Sashe 90
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Komawa yai ya cigaba da lissafin ta in da ze ɓullowa Farhan, ko sau ɗaya ta yadda ta saurare shi, taji uzurinsa, yayi mamakin yadda ta rufe ido ta nuna ba ta ko ƙaunar ganinsa, tabbas be kyauta mata ba, amma har ga Allah idan Farhan ta guje shi be san yadda ze yi ba, saboda yana matuƙar ƙaunar ta.
Farhan kuwa suna tafe a hanya tana rera kuka, ga hannunta na ta zubda jini, Asibitin su Abbas ta sa me Napep ya kaita.
Ta sauka ta biya shi kuÉ—insa, ta shiga sedai Abbas É—in baya nan, wata Nurse tace bari suyi attending É—in ta ai dressing É—in hannun, amma tace ita Abbas take nema, ga wayarta ta É—auke ba caji, da wayar Asibiti ta kira shi, ta sanar da shi cewar ga ta a Asibitin su tana jiransa.
Ai cikin hanzari ya kamo hanyar zuwa Asibitin, saboda yadda yai kwanaki yana zuwa gidansu bata nan, kuma taƙi yadda ta gaya masa in da take.
Yana zuwa ya tarar da ita a reception, ta naÉ—e hannunta da mayafinta.
Da hanzari ya ƙarasa in da take yace "Farhan, ya akayi ne lafiya kuwa?"
Idon ta fal ƙwalla tace "ciwo naji"
Yace "subhanallah, garin yaya? Meyasa baki bari an duba ciwon kan in zo ba?"
Ta share hawayen fuskarata tace "saboda so nake ai min a hankali, kuma na san kai a hankali za kai min"
Yace "ok to shikenan, mu shiga emergency in duba"
Ta miƙe, yana tafe tana binsa a baya, har suka shiga, ta kwance mayafin, ya fara duba ciwon, ya kalleta yace "dame kika ji wannan ciwon?"
"Kwalba" ta ba shi amsa kai tsaye.
"Garin yaya?"
Shiru tai ba tace komai ba, duk yadda yai ta gaya masa amma ta ƙi, ya ƙyaleta yai mata dressing, ya ɗakko mata magani, da jakar kayanta da ta zo da ita, ya kai motarsa tana biye da shi zuwa motar.
Sam Abbas be mata maganar a ina take kwana ba, da rashin É—aga wayarsa se ma sannu da yake ta jera mata.
Suna tafe amma tai shiru, tana ta saƙawa tana Warwarewa, gani take kamar har yanzu abubuwan da suke faruwa sharrin ƙwayoyin da take sha ne, amma ba Sadik ta gani a zahiri ba.
Har sukaje gida ba ta ce masa uffan ba, ta sauka ta É—au jakarta ta ta kalleshi tace "Nagode sosai doctor, Allah ya saka da alkhairi" be amsa ba se É—an tsura mata ido da yayi, sannan yace "ki kula da kanki sosai, ki kula da shan magani"
Ta jinjina masa kai ta wuce, Umma na tsakar gida tana aiki Farhan ta zo tai salama ta wuce, ta amsa mata ba tare da ta kuma ce mata koma ba, ita ma Farhan ba tace koman ba ta wuce ɗakinta, ta samu guri ta zauna a gefen katifarta, ta dafe kanta tai shiruu tana sake tunani tabbas Sadik ɗin ne dai ya ke ƙoƙarin dawowa duniyarta.
Tabbas dawowar Sadik duniyar ta barazana ne a gareta da ka iya jefata cikin wani mawuyacin hali wanda yafi wanda take ciki a yanzu.
Ta miƙa hannu ta janyo pillow, ta kwanta a kai tai shiru, wasu irin hawaye da bata san dalilin zubarsu ba suka shiga zarya da rigr rigen fitowa daga idonta, ko a mafarki ba ta taɓa tunanin za ta sake sanya Sadik a idonta ba.
