← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 118

Sashe 76

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya lou nake ai tunda na ganku na warke Mami za ki dinga yi mini magana yanzu? Za ki dinga hira dani? Kuma za ki dinga siya mini abu irin n Zainu kin daina bari na cin mutuncin halittata?"

"Ina tare dake Ridayya ki yafe mini na yi kuskure ka cutar dake"

"Na yafe miki ba ki mini komai ba" daÉ—i ya ishe Ridayya tana tuno maganar Zameer da yake cewa bata da kowa bata da gata to ya zo ya gani iyayenta suna raye.

"Baffa don Allah yau É—aya ka ce ni Æ´arka ce bani na yi kai na da na san inda zan samu farar fata da kyau irin na Zainu dana samu"

"Shalalen Ustaz you're my darling daughter my love you're my favorite person. Na yi laifi da kuskure ban san yaushe ba kuma ba zai daina kukan hakan ba duk wanda yake da saka hannu a kan faruwar komai ba zan taɓa yafe masa ba"

Baffa ya rungume Ridayya yana jin wani tausayinta soyayyar da yake mata tun tana ciki wacce ita ta yi sanadiyyar lalata komai ta dawo masa sabuwa fil a zuciya. Mami kuka take da dukkan ƙarfinta raba uwa da ɗa akwai ciwo kuma dafini mai girma a zuciyar ko wacce mahaifiya idan ta tuna bata bawa Ridayya tarbiyya sai ta ji hankalinta ya tashi shi ya saka wani lokacin komai take yinsa da ka, dukda Ustaz ya taka rawa iya karfinsa wajan gina ta a kan turbar arziƙi. Addini, biyayya, tsare mutunci, suttura da ilimin zaman rayuwa amma tarbiyyar uwa daban take role ɗin uwa is best a rayuwar ko wanne ɗa.

"Mami ni ma ina son kayan irin na Zainu"

"Ridayya ke dai kishi halittarki ne ƙanwarki ce fa, ke ga Little kin ajjiye da abinda kika haifa na fari yana nan da tuni ya yi wayo fa amma kina acting like a baby"

Cewar Yaya Balkisu tana dariya. "Mu dai yanzu baby ce a wajanmu dole ta nuna mata wawta irin ta Æ´aÆ´an fari da kuma sangartata Ustaz ya yi"

Cak Ridayya ta tsaya da murmushin da take sai kuma ta miƙe ta ce "Baffa ina Abbieyna?"

"Ki ce ina Yaya Bilal ko Ustaz ki daina cewa Abbiey Ridayya"

"Shi Babana ne, yana ina?" Baffa ya sauke numfashi ya ce

"Kusa da ɗakin nan ki fita a hankali" da ƙyar ta jira ta saka wula duguwar riga ce a jikinsa wacce komai nata ya fiddo ta yi mata kyau ko slippers bata saka ba ta fita tana ƙoƙarin shiga room ɗin Umma na fito wa

"Ina yini Umma?"

Da faÉ—a bakinta na rawa saboda kallon da Umma ke yi mata.

"Ina yini ban ganshi ba, umma kuma ke neme ta idan kin zo don ganin Ustaz ne to ki koma domin babu ke babu shi"

Jikin Ridayya ya yi sanyi idanunta ya cika da hawaye ta ce "Abbieyna ne fa don Allah ki bar na shiga"

"Zan ga uban wanda ya isa ya saka ki shiga"

A sanyaye ta ce "Me na yi miki Umma ki yi haƙuri idan na miki laifi"

"Ai kinfi É—an dako sanin tasha. Ba ki mini komai ba kawai na tsane ki bana son ganinki tare da Muhammmmd"

Mardiyya ta ƙara su wajan ta ce "Umma the car is ready likitan ya bada sallama"

Umma ta ce "Ok ƴar arziƙi irin albarka wanke hannu ka taɓa farar mace alkyabbar mata haske mai haska ko wanne duhu, farar mace baku da yawa a duniya dai a Aljanna, idan mutum bai auri farar mace ba kuɗinsa ne bai kai ba" Mardiyya ta yi wani irin fari da idanu ta ce "Na gode Ummana"

Ridayya ta ji ta muzanta jikinta ya ɗauki rawa ta juya da gudu ta tsaya wani corridor ta yi kuka kamar ranta zai fita sai kallon baƙar fatarta take me ta yi wa Umma haka ne? Idan ta yi mata laifi to a kan me zata hanata zuwa Abbiey? Kukan da ta yi mai yawa ya saka kanta sarawa tare da fara ciwo.

Duguwar jallabiyya ce a jikinsa ta maza saboda aikin da yake mararsa an bashi da wani ɗan sanda yana takawa da shi, fuskarsa a kame baka gane halin da yake ciki furr Umma ta hana shi shiga wajan Ridayya a haka suka shiga mota Junaid ya kai su can gidan Ustaz ɗin. Ustaz hankalinsa yana kan Ridayya a haka ya bar asibitin. Ridayya tana komawa ciki suma aka sallame su ta zama wata so silent maganganun Umma na yawo a kanta lokaci zuwa lokaci tana kallon baƙar fatarta.

Zameer ne jingine da cikin wata jibgegiyar mota ya sha shadda sai É—aukan Idanu take kamar kodayaushe waya iphone ce a hannunsa ya manna bluetooth magana yake kamar an yi masa dole idanunsa a kan Alhajin ya ce

"Idan ka siyi filin haka to idan bai ba ka bar shi akwai masu siya da yawa"

Mai siyin filin ya dinga kallon makeken filin da girman gidan da zai samar bai ɗauka kuɗin da Zameer ɗin zai buƙata kenan ba domin ya yi sauƙi fiye da yadda ya zata ya ce

"A'a nikam filin ya yi mini idan miliyan 25 É—in ne matsayarka shi kenan sai ka bani takardun fili ga shaidu ga dillali ni kuma na baka takardar banki ko transfer ko cash"

Zameer ya ɗan taɓe baki yana danna waya a nutse ya ce "No transfer ɗin zai fi" Ya ce "Ok takardun filin?"

