Sashe 101
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ledar hannunta ya ƙurwa ido, tana ƙoƙarin wuce shi ya fizge ledar hannunta, ya buɗe maganin tari ne da wasu ƙwayoyi a ciki, se da kan Sadik ya sara yace "Farhan, yanzu kuma meye damuwarki da zaki sha wani abu?"
"Ka aikeni ne? Bani ledata in wuce".
"Ba zan bayar ba, Wallahi ka fita daga sabgata na gaya maka".
"Ba zan fita ba, ki kiyayeni Farhan ki bar ganin ina lallaɓa ki, Farhan meye daɗi a cikin wannan shaye shayen da kike?"
Farhan na ɗaga kai ta ga motar Abbas na shigowa, ta ɗaya ɓangaren kuma Abba ne ke tunkaro gida shima.
Kasa motsawa Farhan tai daga in da take, se tsananin bugawa da ƙirjinta yake.
"Ke Farhan, ban hanaki tsayuwa da wannan yaron ba?" Abba ya fara magana tun kan ya ƙarasa.
Kasa Magana tai, Abba ya ƙaraso ya dinga faɗa ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, kamar ze ari baki, daga Sadik har Farhan aka rasa me motsawa.
Abbas kam zama yai yaƙi fitowa daga cikin motar.
Abba ya cigaba da sababi, "ke banda shashanci me zaki da wannan yaron? Ina Hankali ya gama ratsa shi? Wuce ki bar nan kan in saɓa miki, kai kuma zan maka kashedi na ƙarshe, kar in sake ganinka a ƙofar gidana, ko ta rasa mijin Aure ba zan taɓa aura mata mutumin kawai irinka ba, dan haka ka ƙyalemin yarinya tai Aure na karɓi kuɗin Aurenta bana son shirirta da RUƊIN ƘURUCIYA".
Huzaifa yana tsaye a soron gidan su Farhan yana jin komai, ya jinjina kai a ransa yace "wannan ne Sadik ɗin kenan? Idan kuwa hakane Abba yana shirin sake tafka kuskure dan haryanzu Farhan tana son Sadik'.
Farhan ko lura da Huzaifa ba tai ba, ta wuce cikin gida ranta a ɓace ba tare da ta san dalilin ɓacin ran ba.
Se da Abba ya gama faÉ—ansa, Sannan Sadik ya juya, yana jin wani irin jiri ya nufi motarsa, kasa buÉ—ewa yai ya jingina da jikin motar tare da dafe kansa.
Dafa shi yaji anyi ance "É—an uwa ya dai?"
Sadik ya É—ago ya kalli Huzaifa yace "bakomai".
"Naga ka dafe kanka"
Sadik yace "No bani da lafiya ne, kaina yana min ciwo, amma magunguna na suna mota zan sha insha Allah, nagode sosai".
Yace "idan ba zaka iya tuƙin ba, ka jira ka samu sauƙi"
Sadik yace "No, zan iya nagode sosai".
Haka Huzaifa ya koma cikin gidan su Farhan, sedai abun mamaki ya tarar Abba ya cigaba da sababi a tsakar gida, da ya leƙa ɗakin Farhan kuwa, hangota yai ta dunƙule guri ɗaya tana kuka.
Huzaifa a ransa yace "Akwai damuwa, na rasa dalilin da yasa iyayenmu ke yanke hukunci da zuciyar su, maimakon ƙwaƙwalwa.
Duk abun nan da ya faru, akan idon Abbas ya faru, a hankali ya ja motarsa yai baya, kan Sadik ya rarako tasa motar ya zo ya buga masa, dan ya lura yaron RUƊIN ƘURUCIYA na damunsa.
Abba me ya tsare Sadik a bakin ƙofar shiga falo yace "daga ina kake?".
Sadik yace "Naje shan iska ne?"
Abba ya girgiza kai yace "Kafin ka mace mana saboda soyayya, ka gayawa yarinyar zamu zo nema maka izinin Aurenta.
