← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 118

Sashe 59

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani baƙin ciki Sadauki ya ji zuciyarsa kawai ya miƙe ya nufi kitchen ɗin a ransa yana mamakin waye shi a wajan Mahmah? Mene ya sanya yake yawan haɗuwa da shi? Kuma shi ne wanda yaje gidansu yana neman Ridayya kuma ga Ridayya ga shi what's going on?

Bayan tashin Sadauki Mahmah ta kalli Ustaz ta ce "Muhammad-Bilal ya kamata ka yi haƙuri da dukkan abubuwan da suka faru ka ɗauki ƙaddara, Ubangiji shi ke rayawa kuma shi ke kashewa, shi ke samar wa kuma shi ne ke kwacewa, shi ke tadawa kuma shi ne sarkin dake kashewa. Ka ɗauka Ubangiji ya fi ƙaunar su Baffa da iyalanka shi ne yasa ya amshe su, suka koma gare shi dole ka yi haƙuri ka ɗauki ƙaddara ka sakawa ranka cewa kaima ranarka na zuwa. Ka yi amfani da damarka ka ribaci lokacinka..."

Ta ɗan yi shiru, ta ɗora da faɗin "Aure! Ka yi aure Ustaz don Allah ka raya sunnar ma'aiki sallahu Alaihissalam, ka tara zuri'a yadda Ubangiji zai yi alfahari da kai wannan zaman da kake babu mace a gefenka is not good rashin aure ga baligi babban mutum irinka babbar matsala ce, shi aure ni'ima ce yana ƙarawa mutum nutsuwar zuciya da ɗauke damuwa rashin yinsa kuma yana taɓa kwakwalwa da gurɓata tunanin mutumin daya isa yin shi. Don Allah don Annabi Muhammad-Bilal ka yi aure kar ka tsufa a gida ƴan'matan su dinga gudunka nasan ba rasa matar aure ka yi ba, a taimaka a daure"

Ya kalli Mahmah sai kawai ya jinjina mata kai alamar “In sha Allah” don baya jin zai iya magana ya miƙe da Little Bilal a jikinsa wanda ya rungume Ustaz ya kwanta jikinsa tamkar jikin babansa, ya kama hannun Nadra yana ta tsaye bai ce komai ba. Fahimtar hakan yasa Mahmah cewa.

"Za ku fita kenan? Allah ya tsare Nadra banda ƙiriniya domin nasan halinki" nan ma jinjina kai kawai ya yi kana ya nufi waje da yaran a ransa yana ayyana inama yaran shi ne. Mahmah ta raka Ustaz da idanu ta ce

"Ikon Allah Ubangiji ka kawowa wannan bawa naka sauƙin rayuwa, a yi mutum magana ma wahala take masa? Sai ya ƙaraci zaman shi tari bai yi ba?"

Da sauri Sadauki ya saka ƙafa ya daki ƙofar ta buɗe ya kutsa kai ciki. Kwance ya ganta yashe a ƙasa jikinta nata rawa sai kakkarwa take ga abinda ya ɗora yana kamawa.

Ya kashe gas ɗin ya sauke tukunyar ƙasa zuciyarsa sai harbawa take ya tsuguna gabanta muryarsa a harɗe yake faɗin

"Shanshan lafiya? Me ya sameki?" Shiru bata amsa ba. Ya tattare bakin hannun rigarsa yana ƙoƙarin ɗaukarta yaga ta saki fitsari ya fara gangarawa zuwa bakin kitchen ɗin. Sadauki ya tsaya yana kallon ikon Allah domin bai taɓa ganin mutum kuma mace rana tsaka da fitsarin kwance ba.

"Hamza wai lafiya ne na jika shiru?"

"Mahmah"
Shi kawai Sadauki ya iya cewa Mahmah ta leƙo ta kalli Ridayya da tunda ta yi fitsarin ta dawo hayyacinta, tsananin kunya ne ya saka ta kasa motsawa tunani take mai ya saka ciwon ya motsa mata a gidan da bata iko da shi? Me ya sa ta yi fitsarin a gaban wanda ba muharraminta ba? Ta ƙara cure wa waje guda tana jan wani irin numfashi.

