Sashe 108
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baka faɗa mini yaran waye ba? Ni dai na gama tunani daga dangina har naka babu mai haifar kyawawan yara kamar su" Baba ƙarami ya juya ya sake kallon yaran a hankali ya ce "Ko?" Ta ce "Wallahi fa, Mardiyya kawai nake saka ran zata haifawa Muhammad kyakkyawan yaro kamar shi ko fiye da shi"
"Me ya sa kike tunanin namiji zata haifa kuma kyakkyawa kamar gwarzon ɗana" ta matsa kusa da shi ta ce "To ai haka ne kuma juma'ar da za ta yi kyau Hausawa suka ce tun daga Laraba ake gane ta, Mardiyya nada kyau haka Babban mutum kuma an ce abin cikin ƙwai yafi ƙwan daɗi kaga dole ɗan za su haifa shi da Mardiyya ya zama kyakkyawa" Baba ƙarami ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "Haka ne kam, kina da taki gaskiyar"
"Ni sai naga kamar baka ƙaunar yarinyar nan baka mayar da hankali akan lamuranta karka manta daughter-in-law ɗinka ce fa" Cikin sauri ya juya ya kalleta yana waro idanunsa waje ya ce "A'a karki mini sharri matar, ai jinin ka wuya za shi you're just like a drive mu duka passengers ne a tafiyar nan sai inda kika ajjiye mu, nina isa naƙi zaɓin uwar gidan Tahir" ita dai duk bata gane me yake son cewa ba, don haka ta tattara maganar ta ajjye waje guda. "Ki mini wata alfarma ɗaya mana Hadiza"
"Wacce alfarma?" Ya fito da A.t.m guda biyu ya ajjiye mata kana ya nuna mata jariran ya ce "Haɗaɗɗun kayan barka nake so ki haɗu na Triplets masu kyau na gani na faɗa, komai da kika sani na yara ki haɗu" Umma ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Wannan kam ai ba alfarma bace ko su waye waɗannan na san suna da muhimmanci a rayuwarka sosai. Zan wa wata friend ɗina magana da take kawo kaya irin wannan daga waje sai na yi mata list na duka abinda muke buƙata, sana'arta kenan ai" "To madallah ba damuwa a yi hakan"
"Uwar yaran fa?" Ya ce "Me fa?" Ta ce "Ina nufin me za a siya mata?" Baba ƙarami ya yi shiru can ya girgiza kai ya ce "Iya yaran dai kawai"
"A'a ba za a yi haka ba, uwar kam ai ta cancanci a yi mata ni zan haÉ—awa uwar da kuÉ—ina kaga sai na kai daga nan naga yaran so ma sha Allah"
Yana miƙewa saboda kiran sallah ya ce "Lallai to muna godiya" har zai tafi ta ce "Don Allah yaushe ɗana zai dawo gare ni ne? Idan fushi yake wallahi hukuncin daya ɗauka ya yi yawa ina jiye masa fushin uwa Baba ƙarami, yana da kyau ya dawo kafin matarsa ta sauka ga kuma hakƙin matarsa" A hankali ya ce "Zai ba ki mamaki ne soon zai dawo ki shirya tarɓa ta musamman domin ya yi aure a inda yake"
Da wani irin tashin hankali Umma ta ce "Aure kuma? Shi babban mutum ne ya yi aure ba tare da mun sani ba, a wani gari? Waya aura? Ƴar waye?" Duk hankalinta a tashe yake wani gefen kuma tana jin hakan ba komai bane idan har ba Ridayya bace kuma daman tuni ta raba shi da ita, tana mace tana raye wama ya sani ne? "Zan je sallah zan miki bayani idan na dawo ki haɗa mini tuwon nan ki saka man shanu" jiki a sanyaye ta ce "Tom"
Baba ƙarami na fitowa Main parlor ya ci karo da Junaid ya fito yana gyara hannun riga alamar ya yi alwala ya ce "A'a Junaidu dawowar yaushe?" Yana murmushi ya ce "Yanzu ne Abba"
"Lalle kaga ina son magana da kai kowa idan mun idar da sallah" Junaid ya jinjina kansa suka jera tare da nufar masallaci sosai Junaid da Khaliperh sukai mamakin ganin Burhan a masallacin kusa da Baffa sahun farko har aka idar kuma basu ce komai ba. Baffa ya gai da yayansa yaran suka gaida shi Burhan dake É—an janye jiki ya ce "Barka Abba"
"Yawwa Burhan" Burhan bai kalli inda su Junaid suke ba ya yi shigewar shi cikin gidan da mamaki Abdallah ya ce "Baffa me wannan yake a gidanmu kuma?"
Cikin ko in kula Baffa ya ce "Nina kira shi?" Ya faɗa fuska a kame ba alamar wasa suna shigowa parlour suka samu Zainura tsaye ita da Mami suna kallon tafkeken frame ɗin ƴan ukun wanda aka maƙala a main parlour gabaɗaya bata lura da Burhan dake zaune saman kujera ya zubawa bayanta idanu hatta Mami bata lura dashi ba Zainura ta ce "Mami yaran waye waɗannan don Allah i love them wallahi" Mami ta zubawa yaran idanu musamman na tsakiya ta juya ta kalli little Bilal ta ce "Waya saka frame ɗin nan?" Zainura ta ce "Ni ma a haka na gani kuma akwai a ƙaramin parlonki ma akwai ana Baffa" Kafin Mami ta yi magana sun ji sallamar Baba ƙarami cikin sauri Mami ta shiga part ɗinta domin babu ko mayafi jikinta Zainura ce ta uzzura mata ta fito. Baffa ya dubi ƴar rigar dake jikin Zainura iya qwwia cikin sauri ya ce "Zainura wanne shirme ne nan za ki fito haka?" Ta yi narai narai da idanu ta ce "Baffa naga dama haka nake zama" ya lura dai ba zata fahimta ya nuna mata hanyar part ɗin babarta ya ce "Leave" wajan ta bari cikin sauri Burhan daman tuni ya ɗauke ya fara danna wayarsa da bai jima da siya ba sbd zaman shagon kati da yake yi yanzu.