Murmushi ne ya bayyana a fuskar Sadik, sedai lokaci É—aya murmushin ya É—auke, bayan tuna furucin Abban Farhan, da kuma Nana da ke bayan Abba, tana son su gama Magana ta wuce, da alama Abba be san tana tsaye a gurin ba, aikuwa maganar Abba ta soki zuciyar ta, take idanunta su kai ja, ta juya cikin hanzari ba tare da Abban ya ganta ba.
"Magana nake maka, amma ka tsaya kana kallona".
Sadik yace "to Abba, nagode sosai Allah ya ƙara girma".
Abba bece komai ba yai gaba abunsa.
Sedai Sadik ya rasa ƙwarin gwiwar da ze tunkari Nana, Wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa.
Nana yadda ta ga rana haka ta ga dare, saboda yadda zuciyar ta ke mata wani irin zafi, ta rasa in ds zata saka ranta taji daÉ—i, haka ta kwana sirr ba bacci, se nafilfili da adduoin da dinga yi, Akan Allah ya yaye mata son Sadik, da wannan kishin nasa da ke damunta.
Washegari da Sassafe Mother ta ƙwanƙwasawa Nana ƙofar ɗaki, da yake a cikin gida ta kwana yau, tace wa Nana ta shirya zasu tafi ƙauye.
Abun ya bawa Nana mamaki ƙwarai, ta tambayi Mother dalili amma Mother tace mata, Hakimi ne yake son ganinsu.
Abun mamaki daga Mother se Nana, se Jidda, har da Mummyn Khairat suka tafi a mota É—aya, Su Abba wai tun Asuba suka tafi.
Nana tai jigumm ba tare da sanin meke damunta ba, Sahal ma kasa riƙe shi tai, se Mummyn Khairat ce ta karɓe shi, haka suka tafi ba wanda yakewa wani magana.
Sam Nana ta dena ji ta dena gani na wucin gadi, ta dena gane komai se tsintar kanta tai a cikin turakar Hakimi bisa jagorancin Mother, tana zuwa ta tarar da gawa, ga Inna da Abba, ga Sadik har da Faruk, sun kewaye gawar idanunsu sunyi jawurr.
Jiki na rawa ta Æ™arasa, ba tare da wani ya dakatar da ita ba, ta É—aga bargon da aka lulluÉ“e Hakimi, tai tozali da kyakywar fuskar Hakimi, cike da haiba da kamala kamar tace 'tashi Kyakywan kakana, kamar yadda ta kanyi, in ta so tsokanar saâ—â—â—
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680
AFUWAN BA EDITING.
Jikin Nana ne ya ɗau rawa kamar zata fita daga hayyacinta, ta nemi guri ta zauna daɓas, idanunta sukai jawur.
Can cikin ƙaraji Nana tace "Inna, dan girman Allah ki tasheni daga baccin nan da nakeyi, ki cemin mafarki nake ba Alhaji ne ya mutu ba, dan Allah ki tasheni dan girman Allah".
Usman yace "Nana se haƙuri,ki sassauta muryarki, dama duk me rai mamaci ne, kiyi haƙuri ki yi masa Addu'a".
"Ba zan ba ni ku ƙyaleni, dan Allah Inna ki tashi Alhaji, ki ce masa ya tashi kar ya tafi ya barni mana".
Inna da take zubda hawaye, ta janyo Nana jikinta tana duddukan bayanta a hankali alamar rarrashi.
Tabbas duk wanda ze ji rasuwar Hakimi barin Nana ne, tun da Allah yasa su Inna suka rasa iyayen Nana suka É—au son duniya suka É—ora mata.
Banda Inna a tsaye take akan tarbiyyar Nana, ds a sangarce za ta tashi, dan ta Hakimi shi be ya takurawa Nana, duk abunda take so shi yake mata, kasancewar yaransu duk sun rasu se Abba, ita kaÉ—aice jikarsu da ke gabansu, Nana ko dangin mahaifiyarta ba ta wani sansu ba, saboda ba zuwa take ba, iyakaci sedai su su zo, sam Hakimi baya son tai nesa da shi.
