← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 118

Sashe 62

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wacece Ridayya mene haɗin ta da Bilal abinda ya faru ya yi confusing ɗina, dana juya naga Little na ƙara kallon Ustaz sai tsoro ya kamani kamannin Muhammad-Bilal nake gani kwance a fuskar Little hakan ya tabbatar mini akwai alaƙa mai ƙarfi ta jini a tattare dasu duka biyun, da Ustaz ya yi aure zan iya cewa wannan yaron jininsa ce ya fito ne daga ƙwan halittar Ustaz na haihuwa"

"Tajuddeen ina magana"

Mahmah ta faɗa tana taɓo Tajj daya zurfafa a tunani, ya tuna sanda Majnun yake cewa Ridayya ita ce wacce ta bashi tsoro a lokacin a area ɗin su Ustaz ne, ya tuna sanda ya yi mata gani na biyu furucin data faɗa ta kira sunan “Abbiey” abu mai muhimmanci kamannin Ustaz da Little da yadda Ustaz ya riƙe fuskar Ridayya ɗin banda yana da kusanci da ita ko farcenta ba zai taɓa ba. What is going on? Meke ɓoye?

Ya miƙe tsaye yana ƙara zurfafa tunaninsa a matsayinsa na police mai rang ɗin DCP a firgice yana dafe kansa ya ce "Bilal's adopted daughter?"

"No! But how ya akai ban taɓa tsayawa na yi tunani a kan haka ba? Why Tajuddeen mene ya saka duk wannan wahalar da Ustaz yake sha na neman yarinyar nan ashe ina tare da ita? No wonder Ustaz ya damu da batun Junior ashe jininsa ne tsatson shi" Tajj ya shiga damuwa lokaci guda amma daya tuna wani abu sai ya ji damuwar ta kau babu ita dole ya idda nufinsa a kan buƙatar zuciyarsa.
Zama ya yi tare da yi wa Mahmah bayanin komai ta jinjina kai ta ce

"Allah Alhakkamu sarki gagara misali Ubangiji ya sa ƙarshen wahalar kenan, Allah ya jiƙan iyayensu da rahama gaskiya na yi wa Muhammad murna da farin ciki dole ya ruɗe sosai shekarun da yawa kuma akwai shaƙuwa tsakanin zuciyoyin guda biyu"

Ustaz na fita motar da yake amfani da ita idan ya zo Kano ya shiga, ya jima yana sauke numfashi da tunanin ta inda zai ɓulluwa lamarin Ustaza da kalaman da zai yi amfani da su wajan rarrashinta na nesan ta kansa da ya yi da ita, zai ɗauki duka laifi ya ɗorawa kansa ita ɗin yarinya ce kuma macace mai tarin rauni da ƙalubale bata da wani zaɓi zai amshi laifin da hannu bibbiyu.
Ya miƙa hannu da ƙyar ya daɗo gudun a.cn motar tare da kunna karatu duk dan ya samu nutsuwa zai ciccije bakinsa yake komai na Ustaz special ne daga yanayin kallonsa zuwa buɗe baki da sarrafa harshensa. Ya ɗauki lokaci kafin ya zame hular kansa ya ajjiye a gefe sumar kansa ta baje ta sakko wacce ta sha gyara da saloon ya yi key tare da yin Bismillah ya bar gidan bakiɗaya.

Har bayan la'asar Ridayya bata daina kuka ba, kewar Abbiey ya dame ta domin da gaske bata yar da shi ta gani a ɗazon ba. Tana zaune ta idar da sallah tana karatun Alkur'ani ko ta ji sauƙin raɗaɗin da zuciyarta ke yi mata wayarta ta fara ringing ta duba a hankali taga an saka “Sahibi”

Ta lumshe idanunta ƙofofin zuciyarta na buɗewa ba zata manta ba shi ne ya yi saved number a haka ta ɗauki kiran tana manna wayar a kunnenta.
"Hello"

"Amincin Allah ya tabbata ga ruhin Hamza Hamdan Hamish barka da yamma Shanshan"

Ya faÉ—a a kasalance ta cikin wayar yana sauke ajjiyar zuciya. Ridayya ta É—an juya idanunta a nutse ta ce

"Ina yini ya mother?"

