← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 115

Sashe 40

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana tana ji ta na gani, da daddare Inna ta haɗa mata kayanta, ta na yai tana mata nasiha akan tayi haƙuri da abunda Allah ya hukunta akanta.
Nana taiwa Inna banza, ta cigaba da sharɓar kukanta.

Inna ta kalleta tace "Nana ba zaki dena kukan nan ba ko?"

Cikin kuka Nana tace "Inna ya za ai in da ne kuka, bayan ba kwa sona, kun Auramin wannan Yaron, wanda a gabanki yake cewa ya tsaneni ni"

"To Nana, Allah ya riga ya hukunta lamarinsa, ba yadda kika iya, sannan karki sake ce masa yaro, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, kiyi masa biyayya, duk abunda yakamata in gayamiki na sha gaya miki a baya, bake ba fito na fito da shi, matsayinsa a gurinki a baya daban, a yanzu ma daban, dan haka ki nutsu kiyi haƙuri"

Ƙara rushewa da kuka Nana tayi, tana "Innalillahi wa innalillahi raji'un, nikam na shiga uku wallahi bana sonsa"

Tun Inna tana rarrashin Nana, se data zageta tsaf a daren nan.

Ita kanta Inna ba ta so Auren Nana ya zo mata a haka ba, taso Nanan ta É—an tasa tai gagarumin bikin aurar da jikarta É—aya mace da aka mutu aka bari, sedai wannan Auren da a kai na gaggawa shine mafita, akan samuwar abunda ze rusa farincikin ahalin gaba É—aya.

Sadik kuwa tunda aka ai ɗaurin Auren nan yaƙi magana, se ajiyar zuciya da yake tayi, wadda take nuna yana cikin damuwa.
Sedai ta gefe ɗaya yana ji a jikinsa, babu inda Auren ne zeje, dan baze taɓa iya zama da Nana a matsayin matarsa ba, wannan kudahumar 'yar ƙauyen mara kunya, ya san ba yadda za ai Mother ta yadda da Auren nan ba. Dan haka dole ne a raba shi.

Da safe da Abban Farhan ya zo, ya tarar Farhan ta tashi, har an taimaka mata tai wanka, sedai ta ƙi cin Abinci.

Abba ya kalleta yace "sannu Farhan, ya jiki"

Farhan tace "da sauƙi Alhamdilillah, Abba ina Umma?"

Abba yace "tana nan Lafiya, tace a gaishe ki"

Farhan tace "ba zata zo ta dubani ba?

"Kinga Farhan, mu bar wannan maganar, Anty Uwani da Hauzaifa suna nan tafe tazo ta zauna da ke, amma haryanzu likitan be gayamana meke damunki ba"

Farhan ta É—an gyaÉ—a kai.

Abba yace "Farhan Hajiyar nan tana da kirki, duk wannan É—awsiniyar babu ko kwabon mu a ciki, Allah ya biyata da Gidan Aljanna".

"Ameen" Farhan ta amsa.

Suna cikin Magana ne sega Abbas ya shigo, da flask É—in Abinci a hannunsa, suka gaisa da Abba.

Farhan ta dinga kallonsa, tana tunanin a in da ta sanshi.

"Gawa taƙi rami, ba magana?" Abbas yai maganar yana kallon Farhan.

Babu Uniform a jikin Abbas, dan haka ba ta gane likita bane.

Ya kalli Abba yace "Baba babu wata damuwa, zaka iya tafiya gurin Aikin ka, zamuyi ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai, Hajiya tana nan tafe"

Abba yace "eh ƙanwata ma tana nan tafe anjima zata zo ta zauna da ita"

Abbas yace "babu laifi"

Ya Ajiye kular Abincin ya fita.

Abba be jima ba sosai ya tafi, saboda shima yana jin kunyar azo a samu shike jinyarta a matsayin ta na babbar 'yar sa.