"Mimi fitsari? Sadauki jeka ko? Sai mun yi waya da Hajja Azizat"

Ya yi tsaye jikin sink hannunsa harɗe a ƙirjinsa abubuwa da yawa suna wanzuwa a zuciyarsa can ya juya tare da ficewa daga cikin
kitchen É—in.

Yana fita ya shiga motarsa ya nufi gida zuciyarsa cike da tunani kala-kala. Ridayya kasa cewa Mahmah komai ta yi ta miƙe ta nufi bedroom ta wanke jikinta tare da sauya kaya, kuka ta yi sosai mai isarta wani irin kewar dangi da son ganin Abbiey ɗinta ya addabi zuciyarta, shi kaɗai ya san yadda zai kula da ita idan ciwon ya tashi shi kaɗai ya san hanyar yayewar damuwarta shi ne kawai baya damuwa data amsa shi ko ta yi shiru. Ta dawowa a lokacin da komai ya ƙare.

Ta miƙe ta nufi gaban mirror ta zubawa kanta idanu, hawaye ya cika mata Idanu sumar kanta duk ta dameta daman Abbiey ke kula mata da ita ji take tamkar ta aske ta wuta bata son gashin ya dameta duk wani abu da zai saka tana tunawa da Abbiey ɗinta bata ƙaunar ganinsa.

Ta fashe da wani irin raunataccen kuka kamar yarinya ta saka bayan hannunta ta share idanunta "Shikenan ka yi nisa da duniyata? Shikenan ba zan ƙara ganinka ba Abbiey, ba zan nemi yafiyarka ba, ko bamu dawo daidai ba ka yafe mini nasan abu ne mai wahala ka yi mini uzuri ka amshi ƙaddarata matsayin kuskure irin na kowanne bawa. Me ya sa kai ma ka mutu Abbiey kai ne kaɗai kake so na, me ya sa za ka bisu zuwa inda suka je don Allah ko a mafarki ne ka zo Abbiey ka tafi na rayu"

Jikinta ya ɗauki rawa ta durƙushe a wajan tana wani irin kuka

"Zan yi karatun yanzu zan zama abinda kake so na zama, babu ruwana da maza hasalima na tsani namiji ba zan sake yarda da kowa ba, zan tsaya tsayin daka wajan karatu da yi maka biyayya ko da za a kira ni da _Feminist_. Abbiey soyayya guba ce na sha ta kusa illata ni, Abbiey namiji ba É—an goyo bane, na goya shi ya nakasta baya na, Abbiey namiji É—an kunama ne wallahi tallahi Abbiey na tsani maza, kai ne ubana kai ne yayana you still be...."

"Ridayya"

Ta yi saurin goge hawayen idanunta, duk kukan da ta yi amma idanunta tar suke babu ja sai ruwan daya kwanta a cikinsu wanda ya ƙara musu haske sosai.

Mahmah ta ce "Tun ɗazo nake buga ƙofa shiru are you okay?"

"Eh" Ta furta a hankali kanta a ƙasa zuciyarta babu daɗi

"Ki fito ku gaisa da Uncle É—in Nadra zai tafi, ai ya shigo kina kitchen ma"

"Ba zan iya ba"

Mahmah ta kalleta sosai sai ta jinjina kai ta ce "Babu matsala ki kwanta ki yi bacci idan kin farka za ki samu nutsuwa, daman naga Little ya maƙale masa ne yana kuka gashi hadda ɗawainiyya ya yi musu shatara ta arziƙi"

"Ayya Allah ya ƙara arziƙi ki ce masa an gode"

"La ba'asa"

Mahmah ta fita, Ridayya ta kwanta kan gado ta rufe jikinta har fuska kanta da ƙirjinta na yi mata ciwo sosai tana jin Mahmah tana magana ita ɗaya a parlour a haka har bacci ya ɗauketa.

A can parlour Mahmah ce kawai ke hira Ustaz yana zaune saman kujera ya harɗe ƙafafuwansa, mamakin yadda gudun zuciyarsa ke ƙara hauhawa idan ya shigo cikin gidan yake.

