← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 118

Sashe 99

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Good job Zameer ka yi abu cikin sauƙi u are smarter than everyone! Smart smarter smartest u are so lucky ka yi komai muddin Ridayya zata dawo kanka, ka so kanka fiye da kowa karka zama mai yadda da faɗuwa da karaya akan abu" Murmushi ya yi yana shafa samar kansa da lumshe idanunsa he is more than okay gani yake dawowar Ridayya ya zama dole ne. Tafiya ya fara yana barin entrance ɗin gidan.

Sosai Tajj Baita ya shiga tashin hankali fitar maganar nan waje yana nufin komai zai taɓa career MB USTAZ zai taɓa takararsa da jam'iyyar da yake ciki musamman ƴan jarida da ƴan media suka samu labari.

"Abba calm down please jikinka na girma ne kai hakan ya haifar maka da hawan jini ka ciwon ɓarin zuciya ka kwantar da hankali abi komai a sannu don Allah"

"Tajjudeen kasan zafi da raÉ—aÉ—in da nake ji a zuciyata? Idan na rufawa É—ana asiri Ubangiji zai yafe masa wannan zunubin ne?"

"Abba ba kyau karka yanke hukunci akan abun da babu tabbas ba evidence mu fara bincike.....,"

"Kai Tajjudeen! Na san ka san inda zaka samu Muhammad Bilal ka faɗa masa idan har ni na yafe shi ina buƙatar ganinsa nan sa kwana biyu" kana ganin Baba ƙarami kasan he's out of his sense he lost ciwo kawai zuciyarsa ke masa. Junaid ya ya jugum shi kansa kan nasa hayaƙi yake yana buƙatar ruwan sanyi. Tajj Baita ya ce

"Abba ina zanga His Excellency yanzu?"

Wani kallo da Baba ƙarami ya yi wa Tajj ya sanya shi yin shiru tare da yin waje a ransa yana jin dole zai saka a kama Zameer bayan election a sake shi sannan komai ya yi daidai samun nasara ko faɗuwa.

Yanke jiki Baba ƙarami ya yi ya faɗi Baffa da Junaid da Abubakar suka rufu a kan shi nan da nan aka ƙara kiran Dr gabaɗaya matan gidan basu san wainar da ake tuyawa ba hakan kuma ya yi wa Baffa daɗi a rai.

Japan
Dawowarta daga makaranta kenan saboda karatu ya ɗauki zafi shirye-shiryen exam suke ta first semester zangon karatu na farko a jerin sabbin ɗaliban da jam'iyyar Japan ta ɗauka a Kyoto University. Kyoto University is a Japanese national university that was founded in 1897. Ta ƙara samun gogewa da ilimin zaman rayuwa musamman data haɗu da mutane kala daban-daban kuma ƙabila daban-daban ta samu rangwamen tsana daga idanun mutane wasu kuma saboda baƙinta ya yi yawa sai su dunga guduwa tamkar zata shafa musu baƙin zunubi hakan baya damunta a yanzu tana da confidence na fuskantar ko wacce matsala da zata ƙalubalanceta ta samu ƙarfin zuciya da abinda ake kira Self-confidence ga mijinta wanda baya gazawa he is always supports her akan dukkan lamuranta yana nuna mata ita ma mutum ce kamar kowa tana da ikon yin dukkan abinda take so wanda bai saɓawa addinin Muslunci ba.

Zamanta da mijinta MB USTAZ babu komai face farinciki da kwanciyar hankali, dukda akwai samun saɓani irin na ma'aurata wani lokaci duk wacce ta ce bata taɓa faɗa da mijinta ba ko misunderstanding ya shigo ciki ƙarya take, aure ibada ne kuma sunna zama ne na dindin wanda ake fatan sai dai mutuwa ta raba.

