← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 118

Sashe 27

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Ustaz ya dawo da Ridayya daga asibiti ƙaramin yaƙi a kai a gidan, har Baffa na cewa wallahi sai ya ɗaure Ustaz muddin ya ƙara taɓa Ridayya idan kuma da gaske shi ne ya cikinta basu da labari sai a faɗa. Ranar kukan makirci Ammi ta dinga yi tana iƙirarin zata bar wa Baffa gidan, sosai Baba ƙarami ya ji zafin maganar sai bai nuna ba, Umma kuma ta ce idan har ita ta haifi Ustaz wallahi ta sake ganin da yarinyar sai ya san true color ɗinta, ya fusata ya tattara kayansa ya bar garin daman karatu zai je ƙaruwa na shekara huɗu duk a kan Ridayya domin ya bata rayuwa mai kyau, riƙon Ridayya ya dawo hannun Ammi, ta kaɗa ruwan gasara ta ɗora mata cikinta ya kumbura kuma ta hanata ruwa, izaya kala-kala Ridayya ta tashi wata gala-gala sai a kira sunanta bata san ita ake kira ba, kullum tana naɗe kanta yaƙi tsayiwa. Daga ƙarshe maganin bacci Ammi take bata yarinya ta yi ni guda cur tana bacci tana farkawa zata sake bata, har ya yi effecting nata, bata taɓa yi bacci idan ba a bata maganin ba, ta zama ƴar maye wanda ƙarfin maganin ya girmeta ya fara taɓa tunaninta yanzu za ka yi magana yanzu zata manta me ta ce. da ƙyar aka samo ta fara tafiya yi ɗaya biyu zata faɗi ko abinci aka bata ci idan ba gasara ba sa maganin domin su ta sani matsayin abinci sai gayen tuwo. Sanda ta isa saka makaranta Ammi ta ce ba yanzu ba, a tausaya mata ai yarinyar ba wani wadataccen hankali gare ta ba, karatun ma ba lallai ta fahimta ba, dukda cewa akwai makaranta irin ta su ta samu rangwamen hankali. Ustaz har tsayin shekaru huɗu bai dawo ba, ya tafi ta biyar farin ciki ya kama Ammi lokacin ta mallake gida da ita sai yaranta. Baba ƙarami ya daina shiga part ɗin saboda Baffa bai fiya zama ba, arziƙi ya ci uban na da ta ko'ina alheri zuwar masa yake.

ShuÉ—ewar shekaru shida.
(After 6 years)
A hankali ta lallaɓa kitchen ta leƙa tukunyar da ta hangi nama, sau biyu ta taɓa ci amma a rayuwarta tana son nama hannunta na karkarwa saboda rashin ƙwari idanunta na yi mata yana-yana saboda yawan bacci. Wani kyakkawan murmushi ya suɓuce mata lokacin da hannunta ya isa kan tsokar nama ɗaya.

"Ihee Mama, Abbiey"
Domin komai a wajanta Abbiey idan Baba ƙarami ya kira Ustaz sai ya haɗa su, bata iya cewa komai, Ustaz ne yake cewa "Shalale ce Abbiey" da haka ta haddace sunan raɗau a bakinta komai Abbiey. Tana saka naman a baki Ammi na shigowa Ridayya ta yi wuƙi wuƙi da manyan idanunta, tun tuni ta daina kuka ya zama jikinta, a tsorace ta yi baya tsautsayi tukunyar naman ya kife gabaɗaya a ƙasa, Ammi ta ƙunduna ashar ta ce

"Ƴar banza mayya nakashsshiyya tsinanniyar ƙarshen muni mara amfani a cikin mutane wallahi yau za ki san ni ki kai ma ta'addi, daman kin kashi ɗazo a wando" Biba ta leƙo ta ce
"Lafiya Maryam?" Ta ce "Wanne lafiya? Farfesun da na yi wa Alhaji Mansur wanda na haÉ—a da jinin al'adata ta kifo da shi" Biba ta ce "Kutimelesi ina ganinta a murguÉ—e ashe muguwa ce?" Ammi ta finciko Ridayya ta ce "To da fa? Kwana biyu daman bana gane kan Alhaji Mansur cikin bacci zai fara kiran Fatima, Zarahna"

