← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 115

Sashe 52

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watarana anyi karatu a aji, Malamarsu Nana tai mata tambaya, gashi ta san amsar tambayar amma ta kasa bayarwa, saboda tunanin yadda zata haɗo turancin tayi, kawai se 'yan ajin suka kama yi mata dariya ganin yadda tai wiƙi wiƙi da ido, tana tura baki, wani irin takaici ya kama Nana, kawai ta fashe da kuka, ga mamakinta se taga hankalin malamar ya tashi tana ta bata haƙuri tana rarrashin ta.

Nana ta fuskanci ana bawa ra'ayin É—alibai mahimmanci sosai da sosai, ga ba duka ba zagi a harkar koyarwar ta su.

A hankali Nana ta fara sabawa da su, ta dage sosai tana ƙoƙarin mayarwa idan a kai mata turanci.

Yanzu tana hira da Linda sosai, dan bayan Lindar ma har wasu ƙawayen tayi, amma ɗabi'arta ta yawo da hijjabi na nan ba ta dena ba.

Mutane na ta shigowa yiwa Umma Allah Sanya Alkhairi yayin da a unguwa ake tayi da su, wai wannan 'yar yarinyar za'a aurawa Sunusi, wasu sukace Asiri yaiwa iyayenta, wasu suce ita yarinyar ce yaiwa Asiri take son shi, kowa da abunda ze faÉ—a.

Hajiya ma ba a barta a baya ba, Wajen zuwa yiwa Umman Allah Sanya Alkhairi,  sedai se da tai ƙorafi tace "Umman Farhan, meyasa za'a aurar min da Farhan yanzu, tayi ƙanƙanta kuma karatun ta fa?"

"A'a ba haka bane, kin san sha'anin rayuwa da kuma yanayin yaran namu na zamani, kamata yai da sun kawo ƙarfi a kauda su"

"Hakane Maganar ki, amma ai ki godewa Allah, kinga Farhan nustsatsiyar yarinya ce, ba ruwanta da hayaniya irin ta yaran zamani, wallahi ki gode Allah amma yaran zamani suna kangarewa son ran su, amma kinga ke taki a nutse take kamar ke kika zaɓowa kanki"

Umma a ranta tace 'wannan É—in ma dan ba ki san halinta bane'

A fili kuma tace "hakane, amma lokaci ne, idan yazo se anyi"

"Haka yake, amma ze bar mana ita ta ƙarasa karatun ko? Dan ba wanda yasan abunda Allah ze sa ta zama nan gaba"

"Eh yace ze barta, ai ba wani ne a nesa ba fa, Sunusi ne"

Hajiya tace "wane Sunusin?"

"Yaron nam dai Sunusi, Almajirin Malam Labaran"

Hajiya tai galala tana kallon Umma tace "Wannan baƙin yaron me doguwar ƙeya?"

Umma se taji ba daÉ—i abunda Hajiyar ta faÉ—a, amma ta maze tace "ba ruwana sirikinki me dai"

Hajiya tace "Ni ko me Farhan ta gani a jikin wannan tsotsatstsen mutumin? Haba Umman Farhan dan Allah, kyakyawar bafullatanar Yarinya me tarbiyya kuma a rasa wa za'a bawa se wannan"

Umma tace "kayya, banda abunki Hajiya, ai albarka ake nema a aure, su kyawawan, ko masu arzikin nawa aka aura amma Auren beje ko ina ba? Kuma naga ai shima mutum ne yaron, kuma gashi nutsatse ne"

"Eh albarka ake nema a aure tabbas, amma gaskiya wannan haɗin be ba, kowace ƙwarya akwai abokiyar burminta, amma shikenan Allah ya Sanya Alkhairi ya sa ayi da mu".

"Ameen ya Allah, dama addu'a dai ita ce"

Hajiya na shirin tafiya, Farhan ta shigo daga Islamiyya, tana tafe sannu a hankali kamar ba ta taka ba.

Tana ganin Hajiya tai murmushi tare da gaida Hajiyan.

