← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 118

Sashe 58

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shagwaɓe fuska sosai sai kuma ya miƙe tsaye ya ce "Why should I?" Ta yi masa dariya ya fita ya ɗauki wata farar motarsa ya yi waje kafin ya isa gidan Mahmah ya yi sadaƙa babu adadi bai san nawa ya bayar ba, kuma yau kwanan Ridayya uku kenan da yin idda yana lissafe da komai shi ya sa bai taɓa kulata ba wannan ranar yake jira.

Mahmah na zaune a parlour tana kallon tafsir ta ji sallamar Sadauki ta É—aga kai ta kalle shi ta ce "Ikon Allah da alama taurarin sa'ata ne suke haskawa a kan ka Hamza, irin wannan ziyara haka?"

Ya basar yana zama ya ce "Mahmah ai na girma aure ma zan yi daman ana kawo miki ƙarata" Ta ce "Au Hajja Azizat ɗin ce mai kawo ƙarar taka?"

"Uhm na san komai fa, ni unguwa zani kuma ɗan rakiya nake nema" kafin ta yi magana ya miƙe ya nufi bedroom ɗin Ridayya ta girgiza kai ta ce

"Ban hango maka rakiya a nan ba, rikice dai kawai Sadauki matar wanin??"

"Thank God ki ce wani, kuma ai ta yi Idda"

"Idda kuma kai ina kasan ta yi Idda É—in?" Bai yi magana ba ya shige cikin bedroom É—in Ridayya na zaune a gefen gado tana ta yi wa Little Bilal wasa Sadauki ya shigo.
Ta yi saurin rufe jikinta ya taɓe baki ya ce "Tashi zaune" Ya faɗa babu wasa ta miƙe tana riƙe da Junior.

"To kibar nannuƙewa unguwa za ki rakani" Ta yi sauran kallon shi ya ɗaga mata gira yana kashe mata ido kamar ya shiga ranta ya ce

"Da zan rama abinda kikai mini da tuni na yi fa, so get down" Ba zata iya masa musu ba domin a muryarsa ta ji ba wasa kuma ya cika mata Idanu ta miƙe tsaye zata ɗauki vail ɗin abayarta yana juyawa ya ce

"Hijab please"
Ta ajjiye mayafin ta ɗauki hijab ta yi covering jikinta ta saka flat shoe ba ƙaramin kyau blue ɗin hijab ɗin ya yi mata ta fito parlour tana rarraba Idanu Mahmah ta ce
"Saki jikinki Sadauki bashi da matsala ɗan'ƙanwata ne Hajja Azizat, ki je ki raka shi ku dawo ki nutsu dai kar ki biyewa rigimar shi" Ridayya ta jinjina kai

"Muhammad-Bilal zo nan na goya ka" Ya tafi da gudu wajan Mahmah ita kuma Ridayya ta yi waje. A cikin mota ta samu Sadauki yana ta danna wayarsa taga yana bawa waya muhimmaci sosai.

"Ba mayen waya bane, business nake rufo ƙofar"

Rufe ƙofar ta yi a hankali ya yi wa motar key yana kallon hanya ya miƙa mata wayarsa ta kalli wayar a hankali a taushashe kamar mai raɗa ya ce "Kina so ne? Ba bar miki zan ba"

Ta yi shiru da zata iya murmushi da ta yi amma ita a yanzu babu wani dalili da zai zo wanda zai sanya ta yi murmushi sun jima kafin ya yi parking a gefen titi ya yi shiru can ya juyo gabaÉ—aya ya ce

"Bana jin daÉ—in shirun damuwa ce dani ki bani shawara" ta juya sexcy eyes É—inta ba ta ce komai ba ya marairaice fuska ya ce

"Shanshan please do something"

"Allah ya kawo sauƙi" Ya girgiza kansa a hankali ya ce "Juyo ki kalle ni"

Ta girgiza kai ya sake narkar da murya yana É—an fesa numfashin bakinsa dake fitar da mouth freshner ya ce

