← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 118

Sashe 3

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba zan samwa matarka ba, Meer ina son matarka ta san wacece ni da ma'anar zamana a gidan nan, kai da kanka kasan kaf danginka babu mai suna Khairiyya"
Ya girgiza kai a hankali ya ce "Ke da kika san dangin nawa, Ridayya bata sani ba" Ganin yana ƙoƙarin fita ya sa Khairy shan gabansa ta ce
"Ka daina saka mini sunan matarka cikin lamarina, na ga ji da kwana zuciyata na dokawa na barazanar da zan iya samu wajan matarka, ka zaɓa kawai"
Ya juya ya kalleta
"Baki da hankali Khairy, zaɓa kike so na yi? Karki saka na yi abinda zuciyoyi zasu ɓaci"
Yana faɗin hakan ya fice daga cikin ɗakin, bayan ya tabbatar Khairiyya ba zata buƙaci komai ba. Sanda ya fito ko ƙofar ɗakin Ridayya bai kalla ba, ya dai yi mamakin rashin fitowa tsakar gida da ba ta yi ba, bai damu da rashin zuwa gaishe shi ba, haka bai damu sanin abinda ya hanata fitowa ɗin ba, ya yi waje yana baza ƙamshin turaren shi, kamar kullum.

Zameer na fita P.o.s ya ƙarasa, ya cire raguwar kuɗin daya tura a wayar Ridayya, bayan cirar kuɗin wajan mai shayi ya je, ya haɗa masa shayi da biredi da lafiyayyen ƙwai, baya son abincin waje amma bashi da zaɓi, haka ƙaddara ta zaɓa masa. Wayarsa ya ji tana ƙara ganin number Ridayya ya sanya shi sakin siririn tsaki ba tare da wani dalili ba, kira biyar akai masa duk akan idanunsa har ya kammala ya tashi, kai tsaye wajan da suke caca ya nufa maza da yawa kamar shi ke jira.
"Zameer wai a haka kake son ka ciwo miliyan biyun? Baka da rabo a caca" Meer ya yi mitsi mitsi da idanu, ba tare da ya ce komai ba, yana kallon an raba Æ´an wasa za a fara kartawa.
"Gaza ka rabu da shi, yana wasa damu ne sai na ƙarar masa da arziƙin matarsa" AY ya faɗa yana dariya sosai

"Idan bai ci miliyan biyun ba, ai ya sake ciwo mata kamar yadda ya yi a baya....," Cikin tsawa Zameer ya ce "Bana so, zan mannawa mutum hauka yanzu ko da wasa kuka sake furta haka"
A.y ya ce "An bar maganar yanzu na saka dubu hamsin" Gaza ya ce "Na saka dubu hamsin nima" Zameer ya yi shiru
"Kai me ka saka Meer?"
"ÆŠan kunnen goal"
"Goal? Ina ka samu goal?" A.y ya furta da mamaki sosai.
Zameer bai tanka ba, burinsa ya yi nasara a wasan ya tashi da dubu wajan ɗari biyu, wasa ya yi wasa aka cinye shi tun kafin su yi magana ya miƙa musu ɗan kunnen goal ɗin ya miƙe tsaye. Yana miƙewa Usman na zuwa da mamaki yake kallon Zameer kafin ya ce "Zameer ya mai jiki kuma?" Meer ya buɗe ido alamar rashin fahimta Usman ya ce "Ashe kuma mai ɗakinka bata ji daɗi ba, hadda suma" Wani gumi Zameer ya ji yana tsastsafowa daga goshinsa da ƙyar ya ce
"Ka ce me?" Usman ya ce
"Wallahi tallahi nake faÉ—a maka, na É—auka daga asibiti kake ashe baka shina ba? Ai wani mutum ne mai mota kyakkawa da shi daka gani mai kuÉ—i ne shi ne ya É—auketa, kumfa nata fita daga cikin bakinta, a cewar mai É—akina"
A makake Zameer ke sauraron Usman tare da kallonsa, wani irin jirkitaccen yanayin Meer yana son shigarsa da gaske, idan wanda yake zato ne yaushe ya dawo gari? Bai san irin uzurin daya bawa Usman ba, ya san dai tabbas ya yi magana sai dai baya da tabbacin abinda bakinsa ya furtawa Usman É—in.

Zameer ya yi tsaye ya rasa ta ina zai fara kashe gobarar dake shirin tunkaro shi? Bashi da ishasshen ruwan kashe ta, duk wasu ƙasusuwan jikinsa sai da suka amsa yanayin da yake ciki, bashi da matsala da Ridayya, addu'ar shi Allah yasa ba wanda yasan da zaman Khairy a gidan shi. Daga wajan cacar gidansa ya shige lokacin bai samu kowa ba, sai Khairy da Zainaba ta rufeta bayan ya buɗe ƙofa Khairy ta miƙe jikinta na rawa ta ce

"Mun shiga uku Zam, meke faruwa ne wai?" Ya haÉ—e fuska sosai ba walwala, ganin yanayinsa ya sanya Khairy nutsuwa a hankali ta ce
"Mene nufinka na ajjiyeni a gidanka ba tare da sanin matarka ba? Ita ƙarya fure take bata ƴa ƴa, ramin ƙarya ƙurarre ne Zam" A zafafe ya ce
"Ya isa, ya isheni Khairy, ina tunanin lokacin da zaki koma hotel da zama ya yi" Khairy ta riƙe ƙugu tare da yin shewa tana tafa hannayenta biyu

