Sashe 25
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zauna Baffana" Ya nemi ƙasan kujera saman carpet ya zauna ta yi wani kalar murmushi ta ce "A'a koma kan kujera magana za mu yi" Ya yi jim ya ce "Na zauna a kujera Maryam? Na zauna ba matsala?" Ta jinjina kai ya miƙe jiki na rawa kamar mazari ya zauna a kujera ta harɗe ƙafa ta ce
"Mansur kuÉ—in rainon Æ´arka za mu yi magana, duk wata zaka bani dubu É—ari, dubu É—ari da hamsin kuma kuÉ—in siya mata madara da kaya" Ya kalleta ta ce "Ka ji?"
Æarin da jikinsa yake ya tsananta ya ce "Shikenan koda saura? Yanzu zan tura miki kuÉ—in ko sai anjima?" Ta yi murmushi ta ce "Da safe, sai abu na gama ko da wasa kar na ganka a Æ™ofar gidansu Fatima da niyyar zuwa biko" Ya girgiza kai ya ce "Ba zani ba" Ta ce "Good, bacci na ke ji yanzu da safe zan zo ka faÉ—a mini duka abubuwan daka mallaka, ka faÉ—a mini me da me ka mallakawa Ridayya tun tana ciki, ka faÉ—a mini irin abubuwan da Fatima take maka wanda kake so" Ya jinjina kai ta ce "Ka ji ko?"
"E, na ji Allah ya kaimu"
Waje ta yi bita da sauri sai da sukai nisa ta tsaya ta ce "Ya kake bina Baffa salon ka ja mini masifa?" Ya marairaice fuska ya ce "Tambayarki zan yi daman zan iya kwanciya a gado na yi bacci?" Ta ce "E mana jeka" Ya ce "Thank you" Ya juya.
Tana komawa part ɗinta ta samu Ridayya kwance inda ta barta ƙafa ta ɗaga zata taka mata ciki sai kuma ta girgiza kai ta ce "Idan na kasheta mene ribata?" Sai ta ɗauki Ridayya ta yi mata tumɓur har pamper ɗin ta cire ta zaga can baya wajan bola ta saka ɗan'kwali a ƙasa kana ta ɗora Ridayya a kai cikin bolar shirgin gidan ta juya, dare ya raba kafin ka ce me cinnaku sun yayyame saman fatarta sai gantsara mata cizo suke, sun cika gabanta hancinta saman laɓɓanta har cikin idanunta cinnaku ne sai gatsa mata cizo suke ga tsanyin dare tsananin azaba ya sanya jaririyar daddagewa ta yantsara uban ihu cikin tsakiyar daren sakaliyya....
Domin comment ko gyara yi magana ta gmail É—ina [email protected]
Ko kuma ta WhatsApp number 08164069385
Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
*✿ MUNAFUKIN MIJI 14 ✿*
Mikiya Writers Ass.....
BRIGHT PENS🤙🼠free batch
Nimcyluv
Fitowarsa kenan daga shashinsu domin yin shur na azumin Alhamis, tunda ya fito yake jin zuciyarsa babu daɗi, ya yi shiru yana jin yadda iskar gari ke kaɗawa tana bada wata amintacciyar ni'ima mai saukar da nutsuwa a zuciya. Saukar kukan jaririyar ya yi daidai da lokacin da ya ji kansa ya sara, ya yi jim yana son tabbatarwa da kansa abinda kunensa ke jiyo masa. Da sauri ya miƙe tsaye carbin hannunsa na ƙoƙarin faɗuwa zuwa ƙasa, gashi farar jallabiyya ce tas a jikinsa.
Direction na inda kukan ke fitowa yake bi, a haka har ya isa daidai inda bolar gidan take ya waiwaya a hankali, amma bai ga kowa ba zatonsa ya bashi yau ko rashin sa'a ya yi mutanen ɓoye ke son buɗe masa ido? Ya ci-gaba da tasbihi a zuciyarsa. A bin mamaki kuma lokacin jaririyar ta daina kuka, yana ƙoƙarin juyawa ya sake jin saukar kukan nata wanda yake shirin rusa nutsuwar daya gino a kanta, cikin sauri ya fiddo wayarsa ya kunna torchlight tare da haskawa. Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!
