← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 118

Sashe 116

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata biyar bayan dawowarsu suka koma hadaɗɗan gidan Ustaz, Umma sosai take ƙaunar Ridayya da yaran da sukai ƙima sosai da wayo aka haɗa Auren Junaid da wata yarinya Iklas sai Zainura da Burhan akai aure lokaci guda, tsakanin Mami da Ammi mutunci ne kawai Tajj ya samu ya yi aure shima da ƙyar Prof ya bawa Hajja Azizat takardar saki.

Misalin ƙarfe tara na dare ta shigo parlon tana sabga ƙamshi uban ƙamshi kanta a ƙasa ta ɗora mayafi saman ɗaurin ɗan kwalin da ta yi na black and gloden ɗin lace sai walƙiya yake a hankali take ta kawowa har ta zo tsakiyar parlon, tunda ta shigo yake kallon ta da wani expression looking da emotions na shekarun baya da suka shege sai yanzu da suke motsa masa a ƙirji da zuciya ashe ba mutuwa sukai ba kawai dole ta saka suka kwanta. Ya ɗan yi tattausan murmushi irin na manya ya ƙarasa tare da buɗe mayafin kanta ta yi saurin yin ƙasa da kai tana murmushi, bata san cewa dattijon zamani bane sai da ta ji ya rungomo ta zuwa jikinsa ya ce "Allah Allahamdulilah daka mallaka mini Azizatuna.....

Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*MUNAFUKIN MIJI*

Nimcyluv
49-50

Mikiya writers Association.

"Abba" ta furta cike da kunya shi kuma ya riƙe ta da tafukan hannayensa, dukda cewa ita ta yi requested auren a wajan shi, amma ji yake kamar ta shiga zuciyarsa, dukkan wasu ƙofofi na zuciyarsa a buɗe suke ƙara raya kan su suke da farfaɗo abinda ya kusa macewa a tsakiyar ƙirjinsa. Hajja Azizat ta ce "Congratulations" Baba ƙarami ya saki hannunta baya ya yi mata runguma ƴar sunna ya koma ya zauna a hankali ya ce "Allahamdulilah" ta nemi waje ta zauna ta ɗan buɗe mayafin kanta sukai shiru can baba ƙarami ya ce

"When last rabon dana ganki haka kusa dani Azizat?"

"Tun ranar ɗaurin aure na" ta furta cikin ƙasa da murya ya jinjina kai kamar yadda Abbiey yake idan yana son kawar da zancen addu'a ya yi sosai mai tsayi kana ya shafa ya ce.

"Allah ya bamu zama lafiya"

"Amin"

"Am still on your mind kenan? Wanne qualities kika gani wajan tsoho mai tarin jikoki har kikai sha'awar aurena?" Ta yi masa wani irin kallo kafin ta ce "Tun qualities É—in dana gani a baya na nace maka, shi ne dai"

"And you left me, har yanzu ban san dalili ba"

Ta ce "Destiny! Ƙaddara mana ita ce dalilin Abba ta raba mu and now we are together, za mu kasance har abada"

Ya yi murmushi yana shafa gemunsa ya ce "In sha Allah" sai ya kalleta sosai ita dai still da garin ƙuruciyarta daman ba wani jikin kirki gare ta, a goge fatarta take ƴar daidai da ita.

"Tahir ɗin da kika sani a baya yanzu fa bashi bane Azizat, ina da yaro mai shekaru wajan 40 gani da jikokai, anya zan iya sauke nauyin ki kowa? Ba ki yi kuskuren zaɓe na a karo na biyu ba?"

Idanunta a kansa ta ce "I'll never regret in sha Allah Abba,in dai kana so na ai komai mai sauƙi ne" bai ce komai ba ya ɗauki wayarsa ya duba, daman tun kiran farko da ta yi masa ya san kwanan zancen yaƙi zuwa wajanta ne sai da ta gama idda, tana gamawa kuma ta masa text via mail kai tsaye, bai tashi zuwa wajanta ba sai da ya tabbatar igiyar aurensa ta hau kanta, bayan shaidu sun shaida. Ya miƙe tsaye ya ce "Zan shige ni" ta ce "Tun yanzu ango?"

"Kina da wajan ajjiye ni ne?"

"Sosai ma" ya girgiza kai ya ce "Kina buƙatar wani abu ne?"

"Babu sai abu É—aya" har zai tafi ya ce "Me?"

"Bari kaga" ya tsaya ta ƙarasu wajan kafin ya ankare ta rungume shi tare da yi masa kiss a kumatu, ya hangame baki ya zama kamar statue ya ji kamar wani ke jan shi, ta yi masa bye bye yana dai tsaye bayan ya tabbatar ba wanda ya ga wannan abin kunyar ya sauke numfashi ya fice.

Fitowa Abbiey ya yi bayan sun kammala magana da Ridayya ya nufo hadaɗɗan main da yake tsakiya yana gaba tana biye da shi hannunta riƙe da hula, ta dube shi ta ce. "To Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri" a nutse ya ce "Amin, shi ne ma tunda bana jin siyasar a raina"

"Haka ne, kawo na saka maka hular"

Ya rausayar da kansa gefe yana kallon yadda take ɗage amma ta kasa ta bashi hular kuma taƙi shi kuma yaƙi sunkuyo da kansa ƙasa "Abbiey please ka miƙo kan" yaƙi cewa komai sai kallon ta kawai da yake da wani irin yanayi mai fisgar zuciyar duk wata budurwa. Ta ɓata rai sai kawai ya saka hannunsa biyu ya ɗago ƙugunta sama "Saka" tana dariya ta saka masa hular tare da tattare gashin ta tura cikin hular.

