← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 118

Sashe 60

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wace matar?" Da hannu ya nuna mata Ridayya bai ce komai ba.

"Hi" Ridayya ta juya ta kalli Zubby sau É—aya ta É—auke kai. Zubby ta zare Idanu tana kallon Sadauki ta ce

"Goodness! Sadauki wannan abar zaka aura? Kuma a gida za a barka wannan halittar? Yaaakkkk"
Ya gyara tsaiwa sai kuma ya ce "Wakike da suna?"

"Sunan nawa ka manta?" Ya ɗage gira ya ce "Sunan na uwata n da ba zan manta ba? Ke fara ita baƙa ko? Na yi rejecting ɗinki na yi accepting nata shi ne ya ba ki ƙarfin qiwwar cewa haka"

Ya juya ya damƙo hannun Ridayya wacce tuni idanunta ya cika da hawaye ta kalli Sadauki ya yi saurin matse hannunta ya ce

"Wallahi kika bari hawaye ya sauka a gaban kowa zan share su da bakina Ridayya, na tsani kuka mara dalili"

Ta sunkuyar da kanta ƙasa. Zubby dariya kamar me ta ce "Yanzu duk wayewarka da zagaye-zagayen da ka yi a nan ka yar da zango Sadauki? Wallahi kai ka yi abin ni ce kuma da kunya wanna baƙar da kayan idanun za ka kwasa village girl domin babu alamar hawaye a tattare da ita"

Sadauki ya ce "Ridayya ki rama abinda take faÉ—a miki i can't take it anymore, wallahi idan ki ka yi kuka ni na san me zan miki" gabaÉ—aya jikinta rawa yake domin bata saba da wannan tashin hankalin ba. Ya jata fuuuu zuwa mota ya buÉ—e ya dannata ciki ya saka key ya rufe ya dawo wajan zubby idanunsa jajur.

"Kin ci sa a Sadauki baya taɓa jikin ƙazamai kuma baya dukan mata, ita waccan ƴar ƙauyen ita ce zuciyar Hamza Sadauki gabaɗaya ita ce numfashina, abinda baki sani ba irin colour ɗinta nake buƙata mai wahalar samu domin yanzu baƙaƙen mata wahala da tsada suke sadakinsu daban suke, kalar kulawar da za a basu ta musamman ce. Idan za a biya sadakinki da naira na Shanshan da dallors za a biya, ki duba komai na jikinta natural ne halitta da Ubangiji al'arshi ita maza ma tsoro suke bata, ba ke da kika mayar da kan ki ƙaryar kowa ba, ita tana ƙaunar fatarta bake da kike shafa na kan ti ba. I love her the way she is, i love her so much i love her to the square of infinity💕 mother of my childrens"

"Ban yarda za ka aure ta ba" Zubby ta faÉ—a idanunta na sauya dauriya kawai take na cin mutuncin da Sadauki yake mata.

"Idan ban auri Ridayya ba ki ƙaddara Sadauki baya duniya, ni na san saboda ita ne har yanzu ban taɓa budurwa ba, babu macen data isa ta yaudare ni ba a haifeta ba, Sadauki bai yarda da asara ba baya kuma give up zan aureta kuma zan tabbatar miki da haka, useless"

Bayan ya shiga motar ya kasa driving ya cije laɓɓansa cikin zafin nama ya daki kan motar jin kansa yake yana yi masa wani irin hayaƙi, zuciyarsa na tafarfasa bai san dalilinsa na zuwa wajan nan da Shanshan ba, yasan ƙaddara ce wacce ya riga fata ya rasa wanne kalar love words masu taushi da zai yi amfani da su wajan rarrashinta, shi kansa zuciyarsa wata kalar rawa take masa ya buɗe baki zai yi magana ya kasa ya sake buɗewa da nufin magana ya kasa maimakon hakan wani irin sauti ne mai ƙarfi ya maye gurbin maganar da zai yi hakan ya tabbatarwa da Ridayya Sadauki ya fita shiga cikin tashin hankali ainu ta ɗago idanunta daya gama jiƙewa da hawaye ta kalle shi a tsorace yanayin rinewar da idanunsa ya yi shi kaɗai ya bata tsoro ya janye idanunsa murya a daƙushe ya ce

"Can you help me with drive?"

"Ban iya ba" Bai ce komai ya kifa kansa ya É—auki lokaci kafin ya ja motar suka bar wajan.

Ita ce farkon fita ta yi gida da gudu bai bita ba domin yanayin da yake ciki ba nata bane ya nufi gida kawai. Ridayya har dare kalaman Sadauki na yi mata yawa ashe haka soyayyar take? Ashe haka ake faɗawa masoyi? Mai yasa ita sam bata taɓa jin daɗinsu ba, ta rufe idanu ta mirigna she wish a ce ita Sadauki zai mallakawa wannan kalaman domin bata hango ƙarya cikin idanunsa ba, bata da kowa a yanzu har a zuciyarta take gasgata cewa Ustaz ya rasu da yana raye dole zai neme ta. Ta samu kanta da lissafin kwanakin da suka rage da game ɗin soyayyarta da Sadauki.

"Kina yin hawaye zan share su da bakina?" Gabaɗaya tsigar jikinta ta mimmiƙe wani yarrr ita tunda take a duniya ko kiss bai taɓa haɗata da Zameer ba balle irin romantic abun nan, ko idan aka yi kiss ya mutum yake ji?.

Da sallama ya shigo parlourn idanunsa maƙale cikin glasses fitowarsa kenan daga Library yana research a kan wani abu. Jallabiyya ce a jikinsa mai taushi, laushi, santsi kasancewar weekend ne yana gida. Yana ƙoƙarin shigewa ya ji an ce

"Muhammmmd!"

