← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 115

Sashe 94

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba zan taɓa fahimtar ka ba, wai tsaya ita wadda kake tare da itan, me ka rasa a gurinta ta ina ta gaza gayamin ina jinka"

"Abba Wallahi ba abunda Nana tai min, tayi iya ƙoƙarinta a kaina, idan nace zan butulce mata ko in cutar da ita Allah baze barni ba, amma Abba akwai dalilin da yasa nak......

"Kai dalla rufen baki, tashi ka bani guri"

Kamar Sadik ze kuka yace "Abba dan Allah ka saurareni"

"Ka fita ka ban guri nace" Abba yai maganar cikin tsawa, haka Sadik ya tashi ya fita gwiwa a sanyaye.

Nan abubuwa suka sake sha masa kai, ya rasa mema Yakamata yayi.

Haka nan Farhan ta tsinci kanta da tattara kayanta, domin barin Hotel É—in nan, dan tana shakkar Sadinya aikata abunda yace, tunda har yai rantsuwa, to ze iya aikatawa.
Ta tsinci kanta cikin wani nishaÉ—i tun bayan sumbatar da Sadik yai mata.

Mother ce ta shigo kawowa Abba Abinci, tana mitar yadda ta sa aka kira me gyaran solar amma be zo ba, se inji aka kunna, sam taga hankalin Abba ba ya kanta.
"Yallaɓai lafiya kuwa?"

Abba ya girgiza kai yace "kin san me É—anki ya zo min da shi?"

Mother tace "wanne daga cikin 'ya 'yan?"

"ÆŠan Autan ki"

"A'a seka faÉ—a"

Abba yace "wai Aure ze ƙara"

"What?" Mother tai Maganar cikin É—aga murya.

"Wallahi abunda yace min kenan"

"Amma ka tsinka masa mari ko, dan ya dawo hayyaccinsa"

Abba yace "ba wani marinsa da nai ni, sedai kawai na koreshi ne"

Mother tace "lallai yaron nan ba shi da hankali, gaba É—aya yaushe yai Auren farin, da har ze É—akko wannan maganar, da ya a kai masa Auren farkon ma?"

"Rigima mana, irin tasa ai Sadik halinsa se Addu'a, ya zo ya tattara ya koma makaranta, Ya bar su a nan ita na nema mata wata makarantar ta cigaba da zuwa, in ya so ko me raino se a samo mata, wadda zata dinga riƙe mata takwarana"

Mother tace "base an wani samo me raino ba, ta dinga bar min shi zan riƙe"

Abba yace "to shikenan, Allah yayi jagora, amma dan ubansa makaranta ze zo ya koma bana son rigima".

A falon BQ ya tarar da Nana, ta saka Abinci a gaba tana son ta ci, amma Sahal se rigima yake ya hanata cin abinci, kuma da alama tana jin yunwa sosai, se haÉ—e rai take gashi baya gajiya da tsotso.

Sadik ya ƙarasa ya karɓi Sahal, yana rarrashinsa, ita kuna ta fara cin abincin, ya ɗan zuba mata ido sannan yace "wato yanzu kin dena damuwa da ni ko? Ko ki min tayin Abincin?"

Cikin ko in kula tace "am tired ne, dole in zubawa sarautar Allah ido"

Jikinsa ya ɗanyi sanyi, tabbas Nana duk da tarin shiriritar ta, tayi iya yinta taga Ya dawo da walwalarsa, amma abu yaƙi yiwuwa.

"Husna" ya kira sunanta, ta É—ago ido tana kallonsa.

Yace "am so sorry, na san gaba ɗaya ba kya jin daɗin yanayin zaman mu a yanzu, amma kiyi haƙuri komai ze wuce insha Allah".

Shiru tai ba tace komai ba ta cigaba da cin abincin dake gabanta, se ganin hawaye yai yana É—iga akan hannunta daga idonta.

