← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 118

Sashe 10

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mai Æ´ar tsala tunanin me kike haka? Ashe da gaske daman Usman yake kin dawo cikin dare ke da Zameer?" Ridayya ta jinjina gulmar Zainaba da mijinta ta ce
"E, an wuni lafiya Maman Hajjo?" Zainaba ta ce
"Lafiya ba lafiya ba, ina can ƴar nan da tunaninki, to Masha Allah jiki ya samu" Ridayya ta ɗan yi yaƙe haƙora suka bayyana muninta ya sake fiddowa fili.
"Abinci na kawo miki, sai kuma kika ji daga tafiyarki Mai ƙosai ta fara yin ƴar tsala? Mutane babu ko kara" Ridayya ta ce "Allah sarki kowa rabonsa zai samu ai, ni ina tunanin ba zan sake ƴar tsalar ba"
Zainaba ta riƙe baki ta ce
"Ke kowa saboda me? A'a wallahi ai jama'a nata cigiyar mai Æ´ar tsala"

"Ba kuɗi a wajena, ba jari" Zainaba ta yi ƙasa da murya ta ce "Ina adashin da kike yi to? Ki karɓa bayan ƴar tsala sai ki fara siyar da kayan miya ma ai zama haka ba naki bane tunda kalar naki ƙaddarar kenan"
Ridayya ta yi murmushi ta ce "Ai na amshi kuɗin yau da safe har sun ƙare a magani" Baki sake Zainaba ke kallon Ridayya zata iya rantsewa da Allah mijinta mai zaman banza ta ba wa kuɗin.
"Shikenan akwai wata dubu biyar waje na sai na ara miki ki É—ora jarin idan kin manshe da kuÉ—in kya bani ko?" Ridayya ta ce "Na gode sosai Maman Hajjo Allah ya saka" Ta kunce bakin zani ta ba wa Ridayya kuÉ—in kana ta yi mata sallama ta ce
"Zan aiko hajjo ta amshi kwanon abincin"

Da sauri Zameer ya koma ɗaki jin Zainaba ta fito, daman ya fito da nufin karɓar hakƙinsa wajan Ridayya tunda duk nacinsa da Khairiyya ya kasa samun nutsuwa da ita. Ridayya ta jawo kwanon abincin kenan Zameer ya shigo yana ƙamshi ya sha shadda daman ba dai iya ɗaukan wanka ba, ya san takan gayu sosai.
Ridayya bata kalle shi ba ba kuma ta saka hannu cikin abincin ba. Meer ya tausasa murya cikin salo na makirci kamar mace ya ce "Fushi kike dani mai sona? Idan kikai fushi dani ai na shiga uku bani da wani sauran gata" ko tari ba ta yi ba.

Sai kawai ta ji ya fashe mata da kuka yana kifa kansa a cinyarta a hankali kuma ya toshe hanci gudun kar ƙarnin ruwan ciwonta ya saka shi a mai. Ya dinga kuka kamar amaryar da aka ɗaurawa lallai.
"Ki yafe mini kada ki tarwatsa zuciyata da shirun nan naki, nasan na miki laifi Ridha amma kin san halin Khairy yarinya ce ita ba hankali kuma mun saɓa ƴar tsere da cakulkuli da ita, yanzu da kika mare ta da ban rama mata ba zuwa za ta yi ta faɗawa Mama kuma a kan Khairy Mama na iya tsine mini"
Ridayya dai bata ce komai ba ya ce "To shikenan rama marin tunda ba za ki yafe mini ba" A hankali ta ce
"Ina zaka?"

