← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 118

Sashe 61

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka ta yi ta shirya Washegari Tajj ya ce zai yi baƙo sa fita gobe ta cire abayar jikinta ta bar wata ƴar top mai ƙaramin hannu da wando a jikinta iya qwiwa kayan sukai mata ainahin kyau sai baza ƙamshi yake ta sanya man leɓe a baki ta tattare sumar kan nata zuwa tsakiyar kan ta ɗaure da ribbon. Gaban goshin duk sumar ta kwanta ɗan faffaɗan ƙugunta ya zauna das ƙirjinta daidai dana ko wacce budurwa domin Little bai damu da shan nono ba. Tasan yau dole Sadauki zai zo ya kwana bakwai ciff da fara game ɗin. Bayan ta gama shiryawa ta nemi waje ta zauna kiran Sadauki ne ya shigo taƙi ɗagawa a kira na uku ta ɗaga

Ya sauke numfashi ya ce "Shanshan za ki zautar dani" Ta kwaɓe fuska

"I don't know amma kullum ƙara son ki nake" ta yi shiru

"Ridayyerh"

A sanyaye ta ce "Na'am"

"I don't know why I love you, but I do
I don't know why I cry so, but I do
I only know I'm lonely and that I want you only
I don't know why I love you, but I do....,"

"Sadauki" Ta yi saurin faÉ—a a karo na farko ya yi shiru

"The game is over ka je ka faÉ—a mata" A hankali ya ce "ko?"

"Eh" ok kawai ya ce ya kashe wayar. Sai ta ji babu daÉ—i ta kira shi ya ce "Ya akai?"

"Zuwa za ka yi ka faÉ—a mata kenan?"

"E, da matsala ne yau in sha Allah zan faÉ—a mata ki taya ni da addu'a Shanshan" Sai kawai ya ji ta fashe da kuka ta yi saurin kashe wayar ta cillar. Ta jima tana kuka kafin ta ji Nadra ta kinkimi Little Bilal dake bacci ta yi waje..
Da sauri Ridayya ta miƙe gudun kar ta yar da shi tunda ai yafi ƙarfinta ko takalmi bata saka ba riga da wando ne kawai a jikinta ta nufi waje tana kiran Nadra amma ina yariyar gudu take ta ƙanƙame yaron.

Idanun rufe Ridayya ke bin Nadra ta marairaice fuska duk ta ga ji yariyar ta wahalar da ita idanunta ya yi raurau da hawaye daman zuciyarta a kusa take tuntuɓe ta yi da ƙafar mutum ta yi taga taga zata faɗi ta yi saurin riƙe jikinta muryarta na rawa ta ce

"Haba Nadra ki kawo Abbiey na ga ji" ta saka hannu tana goge idanunta. Ganin har yanzu wanda ta buge da ƙafarsa bai motsa ba, bai kuma janye ba fararen jerarrun yatsun ƙafarsa da suke shimfiɗe take kallo. A hankali ta fara bin jikinsa da kallo.

Kyarma da ɓari jikinta ya ɗauka zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi sai da ta yi amfani da dukka ƙarfi hali da jarumta wajan sake ɗora idanunta a kan fuskarsa wacce take kwance a kan waya yana dannawa. Ji ta yi gabaɗaya wasu abubuwa na yi mata yawo he just confusing herself me ya sa yake mata gizau.

Inuwar da ya gani ta cikin wayarsa ya sanya shi kashe wayar domin shigowarsa Kano kenan kai tsaye nan ya nufi ko minti uku bai yi da shigowa parlourn ya tsaya duba wani saƙo ko zarafin zama bai samu ba. Ya kashe wayar tare da ɗago kansa was the first abinda ya a fara gani RIDAYYA tana tsaye tana kallonsa bai san yaushe ne jikinsa ya saki ba har wayar hannunsa ya zame ta faɗi ƙasa duk ƙoƙarin da ya yi amma zuciyarta da gangar jikinsa suka ƙaryata Ustaz, jikinsa ya ɗauki rawa da ɓari naman jikinsa dana zuciyarsa gabaɗaya karkarwa yake.