Da farin ciki ta shigo tun a parlor ta zare safar hannunta dana ƙafa ta cire madaidaicin hijabin wata takarda kawai ta ɗauka ta nufi babban part ɗin data tabbatar yana ciki a hankali ta murɗa ƙofar ta shiga parlorn farko mai ɗauke da haske ta shiga na biyun shi kuma duhu ta ƙarasa har cikin bedroom tana shiga ta hango shi kwance tsakiyar gado ya shiga cikin duvet yana bacci hankali kwance Ridayya ta saki murmushi mai sauti ta zauna kan gadon idan ta kalli MB USTAZ da kyau ta tuna shi ne wanda Ubangiji ya bata shi matsayin miji sai ta ji damuwar da ta yi shekaru da ita duk ta kau daga zuciyarta, ganinsa take tamkar ba a cikin zuri'ar Mai ran ƙarfe yake ba, shi kaɗai daban Ubangiji ya yi masa tsarinsa kaf familyn.

"Now is my turn Abbiey"

Sai tana bacci mai daÉ—i zai fara damunta bata bacci ya isheta yanzu ganin yana jin daÉ—in baccin sosai ya saka ta fara tashinsa ta hanyar zura hannunta cikin sumar kansa data rufe masa fuska a hankali take ya motsa masa kan tana murza tafin hannunsa daidai kunnensa ta ce

"Abbiey Abbiey Abbiey"

Amma ina bacci yake sosai saboda gabaÉ—aya satin bai samu ciakken bacci ba Ridayya ta dinga takura masa "Abbiey mijin"

Duka yana jinta ya yi luf can ya ɗan mirgina ya ɗauki pillow ya rufe kunnensa data miƙa hannu ta fara taɓa shi can zai make hannun yana sake mirginawa abubuwa biyu ke damunsa ba lallai ta fahimta amma yanzu baccin shi ne gaba da komai. Sake hayewa gadon Ridayya ta yi saman jikinsa numfashinta na sauka ta fara bugunsa da ƙarfi cikin magagin bacci ya ce

"Haramun Ustaza haramun zunubi kike É—auka"

"Nima haka kake mini please ka tashi i want...."

"Are you sure u want this?"

Ya faɗa yana nuna mata wani abu ta yi saurin rufe idanunta a hankali shi kuma baccinsa ya fara warware wa wani abu ya danne baccin ya ɗan cije lips cike da mugunta yana juyata ƙirjinsa na matsewa sosai da kyau jikinsa na buɗewa yanayin na shigarsa da kyau yana ɗago kanta ya ce "Because once it is in, you will officially belong to me"

Ta zazzare idanu domin ita kwana al'amarin fitar mata yake daga kanta tana ɗan narke fuska murya shagwaɓe ta ce "Koma bacci abinka bari na gyara maka duvet ɗin"

Ya buÉ—e idanunsa da kyau yana rungume da ita suna daga kwancen ya lumshe ido ya buÉ—e magana yake son yi kuma ya kasa Ridayya ta ce "Allah ya yafe miki Ustaza ke yarinya ce"

Ya ɗaga mata kai alamar “Good” Ridayya ta gyara kwanciyar ta a jikinsa ganin ya mata shiru ta ce "Kasan me Abbiey?"

Ya zuba mata gajiyayyun idanunsa sosai mai É—auke da abubuwa da yawa ya kasa cewa komai ta ce "Karatun daka koya mini shi ne aka yi mana a test kuma na cinye Assignment É—in nan" Ya buÉ—e ido zai magana sai ya fasa ya yi kissig kumatunta muryarsa bata fita sosai da wani irin romantic voice ya ce

""أنا أحبك"
Murmushi kawai ta yi ita har yanzu nauyin faÉ—a masa kalmar soyayya take nauyinsa take ji sosai shi kuma baya takura ta yasan soyayya ba dole sai an furtata da baki ba wani a aikace yake yin komai

"Black tea Zauja ok"

"Right now Abbiey"

Ya sake ta can ciki ya ce "Barakallahu fiiki"

Gani yake komai ta yi yarinya ce ita tana buƙatar uzuri shi ya sa yake sassauta yanayinsa da fushinsa a kanta.

