← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 115

Sashe 92

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin ƙunar rai Sadik ya girgiza Kai yace "bakomai, nagode sosai da gudunmuwar da ka bani, saura Nasir har gidan ubansa zanje in nuna masa waye ni, a rayuwata ban taɓa jin zanyi amfani da dukiyar da muke da ita in wulaƙanta wani ba, amma a wannan na sauya tunani, se na tabbatar da Mubarak da tawagarsa sun wulaƙanta, kuma abunda yai ba ze hanani Auren Farhan ba, sonta nake da gaske ba dan wani dalili ba" ya ƙarasa maganar cikin rauni.

Amin yaita rarrashinsa yana ba shi baki, daga baya ya karɓi tuƙin, dan Sadik ba lallai ya iya tuƙin.

Nana kam ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido game da al'amarin Sadik, gaba É—aya ta kasa gane kansa ta koma yi masa Addu'a kawai, Allah ya yaye masa abunda ke damunsa.

Wasu lokutan kamar zeyi kuka haka ze ta bata haƙuri, yace ya san tana haƙuri ba ta jin daɗin yanayinsa a kwanakin nan, amma tayi haƙuri ta cigaba da yi masa Addu'a, komai ze wuce.

Farhan ta kasa gayawa Abbas Sadik ya dawo cikin rayuwarta, tana matuƙar jin nauyinsa da kunyarsa, kuma idan har tana son ta nesanta kanta da  Sadik to ya zama dole ta amince da Abbas a matsayin miji, ko ba komai ta gujewa rigimar Sadik.

Suna motar Abbas suna hira, yana duba mata hannunta, ciwon ya ɗakko warkewa yana mata sannu, ta ɗan ƙur masa ido sannan tace "doctor"

Ya amsa da "Na'am ranki ya daÉ—e"

"Kana son ka Aureni a yadda nake?*

Cikin hanzari yace "sosai makuwa"

"To ka turo iyayenka gurin Abba, ina son muyi Aure a ƙasa da wata ɗaya, duk a in da ka ajiye ni zan zauna"

Abbas yace "Amma meyasa kika yanke wannan hukuncin haka? Makarantar ki fa?"

"Doctor ina da dalili, makaranta kuma na cigaba a gida ka sedai in ka dena sona"

"Ya ma za'ai in dena sonki, insha Allah zan yadda kika ce, zan turo magabatana insha Allah zanyi Magana da su"

"Angon Farhan" tai maganar da sigar tsokana.

"Na'am Amarayar Abbas" su kai murmushi, suka cigaba da taɗinsu yayin da ƙasan zuciyar ta cike yake da tausayin Sadik.

Abbas kam ya shiga taradaddin yadda ze sanar da Auren da yake son yi ga dangin mahaifinsa, dan ya san dole za suyi bincike akan Farhan, yana tunanin yadda wannan abu ze kasance.
Yaiwa Hajia magana, amma tace ba ruwanta ya tuntuɓi dangin mahaifinsa in sun nema masa shikenan.

Sadik ya kasa gajiyawa da zaryar gidansu Farhan zuwa makarantar su, amma ko sau É—aya ta kasa ba shi damar yi mata Magana ko kare kansa.

Yau ma yana nan zaune a ƙofar gidan su Farhan, Abbas ya kawo Farhan a motarsa, kasancewar magariba ce ba ta ga Sadik ba, Abbas yai reverse ya koma ƙofar gidan Hajiyarsa, tana shirin shiga cikin gida, taji an janyo ta da ƙarfin gaske.

Turaren Sadik kawai ta shaƙa ta gane shine, wani irin huci yake kamar wani kumurci.

"Dalla meye haka?" Tai maganar a hasale.

"Farhan wai me kike son ki maida ni ne? Mahaukaci? Kullum cikin zaryar gidanku nake ki bani lokacinki kin ƙi, kullum sedai wannan ya ɗauke ki a mota wannan ya sauke?"

"Au ai idan hauka ne, kai baka daɗe a cikin sa ba, kwanan nan ka fara ni shekaru biyu na shafe a cikinsa, kuma ba zan taɓa saurararka ba Sadik, dan Allah ka rabu da ni"

"Ba zan rabu da ke ba, Wallahi kika kuma shiga motar wani duk abunda nai miki ke kika siya"

Tace "ikon Allah, saboda ubana ne kai?"

"Saboda ke mallakina ce, Wallahi na kuma ganinki da wani se na illata shi, kar wannan wawan ya kuma zuwa yace ze É—auke ki a motarsa na gaya miki"

Fizge hannunta ta tai tace "ba ma ka da kunya Wallahi, kaifa Aure kaje kayi, se ka zo ka takurawa rayuwata, ka fita sabgata dan saura wata É—aya a É—auran Aure"

"A É—aura miki Aure da Sadik ba"

"Allah ya kiyaye, ko hauka nake aka É—auramin kai se na kwance na yar, mayaudari kawai" yana kallonta haka ta wuce cikin gida.

Sadik be taɓa zaton Farhan tana da irin wannan zuciyar ta kafiya da taurin kai ba, saboda shi sanyin ta kawai ya sani.

