← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 118

Sashe 29

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannu da hanya Babban mutum ya karatu? A zo lafiya" Ya jinjina kai. "Baka ce kana zuwa ba, gashi bani da abinci" Ya girgiza kai ya ce "Nikam yunwa ina ji, da gaske yunwa Umma"
"To Babana girki ya kamani, Ustaz guda da jin yunwa?" Baba ƙarami ya yi murmushi kawai. "Ustaz bani ruwa a fridge mana" Miƙewa Ustaz ya yi ya ɗauki ruwan gorar kana ya nufi ɗakinsa ruwan rubutu ya zuba a ruwan ya girgiza kana ya koma parlour ya bawa Baba ƙarami ruwan, tunda ya sha yake jin zufa na yanko masa jikinsa ya yi sanyi ya ce
"Ka dage sai ɓangaren banki, yanzu gashi ka kammala karatun wanne banki kake tunanin za su karɓe ka?" Ustaz ya yi shiru, ganin haka ya sa Baba ƙarami cewa "Sai kuma maganar aure, yana da kyau ka ajjiye zuri'a" Ustaz ya yi saurin buɗe ido sai kuma ya ce "Aure? Asstagafirullah Allah ka yafewa Abbana" Yana faɗin hakan ya fice daga parlourn.

Da mamaki Ammi ke bin Bilal da kallo irin yaushe ya dawo ɗin nan? Sai kuma ta dake tana kallon Biba data sake zuwa za su wajan Malam domin ƙarasa aiki. Tunda Biba ta kalli Bilal ta ji wani abu ya saukar mata komai nata ya nemi kuncewa ta jima ba taga mutum mai kwarjinin Bilal ba.
Ustaz ya juya ya kalli Zuhura wacce gaba take da shi, ganin kallon da yake mata ya sa ta ce
"Ina yini Ustaz?"
"Ina Balkis?" Ta ce "Ta fita makaranta" Ya haɗe fuska ganin Junaid ya ce "Kai don ubanka jira kake na gaidaka?" Junaid ya ce "Afuwa kai na ƙasa, barka da zuwa Babban mutum, zuwan ba zata haka?" Ammi ta yi murmushi ta ce "Ustaz ya hanya, ashe kana tafe kana lafiya?"

"Ƙalau, Ridayya fa?"
Junaid ya juya ya ce "Ammi ina Ridayya? Ni tun jiya ban sata cikin idona ba" Ustaz ya nufi kitchen haka kawai ya samu kansa da duba CCTV ɗin daya saka ba tare da sanin kowa ba, ya shiga dubawa abubuwan tashin hankalin daya gani sun girmimi tunaninsa jikinsa har wata kakkarwa yake na ɓacin rai zuciyar ta motsa, idanunsa suka juye tare da rikiɗe wa tamkar bashi ba. Daidai lokacin kuma motar Baffa ta sauka a gidan, zuwan Baffa da fitowar Ustaz daga kitchen ɗin sukai daidai. Bilal na zuwa ya ɗaga hannu ya wankawa Ammi mari ta yi baya tana zare ido "Bilal are you out of your sense? Mari fa" Bai yi magana ba saboda gabaɗaya jikinsa rawa yake, ya sake ɗaga hannu ya sauke mata wani mai lafiya ta yi bata zata kifa ta juya ta kalli Baffa ta ce "Kana kalli a kan Idanunka ya mare ni....," Kafin ta ƙarasa magana shi ma Baffa ya sauke mata wasu tagwayen maruka a fuska, da sauri Ustaz ya juya da nufin ɗakko Ridayya daidai nan kuma Anuty Kaltum ta sauka a gidan tare da mijinta General.
Ustaz na zuwa ya kalli Ridayya ya san idan ya nufe ta a haka zata firgita wannan yanayin nasa ba nata bane, ba zata ɗauke shi ba, dole ya fara samun nutsuwa kamar yadda yake idan ransa ya ɓaci, ya nufi bathroom ya mance bai rufe ƙofar ba, ya cire duka kayansa gabaɗaya ba abinda ya bari ya tsaya a tsakiya tare da sakarwa kansa shower idanunsa ya juye ya daddafe hannunsa da jikin bango ruwa na dukan tsakiyar bayansa. Ba zato ya ji an turo ƙofar ana faɗin "Abbiye.... Abbiey" A gigice ya juya yana cewa "No, Shalale haramun ne jikina stop amma ina......

