← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 115

Sashe 15

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai naga mun gaisa, idan na makara za'a iya dukana a makaranta"

"Eh to kuma hakane, amma ba kya iya jure bulalar malam saboda ni ba?"

Ba ta san lokacin da tsaki ya kufce mata ba, dan ji take kamar ta zabga masa mari.

Tace "kaga se an jima, Makaranta zan zo in tafi"

Ta juya ta koma cikin gida zuciyarta na mata wani irin tafasa.

Tana shig gida Umma tace "harya tafi ne?"

"Eh ya tafi, lokacin tafiya makaran yayi"

Umma tace "naga se takwas kuke shiga, yanzu kuma bakwai da kwata"

Farhan tace "eh dama zuwa yai kawai mu gaisa, kuma yai min Sallama ya tafi"

Umma tace "shieknan, Allah dai ya tabattar da al'amrin nan, ayi ai Auren nan kowa ya huta, dan da babanki ze Amince tun yanzu a karɓi kuɗin asan da ƙwaƙwƙwarar magana"

Farhan É—akinta ta shiga tana ba Ameen ba a ranta.

"Ya Allah karka tabattar da wannan lamarin, Addu'a iyaye ga 'ya'ya ba ta da hijabi a gurinka, Allah ka tabattar min da Alkhairi, Amma Allah ka rabani da wannan sunusin bana son sa, Allah kai ka É—ai zan iya gayawa, kai kayi unarni da bin Iyaye, ina musu biyayya daidai gwargwado, ya Allah ka rabani da wannan bawan"

Haka taita Addu'a, muryarta ƙasa ƙasa tana goge hawaye.

Takwas saura mintuna, ta saka hijjabinta na makarantar dare, ta shafa turaren humra me sanyin ƙamshi, ta shafa ta ɗau jakar Islamiyyar ta, daga  tsakar gida kawai ta iya cewa Umma na tafi, ta sa kai ta fita.

Jefa ƙafarta kawai take, tana share hawaye lokaci lokaci, ba zato ba tsammani, kamar daga sama wai anwa wada ƙwace,se ji tai an janyo hijjabin ta ta baya da ƙarfi ta faɗa jikin mutum.

Ware murya tai za ta ƙwala ihu, kasancewar ba kowa a lungun, ammma yadda ya toshe mata baki ya hanata yin hakan.

(Mubarak Babba 🥺)!

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. 
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Ƙamshin turaren sa ne ya fahimtar da ita waye.

"Matsoraciya kawai, komai seki fara ihu"

Ture hannunsa tai, ta ƙwace tana tura baki.

Fitilar wayar sa ya É—akko ya haska fuskarta yace "ya naga kamar ma kuka ki kai"

Yana faÉ—an haka kamar ya tuna mata, se ga wani hawayen na zubowa.

"Farhan lafiya kuwa?"

Cikin shagwaɓa tace "ba kaine ba, kace zaka dimga zuwa ka ganni, amma tunda muka rabu ranar ba ka sake zuwa ba, se damuwa nake".

Murmushi Sadik yai yace "nima ai a cikin damuwar nake, tunanin ki ya hana ni sukuni, nayi tunanin zaki kirani a waya ma, tunda kince in ba ke kika kirani ba kar in kira ki, na É—anyi rashin lafiya ne.
Kuma yau tunda na tashi na kasa nutsuwa, ganinki kawai nake son yi, na daÉ—e a gurin nan ina sa ran ganin wucewar ki, in samu in ganki"

Ta sauke numfashi tace "to kaji sauƙi?"

Yace "Alhamdilillah, na warware kina lafiya dai ko?" Ta ɗaga masa kai tace "lafiya ta ƙalau, kawai ganinka nake son yi"

"To ba gani ba nazo, ko dai haryanzu fushin ne?"

Ta girgiza masa kai sannan tace "Mu bar nan gurin kar wani ya ganmu a gayawa Abba.