"Ka yi kyau sosai kamar karka fita ko'ina" ya lumshe idanunsa ya buÉ—e "Me zan taho miki dashi?"

"A'a ba komai"

Ya haɗe hannuwanta biyu ya riƙe "Allah ya yafe kiki Mimi, hakan kyautatawa iyali ne kuma koyarwar Annabin tsira ne, kawowa iyali tsaraba muddin akwai halin hakan"

"To ka siyo mini vanilla ice cream"

"Banda kayan sanyi" tai shiru tana tunani sosai sai kuma ta ce "Ok Gashasshen nama mai zafi da kuma L&Z"

"An gama beb"

"Thank you" ya rungume irin side hug É—in nan ya ce "I love you"

Ta ja gemunsa da yake mata kyau kullum ta ce "You mean the world to me Hayatee" ya ƙara 10 minutes akan yadda tsara zai fita ɗin.

Umma dake sauraron baba ƙarami ba tare data fahimci me yake cewa ba ta ce "Aure kamar wasan yara kai ne ka yi auren ko dai wani?" Ya kame girka ya ce "Ni ke wasan kenan Hadiza?" Ta ce "A'a, abu ne na ji shi gaba-gaɗi" a hankali ya ce "To da gaske aure na yi wallahi Allah, kuma yau za a kawo amaryar kuma ƴar'uwarki"
"Aure dai irin wanda iyayenmu sukai mana kake magana Tahir?" A fili ya maimaita “Tahir” sai kuma ya yi murmushi ya ce "Shi dai, ai ni mijin mace huɗu ne kuma ban taɓa miki alƙawarin zama dake ke ɗaya ba, ban kuma yi auren don na ƙuntata miki ba, ban yi kuma don bana son ki ba Umma Ubangiji ya ƙaddara auren ya kasance kuma ya kasance ɗin, ki bani ƙarfin qwwa please na shaideki a bayan idanunki kan cewa ba ki da wata matsala, tunda nake dake shekaru nawa ban taɓa bijiro miki da maganar aure ba, na aure ki don ina son ki kuma zan cigaba da son ki don Allah ki cire komai a zuciyarki ku zauna lafiya ita sam bata da matsala"

Ta wani kalle shi tana murmushi ta ce "Waka aura? Ina nufin wace kishiyar tawa?"

"Hajja Azizat, mahaifiyar murgayi Sadauki"

Da wani irin firgitaccen yanayi mai ban tsoro da kuma tashin hankali, daya saka Umma miƙewa tsaye ba tare data shirya hakan ba, baki sake kawai take kallo Baba ƙarami kafin ta haɗiye wani irin yawu mai ɗaci ta ce "Now i understand, cewa za ka yi tsohuwar budurwarka ka aura domin ka nuna mini iyaka ta na cewa a rashin ta ka aure ni Tahir" ya dinga kallon ta ya ce "Amma tsakanin ki da Allah tunda muke kin taɓa ji na yi maganar ta?"

"To bayan ta yi aure ta ya ka aure ta?"

"She has been divorced" ya ce yana kame fuska.

Umma ta rushe da kuka sosai ta ce "Mayya ai na sani wallahi tana sane ta kashe auren domin ta aure ka, kawai zan tattara na bar muku gidan domin sai abinda na gani kawai" Baba ƙarami ya yi murmushi ya nufi inda take yana cewa "Zo ki ji"

6 month later
Kuka take sosai tana gogen hawayen da yaƙi tsaya mata shi kuma yana gefe yana ta yi mata dariya abinsa, ta juya ta kalli Al'hussan dake bacci gabaɗaya watan su shida, ta kalli takardar hannunta daya tabbatar tana ciki ta dube shi ta ce "Abbiey don Allah ka rufa mini asiri, na shiga uku wanne irin ciki kuma? Ni a haihuwa zan ƙare kenan" ya ajjiye wayar hannunsa cikin kulawa ya ce "Ba kowa Allah ke wa wannan ni'imar ba Mimi, ki yi farinciki this time around za ki haifa mini me kama da ke" cikin damuwa ta ce "Ai ba za kaga aibu ba, sai da na ce kar ka yi kar ka yi amma ka yi, gabaɗaya watan su Al'hassan shida ya kake tunanin za su lalace? Da wanne ido zan je gida a ganni da ciki?"

"But ba iskanci kikai ba mijinki ne ya miki shi Mimi" ya faɗa a taushashe kawai ta sake rushewa da kuka, shi abin duk mamaki yake bashi mene a cikin yin kwanika to? Girgiza kai ta yi ta ce "Zan zubar da cikin nan gaskiya ka yi haƙuri" tana faɗa tana miƙe zata bar bedroom ɗin, daman dawowarsu kenan daga asibiti saboda zazzaɓin da take hannu ya saka ya fisgota yana wani irin nishi idanunsa sukai jajir ya ce "za ki zubar da me?"

"Cikin" ta faɗa ba tsoro. Ya matse hannunta ya yi wani irin murmushi ya ce "Wannan shi ne abinda za ki yi har abada naƙi yafe miki"
Chapter 116 · 0% Book details