← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 118

Sashe 101

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wow! U look so beautiful shanshan kin sauya a idanuna sosai" yana magana yana É—an hargitsa sumar kansa alamar ya fara fita daga yanayin da yake na Hamza zuwa na Sadauki.

Ya zubawa cikin Ridayya idanu domin tabbatar da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, idan cikin gaske ne mene haÉ—in budurwar da zai aure da cikin haihuwa? What bring her here? Me ta ke yi a Japan?

Ƙara matsawa ya yi wajanta ta girgiza masa kai irin ya dakata ɗin nan, he just trying to get more close to her a gigice Ridayya ta ce "Stop it, Stop it Stop it Sadauki" jikinta duka rawa yake tsoro da fargabar yanayin Sadauki ya saka mararta riƙe wa, idan ta tuna cewa Abbiey na hanya kamar yadda ya ce sai ta ji kamar abinda ke rayuwa a cikinta zai fito zuwa duniya ne, bata san hawaye ke fita daga cikin idanunta sai da ta ji saukar yatsar Sadauki manuniya ya sharce hawayen ta ɗago ta kalle shi ya mata murmushin a hankali nunfashinsa na sauka da kyar a fuskarta ya ce

"Wai Shanshan wannan sabon yanayin fa? Bai dace dani ba na miki wani abu ne?" A taushahe ya yi maganar Ridayya ta kasa cewa komai bata san haÉ—a idanu da shi tsananin tausayinsa ke addabar zuciyarta, ta san ta masa laifi kuma laifi mai girma "Sadauki ka fahimta mana!" Ta furta a fusge tana ja baya ya bita ya ce "Me zan fahimta bayan abinda na fahimta yanzu? Ki barni kin wofintar dani saboda muradin ki yi karatu? Tunaninki ba zan bari ki yi karatu ba ko mene? And wannan guje-gujen na mene eh?"

"I am sorry very very sorry Sadauki "

"Sorry for what? Zan jira ki zan dinga dakon soyayyar ki a nan ɗina" ya nuna tsakiyar ƙirjinsa da hannunsa ya ce "Har zuwa ƙarshen numfashina, bani nake son ki ba Ridha ruhi da zuciya da gangar jikina ke ƙaunar ki, bana son komai sai rayuwa dake kawai so nake ki riƙe hannuna mu yi rayuwa tare.....,"

"I am sorry Sadauki ka yi haƙuri don Allah...," matse kafaɗunta ya yi idanunsa a rine ya ce "What wrong with Shanshan? Hakurin mene na miki uzuri na fahimci cimma muradinki zan jira da gaske zan jira ki, so halitta ne kuma jarrabwa ce na jarabtu akan ki Shanshan kawai ni ina son ki"

"Ciki gare ni Sadauki ciki ne dani haihuwa zan yi, na haramta a gare ciki gare ni Hamza Sadauki "

Ba kansa ne kawai ya harba ba hatta zuciyarsa sai data girgiza tana neman rabewa biyu a tsakiyar ƙirjinsa, kalmar CIKI kawai yake masa yawo komai nasa yana warware ƙirjinsa na matse masa guri guda, murmushi ya yi mai kama dana masu jin tatsuniya a fusge ya ce "Ciki? Wasan banza kenan" Ta girgiza kai ta ce "Da gaske nake"

Ya tausasa murya ya ce "How? A gida an sani? A ina kika same shi? Kin san uban cikin?"

Ta yi shiru kawai domin tana da yaƙinin Sadauki ba zai fahimce ta ba, tana kuma shakkar faɗa masa cewa ta yi aure ne, cikin sunna ne maƙale a mararta. Sadauki yana da naci da taurin kai kafin ta gama yanke shawarar abin yi ta ji ya damƙo hannunta ya ce "Ciki Ridayya? Abinda ya kawo ki makaranta kenan?" "Ba zaka gane ba Sadauki Please let go of me kar ka saka na shiga fushin Ubangiji"

"Fushin Ubangiji na nawa Ridayya? Kin san me kika aikata zina? Har da cikin shega" a gigice ta ce
"Ba cikin shege bane Sadauki, i am a married woman, am married and live with my husband in this country, ba abinda kake tunani bane wannan dalilin yasa nake baka haƙuri"

Sakin ta ya yi a karo na farka na rayuwarsa a gaban mace idanunsa suka zubar da hawayen da bai shirya zubar su ba, yin kansu kawai sukai ba kuma iya idanunta ke hawayen ba hatta idanun zuciyarsa kuka take ya dafe kai ya shiga kaiwa da kawowa ganin tunaninsa ya yi hijira ya saka Ridayya ɗaga ƙafafuwanta da ƙyar ta bar wajan tsakanin gittawar mintuna ya juyo yana cewa "stop kidding me dear kina son zuciyata ta buga da gaske na san ba za ki iya karya alƙawarin da kikai mini ba, idan na yi magana ne ki yi yafe mini na tuba na bi Allah na biki Ridayya....,"
Shiru! Shi kaÉ—ai yake kiÉ—an shi da rawarsa babi ita babu ko inuwarta da sauri ya rufa mata baya domin yasan wasa take masa.