Mahmah da Tajj suka tsaya kallon ikon Allah ganin abinda ke ƙoƙarin faruwa a kan idanunsa rawar da jikin Ustaz yake shi ne ya fara basu tsoro zufa ta wanke shi tas hatta Nadra tsayawa kallo Uncle ɗin nata take.

Hawaye ya gama wanke fuskar Ridayya idanunta har yanzu a kan fuskar Ustaz. Bai sai yaushe ya ɗaga ƙafarsa ba samun kansa ya yi kawai ba gaban Ridayya ganin abinda ke shirin faruwa ya saka Sadauki saurin juyawa ya bar palroun hannun Ustaz na rawa ya miƙa tare da riƙo ƙafaɗun ya kasa magana sai kawai ya kifa fuskarsa a saman tata tare da....

Idan kin karanta danna share bayan kin yi comment🥰
*MUNAFUKIN MIJI 29*
Mikiya Writers Ass

Bright pens free batch
Nimcyluv

Ganin abin na Ustaz azumin ne ya saka Mahmah kama hannun Nadra ta ce "Mu je ciki"

"Ki haÉ—a da Junior"

Tajuddeen ɗin ya furta da ƙyar yana jin wani abu mai zafi na tsaya masa a ƙahon zuciya, mene ya shiga tunanin Ustaz har haka? Mene tsakaninsa da Ridayya girman tuzuruntakar tasa har ya kai ya fara kama yaran mutane? Gabaɗaya tunanin Tajj ya tsaya wani abu mai kama da zullumi ya fara kawo masa ziyara.

Miƙewa ya yi tare da yin waje ya bi bayan Sadauki domin ya lura da shigowar tasa da kuma sauyin daya gani tattare da shi ɗin.

Bakin Ridayya ne ya fara rawa idanunta a fuskar Ustaz har yanzu ta kasa kallon cikin idanunsa wanda kuma hakan shi yake buƙata, jininta na rawa tana jin saukar numfashinsa a fuskarta yana saukar mata saboda fuskarsa dake ɗan rakaɓe da nata ya kasa furta komai. Da sauri kuma ta yi saurin zame fuskar tana yin baya tare da ƙare masa kallo.

Sai kuma ta shiga girgiza kai while hawaye running down on her face. Ta buÉ—e baki cikin firgitaccen yanayi ta ce

"Mafarki nake da gaske mafarki ba kai nake gani ba, irin mafarkin dana saba yi ne a kullum a koyaushe ba zaka taɓa zuwa gare ni bakai bane you're not my father...... My Abbiey is dead, he is in the grave"

Baki Ustaz ya buÉ—e zai yi magana ya kasa ta yi saurin cewa

"Me zaka ce? Shiru ko na san mafarki nake ni kaÉ—ai ce bani da kowa sai wanda yaga Allah ya taimaki rayuwata me ya sa zaka bar ruhinka ya fito domin ya firgitar dani Abbiey why why why?"

"Don Allah ka yi magana ka ce kai ne ka dawo gare ni baka mutu ba, wayyo Allah wayyo ni Ridayya na shiga uku"

Ji ya yi kamar an saka sofa glue tare da manne masa laɓɓansa ya kasa buɗe baki balle furta komai ya kasa nufar inda yake da tunanin idan ya riƙe ta da hannayensa zata dawo cikin hayyacinta da nutsuwarta. Duk dauriyarsa da yadda ya so riƙe kansa kasawa ya yi jikinsa ya shiga ɓari hatta laɓɓansa rawa yake baya son tunkararta kai tsaye domin a farkon ma, tsananin ta'ajjuji ya saka shi yin hakan da son fahimtar da gaske ita ɗin ce tsaye a gabansa shekaru nawa? Wata nawa? Kwanaki nawa? Mintunawa nawa? Daƙiƙo nawa ya shafe yana jiran wannan ranar?