"Bana iya magana bana kallon cikin idanun mutum, but lemme try. Ridayya ni É—aya ne wajan Mama da Daddy, Daddyna É—an kasuwa ne kuma É—an siyasa yanzu haka shirye-shiryen fitowa takarar house of assembly, kuma ya ja kunnena wai dole na fito da matar aure ni tsoran matan yanzu nake yaudara da cin amana sun musu yawa, amma na ga guda É—aya wacce take tamkar zara a cikin taurari da gaske na ji ina son amma ban iya soyayya ba, ina so sai na iya kafin na fara zuwa wajanta"

A sanyaye Ridayya ta ce "Ayya to Allah ya bada sa a" Sadauki ya marairaice ya ce "Help me"

"Tayaya?"

"Ki bani dama ta sati É—aya kawai na gwada soyayya dake idan na ji na iya sai na je na faÉ—a mata ko?"

Jikinta ya yi sanyi ranta ya ɓaci domin ita ba wannan a ranta da iyakar gaskiyarta ya ce

"Ni na tsani maza"

"Nima bana son matan ai, kawai dake na yarda kinga ni É—aya ne a gidanmu gidan Mahmah babu mace ni ba cewa zan yi ina son ki ba"

"To ai nima ban iya soyayya ba"

Ya ɗan miƙe daga jikin kujerar ya saka hannunsa ya juyo da fuskarta zuwa inda tasa yake a hankali ta ɗago ta kalle shi,cikin saka idanunsu ya haɗe waje guda sun ɗan jima haka Sadauki na jin zuciyarsa kamar zata fito cikin kasala ya ce

"Za ki iya Shanshan, just trust me mu zama true friends komai ya zama confidentiality between us ok?"

Za ta yi magana ya ɗora yatsarsa guda a laɓɓanta ya ce "Shhhhhh kar ki taurin kai Shanshan"

Ta jinjina kai ya miƙa mata hannunsa ya ce "To mu yi musabaha mu ƙulla kuma" Tana kallon shi ya kama hannunta ya ce

"Assalamu Alayki Hamza Hamdan Hamish ana ce mini Sadauki, but ke ki ce Sahibi zan amsa"

Ta É—an lumshe gajiyayyun idanunta ya matse hannunta ya ce "You?"

Cikin sanyin muryarta mai kashe jiki ta ce "Ridayya"

"I knew. Soyayyarmu ta fara yanzu sati ɗaya kawai. Ridayyerh yanzu ke tamkar budurwata kuma matar da zan aura a haka nake kallon ki, ki yi haƙuri da halina ina da naci da taurin kai. Ridayyerh ban miki al'ƙawarin farin ciki har abada ba, abu ɗaya Sadauki ya sani ba riƙon amana ba zan taɓa bari ki yi kuka ko shiga damuwa ba, zan zama ɗan halak a wajanki ki sanyawa ranki Sadauki na ki har abada Shanshan"

Kallonsa kawai take ya saka baki ya hure mata idanu da iskar bakinsa, ta yi saurin ƙifta idanu sai kuma ta ɗan turo bakinta da suke jajur. Sadauki ya kalli laɓɓan data tura sai kawai ya girgiza yana sakin hannunta ya ce

"Nifa kwaÉ—ayi nake ji ice cream za ni sha hope ki sha ko Saheeba?"

Kallon da yake mata ya sa bisa dole ta ce "Eh"

"Eh wa?"

Ta kwaɓe fuska sosai ta ce "Zani Sahibi"

"To Allah ya yi miki Albarka" Ta ce Amin.

Surutu ta gani kala-kala wajan Sadauki bisa namanki taga mata sai magana suke masa haka kawai kuma ta ji ranta ya ɓaci yana lura da ita bata sha komai a wajan ba.

Yana gama yin parking ta buÉ—e ta fito ta yi cikin gida kai tsaye kuma kitchen ta nufa, Sadauki ya zauna a parlour sama da minti goma ya ji murya mai taushi ta yi sallama a palroun ya É—ago kai Sadauki mamakin ganin mutumin ya cika shi wai mai yasa suke yawan haÉ—uwa ne? Ya amsa masa ya nemi waje ya zauna.

