← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 118

Sashe 110

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai sai ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi tana fashewa da kuka, tare da ɓoye kanta a ƙirjinsa tana kuka sosai da dukan ƙirjinsa ƙanƙame ta ya yi da kyau a ƙirjinsa yana dariya sosai dimples ɗinsa na lotsawa idanunsa suka sauya a daidai kunnenta ya ce

"I am always in pain i've never cry for love but you make me cry, my heart hurts my chest is burning i beg you to stay with me amma.....," cikin sauri Ridayya ta hankaɗa Abbiey kan gadon ya yi saurin gocewa zuwa gefe gudun karya danne yaran tare da ƙoƙarin miƙewa zai gudu amma Ridayya ta yi namijin ƙoƙarin hana shi ta hanyar rufe bakin maganganun da yake ɗarsa mata masu zafi a zuciya ta shiga yi masa sumbata ƴar sunna kamar yadda ya koyar da ita....

Abbiey na zaune idanunsa zube akan waya Ridayya kuma hannunta riƙe da Al'hassan mai sunan Sadauki ta yi kwalliya cikin shigar atamfa ta murza ɗauri itama pictures ɗin take kallo "Amma ya akai ka fini kyau a nan Abbiey?"

Ya murguÉ—a mata baki picture É—aya ya É—auka wanda aka jere yaran guda uku akai musu a tare suna ta bacci WhatsApp ya shiga a main account É—insa wanda kowa da kowa yake da shi ya É—ora a status tare da caption É—in.

_Allahamdulilah! Al'hassan, Al'hussan,Gambo_

In one minute reply yafi talatin kamar jira ake cikin mamaki Abbiey ke kallon first person daya fara reply ya É—aga idanu ya kalli Ridayya ya ce

"Mintyna zo" ta miƙe ta ƙarasa tana leƙewa ta waro idanu ta ce

"Umma ce ai"

Ya jinjina kai ya buÉ—e maganar nata inda ta yi reply ta ce

"They're the same babies, Allahumma barik Allah ya yi musu albarka da rayuwa mai kyau cikin aminci ya haÉ—a kan iyayensu"

Abbiey ji ya yi gabaɗaya hankalinsa ya yi gida kewar Umma ta fara addabar shi. Ya kasa ce mata komai kafin ya fita ta ƙara masa magana ta ce "I miss you darling son, hukuncin ya tsauri come back don girman Allah"

Saurin fita ya yi. Daga nan ya ga reply ɗin Tajj inda ya ce "Kan uba, har yara uku Ustaz ka yi ɓarna Allah ga Ustaz ka yafe masa" ya faɗa da emojin na dariya kana ya yi addu'a nan take ya saka status shima.

Junaid ya turo emojin na rawa ya ce "The day i have waiting for, yaran auta da Yaa Bilal" murmushi Abbiey ya yi ya juya ya kalli Ridayya hannu ta miƙa masa suka tafa suna dariya. "Wannan Antyn taki surutu ne da ita"

Anuty Kaltum ce ta turo emojin ta riƙe haɓa ta ce "Ikon Allah har uku" maganganun mutane da yawa suke ta gani har mamaki suke Mami ta yi viewing amma ta kasa cewa komai.

"Wai Mami kunyar ƴar fari take ne Mimi? Kowa ya yi magana banda ita, to bari mu bita har pravt kawai" Ridayya ta ɗora kanta a kafaɗar shi har zai turawa Mami pictures sai kawai ya danna video call Mami ta yi zaton Ridayya ce daman tun ɗazo take ta auna yadda zata yi magana idan Ridayya ce ta haihu akwai buƙatar ta dawo gida a kula da jego, gashi yara har uku tana ɗaga kiran fuskar Ustaz ta fara cin karo da ita sai Ridayya dake dariya cikin sauri Mami ta kashe kiran tana dafe ƙirji Ustaz ya dinga murmushin ya ce "Surukata bafullata na ce"