Wata Nurse ce ta shigo, ta zubawa Farhan Abincin kular da Abbas ya zo da shi, ta takurata taci Amma ƙememe Farhan taƙi.

Ana cikin haka zega Abbas ya sake shigowa É—akin da Farhan take.

Wannan karon da lap court ya shigo É—akin nata, se a yanzu ta gano shine likitan, kuma taga kamanninsa da Hajiyar sa.

Nurse ɗin ta miƙe tsaye cikin girmamawa tace "sannu da zuwa doctor"

Yace "Yawwa ya patient É—ina?"

"Patient gata nan, anma taƙi cin Abinci"

Abbas yace "bakomai, jeki kawai"

Nurse ta Ajiye Abincin ta fita, ya zauna akan kujerar, ya ɗakko plate ɗin me ɗauke da faten wake ya sha Alayyahu da kifi, ya kalli Farhan yace "Hajiya ce ta bani tace in kawo miki kan ta zo, ki karɓa kici"

Ta girgiza kai tace "Na ƙoshi"

"Ki daure kici ko ba yawa saboda ki samu ƙwarin jikinki"

"Naƙoshi" ta faɗa a raunane.

"Hey, karɓi kici nace" ya faɗa cikin tsawa.

A gigice ta karɓa hannunta na rawa, ta fara kokawar cin Abincin, amma kunya take ji, saboda a iya gaban Sadik take iya cin Abinci.

Abbas yace "Sorry kin sa na miki tsawa, daure kici kinji"

A hankali ta fara cakalar Abincin, kamar ba ta so.

Abbas ya É—an kalleta yace "Mhmm hira nake so muyi"

Haushi ne ya fara kama Farhan, dan mutumin nan ya takurata sosai.

"Zan tambayeki wani abu, ina son ki gayamin gaskiya kinji?"

Farhan ta jinjina masa Kai.

"Waye Sadik?".

Wata irin ƙwarewa Farhan tai, wadda ta haddasa sakin plate ɗin hannunta!

(Me ze faru idan aka jewa Mother da Nana a matsayin sirikarta? Wace irin rawa Abbas ze taka a rayuwar Farhan, Ya Sunusi ze kaya da sauran al'amura keep following my pen Ayshercool)

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Abbas ya ƙurawa Farhan ido, ya miƙe yaje fridge ɗin dake ɗakin, ya ɗakko ruwan roba, ya miƙa mata.

Ta karɓa ta ɗan sha kaɗan ta ajiye, ya ɗakko flask ɗin Abincin nan, ya ajiye mata a gabanta yace "oya, ɗau spoon ki cigaba da ci"

Jikinta na rawa, saboda wani irin kwarjini da yai mata, haka ta dinga cakalar Abincin nan tana ci.

Gani yai idonta ya cika da hawaye, da alama dai kamar ya takura mata, ya kalleta yace "ajiye in kin ƙoshi"

Aikuwa kamar jira take, ta ajiye kwanon Abincin.

Ya sake kallonta yace "Oya, gayamin waye Sadik?"

Mamaki ne ya cikata, a ina ya san Sadik? Ya a kai ya san shi?.

"Mhmmm ke fa nake jira"

Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta, tana kokawar maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata.

Yace "shikenan, tunda ba zaki gayamin ba, bari idan Abbanki ya zo na tambaye shi, ko in gaya masa Shi Sadik ɗin yana da Alaƙa da rashin lafiyar ki"

Cikin sauri ta É—ago kai, hawaye na bin fuskarta tace "A'a, dan Allah kar ka gaya masa"

"Meyasa kar in gaya masa?"

"Bakomai"

"Ban yadda bakomai ba, ki gayamin gaskiya ba wanda zan gayawa"

Tai ajiyar zuciya tace "É—an makarantar mu ne" se kuma tai shiru.

Yace "ina jinki, se kuma akai yaya daga nan?"