_You look so beautiful Zinu, and please save ur dress for me...... I love you_
Tsaki ta yi sanda taga saƙon ta rufe idanu da sauri ta buɗe jin tsigar jikinta na tashi da kuma tunanin Burhan data fara. Mami ta ce "Lafiya?" A hankali ta ce "Ba komai" sai kuma ta miƙe ta ce "Mami nifa babyn nan na tsakiya yana mini kama da little Allah, yaran waye don Allah?"
Abinda Mami ta hango kenan har ta juya ta kalli little itama taga kamar a fili ta ce "Allah yaye miki wannan tambayar Burhan dai ya haÉ—u da aiki" cikin sauri ta ce "Why Burhan Mami, wanne Burhan" Mami ta haÉ—e fuska ta ce "Wanda kika baro a parlour yanzu da yake mana sunturi" nan da nan hankalin Zainura ya tashi ta fara hawaye ta ce "To ni mene haÉ—ina da shi kuma don Allah Mami?"
"Oh zan sanar masa ya tattara ya bar mana gida muna da wanda zamu bawa auren ki is that clear baby?" Zainura ƙirjinta ya buga ta kasa magana Mami ta yi murmushin ta ce "To ko dai na bari kya faɗa masa da kan ki?"
"Eh Mami zai ma fi fahimta" Murmushi kawai Mami ta yi a ranta tana jinjina ta ɓarar Zainura. Har Baba ƙarami ya gama cin abinci bai cewa Umma komai ba, ita kuma ta kasa sukuni burinta ta ji ya faɗa mata iyayen yaran amma ya yi gum da bakinsa. Sanda ta shiga bedroom ɗin Mardiyya ta same ta zaune tsakiyar gado da ƙaton ciki gaba Umma ta kalli cikin ta ce "Kila kema dai yara biyu za ki haifa gashi har kin gota Edd naki Daughter"
Mardiyya ɓata fuska ta ce "Wai yaushe Mijina zai dawo ne ni sam na gaji na kasa tantance ke nake aure ko shi?" Da wani irin yanayi Umma ta ce "Rashin kunya za ki mini Mardiyya ni za ki mannawa wannan maganar mai ɗaci a zuciya?"
Fashewa da kukan munafurci Mardiyya ta yi ta ce "Kalamanne suka kwace mini bana nufin hakan, amma ko dutse aka ajjiye da buƙatar a sauya masa wajan zama balle mace kuma mai ciki, akwai haƙƙina da yawa a kan mijina, yanzu ba'a tunanin halin da zan shiga da raina da lafiyata amma babu miji a kusa dani? Yanzu kuma idan na aikata wani abun sai ace mini na aikata zunubi da wannan abin gwara ya sake ni kawai nasan ni ba matarsa bace" ta faɗa gabanta na faɗuwa domin kalaman iya laɓɓanta ne ita kam idan Ustaz ya sake ta ai ta shiga uku balle yanzu da arziƙinsa ya buƙasa. Umma ta ce "Haka ne an yi miki laifi maganar dana shigo na faɗa miki kenan cewa yana hanyar dawowa" cikin hanzari ta ce "Don Allah da gaske Ustaz na hanya kai na ji daɗi in sha Allah idan zai koma tare zamu tafi"
"In sha Allah "
Kawai Umma ta ce amma ƙasan zuciyarta kalmar da Mardiyya ta faɗa ke ta yi mata yawo a zuciya babu kunya ko ɗa'a a furucin Baba ƙarami ta samu yana waya a hankali ya ce "Tajj ya mai jikin?"
"Da sauƙi Abba, ita ta sani kiranka ma"
"Ikon Allah lafiya?" Tunanin Umma ya bata Muhammad ne hakan ya saka ta nemi waje kusa da mijinta ta zauna, ta cikin wayar Tajj ya ce
"Ban san me take buƙata ba Abba, ta dai matsa tana son magana da kai wai akan Shari'a na faɗa mata ai ka daina ka yi ritaya amma dai ta saka rigima ka san yadda ta dawo yanzu abu kaɗan kuka kuma har yanzu taƙi ce mana komai"
Baba ƙarami ya juya ya kalli Umma kamar zai tashi sai kuma ya ce "Bata wayar?"
Tajj ya kalli Hajja Azizat dake cikin baƙar abaya ta yi rolling kanta sai idanunta dake a jeme saboda kuka duk ta rame damuwa ce take ta cin ranta hannunta ta zura tsakiyar cibiyoyinta tana girgizawa a hankali kamar wata Balarabiyya ta zubawa Tajj idanu ya yi murmushi ya ce
"Anty gashi ki yi magana" yana bata wayar ya miƙe jin sallamar Nadra wacce ta yi wayo ta girma kuma sosai ya ɗaga ta sama ya ce
"My queen my happiness an dawo?"
Peak ta yi masa ta ce "Yes Daddy, ina abokina ne?"
"Anjima za su zo shi da Zainura" Nadra ta dinga murna little zai zo. Hannunta ya kama suka nufi bedroom É—in Mahmah.
Tajj na fita Hajja Azizat ta damƙe wayar a hannunta kana ta kai kunne, Baba ƙarami ma shiru ya yi yana jiran me za a ce masa, Umma kuma ta zubawa masa idanu musamman wayar data kasance a speaker.