Sashe 102
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana ko motsi ba ta iya yi, se bin idon Sadik da kallo, ita ma hawaye na zuba daga nata idon.
Mummy tace "Sadik meye haka? Kai da zaka kwantar mata da hankali, se ka sakata a gaba kana kuka kuma?".
Sadik be saurari Mummy ba, ya cigaba da zubda hawaye.
Mother ta shigo, hannunta riƙe da kofi da ta sa aka samo mata madarar shanu ta bawa Sahal, dan yunwa yake ji, yana ta kuka.
"Sadik meye haka kake yi ne?"
itama Mother be tanka mata ba.
"Kai wannan ai shirme ne, tana buƙatar kalma me daɗi da zata kwantar mata da hankali, kai kuma kazo ka sakata gaba kana kuka, wannan ai shirme ne"
Ganin Sadik ba shi da niyyar cika Nana, balle su dena kukan yasa Mother, ta sa aka kira mata dr.
Usman ya kallesu, Sadik ya fiye abun haushi wasu lokutan, wai nan magidanci ne har da É—a, amma yakasa rarrashin Matarsa, ya zauna tayata kuka.
"Wai dan Allah Sadii se a yaushe zaka girma ne? Kai da zaka rarrasheta, amma kun haɗa kai kuna aikin kuka, meye haka?" Yai maganar tare da ƙaraswa ze janye Sadik.
Mummy ce tace "Usman, ƙyale su kowanne dole zeji mutuwar nan, shi da alama bayan mutuwar har da tausayinta da yake ji, ka ƙyale su kawai.
Mother tace 'yo banda abun kunya, gidan surukai azo a tarar ka ƙanƙame mata kana tayata kuka, wannan ai ragwanci ne"
Mummy tace "suwaye sirikan, ba duk abu ɗaya bane? Ku ƙyaleshi kawai".
Sadik se da yai me isarsa, Sannan ya gyarawa Nana kwamciya, ya samu abun fifita ya dinga fifita ta, sedai gata nan ne dai kawai, ba ta gane komai.
"Farhan, yaushe rabon da Sadik ya sake zuwa gurinki?" Abbas yaiwa Farhan tambayar.
A bazata taji maganar ta sa, ta kalleshi da mamaki tace "wace irin tambaya ce wannan?"
Abbas yace "kawai dai na tambaya ne".
"Banji daÉ—in wannan tambayar ba, kana gani ina fama ya rabu da ni ya den bina, kai kuma kana tambayata shi".
Abbas yace "baki tunanin meyasa kwana biyu ya dena zuwa ba?".
"Abba ne yace kar ya sake zuwa, Aure zanyi".
"Hmmm, hakane amma a yadda yake nace miki kina ganin kashedin Abba kawai ze hana shi ya cigaba da biniyarki?" ÆŠan shiru Farhan tai, dan wancan karon ma Abban ya masa kashedi amma ya kuma dawowa.
"Kin san wani abu, ranar nazo na daÉ—e a tsaye ina kallonku ke da shi, har Abba ya zo ya sameku, dui da ba na jin abunda kuke cewa, amma nasan Abba kashedi yake masa, haka nan naji ya bani tausayi yaron".
Farhan tace "to me kake nufi?"
"Ba abunda nake nufi, amma ba shi da lafiya"
"Haba dai? Meyasame shi?" Reaction É—inta kawai Abbas yabi da kallo, wata zabura tai lokacin da zata tambayeshi, wanda ita ba ta san tayi ba.
Abbas yace "nima ban sani ba, yanayin sa na kalla tun a lokacin, naga akwai banbanci da ranar da na fara ganinsa da kuma ganin ƙarshe da nai masa, duk yayi wani iri, akwai alamun rashin lafiya a tare da shi, da kuma damuwa"
Shiru tai ta tafi tunani.
"You still love him Farhan".
Farhan tace "A'a ni bana son Sadik, wai se yaushe zaka yadda da hakan?"
"Kinga yadda yanayinki ya canza kuwa? Ina ta baki dama ne kar in tauyeki, idan haryanzu kina son sa, ni me iya jagora ne in samu Abba in masa bayani yadda ze fahimta".
"Doctor, dan Allah ka fahimceni, a baya na so Sadik, so ba na wasa ba, ya bani kulawa da soyayya a lokacin da na rasa hakan daga in da Yakamata, ya soni ya kula da ni, amma ƙaddara ta gifta, ba zan iya Auren Sadik ba, faɗan da Abba ma yake yi wai me zan da wannan Yaron, kuma idan na ce ina son Sadik ban maka adalci ba doctor"
"Saboda ki min adalci ke se in kasa yi muku adalci? Ai soyayyar gaskiya shine sadaukarwa dan samawa wanda kake so farinciki, abunda iyayenmu basu gane ba, ita soyayya ba yin mutum bace, sirrin Allah ce a zukatan bayinsa, ba kowa ke iya sarrafa soyayya ba, idan kika tabattar min da kina son Sadik, ni kuma zan wuce gaba in wa Abba bayani, kuma batun yarintar sa iyayenmu da kakanni shekaru nawa suke Aure?".
Cikin kuka tace "Ni bana son sa, bana son Sadik doctor, ni dan Allah ka hanzarta a kawo kuÉ—in nan in huta da nacinsa, dan Allah"
Abbas yace "to naji, ya isa dena kukan haka, amma kiyi addu'a Allah ya sa yana lafiya, ranar da ya bar nan da ƙyar ya iya shiga motarsa".
Shiru Farhan tai tana goge hawaye, yayin da ƙasan zuciyarta tsananin tausayin Sadik ya cikata.