"Ke na yi wa kwalliya, nikam ke na yi wa ki yi ta kallon rayuwarki ki na jin daÉ—i, ina tsananin son ki matata farin cikin rai na, mayyar Zameer i love you!" Nan da nan Ridayya ta mance komai daya faru ta ce "Ka ci abinci?"
Ya ce "Ta ya zan ci na hanaki bani kuɗi, nema dai zani" Ta tura masa kwanon abincin da Zainaba ta kawo mata ta ce "Ga abinci nan, kuma ka bawa ƙanwarmu Khairy haƙuri kishinka da son ka ya sa na yi abinda na yi" "Uhm" ya ce yana jan kwanon.
Shinkafa da miya ce da kuma yankan nama guda huÉ—u ga haÉ—in salak, Ridayya sai haÉ—iyar yawu take sai daya cinye tas sannan ya ce "To ke kin ci?" Ta yi murmushi ta ce "E" Ya dinga kallonta gabaÉ—aya ta zama tsohuwa ya ce

"Mai sona aron kuɗi nake so zan biya a yi mini printing na wasu takardu zan kaiwa Alhaji Muttaƙa ya nema mini aiki, da zarar na samu aikin zan fashe gidan nan na yi miki sabo ke da yaranmu, domin har miliyan biyu za a fara bani cikin satin nan muddin yau na kai takardun nan"
Daɗin ya kama Ridayya domin da zarar Zameer ya samu aiki zata fita daga wannan wahalar kuma zai siya mata kayan ɗaki "Har nawa kake so?" Ya ce "Dubu goma haka" Ta ware ido ta ce "Tab sai dai dubu biyar yanzu aka bani aronta na ɗora jarin ƴar tsala, kuma ka san na faɗa maka yar da mukai da Baba ƙarami na cewa Bilal kuma kar ya sake turo mini kuɗi bana buƙatar taimakon shi" Zameer ya zare ido ya ce "Amma ba ki da hankali ai ban hanaki kar ɓar kuɗi wajan shi ba, taimako ne maza ki bashi haƙuri ya dinga tura miki" Da mamaki ta ce "To tunda bana son shi me zan yi da kuɗinsa? Duk wanda zai wulaƙanta ka wallahi bana son shi" Zameer ya ce "Ai ana iya zuciya da komai ban da kuɗi, matsalarku daban taimako daban, bani kuɗin" Ta ɗakko dubu biyar ɗin ta bashi. Daga nan kuma ya dinga kallonta can ya ce

"Ina buƙatar ki"
A tsorace ta ce "Bani da lafiya ka yi mini afuwa, wallahi wannan abun baya gabana" A ransa Zameer ya ce "Banda wannan dalilin ni ma ko inda kike ba zuwa zan yi ba, wannan shi ne kawai dalilin daya sa ba zan rabu dake ba"
A fili kuma ya ce
"Shikenan na gode" Ta girgiza kai ta ce "Zameer ka yi mini uzuri, bani da lafiya ba cima mai kyau balle abin ƙara lafiya da kuzari" Ya ƙanƙance ido
"Ohho ƴan'uwanki za ki bi kenan Ridha, ni kike wa gori? Ridha ni mijinki aljannarki na tafin ƙafata? Kike cewa ba cima mai kyau sata zan yi na ba ki? Ko ni zan zo ki cinye ni, to wallahi hakƙina ko kina so ko bakya so sai kin bani ai sadaki na biya"

Kafin ta yi magana ya cimmata tana kuka da ihu saboda ba daɗin abin take ji ba tsananin a zaba kawai take sha, gashi kamar mahaukaci haka zai shaƙeta idan zai nutsu, wani ihu Ridayya ta yi wanda ya yi daidai da ƙarar ƙarar zagewar wani abu keeeetttt hakan ya yi daidai da ɗaukewar numfashi Ridayya tare da yin ƙaura daga jikinta wanda yake bayyana suman da ta yi.

*✿ MUNAFUKIN MIJI ✿*
_Nimcyluv@arewabooks_

BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Page 6

Ruwan da Ridayya ta ji ana sheƙa mata mai sanyi ya haddasa farfaɗo war ta daga suman hucin gadin da ta yi. "Ɗinkina zai farke, ka tausaya mini ba zan iya ba wayyy...,"
Zainaba ce ta jijjiga Ridayya da ƙarfi ganin kamar bata gama dawowa cikin hayyacinta ba cike da tausayi na halin da yarinyar ta saka kanta ciki ta ce
"Ridayya lafiyarki lou? Me ya sameki na gan ki a yashe kamar gawa? Ina shi mijin naki ya bar ki haka? Wacce kalar rayuwa ce wannan?"