Gaba É—aya Lilly a takure take da zaman cikin barrack É—in nan, makaranta kawai take zuwa, shima a kaita a É—akkota, gashi ba ta saba da mutan gidan ba sam, ga wata irin kewar gida take yi, gani take kamar sun manta da ita gaba daya, a sati sau É—aya tak Major ya bada umarnin ai waya da ita daga can gida.
Babban abunda ya tayar mata da hankali be wuce wani babban soja da kusan sa'an su Daddynta ne ba, da ya nuna yana sonta, tun da ya ganta a barrack É—in, yake sintiri a nan gidan da take, kuma Abokin Daddynta yace ya saurare shi zeyi magana da Daddynta, abunda yace shikenan.
Hankalinta a matuƙar tashe yake, ta san yadda Daddy yake a ƙulen nan da ita, amsa wa wannan sojan shi yafi komai sauƙi a gurinsa.
Sir Nazir kam shekaru uku aka yanke masa a gidan yari, da biyan tarar naira dubu ɗari da Ashirin na abunda ya aikata, in da Allah ya rufa masa asiri a case ɗin ba fyaɗe akace ba, lalata ne da ƙaramar yarinya da kuma zubar da juna biyu.
Shi kansa me makarantar ya rabauta da watanni takwas a gidan gyaran hali, ba tare da zaɓin tara ba, kuma aka kulle makarantar sa kullewa ta har abada.
Ko da garin Allah ya waye, Farhan ta farka da ga Bacci, ta duba hannunta tagan shi da ciwo, hakan ya sake tabbatar mata ba sharrin ƙwaya bane, Sadik ne dai ta gani ya dawo gareta.
'kinyi haukane, mutumin da ya gujeki yaje yai Aure har da ɗa, shine zaki murnar dawowarsa rayuwar ki, shine dalilin shigar ki wannan halin fa, me ze dawo yai miki?' wata zuciyar ta tunatar da ita. Seda tai kuka me isarta Sannan ta miƙe ta nufi banɗaki.
Sadik ya cigaba da zaryar gidansu Farhan, sedai tun ganin da yai mata a Hotel ba su sake haÉ—uwa ba, duk zuwan da ze se ace bata nan.
Gefe guda baya son saka Nana a cikin damuwa, haka nan yake kiranta a waya suyi hira, amma hakan be hana ta gane yana cikin damuwa ba, ganin yadda ta damu sosai yasa yace ze je ya taho da su Ranar Asabar, dan yana kewarsu sosai.
Ko da ya sanar da Mother zeje É—akko su Nana tai murna, dan ko ba komai ta ga jikanta dan tayi kewarsa.
Sedai tace "yanzu kai kaÉ—ai zakaje É—akko su, zaka iya driving har garin nan?"
Sadik yai murmushi yace "Haba Mother, nifa yanzu magidanci ne"
Mother tace "sannu sarkin fitsararru"
Sadik yai murmushi ya fice.
Inna kuwa se gyara Nana take, ita kuwa Nana bata san me ake ba, tai ta mita ita ta gaji da wannan abubuwan da Inna take bata, masu ɓata mata ciki da sata zawo.
Inna tace "shashasha, ke kam Allah ya nunan lokacin da zaki hankali, nan gaba in kika gane amfanin abunda nake miki, kya dawo da kanki ki nema"
Nana ta yamutsa fuska tace "wannan É—in? Ni cikina yai ta ciwo idan kika bani, ni ba rashin lafiya ba amma ki ta bani wannan abubuwan, da masu da É—i da marasa daÉ—i"
Inna tace "dan ubanki duk wannan rawar kan da kike zaki koma gidan miji, haka zaki koma masa ba wani shiri, to karki abunda na saki, ke kin haihu ma amma har yanzu banga hankali ya fara shigarki ba"
Tace "Nifa ba rawar kai nake ba Inna"
Inna tace "kya dai ji da shi".
