Sashe 71
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matsawa tai kusa da shi tana share masa hawayen, tace "dan Allah to ka dena kuka, Allah ze yaye maka damuwar ka, ka dena kaji"
Tai maganar tana zubar da hawaye, maimakon ya dena se ya kwanta a jikinta, yana jin kamar zuciyarsa za ta kama da wuta.
Sumar kansa ta shiga shafawa, tana cewa "Allah Ubangiji ya yaye maka damuwar ka, Allah Munyi tawassalli da sunayenka Allah ka yayewa yayana damuwar sa, ka iya 40 rabbana?" Ta tambaye shi tana kallonsa.
Girgiza mata kai yai alamar a'a.
Tace "Inna ce ta koyamin su, ta sa na haddace su, tace in dinga yawan yi, idan aka ɓatamin rai na karanta ina jin daɗin su sosai, bari in karanta maka kaji"
Ya jinjina mata kai, jikinsa ya É—au zafi , idanunsa sunyi wani irin ja kamar wuta, se jan numfashi yake.
Ta ɗora hannunta, akn ƙirjin Sadik saitin zuciyarsa, se da ta ɗan tsorata ko dai zuciyar Sadik ke ciwo, wani irin harbawa ta ji zuciyar ta sa nayi, da sauri sauri.
A hankali ta fara karanto Addu'oin rabbana rabbana da suke cikin Alqur'ani.
Hannayensa ya sa ya danna hannun Nana sosai a saitin zuciyarta sa yace "Nana ciwo take min, wani abu na barazana ga rayuwata da farincikina, ina jin kamar wani abu nawa me mahimmanci da yake neman rabuwa da ni"
Yai maganar yana kuka sosai kamar ɗan ƙaramin yaro, sosai ita ma Nana take kuka tace "duk abunda yake naka ne, in dai rabonka ne se ka same shi, insha Allah ba abunda ze same ka, yi shiru in karanto maka Addu'oin"
Yai shiru tare da rungume hannayenta sosai a ƙirjin na sa, har ba ya son ta motsa hannun na ta.
Nan ta shiga karanto masa Addu'oin, ya lumshe idanunsa ya na sauraren ta.
Wani irin releif ne ya shiga ratsa Sadik, a hankali ya fara jin sassauci daga tsananin bugun da zuciyar ta sa take yi.
Jin Nana tai Shiru ne ya sa yace "Nana"
Tace "Na'am, ya kake ji yanzu?"
"Alhamdilillah, Nagode sosai naji yana min sauƙi, ki sake karanta min"
"To Alhamdilillah, amma ka san wani abu?"
Yace "A'a"
"Na san za ka ji haushi, amma gara in gaya maka, Aboki Inna ta na gayamin, a duk lokacin da mutum yai nesa da Allah, abubuwan damuwa suna zuwa su dami rayuwarsa, amma idan mutum yana tare da Allah a ko yaushe, to abubuwa na zuwar masa da sauƙi.
Ka ga ba kullum kake salla a jam'i ba, kuma alhalin ba mu da nisa da masallaci sosai, kuma idan ka salla ko tasbihi ba ka yi, shafawa kawai kake ka tashi, balle Azkar É—in safe da yamma.
Alqur'ani ko ba ka karanta ba, ka kunna a wayarka ka saurara, insha Allah zaka dinga samun mafita a cikin Al'amura.
Sannan wannan yawon kallon ball É—in da kake ba yau ba gobe, da yawon darw duk ka dena su, ni Allah ya sa ma ba aljanu ne suka kama ka ba*.
Duk maganganun ta da take, idanunsa a rufe suke, se da tai maganar aljanu Sannan ya buÉ—e idonsa ya kalleta yace "ubanwa Aljanun suka kama??"
Tace "Ni bance sun kama ka ba, cewa nai Allah yasa ba su bane"
"Nafi ƙarfin aljanu su kamani"
Nana tace "da kana Azkar ne se kai wannan cika bakin"
"Dan kin ganni akan cinyar ki kike gayan magana ko?"