"Ni ba ki tambayi ya nake ba sai mother, ni da mother waya fara saninki Shanshan?"

"Yi haƙuri to ya kake?"

Ya mirigna daga hagu zuwa dama yana rungume pillown kusa da shi a hankali muryarsa very slowly and sadness ya ce

"Cewa za ki Mijina ya zuciyarka take ba ya nake ba" Ta yi shiru.

Cikin serious magana ya ce "Ridayya"

"Na'am"

"Waye naga ya riƙe ki ɗazo? Ya riƙe miki kafaɗu?" Ta ɗan yi jim tana tunani ita kam ai babu wanda ya riƙe ta yaushe ma ya zo gidan?

"Ina magana" a hankali ta ce "Babu kowa"

Wata razananniyar tsawa mai lafiya ya daka mata ta cikin wayar wacce ta kaɗa hantar cikin Ridayya tana mugun tsoron tsawa ko ihu a ka yanzu zata gigice. Nan da nan ta ruɗe tana ƙoƙarin kashe wayar a hargitse kuma a kasashe ya ce

"Don't try it" kuka ta fashe da shi sosai ta kasa magana yana ji tana kukan bai ce komai ba can dai ya kashe wayar.

Tsakanin minti biyar da kukan ya kira taƙi ɗagawa saboda tsoro ya yi mata DM da

_"Idan na ruske ki gidan Mahmah abin ba zai mana kyau ba ni da ke Shanshan. So pick my call"_

Tana gama karantawa ya kira hannunta na rawa ta ɗauka ta kasa magana bisa mamakinta sai ta ji ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya mai ƙarfi kuma muryarsa can ƙasa kamar ba Sadauki ba ya ce

"I am sorry Shanshan kar ki yi fushi dani" Ta yi shiru ya ce

"Ridayya ina da zuciya a nan ɗina" Ya nuna saitin ƙirjinsa dukda bata ganinsa "Yeah! Ina da zuciya kuma ina da masifar kishi a kan abinda nake so, idan da akwai abinda Ubangiji ya jarabce ni da shi a kwanakin nan bai shige ba, ke ɗin ƙaddarata ce kuma wallahi tallahi ba ki isa ki zama ƙaddarata ba sai dai mu zama ƙaddara juna. Ki saka a ranki duk inda kika sanya ƙafa za ki ga Sadauki a wajan, kuma ni na fi ƙaunar duk abinda yake bani wahala ko yake nuna mini ƙi so don't ever trying to reject me kar ki ce za ki bani wahala don sai dai mu wahalar da juna, yadda bana iya bacci ba zan barki ki runtsa ba sai dai idan ya kasance kina gefena ina jin saukar numfashinki a ƙirjina ina riƙe dake yadda na san ba za ki guje mini ba"

Tsoro ya kama Ridayya da ƙyar ta ce "Me ya kawo maganar nan Sadauki i think it's over between us, everything is over between us.....,"

"Uhm ko?" Shiru ta yi zuciyarta na bugawa dukda bata ganinsa tsoro da fargabar abinda zuciyarta ke ƙoƙarin ɗarsa mata a kan Sadaukin ya fara gigitata dukda ƙoƙarin da take na danne hakan bata son yarda ko gasgata hakan bata so bata shirya ba, ha dan komai ba sai dan illar da namiji ya yi mata a rayuwa a cikin kunnenta ta tsinkayi kalmar daya faɗa

“I have a feelings for you Ridayya no fall in love with you"

"Sadauki please, the game is over ka je wajanta ka faÉ—a mata"