Mota Zameer ya je ya buÉ—e ya É—akko takarda É—aya ya dawo ya bawa mutumin shi kuma ya shiga duba takardar can ya ce "Kace sunanka Zameer Mahboob Dollar?"

"Sure; ya akai?"

"This land is owned by Ridayya Muhammad Tahir"

Zameer ya ce "Inji uban wa? To nawa ne halak malak idan zaka siya ka siya idan ba zaka siya ba ka bani takarda ba dole"

Dillalin ya ce "A'a ai ba a yi haka ba kasan duniya ta lalace da ɓata gari masu satar filayen jama'a, ko ka mance ba wannan takardar zaka bamu ba? Domin wannan ma ai original ba ce" gaban Zameer ya faɗi jin ance ba Original bace fake ce kenan ko ya? Me ya sa ya yi gaggawar barin Ridayya ta gudu ne? "Eh maybe mantuwa na yi kawo kawai"

"A'a ba a yi haka ba ina zuwa" Dillalin ya faÉ—a yana kwafe wasu numbers daya gani a jikin takardar kira uku ya yi kafin a É—aga ya yi wa Alhaji alama daya kira police.

"Assalamu alaikum kuna magana da Bello dillalin filaye, an kawo wani fili dake unguwar jan bulo kuma an saka Ridayya Muhammmmd Tahir" Shiru ya yi yana jin me ake cewa ya ce "To babu matsala nima naga alama bari a yi hakan"

Zameer na tsaka da danna waya yana jira ya ji shigowar maƙudan kuɗaɗe ya an riƙe shi ya ɗago kai ganin police ya saka shi binsu da Idanu kafin ya yi magana ɗaya daga ciki ya ce

"You are under arrest"

"Arrest akan me kasan waye ni kowa officer kasan waye babana?"

"Sorry sanin waye babanka baya cikin aikina, idan mun je office za ka ji bayani"

Tija ƙeyar Zameer sukai zuwa police station. Suna zuwa suka bashi damar kiran babansa kuma suka zayyana masa laifinsa na sama da faɗi da yake shirin yi da filin wani. "Wani kuma? Filin na matata ne matata kuma hakƙina ce komai nata mallakina ne"

"Ina matar taka take yanzu? Ta zo ta bamu tabbacin kai mijinta ne sai mu sake ta, ku saka shi a É—aki"

Zameer bai san ta ƙamaimai inda Ridayya take amma dole zata dawo gare shi bata da zaɓin daya shige zama ƙarƙashin inuwarsa haka ya saka a ransa kwana biyu ya yi ya fita daga hayyacinsa ko hauka yake ai ba zai kira gida ba, kuma bashi da ƙarfin qiwwar kiran Moo ko Khalid. Ridayya kawai yake nema idanu rufe.

Sadauki na zaune shi da Prof da Mother sai secretary daya shigo yanzu cikin rashin sa'a files ɗin hannunsa suka kwace pictures ɗin zuƙa zuƙan ƴan'mata suka bayyana tare da tarwatse wa a parlourn.
Sadauki ya dinga kallon pictures ɗin da mamaki haka mother. Prof hankalinsa ya tashi ya yi wa secretary alama da idanu cikin faɗa ya ce "Wai secretary how many times zan maka warning akan ka daina bina da photonan masu neman taimakon nan eh? Gabaɗaya baka san aikinka ba ana bata taimako dole ne na ce maka marayu kawai dana kasassu nake bawa tallafi" secretary ya ce "Afuwa ranka ya daɗe wallahi sun takura ne gabaɗaya bikinsu za a yi ke suna buƙatar taimako shi ne suka rarraba pictures nasu, wannan sun fi wata waje na yau na gaji na ce bari dai na yi maka bayani"

"To i can't ba zan iya ba kasan takara nake bana son problem"

"Muga" Sadauki ya faɗa yana amsar pictures ɗin yanayin kayan jikin ƴan matan su kaɗai abin mamaki ne ba su yi kama da masu neman taimako ba shi damuwar neman auren Ridayya ce a kan shi ya bawa secretary pictures ɗin mother ta ce "Daka taimaka shi taimako ba sai an ware wani ɓangare ba, kuma hakan zai taimaka wajan dasa soyayyarka wajan mutane shi ma campaign ne"

Prof ya miƙe tsaye ya ce "Mu je" fita suka yi shi da secretary suna fita ya ce

"Ka kusa kwafsawa wallahi idan Sadauki ya sani na banu"

Secretary ya ce "Wallahi ban san ya aka yi ba"

Prof ya lumshe idanunsa yana sake kallon pictures ɗin hankalinsa duk ya tashi ya ce "Wallahi duk ka firgitar dani a gida na yi niyyar kwana amma ka zaɓa mini guda biyu a yi booking hotel da ɗaki a kula da su ya zama confirmation please i trust you"

Suna gama maganar ya koma ciki ya ce "Yes son ina ne address É—in yarinyar gobe za mu je in sha Allah kar ka damu har da sadaki zamu tafi"

Murmushi Sadauki ya yi ya ce "Best father thank you darling"

"Anything for you dear, iye angon Ridha"

Tashi ya yi mother ta ce "Badai fita za ka yi ba na haÉ—a maka abinci"

"No meeting ne dani zan dawo nan da 2hrs love you wife" kafin ta yi maganar ya fice.
Chapter 76 · 0% Book details