Fita ta yi da niyyar nufar kitchen ta haɗa masa tea ɗin sai ta ji telephone line ɗin gidan na ƙara ta jima bata yi ba da tunani Abba ne ko Baffa ta ɗauki kan wayar muryarta a sanyaye ta ce

"Assalamu alaika/ki"

"Allahamdulillahi! Ridayya are u alone oh sorry her Excellency"

"Daddyn Nadra ina yini"

"Ajjiye gaisuwa a gefe are u alone magana za mu yi ta fahimta bana son mijinki ya sani"

Tabbaci ta bashi ita kaÉ—ai ce lafiya?

"Ridayya daman Tsohon mijinki bai sake ki ba? Guduwa kikai daga gidansa?"

Mararta ta ji ta ɗaure mata wani abu ya yi zillo ta ƙasan marar jikinta ya ɗauki rawa ta ce "Ka...ka...ka kamarya bangane ba"

Tajj Baita ya ce "Nima dai ban gane ba, ta bakinki nake son ji, ya ce daya aureki kina da ciki ba kowa ya yi miki ba sai His Excellency MB USTAZ kuma tun kina ƙarama yake lalataki ya rantse da Allah bai sake ki ba, shin Ridayya da gaske kin yi aure da ciki kuma na Ustaz ne?" Tajj Baita bai san meke faruwa daga ɓangaren Ridayya ba sai ji ya yi ta fasa gigitacciyar ƙara kiran kuma ya katse. Ustaz dake zaune da laptop a gabansa yana duba wani muhimmin saƙo da Muhammad Hassan ya tura masa ta email ya ji ihun matarsa cikin sauri ya miƙe a ɗan gigice yana addu'a ya nufi waje kwance ya sameta bata ko motsi jini na zuba ta ƙasanta bai tsaya jiran komai ya shiga kiran ambulance kafin su ƙarasa ya zura kaya ya sunkuceta sai ambulance.

Some hours left
Girgiza kai kawai yake idanunsa da suka nutsa ciki sosai da maka tantance yanayin su ne zube akan wanda yake tsaye a gabansa, shi kansa wanda yake tsaye ya firgita da yanayin Ustaz ya san halinsa idan ransa ya ɓaci

"Try to understand me ni ban san me ya saka Madam shiga halin da take ciki ba, kawai na san ana buƙatar ganin ka a gida"

"I hate liars, why?"

"Yanzu muje asibitin muga halin da take ciki"

"Tajjudeen Baita ka jima ba kaga rikicina ba, matata tawa ce ba ruwanka da na je wajan ta ko akasin haka. Firstly ka kira matata without my permission, secondly ka ce mata wani abu wanda ya saka ta shiga firgici, lastly ka shigo jirgi ka zo mini nan? Explain why? Menene?"

"Calm down please"

"Calm down? Assatagafirulla Allah ya yafe maka Ubangiji ka Tajjudeen" muryar Ustaz har shaƙewa take Tajj ya buɗe baki zai yi magana ya ji saukar wani mari a fuskarsa ya ƙara jin wani muryar daya jima bai ji ya ji ta masa amo! Da amsa kuwwa a kunne

"What is going on? Meke faruwa don't let me to repeat myself".

"Your wife's ex-husband"

Tajj ya ce yana riƙe fuskarsa sosai marin ya ratsa shi saboda a hagunce ya mare shi shirun Ustaz na nufin ƙarin bayani nan da nan Tajjudeen Baita ya zayyana masa komai da yake faruwa. Kan Ustaz a ƙasa murmushi kawai ya yi ya nufi wajan freezer ya ɗauki ruwa mai sanyi sosai ya ɓalle gorar kai ya shanye tas ya cillar

Murmushi ya sake saki ba za ka taɓa cewa ya damu ba ko maganar ya shige shi musamman furucin Baba ƙarami na cewa zai ɗaure shi, wai ciki? Ya lalata ƴar jaririyarsa shi kuma nasa salon kenan?
Chapter 99 · 0% Book details