"Ai Tajuddeen baya garin ya koma can Katsina saboda abubuwan da suke faruwa, kasan ƙasar nan ta mu sai dai kawai aja mata li'ilafi cin kashin da ake mata ya yi yawa. Can kwanaki an sace ɗaliban makarantar kwana har yanzu shiru kake ji shawo ya saci shirwa, yanzu haka fa an ce an lalata ƴan'mata da yawa wasu ciki nema da su yanzu don girman Allah Ustaz wa kake ganin zai auri yarinya ba budurwa ba?"

Ustaz ya girgiza kai a ransa yake cewa

"Idan har yana son ta, to budurci ba wani abu ba ne, so na gaskiya bashi da dalili Mahmah ki gagauta tuma da neman yafiyar Ubangiji allahumma yahdiki Mahmah zancen ya yi girma"

"Abun ya yi wani iri ko ki ba lallai na bari ba zamani na ciwoka annoba kala-kala"

Ustaz ya miƙe yana gyara zaman rigarsa domin hirar a saman kan shi yake jinta. Nan da nan Little Bilal ya saka kuka da rigima yana miƙa wa Ustaz hannu a dole sai ya ɗauke shi.
"Wannan yaron ba dai son gantali ba, uwarka na can tana kuka kamar ƴar yaye". Ustaz ya rungume Little yana ɗan jijjiga shi a kafaɗa kamar yadda ya yi wa babarsa har bacci ya ɗauke shi ya ɗan faki idanun Mahmah ya sunbaci goshinsa kana ya miƙa mata shi.

"Zaka tafi kenan?"

"Uhm" ya ce yana nufar waje ko ruwa yaƙi yarda ya sha ta bisa da idanu tana "Miskilin mutum ko ƙaddara, Allah ya baka mace daidai kai amma wannan shirun ni kai na ya kusa kassara ni"

Ko da Ridayya ta farka ta ji ƙamshin da ko a mafarki ba zata manta ba, bawai ƙamshin turare bane ƙamshin Abbiey na musamman ne daban yake ta dinga kallon Little Bilal sai ta marairaice fuskarta a hankali tana tura baki ta ce

"Haba Abbiey komai sai ka ɗauke mini na uba?" Shi kuma yaron ya washe mata baki yana lumshe idanu ta cire masa rigar ta ɓoye ta saka masa wata ta yi shiru tana kallonsa ya zama tamkar t.v a gare ta.

Duk yadda Ridayya take ƙoƙarin gujewa buƙatar Sadauki abin ya gagara, ya san duk hanyar da zai bi ya rutsa ta kuma bata da wani dalili mai ƙarfi ita babu kalamai ma a bakinta. Yanayin yadda yake gudanar da abubuwan shi mamaki abin ke bata, yana ƙaunar yin sadaƙa yana son kayan kwaɗayi ta dinga mamakin inda yake samun kuɗi har yanzu kuma bai yi mata magana a kan fitsarin da ta yi ba, ya yi burus da batun ko a chat daya buɗe mata bata fiya magana ba sai kawai ya ce ta yi masa voice kuma kawai ya kirata kafin ta yi magana ya zai ce Shanshan shhhh numfashinki na kira na saurara yana gama ji zai kashe kiran. Abubuwan Sadauki hadda almara ta ɗan saki jiki da shi har ta yi masa murmushi ko dariya a kwana na biyar ke zancen ya sauya ya ɗauketa zuwa wani waje suna tsaye wata ta zo ta rungume Sadauki.

"Wow ashe da gaske Sadauki ne baby Idanunka kenan?" Sadauki ya juya ya kalli Ridayya yaga ta juya baya tana danna waya kamar mai sanin me take amma dannawa kawai take.

"Zubby ya kike?"

"I'm good, ina ka ɓoye ne ko'ina na duba ka baka nan ka bani number ka"

"No, ina tare da matata ne" Zubby ta zare Idanu ta ce

"Mata fa ka ce? Sadauki aure ka yi babu labari? Shi ya sa ka sauya number" bai kulata ba.
Chapter 59 · 0% Book details