Bata ko ganin gabanta a haka take tafiya hannunta duka biyun riƙe cikinta hawayen tausayin Sadauki yaƙi tsaya mata, sama sama take jin ƙarar horn a bayanta a hankali kuma motar ke tafiya tana bin sahun ƙafafuwanta jin haka ya saka Ridayya matsawa gefe domin bawa motar hanya itama motar tsayawa ta yi a gefe. Bai jira an buɗe masa ba ya buɗe da kansa ya fito, jikinsa sanye brown ɗin suit mai kyau ya fito da ƙafarsa ya fito hannu ya ɗagawa wani ya dakata slowly yake tafiya har ya cimmata. Ƙamshin turarensa ta ji ta tsaya ba dai ta juyo ba sai da ya ƙara su ya ɗan taɓa kafaɗarta da sauri ta juya tana goge hawayen fuskarta ta ce "Abbiey"

Ya ɗaga mata gira biyu idanunsa nutse a kanta da ƙyar ta yi yaƙi da zuciyarta wajan dakatar da kukan ta ƙirƙiri murmushi ta aza a fuskarta tana matsawa wajan kusa MB USTAZ ganin a gaban jama'a tana neman shige masa ya yi saurin kama hannunta yana bata side hug tare da tafiya da ita a hankali har zuwa wajan mota key ɗin dake hannun John ya amsa yana basa umarnin neman abin hawa ya buɗewa Ridayya gaban motar ta shiga kana shi ma ya shiga bakinsa ɗauke da addu'a ya fara driving zuwa direction da zai kai su gidan da suke a nan Japan ɗin. "Ni fa ban ɗauka da gaske yau zaka dawo ba Abbiey" bai ce mata komai ba ya dai juya ya kalleta ganin yau halin ya motsa ya saka ta yi shiru can ta ce "Ya hanya ka dawo lafiya? Ya su Umma, Mami, Baba ƙarami da Baffa?" Bai amsa ba sai sautin karatun ban daya ƙaro yana lumshe idanunsa a hankali yake kuma tuna yadda ya ruski Sadauki da Ridayya domin ya gane Sadauki sosai tun a gidan su Tajj da yadda ya riƙe mata hannu da ƙoƙarin rungume ta da ya yi ya cije lips underneath his breath ya ce "Allah ya yafe miki Ustaza"

Sadauki ikon Allah ne kawai ya kai shi hotel ɗin da yake zaune ko wajan abokinsa Riyad su yake ya auna maganar Ridayya a ma'auni na hankali amma sam yaƙi samun gamsuwa da maganar ya ji yaƙi yarda dole ne ya sake ganin Ridayya domin this time around ƙafarsa ƙafar Ridayya zuwa Naija zuciyarsa gabadaya ciwo take masa, he feels like uwa wani abu ke shirin faruwa dashi. Wayarsa ya dauka shiga duba picture ɗinta a hankali yake bin baƙar fuskarta da kallon fararen idanunta masu kyau da tsari ga wasu irin abubuwa na musamman a cikinsu ya yi murmushi yana manne wayar a ƙirjinsa a hankali ya ce "Rest of my life" ya sake lumshe idanunsa underneath his breath ya ce "Shanshan my love" Number hajiya Azizat ya kira ta jima kafin ta ɗaga ya yi shiru itama ta yi shiru can Sadauki ya ce "Are you still crying mother?" Ta cikin wayar ta ce "Kuka kuma? Do i look like a baby to u Hamza?" Zai yi magana ta ce "Ya isa now tell me ya Japan yaushe zaka dawo kuma" Ya cije lips "guess what?"

"No idea son"

"I meet Ridayya"

Da sauri kuma cikin ɗaga murya Hajiya Azizat ta ce "What! Ka yi mata magana a can kuma Japan ɗin?" Cikin rashin fahimta Sadauki ya ce "Me ya sa ba zan mata ba? Bayan da tunaninta kullum nake kwana da tashi, i meet her i talk to her ta sauya sosai na ji kuma na ƙara son ta fiye da ko wacce rana data shuɗe"

"Innalillahi wa'inna illahir raji'un!"

"Wannan salatin fa?" A kasalance ta ce "Stay away from her"

Shuuuuu! Ya ji abu ta cikin kunnensa yana shigewa ya kasa cewa komai sai kawai ya kashe wayar gabadaya ya kasa yin wani ƙwaƙƙwarar tunani. Riyad ya kira ya ji yaushe zai shiga makarantar su Ridayya ya faɗa masa sai basa wani secret abu yana buƙatar information akan haka.

Ridayya na zaune hannunta riƙe da honey ɗin da maid ɗinta Ilhas ta haɗa mata, matar ta jima a gidan MB USTAZ ne da kansa ya saka aka nemo masa mace mai hankali wacce zata kula da Ridayya da abinda yake cikinta, shi kansa da yake namiji bai taɓa ganin ciki mai girman na Ridayya ba, ga tafiya ta saka shi gaba kuma yana tsananin tsoron barinta ita ɗaya, komai yake hankalinsa yana kanta. Mai aikin ta ce "Madam kina huta sosai ƙafafuwanki sun kumbura ga ƙirjinki yana yawan ɗagawa kamar mai matsalar numfashi, cikin ya yi girma dukda da bai shiga matakin haihuwa ba" Ridayya ta ja ajjiyar zuciya tana shafa cikin har yanzu Sadauki ne ke yawo a zuciyarta cikin sauri jima take yin Assatagafirullah! A gajarce ta ce "In sha Allah zan kula"

"Me za a tafa muku naga Alhaji ya shigo"
Chapter 101 · 0% Book details