Seda Hajiyan ta ƙare mata kallo cike da tausyawa, sannan ta amsa tace "Ashe kuma abun Alkhairi ya samu, to ubangiji Allah ya sanya Alkhairi ya kaimu lokacin"

Farhan tai murmushin yaƙe, tare da ƙoƙarin danne wani irin ɗaci da ya taso daga ƙasan zuciyarta, yake ƙoƙarin fallasar da zunzurutun damuwar da ke cikin ƙirjinta, ta hanyar kwaranyowar hawaye, ta nufi ɗakinta.

Kasancewar ba ta salla, har a kai sallar magariba ba ta fito daga É—akin ba, se da akai sallar isha'i sannan ta fito ta tafi makarantar dare, sedai ta layin da Sadik yake ajiye mota tabi, ji take kamar za ta ganshi, sedai gurin wayam, ba motarsa da yake tursasata ta shiga ko yace ze É—agata ya sata motar, mussaman idan su kai faÉ—a.
Duk da wasu abubuwan da suke a cikin motar ya saɓawa ƙa'ida, amma makauniyar soyayyar da ke cin ranta da kuma RUƊIN ƘURUCIYA ya sa take mantawa da hakan ta biyewa Sadik.

Barandar wani gida ta samu ta zauna, ta haɗa kai da gwiwa ta na wata irin sheshsheƙa, ga hawayen kirki yaƙi ya fito se ajiyar zuciya da take ta jerawa.

"Dan Allah Sadik ka dawo, zuwa yanzu zuciyata tayi rauni, ba zan iya jurewa ba Komai ze iya faruwa da ni, ina kewar ka Sadik"

Makarantar da ba ta je ba kenan, se da tai kuka me isarta, lokacin tashi yayi Sannan ta taho gida.

Tana cikin wannan yanayin, ta shiga É—aki ta kwanta, akai sallama wai Sunusi yana nemanta, kuma Umma ta bada amsar tana zuwa.

Tai shiru a É—aki, seda Umma tai mata Magana Sannan ta tashi ta fita.

Kamar yadda ta saba, tana zuwa ta ja guri ta tsaya, ta É—auke kanta.

Yai murmushi yace "Amarya ba kya laifi, yanzu kin yadda kin zama tawo ko?"

"Allah ya kiyaye, idan wannan tunanin kake tun wuri ka dena, har Gaban Abada ba zan taɓa zama taka ba"

"Zancen banza kenan, ai tunda mahaifin ki ya riga ya karɓi kuɗin Aurena da ke, ai aikin gama ya gama, fatiha kawai tai mana saura, baɗi i yanzu in da rai da lafiya kina nan kin haihu ko kin kusa"

Wani irin kallon banza taiwa Sunusi, muddin ta aureshi ba abunda ze hanata shan guba ta mutu, tai saurin kauda wannan tunanin daga ranta, dan sheÉ—an kar yai tasiri a zuciyar ta.

"Dan Allah ki kwantar da hankalinki, wannan É—an yaron da kike biyewa ba Aurenki ze ba, dan ba sonki yake ba, Yaushe rabon da ya zo in da kike, ni É—in ne dai nine me sonki" yai maganar yana dariyar mugunta.

"Ko Sadik ya zo in da nake, ko be zo in da nake ba, zuciyata da tasa abu guda ne, da zasu kasance da juna har ƙarshen rayuwa, kuma babu wani namiji da ze taka matsayin da Sadik ya taka a zuciyata"

Nan da nan Sunusi ya fusata, yace "Ni kike gayawa haka? A gabana kike zancen wani sakarai?"

"Kai ne sakarai ba shi ba, ni mallakin Sadik ce, ba zaka taɓa samu na ba, kuma yadda ka dage kake ƙoƙarin Mallaka ta ta ƙarfin tsiya bayan ka san bana sonka, kaima Allah ba ze ji tausayin ka ba, Allah ya saka min, ba zan taɓa bijirewa zaɓin iyayena ba, amma zan dawwama ina maka Addu'a Allah yai maka abunda kai min" tana gama maganar cikin huci fuu tai gida.

