Sashe 73
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har gari ya waye idon Farhan biyu, ba ta rintsa ba, zuciyarta se suya take, mussaman idan ta tuna abunda su Mubarak Babba su kai mata.
Da safe Umma na can na fafutukar shirya yara su tafi makaranta, Farhan ta É—akko wayar Umma, ta É—akko lambar Mubarak Babba, da ya bata Ranar da ya kawota gida.
Bugu biyu ya É—auka yace "hello waye?"
"Farhan ce" ta bashi amsa.
Yace "Ohh beb ya kike?"
Farhan tace "ina zamu haÉ—u? Ina son ka bani abun nan"
Mamakine ya kama Mubarak, yadda be ji ta tambaye shi, abunda ya faru da ita ba.
Yace "mu haÉ—u a Hotel É—in nan"
Farhan tace "ka jirani ƙarfe huɗu na yamma"
Ta kashe wayar, taje ta ajiyewa Umma, tana ƙoƙarin Fitowa daga ɗakin, su kai karo da Umma, ta kalli Farhan tace "me kike min a ɗaki?"
Farhan ba tace mata uffan ba, ta raɓata ta fice daga ɗakin.
Tana jin yadda Umma ta rakata da zagi, da ƙanan maganganu amma tai shiru ba tace komai ba.
Da Asubar fari Sadik ya tashi yai alwalwa, ya dawo ya tashi Nana dan tai salla.
Daga haka ya fice ya bar mata É—akin, Nana tana alwala tana kuka, har ta zo tai salla ta idar, koke koken ta take yi.
Har wajen ƙarfe tara na safe, se da Nana taji yunwa za ta mata illa, sannan ta lallaɓa ta fito falo.
Sadik na kwance akan doguwar kujera, hannunsa riƙe da remote, Kallo ɗaya tai masa, ta ɗauke kanta daga kallonsa ta wuce Kitchen.
Binta yai da kallo, yana gano zunzurutun fushi a fuskar ta, ga tausayin ta da ya ke ratsa zuciyarsa.
Kitchen ta shiga ta haɗo tea, ta soya ƙwai ta ɗakko bredi ta fito, har zata wuce ɗakinta Sadik yace "ke, ni kenan da yunwa zan zauna?"
Ranta a haÉ—e ta koma Kitchen, ta haÉ—o masa kayan Abinci, ta kawo ta ajiye masa, zata koma É—akinta yace "nemi guri ki zauna"
Ba dan ta so ba, ta samu guri ta zauna tana hura hanci, saboda yadda take jin haushin Sadik.
Sadik ya ci Abincin sa ya ƙoshi, ya ƙare mata kallo yace "wai ke uban me akai miki, se wani huran hanci kike?"
Ai kuwa dama ƙiris take jira, ta fashe da kuka tace "bayan ka lalata min rayuwata, kuma kake tambayata me kai min, a kafi kowa sanin abunda kai min.
Duk yadda Inna ke ƙoƙari a kaina kar in lalace, ta ke tai min nasiha akan in kiyayi maza, shine ka lalata min rayuwata, yanzu da wani idon zan kalli Inna? Sun turoni inyi karatu, ka lalata ni, me zance musu?" Ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka.
A ransa yace 'anya wannan 'yar ta na da kai kuwa?'
A fili yace 'ni kike tambaya me zaki gayawa Inna? Ki gaya mata Sadik ya ɓata miki rayuwa, ga amsa a bayyane"
"Au haka ma zakace, ka cuceni kuma kana gayan baƙar magana? Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, shikenan mutuncina ya zube"
Sadik yace "ai seki bi shi ki kwaso shi, sokuwa kawai"
Baƙin cikin duniya ya ishi Nana, Sadik ya mata wannan abu kuma ya koma yana raina mata hankali, kamar be yi komai ba.
Kamar yadda Farhan su kai da Mubarak, ba tare da neman izinin kowa ba, ta shirya ta fita daga gida, se dai babu wayar da zata kira shi tace masa gata ta zo.