Yace "ok, mota na ta titin bayan layin nan, muje can ba Wanda ze ganmu"

Tace "Makaranta fa zani"

"Ba daÉ—ewa za muyi ba, ganinki kawai zanyi seki tafi"

Tace "to"

Ta bi Sadik zuwa Mota, suka shiga gaban motar da yake motar me tint glass ce, ba me ganin su, ya kunna musu fitilar motar.

Ya dubeta yace "ya makarantar?"

"So boring duk ba daÉ—i"

Yai murmushi yace "nima fa ji nake dama ban gama yanzu ba, wallahi ba ki ji yadda kewarki ta dameni ba, gashi ke ba waya ba balle mutum ya neme ki a waya"

"To ya zanyi tunda ba'a bani ba?"

Sadik yace "da yadda za'ai" yai maganar tare da sa hannu a aljihunsa, ya ɗakko sabuwar waya me madannai(keypad) ya miƙa mata.

Ta sa hannu ta karɓa tana kallonsa.

"Ki ɓoye wannan, akwai layi a ciki, duk lokacin da kika samu dama ki kirani, amma ba zan iya jure yin nesa da ke sosai, ba tare da ko jin muryarki ba"

Farhan tace "Tsoro nake ji, kar a ganta a gida fa"

"Ki ɓoyeta Farhan, in da ba wanda ze gani please, ina missing ɗinki Sosai" ya ƙarasa maganar yana marairaice murya.

Tace "shikenan, zan ɓoye Allah yasa kar a ganta ɗin, idan aka ganta ban san ya zanyi ba*

"Babu ma wanda ze gani insha Allah, ki kwantar da hankalinki kinji my wife"

"To Allah yasa kar a gani É—in"

Yace "Ameen, ko tex ne se ki dinga yi min, my lovely"

Farhan tai murmushi tana jujjuya wayar.

"Kinga ba dan a ɓoye na baki wayar nan ba, ai da Babbar waya zan sai miki ta manyan yara"

"Manyan yara, ai kune manyan yara nikam ba babbar Yarinya bace"

Sadik yai dariya yace "Babbar yarina ce ke Farhan, you are very beautiful, and at the same time kina da innocent soul kina da hali me kyau shiyasa nake ta kula, bana son wani ya ƙwace min ke, dan Allah Farhan ki dinga mana Addu'a, Allah yasa kar a rabamu, Allah ya tabattar mana da Alkhairi a tsakanin mu"

A zuciyarta tace "Ameen" Amma a fili tai shiru.

"Farhan ba ki ce Ameen ba, ko ba kya sona ne?"

Noƙe masa kafaɗa tayi.

Yace "ok faÉ—i Ameen in ji"

"Nifa na faɗa a raina" tai maganar a shagwaɓe.

"Ni ban ji ba ki faÉ—a inji" yai maganar yana kwaikwayon muryarta.

"Uhmm ka bari"

"My Lovely baby, wannan shagwaɓar taki is killing me"

Ya É—akko wata leda, cike da kayan ciye ciye na chocolate yace "ungo ke na siyowa wannan"

"Ta ya zan shiga da Wannan gida? Idan aka ce a ina na samo fa?"

"Kice mijinki ne ya baki, ai ba a shiga tsakanin miji da mata"

Zare ido tai ta kalleshi.

Yaxe "eh mana, tunda ke dai baki da wayo, ga jakar Islamiyyar ki nan ga ƙaton hijjabi, kisa a ciki mana"

Ba ta san yawan yi masa musu, dan haka ta karɓa tace ta gode.

Islamiyyar da Farhan ba taje ba kenan, ta zauna suka cigaba da hirar su a mota.

Seda lokacin tashin su daga Islamiyya yayi sannan yace bari ya rakata bakin layin su.

Suka fito daga motar, ya rakata har bakin layin, sannan ya juya ya tafi.

Zuwan Sadik duk ya mantar da ita wata damuwa da take ciki.