Kamar yadda sanarwa ya zo wa Familyn Rano yau Ustaz yake sauka Nigeria da matarsa daya aura acan kamar yadda Baba ƙarami ya ce, tun safe ake shirye-shirye na zuwan nasu abinci kala-kala, Umma sai farin ciki take dukda cewar hankalinta ya rabo biyu saboda Mardiyya dake naƙuda tunjiya kuma ta haɗa kaya kamar ba'a magana wanda Baba ƙarami ya saka ta yi. Naƙudar Mardiyya bata saka Umma ta yi noticing ƴan uwan Mami da suka cika part ɗinta ba Burhan na can wajan mai gadi saboda baya son hayaniya sai kwaɓe fuska yake lokaci lokaci yake kiran Zainura kamar zai mata kuka wai kansa na ciwo sai ta yi masa dariya ya ce "Ki ce kina so na ko na ji sauƙi" kawai sai ta kashe wayar. Naƙuda ta ci ƙarfin Mardiyya ta sha wahala sosai bata taɓa sanin haka haihuwa take ba, ƙasan zuriyarta wani irin ɗaci take ji ƙarar saukar motoci cikin gidan ya yi daidai da kukan saukar jaririn duniya "Ma sha Allah yaro ya zo duniya a daidai kamar yasan zuwan ubansa" Yaya Balkisa dake taimakawa Umma ta jawo jaririn ta goge shi ta yanke cibiyar ta saka cikin zani cikin murna Umma ta ɗauki jaririn da ganin irin zubin kyan da Ubangiji ya yi masa idanunta rufe ta miƙa hannu jikin jaririn ta riƙo abu kamar hannu kamar kunne da sauri ta kalli zanin ta waro idanu waje ta ce "Balkisa mene wannan a jinin yaron?" Balkisa ta ce "Umma leɓen babyn nan a haka ya sakko kamar hannu kuma macace ba namiji" a gigice Umma tana girgiza abun da ya yi shaƙaf idanunta kamar ya faɗo ta ce "Leɓe kika ce fa Balkisa leɓe na jikin baki?....

Share share share Please with comments
*MUNAFUKIN MIJI*

Nimcyluv
47

Mikiya writers Association.....

*Masu tiktok kuje ku yi following profile É—ina domin mu dinga tattaunawa daku a can...*
https://vm.tiktok.com/ZMrhYsBQE/

Cikin tashin hankali Umma ta ce "Bakin jariri kika ce fa Balkisa? Leɓe na jin baki irin nawa da nake magana kike nufi ko kuma wata tsoka ce ta yi tozo take neman faɗuwa ƙasa haka?" Ita kanta Balkisa mamaki da kallon baiwa da hikimar Ubangiji wajan iya tsara halitta shine ya cika mata zuciya da ƙyar ta zame idanunta akan jaririn ta ce

"Zai fi kyau ki nutsu Umma jaririn na hannunki ki duba da kyau sosai"

"Wannan ba dai jariri ba, sai dai idan ɗan aljanu kawai Mardiyya ta haifa, na rantse ban taɓa ganin jariri mai munin wannan ba, kalli hanci a bulaƙe kuma ya nane ta fata kalli halitta a jikin baki wai leɓe ce ko fa irin hasken jarirai babu a tattare da wannan jaririn" yadda Umma ke magana zai tabbatar da tashin hankalin da take ciki da gaske bata taɓa tsammanin jinin Babban mutum zai kasance haka ba, tana da yaƙinin jinin Muhammad mai ƙarfi ne duk yaron da zai haifa tabbas kamanninsa zai ɗauka.