Ya ɗan lumshe idanunsa ya kwantar da Sahal da yai shiru, yana cin hannunsa, ya zauna a kusa da ita sannan yace "tuba nake my wife, kiyi haƙuri dan Allah, zan canza insha Allah, zamu koma normal yadda muke, ki dena kuka bana son hawayenki Besty" yai maganar cike da kulawa yana share mata hawaye, ita dai ba tace masa komai ba, ya cigaba da rarrashinta.

Bayan sallar isha'i Sadik yai kwalliya cikin manyan kaya, ya tafi gidansu Farhan, amma ya tarar da ita tana zance acikin motar Abbas, ransa ya ɓaci sosai amma be ce komai ba, ya fito daga motar yaje ƙofar gidansu ya samu guri yai zamansa.

Farhan ta ƙi fitowa daga motar Abbas, ta dinga jansa da hira daban daban, har mamaki abun ya bawa Abbas, yace "ya dai na fuskanci hira kike ji sosai, Allah ya kaimu bikin nan a raƙashe babyna"

Farhan tace "hmm ba wani raƙashewa, ai ɗaurin Aure da wuni rana ɗaya kawai"

Abbas yace "A'a, dole ki shirya wani ɗan reception ke da ƙawayenki"

"Ai ni bani da ƙawaye"

"Ahha haba dai, to suwaye zasu raka ki gidana?"

"Dagaske bani da ƙawaye, 'yan uwanmu ne zasu kai ni"

Yai murmushi yace "ke dai abun mamakin ki baya ƙarewa Farhan" haka suka cigaba da hira, daga bisani su kai sallama Ta fito daga motar, ya ja ya tafi.

Ta zo zata shiga gida, ta share Sadik kamar ba ta ganshi ba, ya miƙe ya tare mata hanyar shiga ta dube shi tace "meye haka kuma? Bani hanya zan wuce"

Sadik yace "ba zan matsa É—in ba, me nace miki akan shiga motar mutumin nan?"

"Ban gane ba, wai kai meye haɗina da kai ne, dan Allah ka ƙyale rayuwata ta huta"

"Ba ke ba hutu, idan har ba ni kika Aura ba, tunda kika zauna tsawon wannan lokacin har na dawo baki Aure ba, to ki sani ke rabona ce Farhan, dan Allah ki zama me yafiya"

"Kaga dan Allah ka bani hanya zan wuce gida"

"Yadda kika bashi lokacin ki, nima dole ki bani lokaci, sannan let me warn you for the last time, kar in sake ganinki a motarsa, kuma kar ya sake zuwa gidan nan gurinki"

"Saboda ubana ne kai? Mutumin da zan Aurane nan da ƙanƙanin lokaci, kai na bawa dama a farko ba kai amfani da ita ba, dan haka yanzu damar wani ce"

"Farhan ba ki yadda da duk abunda na gaya miki bane?"

"Na yadda mana, ka manta dani a rayuwarka saboda rashin mahimmanci na, kai Auren ka har da ɗa, ka ƙyaleni nima in Auri wanda nake so ka dena shiga rayuwa ta"

Sadik yai wani murmushin rainin hankali sannan yace "da alama kina kishi da matata sosai, hakan ya sake tabbatar min da kina sona haryanzu, karki kishi da matata ba ruwanki da ita, ko ki tambayi ya sunan É—ana ko?"

Wani takaici ne ya ƙule zuciyar Farhan, zata bangaje Sadik ta wuce, amma ya riƙeta kasancewar gurin ba haske.

A fusace tace "meye haka, ka dena taɓani"

"Meye na pretending kuma in dena taɓa ki, meye ba muyi ba a baya, duk ki ka lalata ni, na dinga cewa Aure nake so, se da a kaimin Aure na nutsu duk ke kika koyamin, kika saba mun da..... Se kuma yai shiru yana wata shu'umar dariya.

Wani takaici ya cika zuciyar Farhan, tare da dana sanin kuskuren da tai a baya, ta biyewa Soyayar RUƊIN ƘURUCIYA.

Kawai ta fashe da kuka.

