← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 115

Sashe 11

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki sa a ranki bashi kika ɗauka, wanda se kin biya shi wallahi, kin san ki bar wancan sokon ya taɓa ki, amma ni kika mareni"

"Eh na bashshi ya taɓa ɗin, ina ruwanka da ni, ka ƙyaleni ka fita daga harkata"

Mubarak yai mamakin ƙwarin gwiwar ta, be taɓa tunanin zata mare Shi ba, saboda kallon sokuwa yake mata.

Da sauri ta shige Mubarak, ta cigaba da tafiya, wasu hawayen baƙin ciki na bin fuskarta, wata muguwar tsanar Babba na kuma mamayeta.

Tun daga nesa ya hangota tana tahowa, ya naÉ—e hannayensa ya zuba mata ido.

Tana zuwa tai karo da shi a tsaye yana kallonta.

"Sarkin kuka me kuma ya faru? Ki tai min asarar hawaye ba dalili"

Ƙara kwaɓe baki tai tana kuka.

"Au abun hadda shagwaɓa, zo ki gaya min menene kuma? Waye ya saki kuka, kowa yana class amma ke kika fito waje"

Yai Maganar yana janyo ta jikinsa, ba musu ta kwanta a jikin nasa, amma ba zata iya gaya masa abunda Mubarak yai mata ba, saboda sanin halinsa, dan haka tace "faÉ—uwa nayi"

Kawai Sadik ya kama dariya "wallahi kin fiye abun dariya, Garin yaya kika faÉ—i?"

Tashi tai daga jikinsa tace "dariya ka ke min ko?"

"Haba ba fa dariya nake ba, zo mu tafi muje ki gayamin waye ya taɓa min ke, garin yaya ma a kai matata ta faɗi"

Ba ɓarin da take yake kallo ba, hakan ya bata damar kallon abunta son ranta tana jin son sa na ƙara ratsa zuciyarta, he's so much caring and funny.

Yace "Princess, gaskiya wannan hijjabin da kike sawa yayi ƙanƙanta, wani zamu siya am so Much jealous"

"To ai ka san idan na sa wanda yafi wannan girma ƙwacewa za'ayi"

Ɗan ƙaramin tsaki yayi yace "kwata kwata wannan tsarin be dace da Addinin mu da Al'adar mu ba, kin ganki kuwa idan kina tafiya?"

Kunyace ta kamata, dan ita kanta tasan kayan sun kama jikinta sosai.

Kenan Babba abunda yake faÉ—a gaskiya ne.

Bin sa take tayi kamar raƙumi da akala, wani ajin ya jata in da ba kowa, da nufin suje yai rarrashi.

Suna zuwa Yasa hannu ya buɗe ƙofar ajin, sedai mummunan ganin da su kai ne ya razanar da su gaba ɗaya.

Dan seda Farhan ta saka ƙara, ya janyo ta da Sauri ya toshe mata baki.

Wata irin kyarma jikin Farhan yake, ba ita kaɗai ba, shi kansa Kamar zuciyarsa ta tsaga ƙirjinsa ta fito haka yake ji, saboda tashin hankali da fargaba.

Duk iya shegen Sadik be taɓa mummunan gani ba kamar na yau ba.

Bakomai suka gani ba face Salma da gangs ɗin ta suna sheƙe ayarsu, wata irin tsuma Farhan take kamar zata shiɗe, wannan wane irin bala'i ne haka?.

Jan hannunta yai suka bar gurin, sedai ya rasa mema ze cewa Farhan É—in, gaba É—aya shima kansa ya kulle.

Ya rakata ajinsu ta shiga shi kuma yai gaba, haka jikinta ya cigaba da kyarma, ta kasa mata abunda ta gani, wanda ya danne wanda ta gani a Office É—in sir Nazir.

Ko da aka tashi, babu fargabar Komai Farhan ta kuma bin Sadik a motar su, zuwa gida sedai ya kasa ce mata komai, ita ma kuma ta kasa ce masa komai har suka kaita gida, sedai yau a titi ta sauka ta shiga hanyar gidan su.