Abu biyu ne zai faru idan ya ƙarasa wajan wanda kuma a yanzu bai isa ya hana zuciyarsa da gangar jikinsa hana afkuwar hakan ba, domin baya da iko da su a yanzu sune suke jan ragamar shi. Idan bai riƙe Ustaza ya sanyata cikin jikinsa ta jiyo ɗuminsa wanda ta saba da shi tun tana ƙaramar, to idan bai hakan ba yasan sauran abinda zai biyo baya shi kansa bai sani ba yana tabbacin sahihiyar runguma ce zata samu matsayin tarba a gare shi.

Yana kallo ta juya tare da shigewa ɗaki ta rufe ƙofar kai tsaye kuma zaman dirshen ta yi saman carpet ta saki wani irin raunataccen kuka na ƙuncin rayuwarta. Tunanin Abbiey har ya kai ya dinga zuwar mata idanu biyu? Ya fito daga kabarinsa yana wasa da tunaninsa tasan tunda ya kasa furta komai to wannan mutum mutuminsa ne kuka take da iya ƙarfinta har sai da ta ga ji ta fara shassheƙa tare da kwanciya saman carpet ɗin duniyar ta mata zafi cikin wani irin sounds na fitar hayayci ta ce

"Allah ya isa Zameer Allah ya isa ka rusa mini rayuwata ka hanani sukuni da jin daɗi na yi regretting sanin ka a rayuwa, ka yi amfani da rashin gata na, rashin farin ciki, kushe da zunɗen da ake mini a kan halittar da Ubangiji ya yi mini ka yi amfani da son da nake maka ka rabani da jin daɗina ban san haka ɗabi'unka suke ba ashe kura ce da fatar akuya ashe kyan ɗan'maciji ka yi ka zame mini ƙarfen ƙafa bani da sukuni sai na fargabar abinda za ka iya yi mini. Ka zame mini MUNAFUKIN MIJI ba tare dana fargaba ka yi mini illa ka yi mini shamaki da dukkan wani ɗa'namiji babu mai dubana idan ya ji zumubin dana aikata saboda soyayya!"

Wani irin ɗaci take ji a duk sanda ta tuna lokacin data bawa Zameer kanta wai saboda kar ya daina son ta ya koma wajan wata ko ya fasa aurenta. Batun bidiyon da ya yi musu ya fi komai ɗaga mata hankali video ne da zai iya taɓa career ɗinta dana iyayenta da suna raye a ranta take jin ko zai yi sanadin da kowa zai guje ta; ta zama mujiya ba zata taɓa komawa auren Giɗaɗo ba.

A tsaye nan Mahmah ta fito ta ruske Ustaz ya gama haɗa zufa fuskarsa ta yi jajur wanda yau ne kaɗai ta taɓa ganinsa cikin hakan, dukda ba komai ta sani game da Muhammad ɗin ba. Ta kalle shi ta ce

"Babban Mutum ka zauna mana, ina fatan yau zaka tsaya kaci abinci ko?"

Numfashi ya haÉ—iye zuwa cikin bakinsa kafin ya yi magana Tajj ya shigo ya nuna kamar bai ga komai ba ya ce

"Saboda Allah ka mayar da hanyar Leges da Kano kamar wajan wasan yara? Kodayake kuÉ—i ke ake shiga jirgi baya yi maka wahala"

"Ni ai na ji daÉ—in hakan ya fi samun nutsuwar zuciya gabaÉ—aya ya sauya tamkar ba shi ba" cewar Mahmah.

Ustaz ya tattare nutsuwarsa yana juyawa zai fita, sai da ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce

"Zan buÉ—e baki a nan in sha Allah Mahmah,
Bari na je muga?"

" To to ma sha Allah babu laifi a dawo lafiya, yau na tarki sa a" Murmushin yaƙe kawai Tajj ya yi yana bin Ustaz da idanu tare da mamakin abubuwan da suka faru a yanzu ɗin kamar gilmawar walƙiyya.
Chapter 61 · 0% Book details