← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 115

Sashe 64

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "to bari in tuɓeki, in ga abunda kika taka da zaki kalli kamarni kice min yaro"

"Nace dan Allah kayi haƙuri fa"

"Naji zan haƙura amma bisa wasu sharuɗɗai"

Tace "to"

"Na farko, daga yau karki ƙara zuwa kaina kina magana ba girmamawa, ba ma kya faɗar suna na, sedai kawai ki fara Magana da ni kai tsaye, to da ga yau am your boss, na gaya miki ke 'yar aikina ce, Boss Sadik zaki dinga kirana.
Abu na gaba, zaki dinga gyaran É—aki da wanken toilet kullum sau biyu a rana.
Kuma zan downloading different receipe, da za'a iya sarrafawa a nan ƙasar, zaki dinga mana girki dan na gaji da yawon siyan Abinci, kuma ki kai jagwalgwalo se na miki abunda ba ki zata ba.
Always talk to me with respect and manners, am not your mate, idan ba haka ba se na tuɓeki na turaki ƙofar gida ki kwana a haka"

Cikin kuka tace "to zan dinga yi, amma dan Allah ka ƙyaleni in saka hijjabi na"

"Ba zaki saka É—in ba, abu na gaba kince ai ba kya sona ko?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Yace "good, dama nima ba son ki nake ba, dan ban yi kalar Auren 'yar ƙauye ba, Naji kina gaywa kakarki zaki samo mata siriki Bature Allah ya temaka, Amma ki faɗa da bakinki"

Ta É—an tura baki tace "Ni ko ma dai saki nawa ne, amma kawai ka sakeni"

"Shikenan, zan sake ki, amma nan da lokacin da zamu kammala karatu, yanzu dai ki kiyaye dokokin da na shimfiÉ—a miki, idan kuwa ba haka ba sena aikata abinda nai niyya"

Da sauri ta jinjina kai tace "to"

"Tashi ki ban guri"

Da sauri ta tashi ta na cigaba da rufe jikinta, ta fice da sauri Daga É—akin.

Bayanta Sadik ya bi da kallo, yai murmushi da be san ya kufce masa ba ya tafi kan mudubi dan shafa maia.

Nana kuwa haki ta dinga yi da taje ɗaki, tace "yau na ga masifa, da ma tun ba yau ba na fuskanci ɗan iska ne Sadik ɗin nan, ya saba taɓa mata amma ban ta ɓa zaton ze yunƙurin yi min tsirara ba, Allah ka kiyayeni da Sharrin sa".

Da safe Nana har fargabar fitowa take, saboda ko haɗuwa da Sadik ba ta ƙaunar yi.

Amma ta tuna da kashedinsa, da sassafe ta tafi É—akinsa ta shiga da sallama, dan gyara masa Sannan ta shirya ta tafi makaranta.

Sedai Ko tashi be ba daga baccin safe, haka ta shiga a gaggauce ta gyara masa toilet, ta tattare iya tsakar É—akin, ta wuce É—akinta dan ta shirya zuwa Makaranta.

A falo ta tarar da Sadik, ya fito jikinsa sanye da dogon wando da vest, ya kalleta ya yatsuna fuska, yayin da ita kuma se sunkuyar da kai take ko haÉ—a ido ba sa son yi.

"Kwomin coffee" ya faÉ—a cikin isa.

"Zan makara fa" ta faÉ—a a raunane.

"I don't care" ya faÉ—a yana É—aukar remote.

Haka ta koma Kitchen cikin sauri, ta na kumbura baki ta dafa, ta zo ta aje masa tai waje ranta a ɓace.

Umman Farhan ta É—aga labulen É—akin Farhan tace "ki je babanki na kiranki a É—akinsa"

Ta É—an lumshe ido Sannan ta tashi, ta nufi É—akin Abban.

Abba ya kalleta yace "Ya akai kika dena zuwa Makaranta ne?"

Tace "bakomai"

"A'a da komai, Gayamin meyasa?"