Sunusi ne yake huci Kamar kumurci yace "Wallahi Haladu zan maka abunda ba zaka taɓa mantawa ba, kai ne ka sace min kayana".
Haladu yace "in sace su in uwar me da su wai, wai meke damunka ne haka?"
"Dole ka faɗi haka mana, ka ɓatamin aikina naga wannan ɗan iskan yaron ya dawo rayuwata"
Haladu yace "ita wa kenan?"
"Farhan matata mana, wannan yaron ya dawo rayuwarta na ganshi a ƙofar gidansu"
Haladu yace "Masha Allah, Alhamdilillah ai dama irin wannan Asirin ba ya daÉ—ewa yake karyewa".
"Kenan ya tabatta kai ne ka sacemin kaya ka ɓata min aiki?"
"Na san yadda kai aikin ne balle in ɓata maka?"
Sunusi yace "ƙarya kake Haladu, Wallahi sena sake sabon aiki a kansu, ba su kɗai ba har kai, za ka ga abunda zan maka, kowa yaci tuwo da ni miya ya sha, zaka san ka shiga aikina ka min shishshigi"
"Wallahi Sunusi idan ba ka ji tsoron Allah ba, se ka wulaƙanta, iliminka be maka amfani ba, yanzu na sake fuskantar dalilin da ya sa wasu ke ƙalubalantar ilimin soro, Alƙur'ani kawai muka sani, bamu san tauhidi da sauran litattafai na addini ba, Alqur'ani kawai muka sani, kuma wasunmu irinka muna amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba, irinka suke surkulle da shi saboda rashin tsoron Allah, Wallahi Sunusi kaji tsoron Allah kafin hakkin mutane, musamman na yarinyar nan ya kama ka".
"Dalla rufemin baki, ka zuba ido zaka gani, daga kai har ita da wannan sakaran a wannan karon zasuga abunda zan musu" daga haka ya fice yana kumbura wuya.
Har bayan la'asar Nana ba ta magana sam, kuma ba ta ci komai ba, gashi rabonta da Abinci tun jiya da rana, se bayan la'asar sanann Inna ta zo kan Nana, ta tashe ta ta tashi zaune amma ba Magana.
Inna ta rungumeta, ta shiga karanto mata adduoi, kusan mintuna Ashirin sannan Nana ta fara ajiyar zuciya, sautin sheshsheƙa kukanta ya fara fita tace "Inna"
Inna tace "ya isa haka kukan Nana, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shi zaki ta maimaitawa"
Zata kuma magana Inna ta girgiza mata tace "yi ta maimaitawa Innalillahi wa Innalillahi raji'un".
Nana tace "Inna dan Allah shikenan ba zan sake ganin Alhaji ba?"
Inna tace "mun rasa shi Nana, Allah ya buƙaci abunsa, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ki ta maimaitawa ki tashi kije, ki alwala ki salla".
Inna ce ta kamota zuwa tsakar gida, mutane na tai mata sannu suna mata gaisuwa, amma ba ta iya amsawa, sedai Inna ta amsa.
Ta rama duk sallolin da ake binta, gurin cin abinci shima haka a kai ta fama da ita da ƙyar Sadik ya sata a gaba sannan ta sha kunu kaɗan, har Sahal ya samu ya ɗan sha Nono.
Bayan azahar Mummy da Khairat suka tafi gida, karon farko a rayuwa Mother ta kwana a ƙauye, tun bayan Aurenta da Alhaji Abdullahi.
Washegari mutane suka dinga ɓarkowa, ciki harda maƙota da 'yan uwan Mother suka dinga zuwa yin gaisuwa, abunka da rasuwar an maida makokin na zamani, aka dinga shiga ana fita a gidan makokin nan, sedai wanda a kaiwa rasuwar zakaga sune cikin matsananciyar damuwa a fuskokinsu.
Abu Kamar wasa, Farhan taga Sadik ya dena zuwa, ta fara tunani kala kala a ranta, anya ba da gaske ba shi da lafiya ba kamar yadda doctor ya faÉ—a ba? Ko dai korar da Abba yai masa ne ya sa ya dena zuwa?.
Shiru tai ta rasa abunda za tai, a hankali ta tashi zaune, ta É—au wayarta ta shiga yanar gizo dan rage zafi.
Sedai labarin farko da tai karo da shi ne ya girgiza ta, mutuwar kakansu Sadik.
Jikinta yai sanyi matuƙa, taji rasuwar ƙwarai da gaske, a nan taiwa Hakimi addu'a sosai.
Tana nam zaune tana tunanin yadda mutuwar kakan Sadik ta daketa sosai, Huzaifa yai sallama a É—akin nata.
Ta amsa masa tare da faÉ—aÉ—a murmushin fuskarta.
"Hajiya Yaya ana nan ana hutawa?"
"Wallahi kuwa, daga ina haka?".
Huzaifa yace "naje wani guri ne, nace ai naga Sadik, ashe ya dawo garemu amma ba labari?"
Farhan ta haÉ—e rai tace "A ina ka ganshi?"
"A ƙofar gidan nan mana, sedai ban ji daɗin abunda Abba yai masa ba, yakamata a fahimci juna, yazo asha biki kawai tunda Allah ya dawo da shi"
"Huzaifa ka san me kake faÉ—a kuwa? Abbas ya kusa kawo kuÉ—in Aurena kuma kana maganar wani Sadik, dan ka bar wannan maganar, ni ba abunda zanyi da Sadik"
Huzaifa yai murmushi yace "ji kamar gaske, a tunaninki abu ne me sauƙi kice kin dena son Sadik a yarda? Ya kamata Abba yai tunani akan lamarin nan kan ya yanke hukunci, ni dai na tafi se anjima" ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, Farhan ta bi bayansa da kallo.