Haka nan ya wuce ya tafi gida, da yaje ya tarar tuni Nana tayi baccinta, yai wanka ya nemi guri ya kwanta ya rungume su ita da Sahal a jikinsa, wani irin tausayin su yana ratsa shi, da da ne se ta jira ya dawo ta bashi Abinci sannan su kwanta, amma yanzu har ta gaji da abunda yake yi.

Abbas yaje ya samu wan mahaifinsa da suke cewa Alhaji, ya sanar da shi yana son ƙara Aure, se da yai mita sosai da sosai, akan ƙare ƙaren Auren nan in ba dace a kai ba baya haifara da ɗa me ido.
Abbas yaita lallaɓa shi, da ƙyar ya amince sannan ya tambaye shi 'yar waye kuma a ina take?.
Abbas ya gaya masa, Alhaji yace "na gane mahaifin yarinyar, na san shi farin sani mutumin kirki ne, wata mu'amala ta taɓa haɗani da shi, zamuje insha Allah daga nan ai binciken da duk Yakamata"
Abbas yace "Alhaji ai ba se anyi wani bincike ba tun da kasan mahaifin ta, kuna kace mutumin kirki ne, itama ta na da kirki"

Alhaji yace "in baka da hankali mu muna da shi, ɗan yau ka haife shi ne baka haifi halinsa ba, dan haka zamuyi bincike tashi kaje" jikin Abbas yai sanyi ƙalau, haka ya baro gidan Alhaji, dan yasan muddin binciken su ya gano halin da Farhan ke ciki, bayan hana shi Aurenta se sun ci masa mutunci tsaf.

Abun mamaki Farhan ta ɗan saki ranta a kwanakin nan, bata yawan ƙunci da damuwa kamar baya da Sadik ya ɓacewa duniyar ta.

Sedai duk da haka yanzu ta ƙauracewa zaman gida, dan sosai take son t nesanta kanta da Sadik, in dai zata cigaba da ganinsa, to tabbas zata iya kasa Auren Abbas, kuma hakan tamkar ta saka alkhairi ne da sharri.

A samarinta ta saka Alhajin nan ya kuma kama mata ɗaki, a wani hotel ɗin, ta koma can abunta, Abbas ya kaɗa ya raya akan ta koma gida, fafur taƙi kuna taƙi gaya masa dalili, abun ya dame shi matuƙa, in dai zeje ze tarar da ita ita kaɗai, be taɓa kamata da wani a hotel ba, amma dai zaman hotel be dace da ɗiyar kirki ba, amma Farhan tai burus da shi, tai zamanta.

Amir ƙanin Farhan har mamakin wannan uban naci na Sadik yake yi, yana ganin kwata kwata ba shi da zuciya, musamman duba da yadda Farhan ɗin ke masa wulaƙanci.

Kamar yadda Alhaji ya alƙawartawa Abbas, sunje neman Auren Farhan, kuma har sun saka ranar da zasu kawo kuɗin Auren, sun nemawa Abbas izini, kuma an bashi.
Watanni uku Alhaji ya saka, dan a cewarsa baze biyewa Abbas ba, dan be ga abun gaggawa a lamarin ba.

Abba ya dinga murna tare da Addu'ar Allah ya tabbatar da wannan lamarin, kar ya watse kamar yadda aka dinga zuwa neman Aurenta abun na watsewa, saboda yanayin rayuwar da take yi.

Sam Farhan ta kasa murna da batun kawo kuɗin Auren, ba ta zumuɗi sam, ta rasa dalili, ƙasan zuciyar ta na ƙoƙarin gaya mata har yanzu tana son Sadik, amma ta dage ta cire wannan tunanin a ranta.

Yanzu ma ta fito daga wanka, ta na sanye da doguwar riga a jikinta, tana zaune tana duba litattafnata, dan haryanzu akwai son karatu a tare da ita, makaranta ce kawai ta fita daga ranta gaba É—aya.

Turo ƙofar ɗakin a kai, ta zuba ido, dan ganin waye haka ya zo mata ba izini ba komai.

Seda ta buÉ—e baki dan mamaki, ya akai Sadik ya gano in da take.

Ya É—an tsura mata ido sannan yace "kina mamakin yadda a kai nasan in da kike ko?"

HaÉ—e rai tai tace "kaga kar ka zo ka samun ciwon kai, ka tafi ka bani guri"

Bece mata komai ba, ya nufi kan dressing mirror ɗin da ke ɗakin, ya kwaso magungunan da ke kai ya zuba a aljihunsa, ai da sauri ta miƙe ta nufo shi, cikin haɗe rai tace "ka ajiyemin kayana malam"

"Na ƙarfi ne ki ƙwata" yai maganar shima ransa a haɗe.

Shiru tai tana huci tana kallonsa.

Cikin tausasa lafazi Sadik yace "Farhan meyasa baki da tausayi ne? Ko iya sintirin da nake miki, ya isa ki sassauta min ki kwantar da hankalinki ki saurareni, nasan na miki laifi amma ki sani da bana sonki, ds Wallahi ba zan dawo gareki ba, haryanzu ina sonki Farhan, dan Allah ki saurareni"

"Kana sona da kenan, amma banda yanzu"

Ya ƙarasa gabanta, ya kamo hannayenta yana kallonta yace "Farhan dan Allah ki sassauta min idan ba so kike in rasa raina ba"
Chapter 92 · 0% Book details