"Gani nai lokaci yana ƙaratowa, ba amfani cigaba da zuwana Makaranta"

Abba ya girgiza kai yace "A'a, Aure da zaki ba ya na nufin shikenan karatunki ba, karatunki na da matuƙar mahimmanci, dan mun riga munyi magana da mijin naki, ze barki ki cigaba dan haka se Allah ya kaimu satin bikin zaki dena zuwa, gobe in Allah ya kaimu ki shirya ki tafi makaranta"

Abba da ya san halin da zuwa Makaranta ke sawa ta shiga, da be ce ta koma ba, amma ba yadda ta iya, haka ta amsa masa cewar za ta koma É—in.

Daga nan Abba yace "Yawwa Allah yai miki Albarka, aita haƙuri da rayuwa, shi Aure ɗan haƙuri ne, ba ni da shakka akan kibda tarbiyyar da muka baki, na san ke Yarinya ce ne ladabi, amma a ƙara ai ta haƙuri, ki bi mijinki sau da ƙafa, ki yi biyayyar Aure, ki nemi aljannar ki, insha Allah ba zaki dana sanin wannan Auren ba, ina sa ran ze kula dake, kar ki kalli duk wani ƙyale ƙyale na rayuwa kwanciyar hankali a zaman Aure, ita ake nema"

"To Abba insha Allah"

"Yawwa ta shi kije, Allah yai miki Albarka"

Ta amsa da Ameen Abba.

Magungunan da Hajiya take bata ne, suka ƙara jefata cikin mawuyacin hali, da ma can ya lafiyar kura, balle yanzu da Hajiya ke aiko mata da kayan shirya amare.

Wani irin feelings ne ke sake takura mata, sedai tai ta juyi akan katifa kamar macijiya.

Ta kan tuno yadda akan Sadik ne ta san wani abu makamancin haka, a hankali take sauke ajiyar zuciya ta na lumshe ido.

A hankali ta fara tunani, ta taɓa jin yadda Taslim da Meena suke hirar, Mubarak Babba ya na ba su abunda yake sa mutum ya mata damuwarsa.

Take ta ji tana son sanin meyake ba su, idan da dama ita ma ya bata ko Allah ze sa ta manta da Sadik, taji sauƙin raɗaɗin da ke cikin zuciyarta.

Se kuma ta tuna ai Ance an kama Mubarak É—in, dan haka ba ta san in da zata ganshi ba.

Dafe goshinta tayi, tana sake rintse idonta, saboda yadda kan nata ke wata irin sarawa kamar ana dukanta da guduma a kanta.

Nazir ne rungume da Lilly a Office É—in sa, yana kwantar da kansa a jikinta yana lumshe ido.

"Please ka ƙyaleni, in tafi bana son wani ya zo ya ganni a Office ɗin nan, zargi ya fara shiga"

Muryarsa ƙasa ƙasa yace "wane irin zargi kuma, ba wanda ze ganmu ai duk ana Class, bari in saka key please karki tafi"

Tace "gaskiya am not in mood, ka ƙyaleni"

Yai ajiyar zuciya yace "to, naji amma yaushe zaki zo gidan, nai missing girkinki"

Lilly tace "Daddy fa ya na gari, ba yadda za ai in zo, ni ka ƙyaleni in huta mana haba"

Murmushi yai yace "duk wannan hutun da ki kai, yaushe rabonmu da juna? Ke ko missing É—i na ba kya yi?"

"Hmmm, ai ni kwana biyun nan hutu na ne"

"Ko dai kin samu wani ne? Shine kike ƙoƙarin juyan baya?"

Dariya tai tace "kai ka sani a layi, kuma ba wanda nake mu'amala da shi se kai, Karma ka sake kawo wannan tunanin a ranka, and lokacin sake ɗaukar allura ta yayi, shiyasa ka ga naƙi sakin jiki, ba na son a samu matsala"

"No karki damu, babu wata matsala da za a samu Insha Allah, allurar za ta iya É—aukar dogon zango a jiknki, but allow me to enjoy please"

Haka suka saka key a Office ɗin, suka sheƙe ayarsu, tsakanin Malami da ɗalibarsa (waiyazubillah, Allah ya shirya mana zuriya).