Mahmah ta fito ɗauke da Little Bilal ta ce "A'a Babban mutum saukar yaushe?" A hankali ya ɗago idanunsa maimakon ya yi magana idanunsa ya sauka kan Little Bilal wanda shi ma kallonsa yake yana ɗago masa hannu yana tsalle kallon yaron kawai Ustaz yake da wani irin firgitaccen yanayi ya kasa furta komai kamar yadda ya kasa daina kallon Little kamar daga sama suka fara jiyo tari daga kitchen ga hayaƙi na tashi a gigice Mahmah ta ce "Nadra ce a kitchen" Jin haka ya saka Ustaz ajjiye wayarsa ya miƙe tsaye babbar rigar jikinsa na ƙara saboda sabbinta dukda dokawar da ƙirjinsa yake na rashin dalili bai hana Ustaz nufar kitchen ɗin ba kai tsaye....

Share and share as so much as you can! Sorry Ustaz🥰 Shanshan tana wajan Sahibi

Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*MUNAFUKIN MIJI 28*
Mikiya Writers Ass...

Bright pens free batch
Nimcyluv

Duk yadda zuciyarsa ke bugawa bai hana Ustaz nufar kitchen ɗin kai tsaye ba, ga wani irin hayaƙi da yake fitowa ya turnuƙe cikin kitchen ɗin gabaɗaya, hakan bai dame shi ba sai na zuciyarsa data ƙarfafe shi ta hanyar ƙara masa ƙwarin qiwwar shiga ciki ɗakko Nadra kamar yadda tunaninsu ya wanzar musu ita ce a ciki.

Yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarsa da nufin shiga ya ji an riƙe masa babbar riga ana faɗin "Uncle ƙani na kuka ƙani yana kuka" cak Ustaz ya tsaya ƙafar daya shigar cikin kitchen ɗin a nutse ya zaro ta, tare da mayar da ita baya yana juya idanunsa sosai da suke zube a kan yarinyar ba tare da ya ce komai ba.

Mahmah ta ce "Babban mutum dawo ka zauna ashe Nadra na bedroom ɗina tana mini wasa da bagaruwa, nasan baka son hayaƙi saboda ciwon kan ka, Sadauki shiga ka duba mene ya haddasa wannan hayaƙin idan dai gas ne sai dai mu fita daga gidan don sharrin shi yawa ne da shi"

Ustaz ya dawo da baya jarumta kawai ya nuna amma zuciyarsa ba ƙaramin tsalle take masa ba tana matsewa waje guda a ƙirjinsa tuni jijiyoyin kansa sun fara bayyana ya zauna saman kujera, ya kasa yin alkunyar ɗauke ganinsa daga kan Little Bilal.

"Mun same ku lafiya?
Yara gida da ayyuka?"

Ya faÉ—a a rarrabe bayan ya gama samun daidaito da tafiyar numfashinsa. A hankali ya saka hannayensa biyu ya É—auki Little Bilal.

Mahmah ta murmusa cikin jin daÉ—in yadda ya É—auki Little ta ce "Lafiya lou Babban mutum, kwana biyu zuwa kano baya yi maka wahala"

Ya lumshe idanunsa ya buɗe bai ce komai ba, sai nutsuwa da sanyin da yake samu deep down na zuciyarsa yana mamakin baiwa da ƙudirar Allah dake samar da mutane masu kamanni iri guda kuma ma bambanta jini, toshe da ƙwayar halittar haihuwa. Sosai ƙaunar Little ta zauna daram a zuciyarsa.

Mahmah ta ce "Sadauki ta shi mana, kana ganin baƙo babu gaisuwa?"

Baya son nuna halinsa da yi wa Mahmah gardama ya kalli Ustaz ya ce "Ina yini?" Tamkar Ustaz bai jima, haka ya yi shiru kai bama zaka É—auka da shi Sadauki yake ba, can ya nisa ba tare daya É—ago kai ba ya ce

"Sannu"
Chapter 58 · 0% Book details