Ko zaman fada da ƙyar Inna ta hana shi yi da Nana, lokacin ta fara girma, akwai matsananciyar shaƙuwa ds soyayya a tsakanin Nana da Hakimi, shaƙuwa ta gaske kuwa.
Wani dogarin Hakimi ne yai sallama a ƙofar turakar yace "A fito da shi, mutane sun idar da alwala za'a shigo da makara a ɗauke shi". (Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya Ubangijin talikai kasa ranar da zamu dawo gareka ta zama ranar farinciki a gare mu, Allah kar ka sa mu mutu ɓatattu kasa mu mutu a tafarkin ka da na manzonka".
Abba jikinsa na rawa ya miƙe, hawaye na zuba a idonsa, Faruk ma kukan yake sosai suka miƙe, dan a ɗau gawar Hakimi, amma Nana ta gigice, ta miƙe jikinta na wata irin rawa, ta riƙe gawar Hakimi tana girgiza kai tace "Inna idan kika bari suka tafi da shi, ba zan sake ganinsa ba fa, Inna kakana a duniya waze mayen gurbinsa, dan Allah kar ku tafi da shi".
Gaba ɗaya ta gigice bata hayyacinta sam, surutai kawai takeyi, duk da jikin Sadik babu ƙwari haka ya miƙe, ya janye Nana daga jikin gawar Hakimi, ta shiga ture Sadik, amma ya riƙeta sosai a jikinsa se miƙa hannu take tana kuka, yai waje da ita.
Gidan ya cika da mutane sosai da sosai, Sadik ya wuce da ita wani ɗaki, ya zauna da ita a ƙirjinsa tana ta fizge fizge se ta ƙwace.
Sadik ya rungumeta tsam a jikinsa, ya shiga faÉ—in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" a kunnenta.
A hankali ta lumshe ido tana wani irin sauke nannauyan numfashi, a hankali ya kwantar da ita, sedai babu tabbacin tana hayyacinta.
Ko da Sadik ya fito har an fita da Hakimi, Sadik ya leƙa yace "Mother, maman Sahal tana can ɗakin ko zaki zauna da ita?".
Mother tace "to shikenan". Ta tashi ta tafi É—akin da Nana ke kwance, wadda a kwance kawai take ba tare da sanin a wani yanayi take ba, suma ko ido biyu.
A kaiwa Hakimi salla, aka kai shi makwancinsa.
Hakimi kam yai jama'a sosai da sosai da sosai, bayan an masa jana'iza ma haka mutane suka cigaba da zuwa gaisuwa.
Bayan an dawo daga kai shi, su Abba suka zauna a waje suna cigaba da karɓar gaisuwa, su Inna kuma na cikin gida, Inna ko iya amsa gaisuwar ba tayi, se jinjina kai kawai, lokaci lokaci ta share hawaye.
Mother se goya Sahal tai, se uban kuka yake yi, saboda yana jin yunwa, Mummyn Khairat ke taiwa Nana fifita.
Sadik yai sallama ya shiga É—akin yace "Mummy ba ta tashi ba ko?".
Mummy tace "kaga dai na kasa ganewa, a sume take ko idonta biyu?".
Sadik ya ƙarasa in da Nana ke kwance, ya ɗagota a hankali ya kira sunanta Husna.
Ta buɗe idanunta da sukai ƙanana ta kalleshi, sedai ba tace komai ba.
"Kina gani na?" Ya tambaye ta, ba amsa se binsa da take da ido.
"Meye yake miki ciwo?"
Nan ma ba amsa se ido kawai.
Khairat ta zubawa Sarautar Allah ido, yarinyar da suke kafsa uban faÉ—a da Sadik, itace Yanzu yake ririta ta a matsayin matarsa.
"Tabbas munyi babban rashi, mun rasa Hakimi, amma kowa na hakane duk zaman jiranta muke yi, dan Allah ki kwantar da hankalinki, muyiwa kakanmu Addu'a Allah ya sada shi da rahamar sa, halinsa na gari ya bishi, dan Allah Husna kiyi Magana bana son wani abu ya sameki". Yai maganar hawayensa na É—iga a kan kuncinta.