← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 118

Sashe 112

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita abin dariya ya bata ma tai ta dariya a hankali ya ce "Come"

Yana faɗin hakan ya kashe wayar. Hannunsa ya wanke tas ya zame ƙasa saman carpet tuwon ya saka da kansa sai marairaice fuska yake da sun haɗa idanu da Tajj kuma sai ya sha kunu ya saka malmala ɗaya tare da yin Bisimillah ya saka yatsu ya fara ci.

Har wajajen magariba Umma bata fito ba, ko da Sadauki ya yi kuka rarrashinsa ta yi har ya yi shiru ya koma bacci, tana zaune da tunani kala-kala a ranta wato rabon yara har uku kuma duka maza ba wasa bane, rabo ya saka Ustaz ƙin yi mata biyayya, rabo ya saka ya bar ƙasar rabo ya kashe Sadauki, rabo ne ya saka ta gudu daga Katsina, lallai rabo abune mai girma yarinyar da take aibata muninta ita ta haifi waɗannan zuƙa-zuƙan yaran? Allahu Akbar, gabaɗaya ta rasa me za ta yi ita kunyar fita take tun bata san uwar yaran ba ta ji tana ƙaunar su sosai, hawayen tausayin Ustaz ya shiga cika mata idanu tana zaune aka buɗe ƙofar tare da shigowa.

Inna ta ce "A gaskiya ba zan ɓoye miki ba an wulaƙanta yarinya kuma anci mutuncin furfurata, ban taɓa ganin haka ba tunda nake a rayuwa wannan cin mutuncin haihuwa ne, da ya yi ciki ya ɗora mata ya kama hanya ya yi tafiyarsa yanzu ya dawo amma ko ya shigo ya ce me aka samu? Saboda ga mara galihu ta haihu ko? Ai yau Mardi ki ƴar iska ce tunda ta haifa muku a ce mata sannu, balle kuma tsarkakkiyar yarinya ce mai haƙuri, ko kuma saboda bake ce kika wage ƙafafuwa kika haihu ba shiyasa kike mana haka ohho" Da mamaki Umma ta ce "Muhammad ɗin bai shigo bane?" A fusace Inna ta ce "Ya shigo gashi cikin rigar mamata, ji wulaƙanci ƴar dabar ina ce ni daya shigo zan masa ƙazafi haka?"

"Ki yi haƙuri bari ina zuwa" ina ta dinga satar kallon Sadauki dake motsi kana ta fice Umma kuma bata san mene yake faruwa da ita ba, bata son fita bata kuma son ƙara kallon babyn da Mardiyya ta haifa dukda cewa Ridayya da yaranta sun zame mata ishara akan tsarin halittar Ubangiji.

Number Ustaz ta kira bai ɗaga ba, tana ƙoƙarin kira ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ta amsa ya nemi waje ya zauna ta ce "Yanzu nake kiranka"

Ya É—aga kai ya kalleta sai kuma ya ce "Ina kusa ai" a hankali ya ce "Barka da hutawa"

"Yawwa. Amma na faɗa maka Mardiyya ta haihu ko? Tana hakƙi a kanka fa babban mutum, ashe daman baka shiga ba balle kaga yarinyar data haifa" shi dai ya yi shiru yana kallon ta idanunsa tuni suka shige ciki Gambo ta ɗauka ta miƙa masa ta ce "Tun ɗazo yake kuka ko abinci yake so"

Ya miƙe ya amshi Sadauki ya rungume shi, sosai yake da rigima kuma ya fi son a ɗauke shi ko irin kwanciyar jarirai bai so, saɓanin ƴan'uwan shi sam baya son haske yana buɗe idanu yake rufewa ɗan duhun daya gani a jikin Ustaz ya saka buɗe idanu yana gurun-gurun da baki.

"Bari na je"

"Yawwa sai ka yi wa yarinyar huɗuba" sai da ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce.

"Zani saboda je da kuma kasancewar ta matsayin matata, amma bani ne uban yarinyar ba" yana faÉ—in hakan ya fice Umma ta ji kamar Hausa kamar ba Hausa ba ta dinga maimaita furucin nasa a zuciya da fili.