"Like seriously? Ni a hotel? Wallahi yadda na faru zamana a gidanka mutuwa ce kawai zata raba ni da shi, zama daram mai naƙuda taga katifa" Bai furta komai ba, sai kansa dake faman juyawa masa.
"Au yaushe akwai É—aran bare kwanÉ—i? Tsoran Ridayya kake?"
Ya girgiza kai a hankali ya ce "Ni ai ban taɓa ce miki ina tsoran Ridayya ba" Khairy ta ce
"Oh! Son ta ka fara kenan? Tausayinta kake?" A karo na farko cikin rayuwar auren su ya ce "Bana nufin haka, ni bance ba kawai nasan ban shirya rabuwa da ita ba" Ya miƙe tsaye yana duba lokaci ya ce
"Zan je gidanmu, nasan dole za su duba Ridayya, zan duba daidai lokacin da zasu fito na kira ki ya zamana zuwanki asibitin ya yi daidai da zuwansu ku shigo kamar tare ok"

"Kuɗin napep?" Zameer ya dubeta yama rasa me ya sanya take son haukata shi haka kawai, ƙoƙarin shigewa jikinsa take shi kuma yana kokawa da zuciyarsa da abubuwan dake fusgarsa da gaske zuwa gare ta, fuskarsa ta shafa ta ce
"Ina buƙatar ka"
"Zuwa anjima" Ya furta yana mata dubu É—ayar data rage masa, É—akin Ridayya ya nufa ya shiga dubawa cikin sa a yaga kuÉ—in da take ajjiyewa na tanadin haihuwarta, ya É—auki kuÉ—in fuskarsa cike da nutsuwa ya duba yaga a dubu talatin da biyar É—ari takwas ne babu, hankali kwance ya fice daga gidan zuwa nasu.

Har kwana biyu Bilal bai sake dawowa ko hanyar asibitin ba. Da yamma Ammi na zaune idanunta akan Ridayya da bacci ya É—auketa ta juya ta kalli Mami ta ce
"Idan ki kaga Ridayya ta koma gidan mijinta ki ce ni ban haifo ba, koda hakan zai zama ajalinta"
Murmushi kawai Mami ta yi bata ce komai ba, cike da baƙin ciki da kuma takaici Ammi ta juya ta kalli Zainaba data zo duba Ridayya ta ce
"Baiwar Allah karki faÉ—a mini abinda hankali ba zai iya É—auka ba, don idan har ya tabbata haka ne sai na É—aure shi"
Zainaba ta gyara zama ta ce "Hajiya ni kaina na girgiza, bani da ƙarfin qiwwar shaida miki yarinyar ba ƴar uwar shi bace, amma ina da yaƙini zaman da suke ba mai kyau bane, tun Ridayya na amarya yarinyar take cikin gidan"
Ammi ta miƙe tsaye ta shiga safa da marwa, tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskarta.
Zainaba gulma na cinta kamar mijinta ta ce
"Allah sarki masu siyan ƴar tsala suka dinga bani saƙon gaisuwa wajanta, nina ɗauka ma haihuwa ce amma ganin kumfa na fita ta cikin bakinta ta saka jikina ya yi sanyi"
Mami dai kanta na ƙasa tana duba azkar, Ammi ta ce "Wacce irin kumfa kamar mai dafarar mutuwa, ita Ridayya ɗin?" Zainaba ta shafa kanta ta ce "Haka fa Hajiya, to dana shiga ɗakinta naga babu komai sai katifa na ɗauka ko sanyi ne ya kamata"
A gigice Ammi ta juya tare da kallon Zainaba, Mami kuma jin maganar ta yi kamar saukar ruwan sama, jikinta ya yi sanyi kamar wacce akaiwa bugun shekararriyar dawa, ta kasa ɗauke ganinta daga kan Zainaba a hankali ta juya ta kalli Ridayya dake bacci, wata kyakkawar bugawa zuciyar Mami ta yi a karo na farko, duk wani rauni na uwa mahaifiya ya fito, sai yanzu ta lura da baƙin da Ridayya ta sake yi, baƙi na fitar hayyaci ga wani ƙaton ƙashi a wuyanta, babu wata sauran ƙiba a jikinta daka ƙashi sai fata, sai siririn hancinta daya sake fitowa.
Naman jikin Ammi har rawa yake saboda tashin hankali ta ce
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, kina nufin duk yawan kayan É—akin da muka kai Ridayya dasu babu? Ina suke ina suka tafi ina Ridayya takai su?"
Zainaba ta ce
"Nidai babu abinda na gani banda katifa ko labulan arziƙi babu" Sai yanzu hankalin Ammi ya dawo kan maganar Ƴar tsala kenan Ridayya ke yin ƴar tsala? Waya ta ɗakko tana duba number kiran farko ko gaisuwa bata tsaya amsawa ba ta ce "Bilkisu ki ɗauki mota yanzu ki biya ta gidan Zuhura ku je gidan Ridayya ku duba mini kayan ɗakinta" Bilkisu ta ce "Gidan Ridayya?"
"Haka na ce Bilkisu ko ba zaki iya bane?" Kamar Ammi na ganinta ta girgiza kai ta ce "Ba zuwa ne ba zan yi ba, wallahi ban shirya ƙunsar takaicin Ridayya da gidanta bane, amma bari na shirya" Ammi kashe kiran ta yi daidai nan Dr ya shigo ya ce
"Hajiya ina mijin nata? Tunda ya kawota bai dawo ba kwana biyu kenan" Cike da ban haushi ta ce "Ba shi ne mijinta ba, Dr daman cike nake da kai ka saurara mini" Dr ya ce "Hajiya ki same ni a office"
Yana faɗa ya fice daga room ɗin rai ɓace.
Chapter 3 · 0% Book details