Maganar Zainaba ya dawo da Ridayya cikin nutsuwarta ta fahimci ba Zameer ne a kusa da ita ba balle ta saka ran samun kulawa daga wajan shi tunda shi ya cillata halin da take ciki a yanzu. A karo na farko tun kafin auren su, da bayan auren su ta ji wani irin mummunan faɗuwa da ladamar abinda ya shuɗe sun dirar matar a zuciya ta ji babu abin da bata ƙauna irin tarayyar aure, rashin mafita da yar da zata fahimtar da Zameer ɗin ya saka take biye masa ba son ransa ba, yana nuna mata ƙarfin ikon shi akan ta matsayin miji.
"Allah na tuba, na tuba Allah ka yafe mini zunubin dana aikata a baya yake bibiyata na ji a jikina, idan har haka ne gwara mutuwa da rayuwa a gare ni" Zainaba ta yi saurin rufe mata baki, ita ma hawaye ne ke sauka daga cikin idanunta kamar yar da Ridayya ke kuka mara sauti mai cin zuciya.

"Komai ya yi zafi maganinsa Allah, Ubangiji baya taɓa ɗorawa bawa abinda ba zai iya da shi ba, ba kuma ya ɗorawa bawa ƙaddarar a domin baya son shi ba, sai dai gwada imaninsa da Tauhidi" Ridayya bata fahimtar maganar Zainaba saboda tsoran daya rusketa da jin yar da ruwa ke gudu ta ƙasan cibiyarta. Zainaba ta yi saurin toshe hanci ta ce
"Ridayya warin mene wannan?"

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Shikenan" Ridayya ta furta a raunace ganin yadda ɗinkin ya farke wajan ya yi jajur kamar yanzu ne aka yankata, ruwan dake zuba na fidda warin. Zainaba ta miƙe ta ce "Zama ai bai kama mu ba, dole a koma asibiti ki kira ƴan gidanku ki shaida musu" fahimtar kuka a rahama yake ya sa Ridayya bata damu da yadda hawayen ya tsaya mata ba, zuciyarta ta bushe tana mata wani irin suya, ta ƙura wa wajan ido numfashinta na fuska. "Babu wanda zan iya kira, domin na bar su"

"Kin bar su kamar ya?" Ridayya ta girgiza kai ta ce "Aurena za su kashe mini ta ƙarfin tsiya, suna son bawa Abbiey ni, na zaɓi mijina domin shi ne Aljannata" Baki sake Zainaba ke bin Ridayya ta ce "Kuma kin tabbata lafiya kike, ma'ana babu Aljanu a jikinki"
Murmushin takaici wanda ya fi kuka ciwo Ridayya ta yi.
"Idan ina da aljanu kawo yanzu da kin sani" Zainaba ta ƙara cewa
"Kuma babu wani asiri da tsinannan can ya yi miki?" Ridayya ta É—aure fuska duk da halin da take ciki ta ce "Ki dai na zagin mijina cin mutunci ne wannan"

"Na ci uwar mijin ba mai ha ya ji, na ci shi ƙandas, na bisa da gudu aikin banza aikin wofi yanzu na ƙara tabbatar da bayan ƙuruciya har da rashin komawa ga Ubangiji da bijirewa iyaye" Zainaba ta ce
"Kin taɓa ganin inda iyaye suka mutu aka sauya wasu? Zaka iya sauya komai banda iyaye da dangi, hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, iyaye ba abin wofintar wa bane Ridayya, a yau kika faɗi kika mutu jimawar duniya shi ne ki arba'in, zai yi sabuwar amarya ta tare a ɗakin da kike gadara da sunan ɗakin miji, gidan aure"
Chapter 10 · 0% Book details