← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 118

Sashe 49

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kokawa suka shiga yi duk ya gigice da tsananin buƙatar ta ita kuma ta yi alƙawarin har gaba da abada idan akwai ba zai ƙara morar jikinta ba. Ta zage iya ƙarfinta ta gantsara masa cizon daya kusan kwashe masa fatar wuya ya saketa ta yi saurin fitowa daga ɗakin tana nufar ɗaya ɗakin da yake da wata mata a ciki.

Wani baƙin ciki ya tukare a wuyan Zameer ganin yadda ya ga samu kuma ya ga rashi amma ko zata mutu sai ya fanshe duka sauran ranakun daya biyo ta bashi. Ya yi tsaki ya fita.

Kuka take tamkar ranta zai fita numfashinta na tsarƙewa saboda yadda zuciyarta ke mata zafi da raɗaɗi, idan ta tuna bata da kowa bata da wanda zata raɓa balle ya ƙwatar mata ƴanci sai ta ji komai ya sare mata ta ji tamkar ta yi giving up ko ta ji kamar ta kashe kanta. Rana zafi inuwa ƙona, ruwan daya dake ka shi ne ruwa ta yarda rayuwa da ƙaddarata a tare Ubangiji ya samar da su kuma sun zama jinin jikinta yadda ba zata taɓa iya guje musu ba.

Ridayya ta yi kuka mai isarta gashi tun tayin abincin da aka yi mata taƙi ci babu wanda ya sake sauraren ta da wani abinci tamkar gudunta suke haka suke mata acting. Kasancewar su gabaɗaya fulani kowa kyakkawa farin tas da shi zai ya zama ta kasance kamar baƙar tukunyar da aka tuƙa farin tuwo a cikinta.

A hankali ta lumshe idanunta tana shafa cikinta da yake ta zungurar mata mara wata iriyar ƙauna mai ratsa fata, jini da ɓargo ke ratsa zuciyarta ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗorawa cikin tana jin shi ne kawai ya rage mata a yanzu.

"Idan kin gama kukan tashi ki fita daga É—akin baiwar Allah" Ridayya ta kalli matar, wacce ta yi saurin É—auke kai tana cewa "Bismillahir Rahmanir Rahim"

A sanyaye ta miƙe tana dafa bango ta fita ta nufi ɗakin tunda tana da tabbacin Zameer ɗin ya fita. Tana fita Iyatu ta ce

"Shatu maza É—akko turaren mayun nan ki turara a É—akin nan"

"Mayu kuma Iyatu?"

"Su fa, au wai ba ki san mayya Giɗaɗo ya auro daga Birni ba can? Ayya ai mayya ce saura ƙiris ta ci ɗari ba ɗaya shi ya sa kika ganta baƙa ƙirin wallahi tallahi"

Shatu ta yi zuru don a duniya tana jin tsoron maye an ce cinye mutane suke tare da soye naman shi su cinye. "Mun shiga uku Iyatu kar ta suÉ—e mu"

"A'a kurwa kurr namanku É—aci gare shi, da kun ganta ku gudu ai kuna ji ko? Kar ma ta kira ku kuje"

GiÉ—aÉ—o na fita ya yi waje can dandali jikin Hanne na rawa ta zo wajansa ta ce "Masoyi ka dawo wai da matarka? Da gaske ba zaka aure ni ba?"

Kallon tsaf ya yi mata kana ya ɗauke kai yana danna wayarsa hankali kwance tunanin yadda zai amshi takardun wajan Ridayya kawai yake domin sune plan ɗinsa da burinsa a yanzu. Hanne ta fashe da kuka Allah yana gani tana son Giɗaɗo tun tana ƙarama kuma shi ma yana sonta tunda ya je birni ya dawo ya wargatsa duk wata shaƙuwa da sukai. Ta zube ta ce "Giɗaɗo ka tausaya mini ni ce Hannen Nahutun Batsari ni ce Hanneka fa Giɗaɗo ko ka manta ne?"