Balkisa ta juya ta kalli Mardiyya da ko zafin haihuwar bai gama sakinta ba, fama ake ta yi ta mahaifa ta faɗo amma abu ya ci tura, dukda an ɗaure amma neman yin sama take wajan ƙirjinsa, hakan ya saka innar Mardiyya ta fara shiga tashin hankali domin tas mahaifa kan kashe mutum jini take sha sosai. Innar ta kalli Umma ta ce

"Haba baiwar Allah ke baki da imani da tausayi ne, kamar ba ki san ciwon haihuwa da zafin naƙuda ba zai yarfawa yarinya magana kike ina laifin ki yi lale da zuwan mai gidan naki? Halitta ɗaya ce dai kuma an haifa"

Wani banzan kallo Umma ta watsawa Inna ta dire jaririn da take jin ranta yana ɓaci a kansa, amma bata isa ta nuna masa ƙi ba saboda jininta ne amma har ƙasan zuciyarta take mamakin yadda yaron sam bai kwanta mata ba. "To Allahamdulilah mahaifa ta faɗo mun gode Allah an rabu lafiya"

"Ma sha Allah, sannu Mardiyya" cewar Balkisa ta shiga goge jinin wajan. Mardiyya ta sauke ajjiyar zuciya idanunta akan jaririn ganin babu inda ya bar mahaifinsa ta runtse idanunta tana jin fargaba mai tsanani na ratsa mata zuciya haihuwarta sa zuwan yaron duniya na nufin abubuwa da dama.

"Me na haifa ne Inna?" Ta furta da ƙyar Inna ta ce "Jaririya ce mace kika samu Mardi"

A firgice Umma ta ce "Mace kuma ke Balkisa ba namiji kika ce ba? Ai da maza jaririn ke kama"

"A'a Umma mace daman na ce miki ai"

Umma dai ta kasa furta komai sai girgiza kai take Mardiyya ta ce "Na yi wa Umma takwara a sakawa babyn Hadiza" zanin Umma na faÉ—uwa ta ce "Wacce Hadizan za a yi takwara? Ba dai ni kike nufi ba Mardiyya"

"Umma mene laifina idan na saka sunanki jikarki ce fa? Ai farinciki ya kamata ki yi ko?"

Umma ta girgiza kai ta ce "A'a na yafe idan an haifi wani a saka, ga innarki nan a saka ko"

Kafin su yi magana Yaya Zuhura ta shigo cikin murna ta ce "Umma albishirin ki?" Ta haÉ—e rai ta ce "Goro"

"Babban mutum ya dawo yanzu, Yaa Bilal is now at home" ba Umma hatta Mardiyya ba ta yi tsammanin jin hakan ba, ta sauke ajjiyar zuciya mai nauyi na farinciki da kuma na tashin hankalin da take tunanin yana gab da rikito mata. Farinciki ya saka Umma ta kasa cewa komai ta riƙe Yaya Zuhura ta ce

"Da gaske kike Zuhura?" "E Umma, yana main parlon ma" Umma ta juya zata fita Mardiyya ta ce "Umma ki tafi masa da babyn na san zai yi farinciki"

Ita dai Umma ko ta kan Mardiyya bata biba ta nufi hanyar fita Yaya Zuhura ta rufa mata baya, Balkisa ta miƙe ta ce "To Mardiyya bari na je na gaisa da ɗan'uwan nawa nima kafin ya shigo"

Inna dake satar kallon Balkisa ta ce "A'a kekam ai sai son barka sannu da ƙoƙari, uwar mijin dai ce naga ta na yi wa jinjirar wani gani-gani ai halittar Ubangiji ce"

Bayan Balkisa ta fita Inna ta ce "Mardi anya ba ki yi gamo da aljanu a wannan cikin ba? Ko kin watsawa Æ´aÆ´an aljanu ruwan zafi ba ki sani ba?"

"Inna me kika gani?"

"Uban uban me na gani, ga abinda na gani nan a cinyarki ki dubi yarinyar nan har wani maiƙon baƙi take yi ke fara ubanta ma jaririn da shi haka kakannin nata" cikin runtse idanu Mardiyya ta ce "Ai Ubangiji da yadda ya kewa kowa tashi halittar"

"Haka fa, na ga alama to Allah ya raya miki"
Chapter 110 · 0% Book details