← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 115

Sashe 22

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna taja wasu seconds tana kallonsa sannan tace "hala kashi ne a gurin da baza ka zauna ba, ka ƙame a tsaye?"

Hakimi yace "kin san saraki, ƙil shimfiɗar gurin ce ba ta masa ba, a samo masa Matashi"

Inna tace "Sarakin wa? Wannan sarautar ba dashi ta dace ba, aka bashi ita, ba wani matashi da za'a bashi, im baze zauna ba yaita tsaiwa, soja"

Sadik dai bece komai ba ya nemi guri ya zauna akan tattausar daddumar da ke gurin.

Nana ta fita tsakar gida, ta samu Jug ta zubo ruwan randa, ta haÉ—o da kofuna, bisa ga koyarwar Inna, ta kawo Musu.

Ta shiga zuzzuba musu ruwan tana miƙa musu, sedai taƙi zubawa ta bawa Sadik.

Hakimi yace "shi wannan laifin me yayi miki da baki zuba kin bashi ba?"

Sadik yace "No, am not thirsty bana sha"

Ɗan ƙaramin tsaki Nana tai, tana hararsa.

A ransa yace 'wannan shegiyar yarinyar ta fara rainin hankalin nata, in mata wani abun wannan tsohuwar ta ji haushi ta fara min masifa"

Inna Kuwa tana kallonsa, yadda yaƙi shan ruwan nan, da yadda yake ta ƙarewa ɗakin nan kallo, kamar ya ganshi a wata duniyar daban.

A hankali Sadik ya silale ya fita, ya tafi mota ya É—au ruwansa na roba ya zauna yana sha.

Mother ta kirashi a waya, sedai duk yadda ya so ya É—aga wayar nan abu ya gagara saboda rashin Network, yai yai ya É—an zazzaga ko ze samu Network amma abu ya gagara.

Ransa ya ɓaci be san lokacin da yace "wannan banzan ƙauyen, Network ma babu dan masifa"

"Wallahi ƙauyen mu ba banza bane, sedai me maganar ne banza"

Sadik ya waiwaya yaga Nana a tsaye hannunta riƙe da wani ƙaramin kwano, da alama aikenta a kai.

"Ke kuma nasa dake ne? Zaki fara bibiyata kina min rashin kunya, bar ganin gidanku nazo, wallahi se in tattakaki"

"Wallahi baka da wannan ƙafar, babu ƙafar da zata iya tattakani in gaya maka, kuma wallahi a garinmu kake gidanmu, zan iya sa dogarai su zane min kai, dan nan ba gidanku bane balle ka ɗagamin murya"

"Ni zaki sa dogaran su zane?" Yai maganar yana nuna kansa.

"Eh kai ɗin zan sa su zamemin kai, gara ka shiga hankalinka" ta ƙarasa maganar tana hararsa tai waje.

Binta yai da kallo, wata ƙwaila da ita se rashin mutunci fal cikinta.

Gajiya yai da neman Network, ya koma cikin gidan yana tsaki da ƙanan surutai, shi ya gaji ma so yake su tashi su tafi, amma yaga basu da wannan niyyar.

Lilly ce kwance akan makeken gadonta, se juyi take daga ita se underwear, ta rasa meke mata daɗi gaba ɗaya, wata irin kasala ke damunta, gashi wata irin wuta take ji a jikinta, babban burinta be wuce sake kasancewa da malamin ta b wato Nazir, ta rasa in da zata saka kanta, gashi sunyi nadamar abunda suka aikata, har yana iƙrarin ze Aureta, amma ita kaɗai ta san me take ji.

Wayarta ce ta fara ringing, banza tai da wayar ta cigaba da juyi, daga wannan angle ta koma wancan, ta nayi tana É—an jan tsaki lokaci lokaci.

Wayarta ce ta sake É—aukar ruri, a fusace ta kai hannu ta É—akko wayar, ta duba se taga Nazir ne ke kiranta.

ÆŠagawa tai ta sa a kunnenta "hello my nazee"

Ajiyar zuciya yai yace "Baby meyasa ba kya É—aga wayata ne?"

