Sashe 8
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na bi adolescence da gudu ba wando, zan watsa miki tafi a nan wajan Balkisu, ina cewa gata duk muka je nema mata amma ta shafa wa idanunta kwallin rashin kunya ta baɗa masa ƙasa a idanu, idan na tuna abinda ta yi wa Ustaz kamar na zunduma ihu haka na ke ji ni da kai na kunyar haɗa idanu nake da shi" Balkisu ta ce "Ba haka nake nufi ba Yaya Junaid, abinda Ridayya ta yi bata kyauta ba amma ba tsana zamu nuna mata ba, ba zamu guje ta ba, tana buƙatar nutsuwa a kuma jata a jiki, ina cewa kaima akwai naka zanen ƙaddarar saboda matsalar Genotype har yanzu ba ka yi aure ba, duk wacce ka samu da sunan mata ana yin gwaji za a ga Genotype ɗinku bai yi daidai ba" Ganin abin na neman zama wani daban ya sa Baba ƙarami kiran Bilal a waya ya ce yana buƙatar ganinsa cikin gaggawa ya umarci kowa ta shigo.
Sallamar Ustaz ya sa suka kalle shi baƙin wagambari ne a jikinsa, sai wata ƴar ƙaramar riga kamar top da wacce akaiwa aiki a jiki ya ɗora hula akan shi, ɗaya hannun rigar a tattare ga audiga a jiki gabaɗaya ya fi kowa girma a wajan hakan yasa ya yi kwarjini sosai. Kansa a ƙasa yana dafe kai saboda jiri jinin da aka ɗiba a jikinsa yasa jiri ke kwasar shi. Ya nemi waje ya zaune ya harɗe ƙafa da ƙaramin carbi a hannunsa can ya juya ya ce "Sannu Abba, gani" Yana faɗa ya yi shiru.
"Na ganka, Ina ka shiga Ustaz?" Junaid ya ce "Baba ƙarami ba ina Ustaz ya shiga ba, cewa za ka yi me ya sameka Ustaz kalli hannunsa, jininka aka ɗauka?" Shi dai Bilal bai tanka kowa ba a ransa yake jin dole ya ci uban Junaid yaga raini na son shiga tsakaninsu. "To Allahamdulillah, yau zan ƙare magana ƙare kuma amsar ka shi ne zai kawo ƙarshen komai Ustaz muddin ka ce kana son Ridayya zan maka Zameer a kotu ya saketa na aura maka ita, shin da gaske kamar yar da Junaid ya faɗa kana son Ridayya?"
"Shi ne kiran Abba?" Baba ƙarami ya ce "E, bani amsa" Ustaz ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa a hankali ya ce "Ridayya ƴata ce, kuma na san babu aure tsakanin uba da ƴarsa" Bai bawa kowa damar magana ba ya fice saboda jirin dake shirin yar da shi a wajan. Yaya Zuhura ta jinjina kai ta ce "Allah ya yi maka gyaɗar duguwa, daman mai ka ci na asham balle ka yi ramakon sallah? Me Ustaz zai yi da Ridayya yarinya duk da lalace ta zama tsohuwa, sai dugun baki da haƙora a waje, ni ɗin nan da nake yayarta na fita kyan gani hatta Amma tafi Ridayya kyan gani fa?"