Tun da ta sauka ta fara tafiya kanta yana ƙasa, sedai ta lura da yadda mutane keta binta da kallo, duk da kasancewar babban hijjabi ne akan Uniform ɗin ta.

Sadik kam yana cike da damuwar yadda ze tafi ya bar Farhan a Makarantar nan, me cike da tarin ƙalubale, babu wanda ya damu da harkar kowa, ita Makaranta neman kuɗinsu ne kawai a gabansu, su kuma ɗaliban suna taƙama da kuɗin iyayen su ne ke aiki, dan haka ba wanda ya isa ya taka su, shiyasa kowa yake abunda ya ga dama.

Yau gaba É—aya kamar mara lafiya haka ta wuni, ta rasa meke mata daÉ—i, har zuwa taje Islamiyya ta dawo, tana tunani wato Salma abunda takeyi kenan shiyasa take mata wasu abubuwan da ta kasa gane kansu gab É—aya ta dinga cewa wai ta na sonta?.

"Farhan" taji an kira sunanta.

Waiwayawa tai, taga wata babbar mace ce, maƙwabciyar su da tare kwanan nan, dan matar ta girmi Ummanta sosai.

Farhan cikin girmamawa tace "Hajiya ina wuni?"

Matar tace "lafiya ƙalau, zo nan Farhan"

Ba musu Farhan ta ƙarasa in da mata ke tsaye a bakin gate ɗin gidanta, matar ta ja ta cikin gidanta ta kalleta tace "Farhan kina saka brezia kuwa?" Turus Farhan tai tana kallon matar, taji maganar ta tata wani iri.

"Kinga ni uwace ba batun jin kunya kowani abu, kin zama budurwa, ba kya ganin yadda maza ke kallon ki? Duk da naga kina da ƙoƙarin saka hannu a hijjabi"

Farhan tai shiru ta sunkuyar da kai, ita kanta abun na damunta, amma tunda ummanta ba ta siya ta bata ba, ba tai mata umarnin sakawa ba, ba ta san ya zata kalli abun ba idan ta fuskanci ta fara sawa ba da izinin ta ba, iya kaci sedai ta saka half vest ta kawo normal vest ta ƙara a kai.

Hajiya ta jinjina kai tace "jeki, zan shigo gidan naku"

Cike da jin kunya Farhan ta fito daga gidan ta tafi gida.

Da daddare bayan ta kammala cin Abincin dare, tana ɗaki tana bitar Alƙur'ani, Abba yazo ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.

Dama sanye take cikin dogon hijjabi, ta fito daga É—akin tace "Abba gani"

Abba yace "Yawwa, kije ga Sunusi can a ƙofar gida ya zo ku gaisa"

Ji tai kamar Abba ya watsa mata wuta, jiki a sanyaye tace "to Abba"

Abba yana juyawa ya tafi, Farhan ta fara hawaye, haka nan ta zura takalmanta, ta fita.

Tun kan ta ƙarasa ƙofar Gidan, warin hammatar Sunusi yai mata sallama, cikin baƙin ciki da ɓacin rai haka ta ƙarasa guri ɗaya ta tsaya.

Wandon jikinsa ta kai kwana uku tana ganinsa da shi, rigar ce ma ya canza.

Ya ƙaraso in da take tsaye ya washe baki yana "manya manya maganin ƙanana"

HaÉ—e rai tayi sosai, ta É—auke kanta.

"Hmm naga alamar miskilanci kike ji yau É—in nan, dama malam ne su kai shawara da Abbanku, suka ce lokaci yayi da Yakamata in fara zuwa gurinki dan mu fuskanci juna"

Farhan a ranta tace "ai kuwa ba zamu taɓa fuskanta ba har abada"

"Nasan dai an gama gayamiki komai, kusan tun bara Malam yace min 'meze hana ya nema min Aurenki, tunda yaga ke yarinyar kirki ce, kuna haryanzu ba wanda yake zuwa gurinki, yace ko in ba damuwa ni ya nema min Aurenki, kuma cikin ikon Allah Abban yai murna da hakan"

Wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Farhan, wato ma anga ba wanda yake zuwa gurinta shine aka ce ya nemi Aurenta, son da takewa Sadik ne yasa ba ta bawa kowane namiji fuskar yi mata magana, balle yazo gurinta.
Kwata kwata Sunusi be iya Magana ba, sqe wani soki burutsu yake, ya kama nan ya kama can, ga uwar dariya sekace wani kwantacce.