Tace "haba Aboki, ni na isa in gaya maka Magana, Allah ya baka haƙuri gaskiya nake gaya maka ne, zamu dinga karanta rabbana nan tare, har Allah yasa kaima ka haddace ka dinga karantawa"
"Naji, amma dai yanzu cigaba da karanta min"
Murmushi tai tana jinjina rigima irin ta Sadik, shi da ta samu a galabaice amma harya samu kansa ze fara masifa.
Tana cikin karanta masa karo na biyu, bacci yai awon gaba da shi.
A hankali ta zame kan Sadik daga cinyarta, ta sa masa pillow, ta tashi ta ja masa ƙofar ɗakin nasa, ta koma na ta, tana masa Addu'a Allah ya ba shi mafita akan abunda yake damunsa.
A hankali ta motsa, ta buÉ—e idanunta da suke mata wani irin yaji, ga kanta da take jin tamkar ba na ta ba, tun tana gani dishi dishi, har Idonta ya fara washewa, se dai ba ta gani clearly.
Kwance take a wani ɗaki, da ba ta san ina ne ba, ta tashi zaune akan gadon da take kwance, ta ƙarewa ɗakin kallo.
Hijjabin ta ta gani a gefe a yashe, ga kamta babu ɗan kwali, ta janyo hijjabin ta ta saka, ta yunƙura ta miƙe tsaye, sedai tsaiwar ta gagare ta saboda yadda take tangaɗi.
Ƙofar fita daga ɗakin ta nufa, ta buɗe ta fito, duk wata gaɓa ta jikinta ciwo take mata, tana tafe tana nema tai karo da bango, a haka ta fito harabar Hotel ɗin.
Safiya ce wajen ƙarfe Goma na tara, haka ta dinga tangaɗi, ta na ƙoƙarin fita daga cikin Hotel ɗin.
Wata mota ce ta dinga mata horn, amma ta rasa daga ina motar take mata horn É—in.
"Ohh Allah yayi yau ma mun kuma haÉ—uwa"
Duk da maye take, amma ta gane shi, mutumin jiya ne, da yaita mata magana ta ƙi kula shi"
Yace "ina zaki ne?"
Ta ɗan yatsina fuska tace "gida zani" ta ƙarasa maganar tana dafe kanta.
"Ina ne gidan?" Ba musu ta kwatanta masa.
Yace "to muje in sauke ki, be kamata ki fita kina maye ba"
Ba musu ta bi shi Mota, ta shiga gaban mota, tun da ta shiga ta kifa kanta, yaita mata magana amma ba ta kulashi ba.
Tiryan tiryan da ya bi kwatancen nata, se ga su a ƙofar Gidan su Farhan, layinsu shiru babu kowa.
Ta fara ƙoƙarin buɗe motar ta sauka yace "gashi mun zo amma ba ki gayan ko sunan ki ba"
"Dan Allah ka ƙyaleni" tai maganar tare da buɗe motar ta fita, ta nufi gidan su.
Yace "Ikon Allah, wannan 'ya akwai mulki"
Da ta shiga gidan shiru, babu kowa ko sallama ba tai ba, ta wuce É—akinta, ta zube akan katifarta ta cigaba da bacci.
Kusan mintuna ashirin, Farhan taji muryar ƙaninta Ameer yace "Laaa Umma kinga Yayan a ɗakinta tana bacci"
Umma a gigice tace "dagaske?" Tai maganar tana ƙoƙarin leƙa ɗakin Farhan, aikuwa ita ɗin ce.
Tace "kira babanku kace masa ga ta ta dawo"
Tun da suka farga ba ta gida, ake nemanta tun jiya, har gurin 'yan sanda aka shigar da report, ana ta cigiya ana nemanta, lokacin da ta dawo ma, Abba ya tafi gurin 'yan sanda, Umma kuma ta na bin gidajen 'yan uwa ko za'a sameta.
Ba a jima ba sega Abba yace "Ina Farhan É—in take?"