Balkisu girgiza kai kawai ta yi zuciyarta bata yi mata daɗi, sauran ƴan mazan ba wanda ya tofa tashi a ciki haka Amma. Mami ta kalli Baba ƙarami kanta a ƙasa ta ce "Zan iya tafiya Baba ƙarami?" Baba ƙarami ya ce "Tashi ki je Fatima Allah ya kyauta ya sauwaƙa" Ta miƙe tsaye ta ce "Amma bari na shiga ciki"
"Mami tun yanzu? To shikenan" Zainura ta miƙe da sauri ta bi bayan babarta, da ƙyar Mami ta kai kanta ɗaki "Mami Yaya Ridayya kar ta mutu" Ta sauke numfashi ta ce "Babu abinda zai sameta, ko wacce kalar mace da kalar ƙalubalan da take fuskanta a gidan aurenta, na yi imani baƙin cikin ɗa namiji ba zai taɓa kawo ƙarshen rayuwar Ridayya ba kamar yar da bai kawo ƙarshena ba, da yawa wasu burinsu kawai su yi aure ba tare da tunanin kalar rayuwar da zasu fuskanta a gidan miji ba, Zainura babu soyayyar har abada fa, da yawa wasu matan haƙurin su yasa ake ganin kamar basu da matsala a gidan aurensu"
Kwana biyar da yin rigimar asibitin, amma Zameer sau ɗaya ya leƙa shima a gigice cikin dare da buƙatar kai da kai ta kaishi, duk yar da yake son samun nutsuwa da Khairy sai ya ji ba kamar Ridayya ba, baya buƙatar komai a wajan Ridayya sai wannan abun. Tana kwance sai numfashi take da ƙyar kamar daga sama ta ji mutum ya faɗa mata ka, za ta yi ihu ya ce "Kee nine Rayuwarki ne, mai sona"
Numfashi ta sauke tana rufe ido "Ina ka je?"
A taushashe ya ce "Aiki nake domin rufin asirinmu da gujewa raini" Ta yi shiru can ta ce "Kwanaki na kira ka cikin dare na ji surutai da wata murya ana cewa a yi a hankali ban saba ba"
Dam! Kirjinsa ya buga sai kuma ya ce "Ƴan fashi, wallahi ƴan fashi ne Ridha wuƙaƙe sun fi talatin akai na" Tunda daga sama har ƙasa ta dinga kallonsa ba ta yi magana ba irin kallon da take masa yasa shi faɗin "E, dake na sha maganin tauri ai wuƙa bata yankata da tuni sun kashe ni" Gabanta ya faɗi ita kam aka kashe Zameer bata da wani saurin gata a hankali ta ce "Na ji sai ihu kake kam" Cikin rashin sani ya ce "Ihun daɗi ne"
"Daɗi kuma" Ya haɗe fuska tare da mitsi mitsi da ido ya ce "Bala'in daɗi ma, saboda wuƙa bata shigata kuɗin da kika bani kawai suka kwashe ai" Ganin yana sauya salo ta riƙe hannunsa ta ce "Bani da kuzari, yunwa na ke ji ka bar ni" Zameer ya ƙara haɗe fuska da kyau ya ce "Ridayya na bar ki hakƙin nawa?" Idanunta na zubar da hawaye ta ce "Shi kansa tarayya sai da nutsuwa da cima mai daɗi Meer, bani da nutsuwar hakan ba zan iya ba"
Ya miƙe tsaye ya ce "shikenan ba komai kwanta na haƙura ko zan mutu ban taɓa ki" Tausayinsa ya kamata tasan hakanma soyayya ce ta ce "Bismillah"
Kuka take sosai saboda tsananin azaba kamar ta yi amai, Zameer ko a jikinsa buƙatar maje hajji sallah ya miƙe yana goge zufa sai yanzu yake jin damuwarsa duk ta kau Ridayya bata da wani amfani gare shi bayan wannan. "Tafiya za ka yi ka bar ni?" Ya haɗe fuska ya ce "Ina da uzuri" yana faɗin hakan ya fice ta kifa kanta ta saki wani irin kuka mara sauti.
Washegari da yamma Baba ƙarami ya zo duba Ridayya ganin ko zama ba ta yi ya sa shi buɗe mata ido tare da kwasarta zuwa gida a cewarsa ba zata koma gidan Zameer ba sai ya gyara halinsa.