"Ba gashi na É—aga ba"

'amma sau nawa na kira baki É—aga ba?"

"Nifa ban san kai bane shiyasa"

"Shikenan, naji muryar ki wani iri, Lafiya dai ko?"

"Lafiya ƙalau, Am just missing You Babyyyyy"

Yace "Ummm, jiya fa muna tare, har kin fara missing É—ina?"

"Yes, let's do a video call, I want see you"

Yace "ok, as you wish my love"

Ya katse kiran, ya kirata video Call.

Sedai seda yai turus ganinta a screen É—in wayarsa, cikin wannan shiga.

Ko a jikinta ta fara yi masa magana "fita za kai hakane, naga kayi wannan kwalliyar haka?"

Da ƙyar yace "wani ɗaurin Aure aka gayyace ni"

"Ok, seka dawo, banda kallon mata Please, duk wadda ta ƙyasa kace mata kana da mata kaji Baby"

"Wai ya naga kina wani ƙara fresh, kim ƙara ja kinga kumatunki kuwa?"

"Haka kowa yake cewa nima kuma na gani"

Nazir yace "kinga se an jima, karki hanani fita, gaba É—aya kin sauyan yanayi bye bye"

Murmushi tai ta kashe wayar, tace "ai gara yanayin naka ya canza, kaji abinda nake ji nima"

Ajiyar zuciya Sir Nazir ya sauke, yana jin sa a wani yanayi na daban, na son sake kasancewa da É—alibar tasa.

A gidan Hakimi kuwa, Da Azahar aka yi funkaso da miyar taushe, ta sha naman kaji da man shanu, kallo É—aya Sadik yaiwa Abincin ya É—auke kai.

Abba da Faruk suka zauna cin Abinci, amma banda Sadik da yake ta cin magani.

Abba yace "Kai Sadik ka wanko hannu kazo kaci Abinci mana"

Sadik ya girgiza kai.

Abba yace "me kake nufi?"

"Abba na ƙoshi"

"Saboda me ka ƙoshi" Abba yai maganar yana kallonsa.

"Abba ni ban zan iya ci ba, bana son wannan abun"

"Aikuwa zaka zauna da yunwa, dan ban san me za'a nemo maka kaci ba"

Inna tace "Yanzu meye aibun wannan funkason da ba zaka ci ba?"

Sadik ya É—an tura baki yace "ni ba naci"

Inna tace "madalla, ka hutawa kanka, kuma babu me nemo wani abun ya baka, kar Allah yasa kaci É—in"

Tashi yai ya fita daga ɗakin, yana ƙunƙuni ya tafi mota ya ɗakko cake, ya dawo harabar babban soro, in da aka ɗure dawakai, ya shiga cin Abincinsa yana kallon dawakai.

Harya gama cin abunda zeci, ya tsyaa yana jiran yaga fitowar su Abba dan su tafi, amma yaji shiru basu fito ba.

Ya koma cikin gidan amma ya tarar da su a É—akin Hakimin, ba su da niyyar tafiya ma, sedai ya tarar ana ta shashafawa Hakimin ruwa a jikinsa, alamar jikin ne ya É—au zafi.

Har la'asar ana fama saboda jikin Hakimi, Abba yace zasu tafi da shi yace be yadda ba, sedai a kira masa likitan da yake duba shi yazo har gida ya duba shi, amma su barshi a turakarsa, yafi son in mutuwa zeyi ya mutu cikin sutura a É—akinsa ba tare da ya wahal da kowa ba.

Inna dauriya kawai take, yayin da Nana ta dinga kuka kamar ance mata Hakimin ya rasu.

Faruk ne ya biyo bayanta, yana rarrashin ta "haba Nana, ya zaki É—aga mana hankali kema, ki dena kukan nan haka, insha Allah ze samu lafiya"

Nana ta jinjina kai amma ta kasa dena kukan, yaita rarrashin ta.

Shi kuwa goga Sadik ya koma mota yai zamansa, yana jiran a gama abunda za'ai azo a tafi gida.

Likita yazo ya dudduba Hakimi, yai masa allurai ya bashi magunguna sannan ya ɗan samu sauƙi.