Mardiyya na zaune bayan ta yi wanka ta shirya ta murza ɗauri tayi kyau ƙwarai abinta sai ƙamshi take wani irin daɗi take ji za ta yi tuzali da mijinta tana jin abinda Inna ke cewa ta ce "Ai kin san tun ina yarinya ba wani kirki ne dani ba, zuwa na yi fa nai mata tas ta dinga kuka tana bani haƙuri idan na yi shiru da baki aka wulaƙanta ki ai ban ma uwarki adalci ba"

Murmushi Mardiyya ta yi ta ce "kin yi maganinta ai yanzu"

"Amma naga wani kyakkyawan jariri a hannunta tubarakallah wallahi aka haɗa jaririn da wannan ƴar taki to cewa za a yi ba mutum kika haifa ba, to daman na ji ƙishin ƙishin wai mijin naki ya dawo tare da matarsa kuma ita ta haifa masa wannan yaran" Inna ta ce tana ƙifta idanu sai kallon ƙofa take. Diyya ji ta yi cikinta ya zuciya abu ya tukare mata a ƙirji idanunta ya yi jajur sai nishi take yi ta ce "Anya Inna daidai kika jiyo?"

Inna ta ce "Habawa ji ne dani kamar maciji wallahi haka akai kuma yara uku aka haifa duka farare idan haka ya tabbata kinga wancan ita ce da gida tunda maza uku ba wasa bane, ki dai kwantar da hankalinki kar jininki ya yi hawa 200 wallahi, kwana nawa ne ya yi miki wani cikin tunda naga baiwarsa kenan"

Hawaye ya cika idanun Mardiyya bawai tabbatarwa ta yi ba, kawai tana tunanin yadda zata iya haɗa Ustaz da wata ƴar macen. Tuna tana tunanin zuwan shi har ta fidda rai kuma Umma bata shigo ba, Balkisa kawai ta shigo sai Baba ƙarami da ya yi mata sannu.

Washegari duka suna Main parlor hadda Ridayya da ta yi wanka cikin wani dakakken lace ta yi masifar kyau, tai fresh sosai sai murmushi take tana kallon Little Bilal da suke ta faÉ—a da Zainura tana cewa "Ba za ka yi mini zaman É—akin ba, tunda babarka ta dawo ita zaka bi"

Shi kuma sai ya maƙale kafaɗa ya ce "Uhm'uhm zani"

"Wai waye surukin namu ne?" Cikin Sauri Abdullah ya ce

"Wai Burhan"

"Burhan?" Ridayya ta maimaita tana sake kallon Zainura, Zainu ta haÉ—e fuska Khaliperh ya ce

"Ta kwafsa ai yarinyar nan, kuma na fahimci Tajj ma son ta yake ga mutumin kirki ta je ta É—akko É—an shaye-shaye"

"Wallahi ba ɗan shaye-shaye bane, kuma yana da kirki" ƙafa Aliyu ya kawo zai haure ta, ta kwasa da gudu ta bar wajan.

Shiru duk sukai ganin Ustaz ya fito cikin wani voyel mai laushi da manyan zane ya ɗora baƙar dara a kan shi ta ƙara fiddo kyawunshi Ridayya ta gefen idanu ta kalle shi ta ɗauke kai, Little ya tafi da sauri yana "Abbiey, Abbiey"

Ya É—auke shi yana shafa kansa kamar zai shige ya dawo ya É—auki Al'hussan a cinyar Ridayya, numfashinta na É—auka a fuskarsa ya É—aga kai suka haÉ—a idanu É—an matsawa ya yi ganin kamar duk t.v suke kallo a hankali ya manna mata kiss a kumatu "Morning Mimi"