Tana nan tsaye ta hango shi yana fitowa daga reception, yana ganinta ya hau murmushi irin na 'yan Duniya yace "My baby, ashe kin ƙaraso?"
Farhan ta kalleshi cikin tsana, dan ko fuskarsa ba ta son gani.
Yace "muje daga ciki ko?"
Ba musu ta bi bayansa, wani ɗaki ya kai ta a cikin Hotel ɗin, ta tsaya tana ƙare wa ɗakin kallo.
Yace "zauna mana, bari in kawo miki abun taɓawa ko"
Farhan ta kalleshi tace "ba shi na zo yi ba, Mubarak me ku kai min ranar da na zo Hotel É—in nan?"
Yace"Normal ne, ki basar kawai beb"
Cikin ɓacin rai tace "Kar ka kuma cemin wata beb, Mubarak me ku kai min? Ka gayamin?" Ta faɗa cikin kuka.
Yai ajiyar zuciya yace "Am sorry, kawai ki ɗau haƙuri, ba shi da amfani sanin abunda ya faru"
"Kamar yaya me kake nufi?" tai maganar hawaye wani na bin wani.
Mubarak yace "Farhan, ai bana alƙawari in saɓa, tun da na ƙyalla ido na ga Sadik ya mutu akan sonki, nai alƙawarin se na miki illa na ɗanɗana masa baƙin ciki me raɗaɗin gaske"
Kamar Mahaukaciya Farhan tace "Meye nawa a ciki? Ni laifin me nai maka? Ina ruwana da abunda ya haÉ—a ku?"
Mubarak yace "ok har kin manta lokacin da kika mareni kenan, kin É—auka kin ci bulus?, na samu abunda nake so, kuma ba ni kaÉ—ai ba ne nai, ko ba Komai na barwa Sadik ajiya me muni.
Mu huÉ—u mu kai amfani da ke, kuma ki sani ko kin kai gaba ba abunda aka isa ai min, saboda ke ba 'yar uban kowa bace, face 'yar talakawa mara amfani, ba ki da kuÉ—in da zaki ja da ni, ai Tasleem ta ga ma min komai"
Farhan ta haɗiyi wata irin muguwar ƙwallar baƙin ciki ta kalli Mubarak tace "ni 'yar talakawa ce, amma ba mara amfani ba, tabbas ka zalunce ni saboda abunda ya haɗo ku da Sadik daban, ni kuma alaƙata da shi daban.
Kayi naka ɓangaren, saura nawa zakaga abunda zan iya yi"
Ta juya ta fice daga ɗakin cikin sassarfa, wani duhu da ƙunci ya mamaye zuciyarta.
Mutum huɗu su kai mata fyaɗe tana maye, wannan wane irin bala'i ne, gurin wa za ta kai ƙara bayan ita ta kai kanta?.
"Duk kai ka janyo min Sadik, tarayya ta da kai ba ta amfana min Komai ba se zunzurutun bala'i, ka sanya ciwo a zuciyata, da fari nayi zaton Alkhairi ne shigowar ka rayuwata, amma yanzu na tabattar da kai ƙaddara ne, insha Allah daga rana me kamar irin ta yau zan shafe ka a tarihin rayuwata, ko a lahira bana fatan sake yin ido biyu da kai, na tsaneka Sadik, na tsane ka Tsana me tsananin gaske.
Zan shiga bariki in tara kuɗin da zan kawo ƙarshen Iskanci da tsageranci na Mubarak babba da tawagar sa.
Ba ni ba Aure, sedai se na rama yaudarar da Sadik da yai min akan sauran maza!.
Da irin wannan maganganun ta nufi hanyar fita daga Hotel É—in, zuciyarta kamar ta tarwatse.