Abba yace baze yuwu su tafi a ranar ba, saboda ko sun tafi hankalinsa ba ze kwanta ba, saboda ya tsorata da yanayin jikin mahaifinsa.

Ai da Sadik yaji labarin a garin zasu kwana, ji yai kamar ance ya kwana a wuta, wani irin takaici ya turnuƙe Sadik, ji yake dama be biyo su ba.

Cikin ikon Allah zuwa magariba Jikin Hakimi yai sauƙi, dan har yana iya miƙewa tsaye da kansa.

Inna kuwa duk tana monitoring ɗin Sadik, yadda yake cika yana batsewa saboda zasu kwana a garin, gashi ya ƙi cin abinci, ruwa ma ya ƙi sha se wanda ya zo da shi na jarka ya Ke shan abunsa.

Saboda rashin network, se message Abba yaiwa Mother, ya sanar mata a garin zasu kwana.

Mother kanta taji haushin batun kwanan nan, dan ba abunda yafi damunta se Autan ta, ta san Sadik ba 'a masa gwaninta, kuma ba komai ne ke burgeshi ba, Abinci ma ba na ko ina yake ci ba.

Da isha'i, Sadik yana alwala Nana ta fito daga banÉ—aki, ita ma tayo Alwala, tana fitowa ta fara yarfe hannu, aikuwa ruwan alwalar jikinta ya sauka a fuskar Sadik.

"Ke wace irin Mahaukaciya ce ƙazama zaki watsamin ruwa a fuska?"

Nana ta waigo ta kalleshi tace "kaine mahaukaci bani ba, kuma wallahi kar ka sake cemin ƙazama dan ban ma abun ƙazanta ba"

"Wallahi idan baki kiyayeni ba sena tattakaki a gurin nan"

"Kaga ka kiyayeni da batun zaka tattakani É—in nan, sedai mu tattaka juna banza kawai"

"Nine banzan?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsa.

"Eh kaine banzan, an faÉ—a banza"

Aikuwa ya É—aga butar da yake Alwala da ita, da ruwan da komai ya jefo mata.

Aikuwa tai gefe tana kiran "wayyo Allah Inna"

Ba shiri Inna ta sallame sallar da take, ta fito tsakar gida hakan yai daidai da shigowar su Faruk daga masallaci.

Inna tace "lafiya meye haka?"

Nana tace "dukana zeyi"

Abba yace "Sadik wai kai meyasa baka girma ne?"

"Abba rashin kunya fa take min, saboda tsabar wulaƙanci ta shiga banɗaki tai ƙazantar ta ta watsa min sauran ruwan kashi a fuskata"

Nana tace "kut, wallahi ni ba kashi nayi ba, alwala nayi"

Faruk ƙunshe dariya yai, yai waje dan abun nasu ƙuruciya ce da shirme kawai.

Abba yace "kai yanzu ba ka ji kunya ba, idan ma hakane ba sekai haƙuri ba, kuyi ta abu kamar ƙananan yara,in dai zaku haɗu sedai kuyi faɗa"

Inna saboda tsabar takaici, ta koma ta cigaba da sallarta, ba tare da tace uffan ba.

Nana ma da sauri tabi bayan Inna, dan kar Sadik ya kuma yunƙurin dukanta.

Da daddare Sadik yaita tsaki, gashi akan lintsumemiyar katifa, É—aki irin na gidan sarauta, amma yaita mita da tsaki, wai É—akin zafi ga ba wuta, ga missing Farhan da yake.

Ƙarshe se message ya tura mata, ya sanar mata a garin ze kwana, yai trying lambarata amma inda yake ba network.

Tun tara na dare ya tura mata message ɗin, amma se sha ɗayan dare ta ga saƙon, tana tsaka da tunaninsa.

Zuwa gari ya waye, jikin Hakimi yai sauƙi sosai, ya samu ƙwarin jikinsa.

Nana ta shiga É—akin Hakimi ta gaishe shi, ta tarar yana bacci ba kowa a É—akin se Sadik, yana zaune yana danna waya.
Chapter 22 · 0% Book details