A hankali cikin muryar tausayi ya ce "E zani, amma ke za ki rakani na faÉ—a mata yanzu ma ai ina rihazal ne"

Ta sauke numfashi ya ce "Ki yi haƙuri please na miki tsawa ban so ba" nan ma ta yi shiru ta ɗauka ba zai sake magana ba ne sai ta ji ya ce

"Zan zo fa, ba rana kawai ki jira zuwana bye ki kula mini da kan ki Shanshan ki shafa mini kan Son"

"To" kashe kiran ya yi ta jingina tana lumshe idanunta gabaɗaya abinda bata taɓa ji ba shi ke ƙoƙarin mamaye ta tare da yi mata shigar saurayi Sadauki yana da rigima kuma da saurin shiga rai don dole tana jin daɗin yadda yake ƙaunar Little har zuciyarta.

Sadauki na gama wayar ya miƙe ya nufi down stairs ya iske mother zaune tana kallo ya ƙarasa kusa da ita ya yi shiru yana kallon waje guda abu ne mai wahala Sadauki ya zo kusa da mother ya mata surutu ba shirun nasa ya bata mamaki ta ɗan taɓa jikinsa ta zare ido ta ce

"Baka da lafiya Sadauki?"

Ya girgiza kai kawai bai ma san me yake ba "Ya zaka girgiza kai bayan ga jikinka nan ya yi zafi, daman tunda ka shigo ka shige É—aki na lura ko abinci baka ci ba what is the matter? Meke damun Sadaukina?"

"Ki yi mini addu'a mother ki sani cikin addu'arki don Allah" Ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da ɗage girarsa kansa na yi masa wani irin ciwo ga zazzaɓin daya rufe jikinsa lokaci guda

"Addu'a kullum cikin yi maka nake ita Sadauki shi ya sa bana son ka saka abu a rai ka ƙwallafa na ci a kai. Ka yi ta addu'a ka ji ko komai ya yi zafi maganinsa Allah duk wata jarrabawa tana tare da nasara"

"In sha Allah love thanks"

Da daddare bayan sallar issha Ridayya na kwance a kan gado damuwarta ta dawo sabuwa fil ga tunanin rashin gata da iyaye ga tunanin Zameer da fargabar abinda zai iya aikatawa a kanta. Ga tunanin video idan ya fita da wanne idanu zata kalli Junior? Ta yi masa bayani ga al'ummar gari da suka shayar da ita maɗaci ga tunanin Sadauki da rigimarsa da sauyin da ya yi na lokaci guda idan ta tuna kalar rayuwar da ta yi a gidan aurenta sai ta ji a duniya ba abinda data tsana irin namiji da kuma aure idan ta tuna ƙauyen Batsari sai ta ji ko sunan Katsina bata ƙaunar ji.

A hankali take jiyo sautin muryar Tajj yana magana yanayin yadda yake shiru ya bata tabbacin bashi kaÉ—ai bane a parlourn koma shi da waye muryar Tajj É—in ita ce a sama wancan É—in kuma maganar tasa gajeriya ce domin sai Tajj ya jima yana magana kafin ta ji ya yi shiru.
Yunwar da ta ci ƙarfinta ne ya sanya ta miƙe bisa dole ta sanya slippers tare da ɗora hula ta fito duguwar rigar bacci ce a jikinta wacce ta kwanta ta haska dark black skin ɗinta hasken idanunta da jajayen laɓɓanta kawai ake gani sai tulin gashin girarta.

Magana yake a nutse hannunsa riƙe da cup yana ɗan juyawa kaɗan saboda zumar dake ƙasan kofin fararen ƙafafuwansa gabaɗaya ya zuba su saman table ɗin da aka jera masa abin buɗe baki daman haka ɗabi'arsa take ko ya tanƙwashe ƙafafuwansa ko ya miƙar dasu saman abu. Kaɗa ƙafar yake a hankali yana jin Tajj na cewa
Chapter 62 · 0% Book details