, suna gaba, tana binsu a baya tana share hawaye.
A falo Sadik ya tarar da Mother, ta ƙarasa da sauri ta rungume Sadik, hadda hawayen farinciki, tace "I miss You my son"
Magana Sadik yake son yi, amma ya kasa se murmushi me haɗe da ƙunar zuciya da yake yi.
Ta É—ago ta kalli Sadik tace "Kai sannu Sadik, duk kayi wani iri Allah sa ba rashin lafiya kai ba, naga idonka duk kai zur zuru"
Sadik kawai ya sunkuyar da kai, wata ƙwallar baƙin ciki ta taru a idon sa.
"Sadik meyafaru ne? Ka gayamin mana"
Tana ɗaga kai sega Abba ya shigo, shida Faruk, taga Faruk da ƙatuwar Akwati, ba ta kai ga yin Magana ba sega Nana ta shigo, tana duƙar da kai kamar munafuka.
Wani kallon banza Mother tai mata sannan ta kalli Abba tace "Sannu da zuwa"
Abba yace "Yawwa"
Sadik na ganin Nana, ya saki Mother ya juya ya nufi ɗakinsa da ke Falon Ya shiga ya rufe ƙofa.
Abba ya kalli Nana da ta ke tsaye a bayan kujera tana rarraba ido yace "ya haka, ke da gidanku ƙaraso ki zauna mana"
A ƙasa Nana ta zauna, tana share hawaye.
"Abba ban gane meke faruwa ba, naga Sadik duk yai wani iri"
Abba yace "An gutsuri wani abu a jikinsa ne?"
Tace "A'a"
"To me kike son ji, ba dai gashi nan an dawo da shi ba, ba su cinye shi ba ai"
Tace "Allah ya baka haƙuri"
Abba yace "Nana, É—au Akwatin kije É—akin da kuka sauka lokacin bikin dr., In ba a gyare yake ba, kiyi magana a gyara miki"
Nana ta ɗau Akwatinta tai gaba, ita ta manta ma ko Mother ba ta gaisar ba, saboda tsabar tsoro da fargabar karɓar da za tai mata.
Faruk kuwa tuni ya fice, dan baya son ganin dambarwar rikicin da za'ai s Gidan, dan ya san ba ƙaramar rigima za'ai ba a gidan.
Ɗakin Sadik Mother ta fara zuwa, ta tarar da shi a kwance akan gadonsa, ya ƙurawa roofing ɗakin ido.
Mother tace "Wai kai meke faruwa ne?"
Sadik ya girgiza kai yace "bakomai"
"Kamar ya bakomai, nagan ku duk wani iri, kuma me wannan yarinyar ta zo Gidan za tayi?"
"Mother, I don't have answer for all this your questions, allow me to rest please"
Mamaki ne ya cika Mother, musamman ganin hawaye na zubowa daga idon Sadik.
"Sadik, meyafaru haka kake kuka?"
Sadik baya son cigaba da Magana, dan haka ya miƙe ya shige toilet ya rufe ƙofa.
Se kuma tai tunanin ko dan harya gama zamansa a garin ba taje ta ganshi bane, shine yake fushi?.
Ƙofar toilet ɗin taje ta tsaya tace "kayi haƙuri Auta, nasan ba a kyauta maka ba, amma ba yadda ban ba Abbanka ya ɗakkomin kai amma yaƙi, nace zanje in ganka nan ma ya hanani, dama nasan ba jin daɗin zaman garin nan kai ba, amma kayi haƙuri kai wanka ka fito, zan kawo maka Abinci in baka da kaina"
Har Mother ta gama surutunta, Sadik be tanka ba sema kunna shower da yai, dan ya dena jiyo sautin Maganar Mother, ya lumshe idonsa hawaye na zirarowa daga idonsa.
Da tsananin Mamaki Mother ta nufi part ɗin Abba, ta tarar ya cire Babbar rigarsa yana waya, ta kalli bedside taga ya ajiye uban goro da alawa, ɗan taɓa baki tayi, ta shiga kawo masa Abinci.
Be ce mata uffan ba ya fara cin abincin sa, ta kalleshi tace "Dan Allah Yallaɓai meke faruwa ne?"
"Wai me kika gani ne?"
"Ganinku nai gaba É—aya wani iri, kamar wani abu na faruwa"
"Ba abunda yake faruwa se Alkhairi" ya bata amsa.
Can ya É—ago yaga yadda ta zuba masa ido yace "yawwa ina fatan an bawa Nana Abinci?"
Ta É—an yatsuna fuska tace "namanta ne, bari in magana a bata"
Ta miƙe ta fita, tana zuwa falo Khairat ta dawo daga Makaranta, tace "Mother na dawo"
"Sannu da zuwa, Sadik dai ya dawo"
Cikin murna Khairat tace "Allah sarki bestyna, yana ina?"
"No, karki je in da yake yanzu ban san me akai masa ba, naga baya walwala"
"Amma dai lafiyarsa ƙalau ko?"
"To gashi nan dai ban gane masa ba"
Khairat tace "ina ga fushi yake, bari in bari zuwa anjima na je gurinsa"
Mother ta manta da abunda ya fito da ita, ta É—akko kwanukan Abinci ta shiga É—akin Sadik, amma ta tarar da shi a kwance, ya lumshe ido ksmsr me bacci.
Mamaki ya kuma kamata, yana jik motsinta, amma ya rufe ido kamar yana bacci, ta ajiye masa Abincin ta fita daga É—akin.
ta koma gurin Abba, ta tarar ya gama cin Abinci, ya kwanta.
So take ta kuma masa magana, amma yaƙi bata fuska sam.