A gigice ya saki wayarsa dukda ƙasan zuciyarsa bai gama tabbatar masa daba gamo ya yi ba, ya saka hannu a fili kuma cikin kamilalliyar muryarsa ya ke azakar na neman tsari da kariyar Ubangiji. Da duka hannu biyun ya ɗauki jaririyar yana matsawa wajan haske, ya runtse idanunsa da sauri lokacin da ya yi tozali da Ridayya, fatar jikinta ta kumbura jini sai zuba yake tako'ina a jikinta, da sassarfa ya nufi ɓangarensa ya shiga bedroom ya rasa abinda zai yi duka wannan abubuwan bai san su ba, sai jaririyar ya gama sha'aninsa a gidan bai kalle shi ba, balle ya san yadda ake kula da su.
Ruwan shower ya kunna yana ƙoƙarin zuba mata sai kuma ya girgiza kansa ya koma ya kunna hiter kafin ruwan ya yi zafi ya nufi saman gado, ya ɗora Ridayya a ciyarsa. a hankali yake bin fatar jikinta da kallo, dukda kasancewarta jaririya amma sam bata da hasken fata gashi da cinnakun da fatar suna neman zama ɗaya ga jinin dake fita duk ya dagule fatarta.
Audiga ya É—akko ya dinga share jinin yana marmasar da cinnakun amma tamkar na asiri sun kafe gashi sai tsala ihun azaba Ridayya ke yi. Ustaz ya inda zai saka kansa idan ya tsora mata idanu sai kawai ya sauke ajjiyar zuciya, da ace shi ma'abocin kuka ne da karaya da lamarin rayuwa da tuni ya raunata. Ya ci-gaba da gogewa har jinin ya fita a hankali ya dinga kaÉ—e cinnakun wasu su fita wasu kuma suna nan. Ya ajjiyeta sai kuma ya dawo ya É—auketa gani yake tamkar wani abu ne zai sameta idan ya bar ta. Ruwan zafin ya haÉ—a daidai wa daida, ya saka detol a ciki.
Zabura Ridayya ta yi sanda ruwan ya ratsa ta, ga sabuwar fata ga ciwo ga zafin ruwan wanda Ustaz ya kasa fahimta ya ɗauka duk ciwonne ya sata kuka, ya dinga wanke mata jiki a hankali kamar ƙwai ya gama ya sake haɗa wani ruwan ya mayar da ita har fatar ta ɗan washe cinnakun suka fita a towel ɗinsa ya naɗe ta, tare da fitowa.
Farar jallabiyyar Ustaz ta ɓaci da jini ya ajjiye Ridayya saman gado zai juya ta canyara ihu ya yi saurin dawowa ya ɗauketa ya sata a kafaɗa. Fatar wuyansa ta fara tsotsa kamar ta samu nono.
Murmushi ya saki mai taushi jin yadda take ƙoƙarin neman abinci ido biyu, sakkota ya yi sai ta fara motsi da nishin kuka ya saka mata yatsarsa a hannu da sauri ta fara tsotsa tana sauke ajjiyar zuciya. Ustaz ya lumshe idanunsa wani irin tausayi ya kama shi, bai taɓa ganin wannan rashin imanin ba ko a fina-finai Hausa da littafan Hausa ta marubuta suke yi. Ruwan zam-zam ɗin daya jiƙa tare dabinon ajwa ya ɗakko ya yi kauri sosai ya bata ta dinga sha, sai ta sha sosai kana ya cire. Jin ta yi shiru ya miƙe ya watsa ruwa a jikinsa ya sauya kaya daga jallabiyya zuwa three qauter Ustaz baya son kaya masu nauyi shi ya sa ba kowa ke shigowa bedroom ɗinsa ba, idan har shi kaɗai ne za ka iya samun shi daga shi sai trouser.