Be taɓa zaton Farhan na da baki haka ba, ba ta taɓa masa rashin kunya Kamar haka ba, maganar ma ba son yi take ba, amma yau ta wanke shi tsaf ta nanata masa ba ta son shi.

A hankali ya fara jan silifas É—insa, ji kake sharaf, sharaf, sharaf ya nufi makwancinsu.

"Baban Soyayya, anje gurin amaryar ne?" Haladu yai maganar yana dafa kafaÉ—ar Sunusi.

"Bari Haladu ina cikin damuwa wallahi"

"Damuwar me kuma, kai daka kusa zama Ango?"

"Bana tunanin Aikin da nai akan Yarinyar nan ya kamata, yauma ta sake jaddada min ba ta sona, wancan yaron take so"

"Too, ikon Allah abun be kamata ba kenan?"

"Alamu sun nuna hakan" Sunusi yai maganar cikin damuwa.

"Aikuwa ina tunanin ita ma ba haka take zaune ba, dan haka seka sake sabon shiri".

"Hakan za'ayi Haladu, zan sake shiri dole kan bikin nan, dole ta fara sona"

"Gaskiya ne, se ka bada himma"

Ɓangaren Lilly ma, abun duniya ya isheta sosai, yadda babanta yaci mutuncin Nazir ba ta ji daɗi ba sam, ta ƙallafa rai akan ze mata aure kamar yadda ta buƙata, amma ya watsa mata ƙasa a ido, gashi a yadda take ji gaskiya ba zata iya rabuwa da sir Nazir ba.
Gaba daya kunyar yadda zata tunkare shi ma take ji.
Ta kirashi ba adadi, amma yaƙi ɗagawa ta tura masa tarin saƙonni, nan ma ba wanda yai mata reply, ta whats app ma duk be duba messages ɗin ba balle yai mata reply.

A ɓangaren sa kuwa, yaji zafin abunda mahaifin Lillyn yai masa sosai da sosai, ta wani ɓangaren kuma yaji gara ma da akai haka, shikenan ya huta ba shi ba Auren Lillyn, kowa se ya kama gabansa.
Amma da yake Allah ba Azzalumin sarki bane, se wata irin soyayya da ƙaunar Yarinyar suka sake shigarsa, kwana biyu da ba ya amsa wayarta ma, jinsa ya dinga yi kamar a prison, Tabbas shigowar Lilly ratuwarsa ƙaddara ce.
Tabbas rabuwa da ita ba abu ne me sauƙi ba, dan sunyi sabo ba ƙarami ba, ga kusanci da suke da shi da juna.

Se da ya jera kwanaki biyu, ba ya zuwa makarantar, abun ya ƙara damun Lilly Sosai da sosai, se a rana ta uku sannan ya zo, ranar shi ze shiga ajinsu first period, kallo ɗaya tai masa ta san ba ya cikin walwala, dan ransa a haɗe yai lesson ya fice ko in da take be kalla ba.

Yana fita da 'yan mintuna, ta bi bayansa ta tarar da shi yana marking papers, yana ganinta ya haÉ—e rai sosai ya cigaba da abunda yake, ta ja kujera ta zauna.

Ba tare da ya kallet ba yace "can You Please excuse me, i have something to do now"

"Korata ka ke?"

"Me ze sa ba zan koreki ba, haka shine masalaha ai"

"Amma ai ba ni nai maka laifi ba, babana ne"

Ya ɗago ya kalleta yace "amma ta sanadin wa akai min, ok dama kin gayyace ni gidanku ne dan a ci min mutunci, a ci zarafina? Kin san mahaifinki ba ze amince ba kika sa naje ya min wulaƙanci?"

"Dan Allah ka fahimceni, wallahi be nuna min ze maka haka ba, kawai yace min yana son ku gana ne, wallahi ban san haka ze ma ba, ni kaina banji daɗin abunda yai maka ba dan Allah kayi haƙuri"

"Naji na haƙura, amma daga yau kawai mu haƙura mu yanke duk wata alaƙa da ke tsakanin mu, tun da mahaifinki ba ya so, kar inje ya sa a kassarani, ni kaɗai ne namiji a gurin mahaifiyata"
Chapter 52 · 0% Book details