Farhan kusan kwanaki biyar da haÉ—uwarsu da Sadik, ta kulle duk wata hanyar da zasu sake haÉ—uwa ta toshe ta, sedai hakan ya kasa yi mata daÉ—i, tana son ko sau É—aya ta sake sa shi a idonta ko taji daÉ—i.
Idan ta tuna abunda yai mata, se taji wani irin mugun haushin kanta Ya kamata.
Da Sadik ya je ɗakko su Nana, Nana tai mamakin yadda ta rame sosai da sosai, Hakiki yai musu nasiha sosai da fatan samun zaman lafiya da zuriya ɗayyiba, Sadik ya ƙanƙame Sahal yana shafa shi, yana jin kamar ya Shekara be ganshi ba, wata irin ƙaunar yaron na sake kama zuciyar sa.
Bayan sallar azahar suka kamo hanyar dawowa Kano, Nana ta haÉ—e rai tana tura baki.
Sadik yace "Madam ya dai?"
"Besty ni kamar ba kai murnar gani na ba, ta Sahal kawai kake"
Ya gyara zamansa yace "Ai ke no matter how zan nuna miki yadda nai missing É—inki, ba zaki gane ba se mun fi haka yawa"
Tsit tai ba ta kuma magana ba, yace "ya ki kai shiru kuma?"
Tace "bakomai" yai murmushi ya cigaba da tuƙinsa, sedai tana kallon yadda fuskarsa babu walwala, damuwa kwance a fuskarsa.
Abun Allah Mother, har da sawa ayiwa su Nana girki, aka gyara musu BQ, a cewarta ba zata iya da fitsarar Sadik ba, su koma can su zauna, kan Abba ya dawo a ga yiwuwar komawarsu London, dan har yanzu ba a yanke yanayin komawarsu ba, saboda Sahal.
Nana tai mamakin yadda Mother ta karɓeta, suna zuwa ta karɓi Sahal, sati ukun da tai ba ta ganshi ba, ta ga ya ƙara girma da wayo, sedai ta bakin inna Sahal ya fara gane uwassa, dan Kuka ya dinga tsalawa Mother, seda Sadik ya karɓe shi Sannan yai shiru.
Mother tace "yau naga fitsararen ɗa, har ka san iyayenka? Aikuwa ƙyuya ba'a nan gidan ba".
Tun da Sadik ya kawo Su Nana ya fice cigaba da farautar neman Farhan.
Nana kuwa turaren wuta ta kukkuna a BQ É—in, irin wanda Inna ta sa aka haÉ—a mata da na barka da ta samu.
Sahal kuwa dama yana gurin Mother, duk da kukan da yake yi, ta goye shi har yai shiru.
Nana Ba ta sake saka Sadi a idonta ba, se bayan sallar isha'i.
Ya dawo ya tarar ta sha kwalliya cikin ƙananan kaya, Ta gyara Sahal cikin kayan baccinsa se se bacci yake.
Nana ta gabatar masa da Abincin da Mother ta aiko musu, sedai taga se cakala yake yi, ta sashi a gaba da mita da tambayar meke damunsa, ba shi da amsar ba ta, dan haka ya dinga tura Abincin nan, ba dan yana jin daɗinsa ba, sedai bayan yaci Abincin yaji daɗi dan rabonsa da abinci ya ci ya ƙoshi har ya manta.
Sedai duk yadda yake iƙrarin yai missing ɗinta, da yadda tai masa kyau amma ya kasa komai saboda damuwar da ke sasaƙar zuciyar sa.
Nana ba ta damu ba, ita rungumetan da yai ma a jikinsa ya ishe ta nishaÉ—i.
Abu kamar wasa Damuwar Sadik ta shafi Nana, duk baya walwala, sedai in ya ɗan ɗau Sahal, ga tunani da rashin cin abinci da yake, tayi tayi amma ya ƙi gayamata damuwarsa.
Yanzu ma bacci take, amma ta buÉ—e ido taga Sadik a zaune, ya zubawa window ido.
Kawai ta fashe da kuka, gigice ya juyo yana faÉ—in "lafiya kuwa?"