"Riƙe mini ita Biba" wuƙa Ammi ta ɗakko ta ɗora a saman gas, wuƙar nan ta yi jajur da ita kamar a maƙera sai ka ce mai shirin yin walda "Fito mini da harshenta, buɗe bakin nata ki riƙe kafura mahaukaciya da kyau" Biba ta buɗe bakin Ridayya tare da zaro ɗan ƙaramin harshen yarinyar duk miyar data shafi wajan tana nan, babu tsoran Allah babu tunanin zata mutu tabar yaranta a duniya cikin rashin tausayi da imani Ammi ta ɗakko wuƙar nan daga gama yin jaa a wuta ta manna wa Ridayya a harshe......

*Wannan page ɗin na ku ne stepmother Jama'a mutuna a kodayaushe mutuwa na kusantarmu, yanzu ne, anjima, gobe ne jini. Only God knows. Uwar gida da amarya ku ji tsoron Allah, babu amfanin cutar da ɗan kishiya, matsalarki da kishiya daban, babu ruwan yaranku ciki, wallahi wallahi duk wanda ya wulaƙanta ɗan wani sai Ubangiji ya musu hisabi. A cikin Alkur'ani Ubangiji da kansa ya bawa maza damar auren mata huɗu cif, banga dalilinki na shigowa ki kori wacce take gidan ba, maza sun bar mu da wahala, saboda kawai ki mallaki miji sai ki haukata kishiyarki ko ki sabauta ta, ko kuma kai saka tsanarta a zuciyar miji ko ki saka mata warin jaɓa, ko ki musu farraku da ɗa da dukiya Allah kaɗai ya san mai morar su wallahi. Ku ji tsoran Allah ku ji tsoron wallahi cases ɗin da muke karɓa wajan aikinmu Allah ya yi yawa da su mene amfanin yin abinda ba zai maka amfani a lahira ba😭😭🤲🏻*

Bana jure sharing don Allah idan kin karanta ki yi sharing fisabilillahi🌚 idan ba a sharing zan mayar da posting iya wattpad da channel ɗita ko Facebook group nawa.

Domin gyara ko sharhi
[email protected]

Na'ima Sulaiman Sarauta
08164069385

*✿ MUNAFUKIN MIJI 15 ✿*
Mikiya Writers Ass.....

BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv

_Wannan shafin naku ne masoya Munafukin miji masu ƙaunar Zameer da shalalen Ustaz🤓 Drama section, Munafikin miji fans, Sarautar's Library gidan da aka kusa ƙwace shi daga hannuna🤣su Oum Safna,su Balkisa su Oum shaheed su Mom sani writer ɗin Surukata. Ga na musamman ajin tubarkalla Nimcy paid library, da jama'ar Nimcyluv readers hub. My WhatsApp channel people🥰🥰 much love Bright pens na godiya_

"Biba sake riƙe mini tsinanniya gayyar na ayya gayyar assha, wato ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu ko? Yadda uwarki ke son kwace mini miji, haka kike so wargatsa mini plan na yi biyu babu,uku ba ko ɗaya? Ki zame mini ƙarfen ƙafa mai wuyar fidda wa?" Ammi ta faɗa tana sake ɗora wuƙar a saman wutar gas ɗin. Biba dake riƙe da Ridayya, kamar wacce ta riƙe sa'arta sai haki take saboda wahala ta ce
"Ina ganin ki rabu da ita haka, she's to young da wannan azabar taki Maryam, matsalarki da uwarta daban, matsalarki da yarinyar daban, look at her? Shekara shida amma kamar Æ´ar shekara huÉ—u duk ta tsamure kodan rangwamen hankalinta kya saurara mata please"