Khairat ta tattare kayanta ta bar gidan Mother, tana cikin damuwa sosai, saboda tun daga lokacin da Faruk ya ƙi amincewa da soyayyar ta, ta ji zaman Gidan ya isheta, ta tattara ta koma na su gidan, ta na cigaba da jin yadda ta ke matuƙar jin kewarsa.

Kwana biyu Nana ta É—an nutsu, ta rage yiwa Sadik tsiwa da rashin kunya, dan da gaske ta yadda ze mata tsirara, ita kuwa da yai mata tsirara ga ra ta bi shi a sannu.

Sadik kuwa ya samu dama, ya ke juyata yadda yake so, saboda ya gano lagonta, dan har gugar kaya yake sata, yai ta sata aiki kamar baiwa.

Yau da daddare Sadik ya samu Nana a falo, tana duba litattafanta.

"Jeki shirya zamu fita" ya faɗa a taƙsice.

"Ina zamu?"

"Ban sani ba" ya bata amsa.

Seda ta ɗan tura baki, sannan ta miƙe.

"Idan kika sako wannan uban hijjabin, sukace kin ɓoye bom ba abunda yai min zafi kamaki za suyi su kaiki prison"

"Kai wannan masifa da me tai kama?"
Tai maganar tana jan ƙaramin tsaki.

Doguwar rigar abaya ta saka, da mayafinta sannan ta fito.

Seda ta É—an jira Sannan Sadik ya fito, haka ta biyo bayansa tana mamakin in da za su a daren nan.

Taxi suka hau, suka tafi ba tare da ta san in da za su ba.

Wani katafaren mall suka je, Tun da Nana ta zo London ba ta taɓa yawo aka garin ba, nan ta saki baki ta na kallon ƙayatuwar garin.

Cikin mall ɗin suka shiga, Nan Nana ta zama cikakkiyar 'yar ƙauye saboda kallo.

Ya kalleta yace "ki shiga ki ɗau abunda kike buƙata"

"To ina zan je?"

"Bakiga in da mutane suke bi ba?"

"Dan Allah ka zo muje, ni wallahi ba zan iya zuwa nikaÉ—ai ba".

"Tun da cinye ki za suyi ko?"

"A'a dan Allah ba danni ba" tai maganar tana langaɓe kai.

Guntun tsaki ya ja, yai gaba ta bi bayansa.

Nan ta dinga É—ibar abunda ta ke so, abunda Sadik ya siya babu yawa, yace ta zo su tafi.

Ta kalleshi tace "to kayan fa?"

Be kulata ba ya kuma yin gaba, tana binsa kamar jela.

Farfajiyar mall É—in suka koma, ya sa aka kawo musu coffee, be ce ta sha ba, be ce kar ta sha ba, shi dai ya É—au na sa yana sha.

Wayarsa ya É—akko ya daddana, ya saka a kunnensa.

Nana ta É—au coffee É—in ta tana sha, tana lumshe ido da alama yanayin yana mata daÉ—i.

"Hello Mother"

Se da cikin Nana ya kaÉ—a jin ya kira sunan Mother.

"Sadik, kai kuwa meyasamu wayarka? Duk na bi na É—aga hankalina, har na fara shirye-shiryen sawa a duba min kai, fiye da wata guda wayarka ba ta shiga"

Sadik ya É—an gyara zama yace "Abba ne da ya zo, yai seizing É—in wayata, ban san dalili ba, se da na sai wata na canza sim, so ban samu liscesne É—in amfani da layin bane, se jiya shiyasa kika jini shiru"

"Kai, amma hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, wallahi na shiga damuwa sosai, amma ni sam be nuna min cewar ya zo in da kake ba, cemin yai gurin 'yarsa zeje"
Chapter 64 · 0% Book details