Ta sunkuyar da kai taƙi magana.

"Ko dai yana takura miki ne a makarantar, yana miki abunda ba kya so?"

Tace "A'a"

"To gayamin, Why you don't want him to leave you?"

Ta É—aga kai ta kalli Abbas, tana mamakin yadda akai yasan wannan abubuwan haka.

Yace "Anyway, tunda ba kya son maganarsa, Yaushe kika fara rashin lafiya?"

"I don't know" ta bashi amsa.

"As how? I mean Yaushe kika fara jin wasu alamu na rashin lafiya"

"Ba zan iya tunawa ba, kawai ina yawan jin faÉ—uwar gaba ne, bana kuma iya cin Abinci, and i thinks am having cancer"

Zaro ido yai yace "how do you know that? Ke kin san meye Cancer kuwa?"

Ta share hawayen fuskarta tace  'ban sani ba amma ina tunanin ina da tabbacin haka"

"Asibiti kika je aka gaya miki haka?" Yai maganar yana kallon ta.

Tace "No, ina gani a tv, ana faÉ—ar symptoms É—in, and am having some of the symptoms"

Yace "Well, a ina kike jin Symptoms É—in? And wace irin Cancer kike tunani?"

Tai shiru ba tace komai ba, sema sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.

Yace "na gane, but for how long kika fara jin Symptoms É—in?"

"Almost a year" ta faÉ—a cike da kunya.

"Karki kuma jawa kanki wannan masifar, is not a cancer, ba yadda zaki zauna da wannan ciwon tsawon shekara guda ba tare da kin fara shan magani ba, ace bata nuna ba, what You Are feeling is just a homonal activities, ki kanji ciwon a lokacin da kika kusa fara al'ada ko bayan kin gama da wasu 'yan kwanaki, is normal, Da kinyi Aure zaki dena ji, da zarar Sadik ɗin ya fito a kai Aure zaki nemi ciwon ki rasa, alamu sun nuna kina buƙatar Aure ne, da zarar kimyi Aure zaki dena ji, sedai maybe when you are pregnant in the first trimester zaki ji ciwon, ko makamancin haka"

Farhan ji tai kamar ƙasa ta tsage ta shige, saboda tsananin kunya, kuma hankali kwance yake mata bayani.

"Ko akwai wani abu da yake damunki deep down inside your heart bayan wannan?, a shekarun ki be kamata jininki ya hau Sosai ba"

Ta girgiza kai alamar bakomai.

Yace "Mhmm Yaushe Sadik É—in ze zo dubaki ne?"

Jin tambayar da yai mata yasa Ta É—auke kai daga kallonsa, tana hawaye.

A take ya fara gano matsalar Farhan, yace "he broke your heart ko?"

Tace "No"

Ya ɗan ƙura mata ido, tayi yarinta da Love Crises, she's very young, koma dai menene, akwai depression a tare da ita, Kuma da alaƙa me ƙarfi a tsakanin ta da Sadik.

Yace "ajin ki nawa yanzu?"

"Jss3" ta bashi amsa.

Ya É—anyi shiru, gaba É—aya ba ta fi Shekara goma sha huÉ—u zuwa sha biyar ba, amma tana É—auke da damuwa,
Yace "Shikenan, bari in bari ki sake samun nutsuwa, ma cigaba da maganar, amma tabbas ina son jin a gayamin waye Sadik É—in nan"

Ba tace masa komai ba har ya fita daga É—akin.

Nana kam an haɗa mata akwatinta cif, dan har an kai akwatin mota, ta ƙanƙame Inna tana kuka tace "Inna meyasa zaku turani in da ban san kowa ba? Wallahi Inna bana son yaron nan, Inna ya akai kika dena sona, da kula dani kika yarda a tafi dani in da babu idonki a kaina? Haba Inna ta, da wa zan rayu babu ke a in da nake"
Chapter 40 · 0% Book details