Abu ɗaya nake nema wajanku shi ne sharing fisabilillahi saboda Allah🥹😢🤲🏻 sai kuma comment. Wannan littafin free book ne masu tambayata ko free pages ya kusa ƙare wa, idan kuɗinne ya muka yawa sai na yi dropping Account number no wahala ai🤓.

Domin gyara ko sharhi
[email protected]

Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08119237616

BRIGHT pens na godiya

*PAGE 16*
Bright pens🤙🏼free batch

Duk saurin Ustaz wajan dakatar da Ridayya daga shigowa cikin toilet ɗin, haƙarsa bata cimma ruwa ba. Ya dafe kai yana murza goshinsa da zufa ke fesu wa ta tsakiyar wajan. Cikin saurin kuma ya saki labulen dake tsakanin jacuzzie da mirror wajan shigowa. Ridayya ganin bata ga Ustaz ba ya ɗan leƙa kanta cikin sanyin muryarta ta ce "Abbiey, nine, gani" Ta furta idanunta na rufe wa sosai srup ɗin da Ammi ke mata ya yi matuƙar tasiri a kwakwalwarta, she's always sleeping. "Abbieynaa!" Ridayya ta furta tana mai janye idanunta ta buɗe su da ƙyar, saboda wani irin maganaɗisun bacci dake ribatar idanunta. Ustaz dake tsaye dafe da kansa gabansa sai tsananta bugawa yake, da ƙyar ya samu ya zura jallabiyya a jikinsa ko hiramin bai samu zarafin ɗaurawa ba ya ɗaga laubulen ya fito, idanunsa ya sauka a kan ta, ganinsa tsaye a gabanta ya saka ta buɗe bakinta tare da yin murmushi. Ya girgiza kai a hankali ya sunkuya ya ɗauketa a kafaɗa suka fice daga toilet ɗin zuwa bedroom ɗin Ustaz.

Ƙoƙarin kai hannu take zata taɓa tsayayyen gemunsa dake zubda ruwa ya yi saurin riƙe ɗan mitsitsin hannun nata, idanunta zube a kanta ya ce "Na roƙe ki Shalale ki ce ba kiga Abbiey yanayin haramci ba..," Ta yi shiru tana kallonsa ya janye idanunsa sai kuma ya juya da sauri bayan wani abu ya zo ransa ya cafke hannayenta muryarsa a daƙushe ya ce "Me hakan ke nufi Shalale? Da gaske ban fahimta ba, nikam ban fahimta ya zan yi da al'ƙawarin dana ɗaukar wa kai na? Kin rusa komai kin rusa tunanin Abbiye Shalale" Ya yi baya tare da kwanciya yana rufe ido, kokawa yake da tunaninsa wanda ya rabu kashi-da-kashi. "Babu mai ganin tsaraicina sai matata!" Kalaman suka dawo masa, koda wasa ya faɗi abu to gaskiyar kenan, ya zai yi da wannan jirkitaccen al'amarin? Ya miƙe tsaye kamar zai fita ya dawo ya durƙosa daidai tsayin Ridayya duk ya gaji da magana, kuma da taimakon shi dole bakin Ridayya zai buɗe, ya kalli cikin idanunta da suke sauya masa kala a kullum a kodayaushe a taushashe ya ce "Shalale kin ga abin a halin da matarsa ce kawai zata gansa?" Cikin rashin fahimta Ridha ta kalli Ustaz, jin ya ambaci sunan Abbiye ya saka ta yi murmushi dimples ɗinta na lomawa kana ta ɗaga kai, Ustaz ya yi saurin girgiza kai yana runtse gajiyayyun idanunsa masu laushi, faɗuwar gaba na wanzuwa a ko wanne lungu da saƙo na ƙofofin zuciyarsa, ya tsune laɓɓansa a nutse ya ce "Subuhanallahi! Hakan na nufin...?" "Zata zama Matarka idan har da gaske al'ƙawarin zuciya ne, kuma zuciyar ta Ustaz Muhammad-Bilal"