Babu wanda ya san Ridayya na gidan ya gargaɗe ta kar ta faɗawa Zameer inda take yana fita daga ɗakin ta masa message ya yi haƙuri ya yafe mata kar ya zo asibiti bata nan tana gidan Baba ƙarami. Sanda saƙon ya isa Zameer na ɗaki Khairy kwance a gefensa tsaki ya ja don tafiyarta bai dame shi ba muddin ba hakƙinsa yake buƙata ba.
Cikin dare Ustaz ya shigo domin ya jima a waje saboda a gobe ne zai koma Lagos har ya shige kitchen ya ji kamar motsi, ya dinga mamakin waye a kitchen kuma cikin dare? Har zai juya sai kuma ya juyo ihu da da kuma ƙarar faɗuwar kwanoka da sauri ya nufi kitchen ɗin domin ganin waye a ciki....
Page 5
Idanun Ustaz ya sauka akan abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwarsa, ya yi zaton wani a cikin kitchen ɗin, amma mummunan ganin da ya yi ya sanya ya ɗan yi baya a tsora ce tare da rufe idanunsa can ƙasan zuciya Ustaz Bilal ya ce
"Ya subuhanallahi! Asstagafirullah" Ridayya ya gani da Zameer kwance a ƙasan kitchen ɗin, turmi da taɓarya, ya saka hannu ya shaƙe mata wuya sai shure shure take tana kakari tamkar na fitar hayyaci ko zarar rai.
Ustaz da ƙyar ya ja ƙafafuwansa da nufin barin wajan domin jiri ne ya ji ƙoƙarin yasar da shi a ƙasa, al'amari Ridayya kullum girmama yake yana sake lalacewa.
Karo suka ci da Baba ƙarami daya fito hakan ya sa Ustaz tsayawa tunda ya ga lokacin assalatu bai yi ba, balle ya yi zaton Baba ƙarami sallah ya fito yi.
"Ustaz ba dai ya zo kake dawowa ba?" Ustaz ya kalli baban nasa a hankali ya ce "E, dawowar kenan" Cikin gamsuwa ya jinjina kai yana mai faÉ—in.
"Ai tun ɗazo nake jiranka mu yi magana, har dare ya yi shiru ka jira ni a parlo zan duba naga ta'addin me nake ji tun a shashin baya har hanyar kitchen" Kafin Ustaz ya yi magana Baba ƙarami ya nufi hanyar kitchen ganin da gaske can ya nufa, kuma baya fatan ace mahaifinsa yaga abinda nasa idanun ya gani da ɗan saurin harshe ya ce
"Abba, ni ne fa"
Baba ƙarami ya tsahirta da tafiya ya ce "Kai ne me?" Kan Ustaz a ƙasa
"Ruwan zafi na haÉ—a, na É—an zaga baya ne"
"Ruwan zafi a daren nan Mai babban suna? Kamar wani ƙaramin yaro kake suntiri da ɓuruntu?" Shi dai Bilal bai ce komai ba, domin baya buƙatar sake shimfiɗa wata ƙaryar akan kare Ridayya, ya nufi hanyar parlour. Yana zama Baba ƙarami ya zauna yana ƙarewa ɗan nasa kallo a nutse ya ce
"Bilal?" Da Idanu kawai Ustaz ya amsa Baba ƙarami ya ɗora da faɗin
"Ridayya tana gidan nan, na ɗakkota daga asibiti rayuwar yarinyar nan abar dubawa ce, bai kamata a ƙarancin shekarunta a ce tana fuskantar ƙalubalen gidan aure da matsalar miji ba, kasan rayuwar Ridayya ka fi kowa sani da halin data tsinci kanta a baya, me ya sa ba zaka aureta ba?"
"Aure Abba?"
Baba ƙarami ya yi murmushi ya ce "Shi fa, naga ba haramun bane" Ganin Ustaz na shirin miƙewa ya saka cikin bada umarni Baba ƙarami ya ce "Kar ka kuskura ga tashi, ko baka son Ridayya zaka aureta"