Ta yi saurin ware ido da sauri ya ɗago kansa suka haɗa idanu da Baba ƙarami, bai yarda ya sake kallon wajan ba ya nufi part ɗin Mardiyya ganin inda ya nufa ya saka Ridayya jin wani abu a ranta mood ɗinta ya sauya. Mardiyya na zaune cikin kwalliyar atamfa gilita babyn na hannunta ta ji ƙamshin Ustaz cikin sauri ta ɗaga kai ta ganshi tsaye bakin ƙofa hannunsa riƙe da baby, ta yi murmushi tana ajjiye jaririyar ta miƙe ta ce "Oyoyo sweetheart barka da zuwa" kafin ta rungume shi ya gefe tare da shiga cikin bedroom ɗin nata, ya zauna saman stool ta ƙarasa ta zauna ta ce "Good mrng"

Shuɗewar wasu seconds ya ce "Sannu, ya jiki?" Ta ce "Alhamd, ya hanya kana dawowa babynmu na zuwa duniya" ya ɗan yi mitsi-mitsi da idanu ta ɗakko yarinyar ta miƙa masa ba musa ya ɗora Al'hussan a cinyarsa ya amshi yarinyar ya zuba mata idanu can ya ce "Allah ya sa mata albarka"

"Sweetheart ya naga kamar baka farinciki, first born ɗinka ce fa kuma ba wani gift na haihuwa" tunda take bata taɓa ganin murmushin Ustaz irin yau ba, sai hakan ya yi mata daɗi sosai ya yi murmushi ya ce "Zan bada gift ai kin cancanci hakan ko dan riƙo da tarbiyya" bata kawo komai a ranta ba ta ce "Haba sweetheart ai ba komai don na haifa maka baby"

Ya miƙe tsaye ya ce "Zan je abu, ga wannan" ya miƙa mata envelope mai ɗauke da kuɗi ya ɗora akan jaririyar, ta ce "But is true?"

"For?" Ya tambaya yana ware mata idanu to be sure ya ji tambayar ya dai share ne ta ce "Da gaske wannan É—anka ne? Kuma ka yi aure?"

Ya ɗan lumshe idanunsa yana rungume Al'hussan a ƙirji ya ce "E, daman ai ina da aure yara kuma nawa ne Mardiyya"

"Wace matar daka aura?"

"Ridayya Mansur Rano, Ridayya ƙawarki aminiyarki tun kuna yara" yana faɗin hakan ya juya a firgice kamar zata jawo shi amma tana shakka ta yi saurin shan gabansa ta ce "Ridayya ka ce? Wace haka wanann mummunar yarinyar she can't be your wife bayan ka sake ta?"

Ya dinga kallon ta duk yadda yake ƙokarin danne zuciyarsa yaga bai ci mutuncinta ba tunda da gaske tana hakƙi a kan shi kuma har zuciyarsa yayi niyya zama da ita idan ya so ya ji da rigimar Mimi shine take masa ihu aka, ko waye ya faɗa mata ana masa ihu a ka ya haɗe rai sosai a dake ya ce

"Ke bana son shirme matsa mini" bai zata ba ya ji ta cakumi wuyan rigarsa ta ce "Wallahi ƙarya ni,ni za ku ci amana bayan kowa ya san cewa ka sake ta sai dai idan zaman kasuwanci kuke tare a inda ka ɓoye ta" wani kyakkyawan mari ya sauke mata wanda ya sanya ta fasa gigitaccen ihu hakan ya saka Inna farkawa daga bacci a razane tana "Wanne ɗan mara wulaƙancin ne wannan"

Daidai nan Baba ƙarami ya ƙarasu tare da Umma da har yanzu bata fita daga shock ba ta ce "Muhammad ka bar ni cikin duhu ban gane cewa ba ƴarka bace"

Ya juya ya kalli Umma ya kalli Baba ƙarami kana ya kalli Mardiyya dake rusa ihu Inna na tsaye ya ce "To yaushe na yi cikin? Babu wata ƴa mace dana sani a duniya sama da Ustaz kuje ku tambaye ta ita ta amshi budurcina a can Japan, Ridayya kawai ta gani a halin daya kamata daman ace ita ta ganni, bayan tafiya ta da yaushe ta samu cikin? Ta muku bayani bani da lokacin hakan"
Chapter 112 · 0% Book details