"Na saurara mata? Kin san me kike cewa Biba, kin san baƙin ciki da takaicin dana ɗanɗana dalilin uwar yarinyar? Kin san halin dana shiga sanadin Fatima? Ai wallahi ko zan ƙarar da komai nawa ba zan saurara ba sai na kai ga gaci, this is my promise" Biba ta girgiza kai domin haka kawai tausayin Ridayya ya kamata, ita kanta ta tsani kishiya ko a mafarki bata fatan ace yau gata da kishiya balle a zahiri? Kuma burinta ta rayu daga ita sai ranta banda ƴaƴan kishiya. Ta kalli Ridayya da wani irin yawu mai kauri ke dalala daga cikin bakin nata,bata zaro harshenta da ya yi jajur yana tsastsafo da jini, fatar wajan ta ciro, idanun yarinyar kamar zai faɗo ƙasa saboda masifar azabar dake ratsa mata jiki, tana kaiwa gurɓatacciyar kwakwalwarta ziyara tare da game dukkan wani sassa na jikinta da suke motsa ji da gani.

"Ba kyau azaba da wuta, Ubangiji kawai ke da ikon haka, kurman da ita kike son yi ne?". "Ta kurman ce mana Fatima ke da asara bani Maryam Æ´ar Alhji Shitu ba"

"Malam Shitu dai, don bani da labarin Malam ya je makka, ke fa matsalar dake damunki hadda talaucin daya yi miki katutu a gindi" Ammi bata kula Biba don taga alama tunan silili take ƙoƙarin yi mata. Ta cafko harshen Ridayya tana ƙoƙarin manna mata wuƙar suka ji an ce.

"Ammi, Ammi me kike ƙoƙarin yi haka" Ta yi saurin cillar da wuƙar tana haɗe rai kafin ta ɗauki Ridayya idanunta zube a kan Junaid ta ce "Daga ɗora girki fa na nemeta na rasa, sai ihun ta na ji a kitchen, kasan ta da kwaɗayin nama kamar jikar mafarauta shi ne ta kifo da tukunyar ta ƙona kan ta" Junaid ya kalli kitchen ɗin, kana ya kalli Ridayya dake miƙo masa hannu tana sauke ajjiyar zuciya idanunta ya ƙafe sun ƙara girma, harshen data zaro yake kallo da sauri ya matsa yana kallon wajan ya ce "Me kuma ya sameta a baki?". "Ƙonar da nake faɗa maka ce ai"
"Bai yi kama da wacce ta ƙone ba, sai dai ƙona ta a kai, kalli shatin wani abu fa?" Ammi ta kalli Junaid gabanta na faɗuwa sosai ta ce "Me kake nufi? Ni zan ƙona ta ko kuma Biba data taimaka mini na ɗauke ta? Yarinyar daba hankali gare ta shi ya sa na ce babu mai saka ta a makaranta yanzu, ni zaka ɗora wa alhakin hakan Junaid?"

Ya girgiza kai murya a ƙasa ya ce "Ki yi haƙuri Ammi, bana nufin haka" Yana faɗa ya fice, ta leƙa ganin ya fi ta ta dungurar da Ridayya a wajan tare da yin part ɗinta, Biba ta bi bayanta a ranta tana jinjina abubuwan da suke mata yawo a kan ta.

Suna fita Ridayya ta miƙe tana yarfe hannunta, tare da fito da harshen waje domin samun sauƙin abinda take ji, da zarar iska ta kaɗa sai ta ji kamar yanzu ne Ammi ke manna mata wuƙar, majina, yawu suka haɗe mata sai kuma a lokacin ne ta fara neman hanyar gudu inda bata taɓa yi ba a gidan ta nufa, rashin ƙwari da ƙarfin jikin da bata da shi suke neman yasar da tsamurarren jikin nata. A jikin bishir zugale ta raɓe hawaye na bin idanunta sai nishi take da haki tana son yin kuka a fili ta kasa.

Shigowar shi kenan cikin gidan, tunda ya shigo ya samu kansa da faɗuwar gaba mara dalili. Ya yi jim a daidai mararrabar data haɗa shashin biyun, na Baba ƙarami dana Baffa. Yana ƙoƙarin nufar part ɗinsu ya ji saukar siririn muryarta a cikin kunensa.
Chapter 27 · 0% Book details