Ya ja tsaki ya miƙe tsaye ko inda take bai kalla ba ya yi gaba a wajan gani yake gabaɗaya ƴan'kauyen ba sa'aninsa bane shi ɗin dabanne a cikin su.

Rayuwa ta yi wa Ridayya zafi duk ana ɓoye mata har ta fahimci kallon da suke mata na mayya bata uhm bata un'uhm bata walwala bata sukuni damuwa sun yi mata tsaye a zuciya ko bacci bata iyawa yadda taga rana haka take ganin dare idan an sammata abinci ta lasa wani lokacin ta kalle shi a Idanu ta nutsu ta gane mene asalin so ya ake jinsa a ƙirji da zuciya? Amma kwakwalwarta ta gaza bata damar yin hakan. Ta zama tamkar wata sauna gashinta kullum ƙara yawa yake kamar buzuwa. Yatsarta da take sha tun tana ƙaramar yarinya shi ta dawo sha yanzu. A haka watanni suka shura mata har zuwa wajan wata uku da zuwanta cikinta ya shiga wata na takwas.

Da sassarfa ya shiga sakkowa daga strains ɗin benen idanunsa a ɗan lumshe daga shi sai gajeren wando da wata milk ɗin Armless daya buɗe zip ɗin gabanta a ɗan gurguje yake sakkowa ɗin bakinsa kuma bai fasa ƙwalla mata kira ba.

"Mother mother mother"

Tunda daga kitchen take jiyo muryarsa a narke rikicinsa bata tsoro da mamaki yake hannunta duk fulawa ta fito a ɗan gigice tana mai tsayawa ganinsa zaune a ƙarshen step ɗin benen ya tanƙwashe ƙafa ta ce

"Sadauki lafiya kake? Wannan kiran fa?" Ya ƙura mata Idanu

"Magana za ka yi Sadauki ba kafe ni da wannan idanun naka ba" Hajja Azizat ta faɗa tana kallon tilon ɗan nata wanda take ji har ƙasan zuciyarta zata iya sadaukar da komai nata akan shi. Ta rikice ganin yaƙi magana ta ɗauka ko bashi da lafiya ne? Tunda yake bai taɓa cewa wassh saboda ciwo ba...

Ta koma kitchen ta wanke hannunta tana bawa Dija umarnin ƙarasa wanke-wanke ta dawo gani ta yi baya parlourn da sauri ta nufi bedroom ɗinsa nan na baya ciki daga can ta ji sautin kiɗan jitan shi ta nufi wajan, ta tsaya saroro tana kallonsa ya tuɓe rigar sai training yake a gym ta ce

"Sadauki" Ya juya ya kalleta yana É—aga mata hannu tare da juya yatsunsa alamar "What Mother?" Ta kashe sautin jitan kana ta rage gudun injin ya marairaice fuska sosai yana kallonta ta ce

"Ka bani tsoro Sadauki ba ka ji zuciyata ba, baka da lafiya ne? Mene ya sameka? Are you okay?"

"Mother" Sadauki ya faɗa yana sauka ya ce "Kin taɓa ganin Sadauki ya yi rashin lafiya?"

"To wannan kiran gaggawar na mene?"

"Just to see you Mother, na farka na leƙa bedroom bakya nan shine na biyo ki fa"

Ta dinga kallon shi ya É—aga hannu ya É—ora a kafaÉ—arta suka fita waje ta ce

"Yaushe Sadauki zai girma ne ni Azizat?"

"Sanda na yi aure, ko na yi aure ban taɓa girma wajan Babata da Matana Allah idan ban muku shagwaɓa wa zan wa?"