Ustaz bai juya ba, domin ya fi kowa sanin mamallakin muryar. Umma ta ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin ta juya ta kalli Ridayya ta kuma kalli Ustaz kana ta ce "Sai ka ce rainon matarka kake bamu da labari" Ya yi shiru ta taɓe baki kana ta ɗora da "Da sake an bawa mai kaza ƙafa, ka gaggauta sauya tunani" Sai a lokacin Ustaz ya kalli Umma kamar ba zai yi magana can dai ya girgiza kai ya ce "Umma please, kai na ciwo yake" Domin bashi wata magana bayan wannan ɗin, bayan ita kuma bai san wacce magana zai furta Umma ta gane tsakaninsa da Ridayya zumunci ne kawai. Umma ta ce "To, ta dai haramta a gare kuma, she's not your type, kwailar ma?" Ya kalli Ridayya sosai kana ya kalli Umma ya ce "Mene kwaila?" Ta ce "Baka sani ba?" Ya yi shiru ta yi murmushi ta ce "Kwaila ana nufin ƙaramar yarinya, ƴar mitsitsiyya wacce bata fara irgan dangi ba, balle batun al'ada" Ya sake juya idanunsa duk a gajiye yake daga jiya zuwa yau "Irgan dangi?"

"Nono irin na ko wacce ɗiya mace nake nufi Ustaz" Ustaz ya yi saurin rufe ido yana miƙewa tare da toshe kunnensa ya ce "Ya Rasulullah Asstagafirullah, ba a kunnen Muhammad-Bilal ba" Umma ta ce "Tunda na yi saƙo ba? Shekarar ta shida kai kuma shekara ashirin da biyar, ƙanwarka ce babu wani zance bayan wannan" Har ta fita ta tuna abinda ya kawo ta, ta ce "Ana kiran ka a sashin Baffa" Tana furta hakan ta yi waje tana jan tsaki, halin Ustaz gabaɗaya a bauɗe yake ta rasa waya gado? Tana fita Ustaz ya juya ya kalli Ridayya da ta yi shiru idanunta a kasalance ya saka ƙafa tare da zungureta ta buɗe ido a gigice jikinta na rawa da ɓari tunaninta Ammi ce, domin komai yana zaune a ranta daram kamar yadda al'amarin ya nuna a karatu, haddar ƙaramin yaro, kamar rubutu ne a kan dutse ganin Ustaz ya saka ta kwaɓe fuska za ta saki kuka.

"Ni zan yi kuka ba ke ba Shalale, kin ga abinda kika jawo, zan nema miki gafarar Ubangiji ƙuruciya ce da rashin sani" Ya miƙe tare da ɗaukan ta ya nufi ɓangaren Baffa cikin takun nutsuwa da zallar kamala, dab da zai ƙarasa annurin fuskarsa ya ɗauke ya yi kicin-kicin da fuska tamkar ya ce ya shiga uku, ya tsuke girarsa har haɗe wa take saboda tsabar baya son raini. Yana zuwa Ammi dake dafe da fuska domin marin Ustaz ya gigita ta, kunya take ji ya sauke hannunta a ga zanen yatsun shi daya kwanta a fuskarta. Baba ƙarami ya kalli Ustaz ya ce "Muhammad-Bilal mene hujjarka na marin matar ubanka?" Ustaz ya yi shiru domin haka nan ya ji baya buƙatar wani surutu, ya tsaya iya shi da ita Ammin.
"Ina magana ka yi shiru?" A hankali ya ce "Abba!"
Ya faɗa yana nutsa idanunsa cikin na Baba ƙarami "Ba'asi nake tambaya, domin ba zan lamunta ba" Ustaz ya yi shiru Baffa ya juya kan Ammi ya ce "Ke me ki ka yi masa, ya ake neman haukata mini tunani ne a cikin gidana?" Ammi ta ce "Ni ni ni ce da laifi, amma ya shige ba komai na yafe masa" Anuty Kaltum ta buga shewa tare da yin tafi ta ce
Chapter 29 · 0% Book details