Ya leƙa ɗakinta ya ganta a sharɓe tana bacci, take jikinsa yai sanyi yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah na san wannan jarabtace ka jarrabe ni, Allah ka shirya min 'ya ta" yai maganar idonsa fal ƙwalla, ko ba a gaya masa ba ya san a cikin maye Farhan take saboda surutan da take.
Ya koma ɗakinsa, wata irin ƙwallar baƙin ciki ta taru a idon sa, Umma ta biyo shi tana Malam meye abun yi akan Yarinyar nan, ni kam na gaji da wannan lamarin, ba yau ba gibe ta dinga janyo mana abun Magana".
Abba ya girgiza kai yace "kiyi haƙuri, muyi shiru da bakinmu mu dinga mata addu'a, takura ko tsauri ba za suyi aiki ba"
Cikin kuka Umma tace "kaga irin abunda nake ji ko? Da an haƙura anyi Auren nan da shikenan, koba Komai tana can Asirin mu a rufe, amma yanzu watan tonon Asirin mu ya tsaya, Malam kwana fa tai a waje, a ina ta kwana?"
Abba yace "kar ma ki kuskura ki tambaye ta a in da ta kwana, ba abunda hakan ze haifar banda ɓacin rai, muyi mata Addu'a Allah ne ya jarrabe mu, na san jarabta ce, yarinya ta me hankali ce da tarbiyya, Allah ya shirya ta"
"Shikenan, babu wani mataki da zaka É—auka akan ta?"
Abba yace "to in ba addu'a ba, so kike in tsine mata? Ko kuma in koreta ta bar min gida? Addu'ar dai ita ce mafita"
Umma ta dinga kuka, Abba na mata nasiha, saboda hawayenta masifa ne a Rayuwar Farhan.
Se bayan la'asar Farhan ta gama dawowa hayyacinta, taje tai wanka ta jera sallolin da ake binta, ba tare da shakkar laifin da ta aikata ba, ita babbar damuwarta haÉ—a salloli da tai.
Shiru tai tana ƙoƙarin tuna abunda yafaru da ita, Gabanta ne yai mummunar faɗuwa da ta tuna, taje tana jiran Babba ya bata magani ne, aka ba ta ruwa ta sha, daga nan ta farka ta ganta a ɗakin Hotel.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyafaru da ni to? Meya sameni, me sukayi min? Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah yasa ba keta min mutunci su kai ba, naiwa Sadik Alƙawarin komai daren daɗewa ba wanda ze mallake ni se shi"
 'ji banza, yana can yai Aure, maimakon ki ta kanki, amma ke ta wani Sadik kike, bayan shi yana can yana shagalinsa' wata zuciyar ta tunatar da ita.
Wani irin gumi ne ya shiga keto mata, jikinta ya hau rawa, kenan bugar da ita sukai, su kai mata fyaɗe? Shikenan mutuncinta da kimarta, Mubarak ya yaudareta kenan, sun haɗa kai da 'yan ajinsu sun cutar da ita, shiru tai ta shiga tunanin yadda ake labarin taƙadirancin Mubarak.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un" shine abunda Farhan ta faɗa tare da dafe kanta, ta fashe da wani irin gigitaccen kuka, tabbas ta ta ta zo ƙarshe rayuwarta ta ɓaci.
"Wace irin masiface haka take bibiyata, da ga wannan se wannan, shikenan ba ni sa sa'a rayuwa ta? Astagfirullah wa atubu ilaih" ta shiga jujjuya kanta da ya riga yai mata Wani irin nauyi.
Da safe har Nana ta tafi Makaranta, Sadik baccin sa yake, tun da yai sallar Asuba ya koma gado ya naÉ—e ya cigaba da baccin sa.
Ba ta tashe shi ba, saboda yadda ya sha wahala jiya kan yai bacci, dan haka kawai ta tafi makaranta.
Ko da ta dawo gida, Sadik ba ya nan, nan ta tabbatar da lallai ya samu lafiya, tun da harya samu ƙafar yawo.