Waje ta nema ta zauna ta ce "Wallahi da za ka yi auren da na ji daɗi sosai na samu jikokai kaga kai kaɗai Allah ya bani" Ya girgiza kai yana ɗaukan ƙafa ya ɗora saman table yana mai sauya channel zuwa kallon ball ya ce

"Da kowa zagewa zan yi nai ta haihuwa, matana ta haihu nima na haifa"

"Ikon Allah. To ka fito da matar auren mana"

Ya ɗan ɓata fuska sai kuma ya girgiza kai ya ce "To har yanzu babu ƴan'matan" Mother ta ware Idanu sosai ta ce "Duk tarin ƴan matanka Sadauki? Kiran yau da ban na gobe daban"

Ya yi mata shiru kawai don hankalinsa ya koma kan ball wasa ake bugawa sosai tsakanin Hala Madrid da Bercelona. Ta ce

"Ina magana fa"

Ya juya ya kalleta sosai tasan lissafin abinda zai faɗa yake can a nutse ya ce "Su duka ƴan matan suke so na, ina son samun wacce zuciyata ta nutsu a kanta Mother, ina son soyayya sosai, ƙauna, tattali da kulawa ina son macen da ni zan koya mata mene soyayya da yadda zata so ni, wacce zan sha wahala a kan ta sosai. Sadauki na son soyayya" Ya faɗa hankali kwance don har a ransa yake jin normal ne

Hajja Azizat ta riƙe haɓa ta ce "Naga abinda ya dame ni" Sadauki ya ce "A'a fa ki daina salati kamar na faɗi mugun abu, a duniya babu abinda yafi daɗi irin zama da wanda zuciyarka ke tsananin so"

Tana ƙoƙarin magana ya buga ihu ya miƙe yana "Go goooo!" Daidai nan wani ya shigo cikin parlourn Sadauki ya tafi da sauri ya bawa mutumin hannu ya ce

"Gooo Daddy mun cinye ku goo" Daddy ya girgiza kai kawai ya ce "Yau ɗaya Madrid sun abin ƙwarai" Sadauki ya ɗan rusuna sosai har ƙasa ya ce "Good morning Daddy"

"Morning Friend, ya jita? Ya kuma business?"

"Good" Daidai nan wayar Daddy ya fara ringing aka saka secretary a number bai É—auka ba sai da yaga Hajja Azizat na kallonsa ya É—aga ya ce

"Laminu ya akai ne?" Ya yi shiru can ya ce "Oh waje mai kyau please, ya yi tsari da ƙawa a shirya sosai don na daɗe ban yi ba, a fa shirya?"

Ya kashe wayar Hajja Azizat ta ce "Sannu da shigowa Prof"

"Yawwa wife, ya rigimar É—anki Sadauki" Ta yi murmushi

Ƙara wayar Prof ta yi notification ya shigo Sadauki ya kalli screen ɗin wayar ya ce "Daddy wannan secretary ɗin baya ga jiya da turo maka pictures? I noticed that" Prof ya miƙe ya ce

"Yhhh pictures É—in motoci ne sababbi da zan siya na bawa secretary aikin hakan yanzu ma can zani"

"Yanzu ka shigo tunjiya kuma yanzu zaka sake fita?" Ya ce "To ya za a yi ni kaina ina buƙatar iyalai na kusa dani, na yi kewarku sosai wallahi"

Jikinta a sanyaye ta ce
"To Allah ya tsare ya kiyaye ya bada sa a" Prof ya É—an bawa Hajja Azizat side hug ya ce

"Love you wife soon zan dawo" yana ƙoƙarin fita Sadauki ya ɓata fuska ya ce "Daman baka so na ka fi son Mother"

"Banda ciwon baki me kake saka mutane Sadauki? Shekaru 30 ciff kake wannan shekarar fa, and idan ban so matata ba wakake tunanin zan so?" Ya haÉ—e rai shi dai ganin hakan ya saka Prof rungume Sadauki ya ce

"Stubborn friend i love You" Sadauki ya É—age gira shi ma.

Bayan Prof ya shiga mota driver ya ja ya kira number secretary É—in a hankali bayan an É—auka ya ce "Sweetheart Lina ina bisa kan hanyar hotel É—in...."
Chapter 49 · 0% Book details