Sedai ta na zuwa gida ta fara fargabar kar a gane ba taje makaranta ba.

Da daddare ta tura ƙofar ɗakinta, ta ɗakko wayar nan, ta saita komai a silent.

Tana cikin saitawa se ga message É—in Sadik "Hi sweetheart, kinyi bacci ne?"

"No banyi bacci ba, ya kaje gida?"

"Lafiaya ƙalau Alhamdilillah, meya hanaki bacci har wannan lokacin?"

"Thinking of someone very important to me"

"Wow, who is that lucky?"

"Youuuuuuuu"

Abun mamaki, Farhan ta zage suka dinga hira kamar ba ita ba, da yake ba a gabansa bane, ta dinga tura masa saƙonnin soyayya.

Har kusan ƙarfe ɗaya na dare, sannan su kai sallama, ta je ta ɓoye wayar.

Sedai bayan sunyi sallamar Sadik ya shiga aikin nasa na tunani, kullum sake jin Farhan yake a cikin zuciyarsa, sedai ya kasa tuna menene mafita akan wannan lamarin, ya rasa ta ina ze fara samun mafita, ga tafiya zeyi Gashi yasan ko giyar wake ya sha, Babu yadda za'ai Farhan ta jira shi tsawon shekaru bakwai ba tai Aure ba, ga ƙudurin iyayenta na son Aurar da ita da zarar ta kammala Makaranta, gashi ya rasa goyon bayan iyayensa akan abinda ke damun sa.

Lilly kam tai ta É—ar É—ar ko Mamanta za tai noticing wani canji a tare da ita, amma taga sam mamanta ba ta fuskanci komai ba dan haka Kamar wasa, Lilly da Nazir suka koma suka jone kamar yadda suke a baya.

Sema sake samun kusanci da su kai da juna fiye da baya.

Farhan ta cigaba da zuwa Makarantar ta, wasu lokutan da wayar take tafiya makarantar, idan an fita break ta É—au wayarta ta samu wani gurin, suyi ta waya da Sadik.

Yau kamar yadda ta saba tai wayar ta gama, zata koma aji taga Mubarak Babba ya zo makarantar, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, dan yace in dai yana raye seya rama marin nan da tai masa.

Aka tashi daga Makaranta, ta kasa ko fitowa daga aji saboda tsoron ba ta san meze mata ba.

Da ƙyar ta samu ta fito daga ajin, tana waige waige da niyyar ta samu dama ta gudu gida, yau take sake ganin Ranar Sadik a makarantar nan, duk abunda ze faru ba wanda yake raɓarta saboda a na tsoron sa.

"Leƙe leƙen me kike? Gani nan a bayan ki, dama ai dan ke nazo"

A razane ta waiwayo taga Mubarak Babba, a tsaye ya zura hannayensa a cikin aljihun wandon sa.

Razana tayi taja ta tsaya tana kallonsa.

"Ke da kin ɗauka da wasa nake da nace sena rama marin da ki kai min, ko a zatonki ƙarya nake da nace sena samu abunda nake so a tare da ke?" Yai Maganar yana takowa gabanta, ita kuma tana ja da baya, har ta kai bango.

"Yanzu ai gaki, ba wannan shashashan da kike taƙama da shi ze tare miki, ba abunda zan miki a yanzu, saboda nan be dace da gurin ɗaukar fansa ba, amma ko a jima ko a daɗe zamu gauraya, ina nan akan bakana, sena ƙetara abunda Sadik a kasa ƙetarawa"

Yai maganar yana dariya da ƙoƙarin kai hannunsa fuskarta.

"Kai Mubarak meye haka?" Da sauri Mubarak ya waiwaya, yaga Amin.

Amin yace "meye haka kake ƙoƙarin yi ne?"

Babba yace "ina ruwanka da abun da nake ƙoƙarin yi? Ina taya kaya ne"
Chapter 15 · 0% Book details