Cak ya tsaya domin Hajiya bata taɓa yi masa irin wannan kiran ba, irin kiran yaran nan. "Dawo ka zauna"

Ya nemi waje ya zauna ya ajjiye wayar hannunsa da diary É—insa da yake ajjiye muhimman abubuwa. Babu wasa a fuskarta ta ce

"Wacece ni? Mene matsayina a wajan mahaifinka dama kai kan ka?"

Ya dinga kallonta "Ba kallona za ka tsaya yi ba, yau dole na kawo ƙarshen abubuwan da suke faruwa"

"Kaka, wacce ta haifi Abba" Yana faɗin hakan ya miƙe ta ce

"Ban gama ba" ya koma ya zauna. Ta kalle shi sosai ta kalli Mai ran ƙarfe ta ce

"Ka kawo mini dalilinka kuma na karɓa na amsa matsayin hujja mai ƙarfi, saboda yaran zamani ba ko wacce mace ce zata iya zama da namiji da ba zai sauke hakƙin aure ba. Na kuma yi wa ita Mardiyya bayanin komai amma ga mamakina ta ce mini ta amince zata zauna da kai a haka, ba zata taɓa kokawa ba, babu gori babu tashin hankali ba zata taɓa magana akan hakan ba. Wannan yarinya ƴar halak ce gaba da baya irinta kuma ake buƙata a aure ba riƙe sirrin miji dana aure"

"Muhammad idan har ka yarda ina da iko da kai ina son ka amince da batun auren Mardiyya, rashin amincewar daidai yake da cewa aurenne baka buƙata kuma wallahi zamu tattara mu bar maka gidanka in sha Allah"

Babu mai iya gane yanayin Ustaz balle ka fahimci yadda ya ɗauki zancen fahimtar halin da yake ciki daidai yake da fahimtar abinda mace mai ciki zata haifa mace ko namiji ya ɗauki daƙiƙo kafin ya fesar da iska yana kuma jan wata ciki zuwa ƙirjinta dake masa raɗaɗi a hankali ya ce "Allah ya sa albarka"

"Amin Amin. Kuma ka dinga amsa kiranta kuna hira ku fahimci juna tunda babu wani babba jagora Mai ran ƙarfe zai je da kansa Kano wajen iyayenta ya nema maka aurenta ai yarinyar nutsastsiyya ce kyakkawa da ita"

Da ƙyar ya ja ƙafafuwansa zuwa cikin bedroom ya yi shiru yana kallon abun tamkar a mafarki taya zai fara iya magana da mace shi yanzu? Balle zama gida ɗaya da ita, ɗaki ɗaya gado ɗaya bashi da wannan confidence ɗin dole ya nemi Mardiyya su yi magana important kuma confidentiality. Maganar Tajj ya gani a WhatsApp.

"Ka zo kano bana nan, wai zaryar me kake ne giss me" ya karanta sai bai bashi amsa ba.

"Munga abin arziƙi da ka yi wa takwaranka muna godiya, kasan Mimi bazawara ce ta yi idda kuma na ji hankalina ya kwanta da ita in sha Allah zan aureta amma har yanzu ban furta mata ba, bana son na yi mata dole ko kuma taga saboda na yi ɗawainiyya da ita" Sosai Ustaz ya karanta ya kuma karantawa. Can ya fara typing sai kuma ya tsaya

"Say something please"

Nan ma Ustaz ya ci-gaba da typing sai ya tsaya. "Talk mana bani da aminin daya shige kai Mohd"

"Ka rabu da ita"

Shi ne kawai abinda Ustaz ya turawa Tajj duk tsayin typing É—in.

"But i love her"

"Ok" Ustaz ya rubuta yana fita daga whatsapp É—in yana ganin kiran Tajj ya share.

Ta juya ta sake juyawa sai kuma ta kasa daurewa ta ce "Yanzu mene tunaninka idan Ridayya ta bayyana ana nufin haÉ—ata aure da Babban mutum ne?"

"Haka ne" Umma ta ce
"Bana tunanin zan amince a gaskiya gabaɗaya yarinyar ta siri mini duk irin wahalar da ya yi da ita ta rabu da shi ta auri wani, sai ta jeme ta lalace take ƙoƙarin tashi daga aiki sannan za a haɗa auren?"

"Ya taɓa ce miki yana son ta ne?" Baba ƙarami ya faɗa yana ajjiye jaridar hannunsa. Umma ta haɗe fuska tana kaɗa ƙafa ta ce

"Ko da wasa amma ai wawa ba mahaukaci bane ni fa uwa ce ina fahimtar abinda ba kowa zai fahimta daga wajan Ustaz ni bana ra'ayin haka ya samu wata ya aura kuma na fara gajiya da ɓoye kai na daga wajan ɗana"

"To ba shakka sannu uwa, idan Ustaz na raye Ridayya na raye kuma bata da auren wani a kanta ita da Ustaz tamkar sun zama miji da mata ne wannan rubutaccen al'amari ne daka rubutacciyar ƙaddara"

"To wallahi idan har ina raye hakan ba zai faru ba, ka rubuta ka ajjiye" ta miƙe fuu ta yi ɗaki. Baba ƙarami ya girgiza kai yana mamakin sha'anin mata duk abinsu wani lokacin zai su shafawa idanunsu toka.

Tajj ya sake ɗaukan Ridayya zuwa asibitin bela suka ƙara duba fatarta suka sauya mata mayuka daidai da kalarta, na wanka na shafawa da kuma na sha. Kasancewar sun ga ji ya sa kai tsaye yayu gida da niyar da yamma ko zuwa dare ya je ko ya aika asiyo mata mayukan.
Chapter 60 · 0% Book details