Nana ta gama fushin ta ta sakko, dan ba za ta iya dogon fushi da Sadik ba, dan ta fuskanci idan ta biye masa, haukata ta zeyi, dan ba shi da aiki se tsokanar ta, da takura mata be kuma gigin cewa ze mata wani abu ba, hakan ya sa ta ɗan sakko daga fushin da take, amma haryanzu idan ya so ganin ɓacin ranta, se ya kwanta a jikinta, nan za tai ta mita tana cewa wallahi ba ze sake lalata ba.
Yau sun gama cin Abincin dare, Nana tace "Friend nifa gaskiya Islamiyya nake son shiga, dan Allah ka sani a Islamiyya mana"
Sadik yace "ke kinga wata Islamiyya a nan ne, to ni makarantar addinin Musulunci É—aya na sani a garin nan, kuma tana da nisa sosai daga nan gidan, sedai in biya miki ta online ki dinga yi a system É—ina"
Tace "yawwa, amma fa nagode Sosai, Allah ya saka da Alkhairi Autan Mother" yai murmushi kawai ba tare da yace mata Komai ba.
Tana nam zaune ya ɗakko System ɗin sa, yai mata registration na Online islamic classes, hatta kuɗin da ake buƙata ya biya mata, nan Nana ta dinga murna tana masa godiya, tare da yi masa Addu'oi kala kala.
**********
"Khairat, wai meke damunki ne? Kullum kina É—aki kamar me jego"
Khairat ta ɗan ɓata fuska tace "ba Komai fa"
"A'a ban yadda bakomai ba, ke kenan kullum a ɗaki, Mother ta kirani a waya ba a dadi, akan kije amma kin ƙi, kwata kwata kin ɗauke ƙafarki daga gidansu"
Ta tura baki gaba tace "to ni Mummy me zanje Gidan in yi?"
"Kamar ya me zaki je ki yi, da me ki ke zuwa yi?"
"Mummy gidan fa ba kowa, daga ni se ita da 'yan aiki, gidan is boring wallahi"
"To amma duk da haka, zaman ki a gidan ma É—ebe mata kewa, kinga ita kaÉ—ai ce a gidan"
Khairat tace "hmm Allah sarki, gidan b kowa yanzu, Sadik yana can, ni shi nake son in ga yadda ya zam, gashi tun da ya tafi ko a waya, be taɓa kirana ba, Mother tace min ya canza layin da yake amfani da shi a can, na karɓi sabuwar lambar ta sa amma ba ta shiga, tace min lokuta da dama idan ba shi ya kiraka ba, wayarsa ba ta shiga"
Mummy tace "hakane, amma mahaifinsa ne ya sama sa takunkumi, ya ƙayyade masa iya wanda ze dinga kira da layin, an saita layin na sa da iya lambobin da ake so ya dinga ta'amalli da su, haka HAUWA tace min"
"Taɓ, gaskiya an matsan ta masa da yawa, gashi an haɗa shi da 'yar ƙaiye haka ze ta fama"
Mummy tace "yawwa, ni se da ki kai wannan maganar ma, sannan na tuna da batun Yaron nan Abdul, ɗan Gidan Hajiya Azumi, dan ubanki Khairat meye aibun yaron nan da yace yana sonki? Kike wa ɗan mutane wulaƙanci lafiyar ki ƙalau kuwa?"
"Haba Mummy ni fa Yarinya ce, kalleni 'yar Yarinya da ni kawai kuma se in fara wata Soyayya?"
"To meye a ciki, so kike se kin tsofe tukuna, abunda wasu ke rububin nema ido rufe, shi fa Dagaske yake Aurenki yake son yi"
Khairat tace "Wallahi Mummy baƙi ne"
"To baƙin a wuyanki zaki rataya shi? Ina ruwanki da baƙinsa, dan kina fara akace dole se kin Auri fari?"
"Mummy wallhi shi na sa baƙin yai yawa, bana son shi ne ma wallahi"
"Haba Khairat, ina wani baƙi a nan gurin, yaro da sana'arsa da rufin Asirinsa da komai, ai ba kala ake dubawa ba, in da za'a samu kwanciyar hankali"