"To me nai miki kuma zaki min kuka, daga tuna baya se kuka, mara kunya kalli da É—an mayafin da kike shiga motar wani, Allah sarki i miss my old Farhan so much".

Kuka take sosai har da sheshsheƙa, yai mata banza kuma yaƙi bata hanya ta wuce, se da tai me isarta Sannan yai ƙasa da murya ya kai bakinsa kunnenta yace "munyi kuskure a baya, wanda nine dalilin hakan, son da kike min da ƙuruciyar da ke kanmu ya sa soyayyar mu da shaƙuwarmu ta kai mataki me wuyar mantawa, Farhan ke yarinya ce me nutsuwa da tarbiyya, a dalilin soyayyata duk kika canza, idan na gujeki Allah baze barni ba, duk wanda zaki Aure nan gaba ze iya yai miki gori, ni kuwa fa nine silar komai, kuma yanzu ba ki ga na ƙara girma ba, har ɗa ne fa dani, kyakykyawa kamar mamansa".

Tsaki Farhan tai, zata raɓashi ta wuce ya sake riƙota yace "to meye na fushin kuma? Matata Tana da kyau sosai kamar ke ɗin nan, ki rage kishi kuma ki yarda haryanzu kina son Sadik ɗinki, ki kulamin da kanki, I love You" ya ƙarasa tare da sumbatar kumatunta.

Ya cikata, ya juya cikin takunsa a nutse ya nufi motarsa, yayinda galala tabi bayansa da kallo.

Seda motarsa ta bar layin, Sannan jiki a sanyaye ta shige gida.

Da safe Sadik yana bacci, wayarsa ta fara ringing, ganin Abba ne ya sa Nana ta É—aga kiran, suka gaisa ya tambayeta ina Sadik, ta sanar masa bacci yake, yace idan ya tashi su zo duka yana son ganinsu.

Se wajen goma sannan Sadik ya tashi, bayan ya karya Nana ta sanar masa da kiran Abba, suka shirya zuwa cikin gida, kai tsaye part É—in Abba suka wuce, suka tarar da shi ds Mother a can.

Suna zuwa Mother ta karɓi Sahal a hannun Sadik tana masa rawa.

Suka gaida su Abba, Abba ya kalli Sadik yace "kai me ka shirya ne akan komawarka makaranta?"

Sadik yace "Makaranta kuma Abba?"

"Eh mana Yakamata ka koma"

Sadik yace "dan Allah Abba ka ƙyaleni ba se na koma bs, ai min transfer in dawo Nigeria"

"Saboda ba ka da hankali? Ka koma makaranta ita ma na fara tuntuba in da za'ai mata registration ta koma makaranta a nan, takwarana kuma Kakarsa tace zata dinga riƙe abunta taje makarantar ta dawo"

"Abba dan Allah ka barni a nan, ba zan iya komawa makaranta in bar su ba"

Mother tace "zama ka faÉ—i gaskiya ne"

Abba yai mata alama da ido, akan karta tonawa Sadik asiri a gaban Nana.

Abba yace "yanzu ka gwammance in asarar kuÉ—ina kenan?"

Sadik yai shiru ya sunkuyar da kai ƙasa, Abba yace "tashi kaje zan nemeka"

Suka fito shi da Nana, cikin damuwa Nana tace "besty, da Sahal ya isa ysye da na yaye shi na bika, naga Abba ya fi son ka koma"

Sadik yai ajiyar zuciya yace "zaman baze min daÉ—i ba, ba zan iya zuwa in zauna nikaÉ—ai ba, ke kin san meyasa, Abba ba za su fahimce ni ba"

Ƙunshe baki tai tana masa dariya, yace "au dariya ma kike min ko?"

"To Besty kai ɗin ne ai se a hankali, ai gara ma ka tafi ko nayi ƙiba"

"Wallahi duk na damu, kin rame sosai Besty, kin fi ƙiba da muna London"

Nana tace "to ya zanyi? Shayarwa Sahal ba shi da haƙuri gurin ci, gashi kai kuma duk ka canza abun yana damuna sosai"
Chapter 94 · 0% Book details