Sai a lokacin ya samu damar ƙare wa yarinyar kallo, idanunta rufe har yanzu babu wanda zai ce ya taɓa ganin su. Idan ka ce real definition of blac skin kai tsaye Ridayya ce, baƙin mai duhu sai da yana haske za kaga har ɗaukan idanu yake, yanayin shi bama mai irin maiƙo ɗin nan bane ya fi kama da baƙi irin na ƴan Ethiopia. Laɓɓanta jajur suke duk da suna da girma da kauri amma kamar a tsaga jini ya fita, gashin gira a cunkushe suna neman haɗe wa waje guda, ga gashin ido zara-zara sumarta har ta shige goshi ko'ina na jikin Ridayya suma ne.
Ya kai hannu ya taɓa lips ɗin da sauri ya ɗauke hannun yana yarfe wa jin kamar fatar wajan zata ciro saboda laushi ya rufe ido kamar mai koyan magana ya ce
"Ya subuhanallahi!"
Yana faÉ—in haka ya yi shiru, har gari ya yi shiru dab da subhi Ustaz na zaune ya saka Ridayya a gaba da kallo a hankali ya zunguri cibiyarta.
"Open your eyes shalele"
Kamar tana jinsa haka Ustaz ya ga idanunta sun buɗe ta kalli sama da sauri ta rufe saboda haske, can ta ƙara buɗewa ta ƙura wa waje guda da kallo, Ustaz sai yaga kamar shi take kallo bai san kallon ƙoda bane. "Allahu Akbar, Ma sha Allah laƙuwata illabillah"
Idanun Ridayya irin su a kaf gidan, tsarin halittar da Ubangiji ya yi mata daban yake, kamar yadda kamanninta ya sha bambam dana jama'ar gida haske tas da su kamar ƙwalla ta kwanto manya wanda idan ta kafe ka da su sai ka firgita, akwai wani irin sirri a cikinsu.
Ya kwanta gado ganin kamar tana jin sanyi ya saka ya cire towel ɗin ya ɗora ta a saman ƙirjinsa ya rufa mata towel ya rungume ta, a ransa yana so ita ma ta ji ɗumin jikin uba mahaifi.
"Babana" Ya ji kiran sunan a saman kansa, bai buɗe ido ba ya sake bubbuga pillown da yake kai ya ƙanƙame abu a ƙirjinsa ƙafarsa ɗaya a ƙasan gadon wacce yake jijjiga wa har bacci ya ɗauke shi. "Za ka yi missing jam'i ka ɓatawa mutane lokaci"
Bakinsa ɗauke da addu'a ya buɗe ido, sai kuma ya ƙanƙance su ya kalli Umma ta ce "To Babana kar ka mini faɗa, mutum kamar rainon iska ya ce wai baya son magana a saman ka? Baya son faɗa baya son tsawa?" Ya sake shigar da idanunsa ciki ya kalli Umma can ya girgiza kai a hankali ya ce
"Faɗa da asubar nan faɗa Umma? Kai na zai cire nikam zai cire" Idanunsa sukai jajur. Umma ta riƙe haɓa ta ce
"Me kake ƙanƙame wa ne haka Babana?" Ya shiru ta miƙa hannu zata cire towel ya yi saurin riƙe wa ya kalli Umma yana kicin-kicin da fuska ya ce
"Tsaraici na, umma tsaraicina za ki yaye?"
"Gidanku kai da tsaraicin, ni uwarka ce har wanka na yi maka ko yanzu ta kama ki tas zan wanke ka" A gigice ya ɗago Ridayya daga ƙirjinsa da numfashinta ke sauka a hankali ya leƙa, wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke shi kam da idanun Shalale biyu ai Umma ta gama zubar masa da girmansa wallahi. "Matata kawai ke da ikon ganin tsaraicina, ki tausaya mini a rufe maganar nan nikam"
"To da za ka yi auren ma ni ba haka ba? Ni tun da ƙuruciyarka nake ganin matarka" Ta faɗa tana mamakin abinda Muhammad-Bilal ke ɓoye wa a ƙirji. "Ni fa ba zan aure ba" Gaban Umma ya faɗi ta ce "Me kake nufi"