Ita ko malamanta na Islamiyya da suke alarammomi mahaddatan Alqur'ani, a nuste take ganin su, Amma Sunusi ya fita daban gaba É—aya.

Har ya gama surutun sa, Farhan ba tace masa ci kanka ba, yai surutan harya gaji yai mata sallama, ya tafi.

Wani marurun takaici ne ya ƙule zuciyar Farhan, ga Sadik me za tai da wani Sunusi?

Ta dawo gidan ba daÉ—ewa taji sallamar Hajiya, Umma ta amsa ta bata gurin zama suka zauna a tsakar gida.

Hajiya tace "Maman Farhan, wani shishshsigi na zo nai miki, amma lamari na 'ya'ya shi É—a na kowa ne ko ba haka ba?"

Umma tace "hakane"

Tace "yawwa, Magana ce game ds Farhan, duk da na ga ku al'adar ku ce ba'a bawa ɗan fari kulawa, amma 'ya'yan da a kaiwa wannan ban da na yanzu, Farhan ta zama budurwa ba ta da ƙawar da ta wuce ki.
Ki duba yanayin jikinta, Allah ya bata garin jiki yakamata ace ta fara saka brezia saboda yanayin jikinta, Yakamata ta san mahimmancin kula da jikinta, duk da naga 'yar ta mu nutsatsiyya ce Alhamdilillah, amma saboda yanayin al'adar taku nace ni bari in zo da kaina in adana 'ya ta, da na kirata na mata magana ni da ita, amma naga ba haka yakamata ba, yanzu ina Farhan É—in?"

Umma tace "tana ɗakinta" taiwa ƙanin Farhan ɗin umarnin ya kira Farhan.

Farhan ta fito tsakar gida, duk da takaicin da ke cunkushe a zuciyar Farhan, a haka ta gaida Hajiya.

Hajiya ta miƙowa Farhan ledar viva tace "Farhan ga brezia nan ni na siyo miki da kaina, a adana wannan baiwat da Allah ya bayar, dan ba kowa yake bawa ba, a adana yadda yakamata Allah ya fito da danƙareren miji na gani na faɗa"

Kasa É—aukar ledar Farhan tayi, ta É—aga kai tana kallon Ummanta, amma taga Umma na kallon wani gurin daban.

Hajiya tace "Au ba zaki ɗauka ba, jira kike se ta baki umarnin ki ɗauka, maza ɗauki kije, idan Allah ya haɗaki da 'yan banzan samarin nan na zamanin, sukai miki ba daidai ba, ko wani ya taɓa kya nutsu ai tashi kije"

Gaba ɗaya wat irin kunya ta mamaye Farhan da Umma, sam Umma ba ta ji daɗin maganganu nan da Hajiya ta faɗawa Farhan ba, wata irin kunya ta lulluɓe ta.

Farhan tace "Nagode" ta É—au ledar ta tafi.

Tan zuwa É—akinta ta zazzage ledar, taga brezia ce guda bakwai, sababbi ga turaren humra hadda su hoda da jambaki.

Da sauri ta miƙe ta fara gwadawa, ta saka sannan ta kawo rigarta ta mayar se ta ga rigar ta ƙara zama a jikinta.

Se kuma kawai taji kunyar kanta ta kamata, wai yau ita ce da saka brezia, farin cikin samun wannan kayan, yasa duk ta manta da wasu damu wowi da suka dameta.

Washegari da taje school kuwa, Sadik ya dinga cewa "wani abu ya canza a tare da ke Farhan, amma na kasa gane ko meye"
Chapter 11 · 0% Book details