Sashe 31
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
(Wata kishiyar Alheri ce wata kuma sharri mata a dinga jin tsoran Allah, bana son labarin nan ya ja ni da tsayi amma yanayin comment da supporting naku shi ne ƙarfin qwiwata. Bright pens na matuƙar godiya).
Domin gyara ko sharhi
[email protected]
Ko WhatsApp
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 17 ✿*
Mikiya Writers Ass.....
BRIGHT PENS🤙🼠free batch
Mami ta tsare Baffa da kallo zuciyarta na yi mata soya, ta girgiza kai tare da miƙewa zata fice. Baffa ya tare ta faɗin "Yawwa na ce ki tattara dukkan furnitures ɗin dana siya miki, na bar wa Ammi su" Maganar ta doki zuciyar Mami ta juya a sanyaye ta ce "Ban gane na tattara kayan ɗakina na bar wa kishiyata su ba, explanation please?" Cike da faɗa Baffa ya ce
"Ba wani explanation Hausa ce dai na san kina ji ko Fatima?" Ta jinjina kai alamar E, kafin ta ce
"Bana tunanin akwai wani yare da ka iya wanda ban iya shi ba, ma'ana da hujjar tattara furnitures É—ina na bawa wata ne ban wani ba Alhji Mansur, cikakken bayani"
Kamar zai make ta haka ya tunzura ya ce"Maryam ɗin ce wata? Abokiyar zaman ki ce fa. Ok fine zan maimaita ki tattara komai na ki na bar wa Maryam su ina nufin Ammi, kawai yanzu nake ganin ita ta cancanta da kayan bake ba, kuskure na yi wajan siya miki su wallahi tallahi" Mami ta dinga kallon Baffa ta kasa cewa komai ta fice idanunta na cika da hawayen baƙin ciki.
Mami na komawa bedroom ɗinta ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, damuwar zuciyarta gabaɗaya ta addabe ta, duk yadda tasu ta yi sharing ɗinta ta wani ta gagara, gashi babbar damuwarta a duk sanda ta buɗe baki da nufin yin addu'a wajan faɗawa Ubangiji halin da take ciki, sai ta ji kamar an rufe mata baki ta kasa ambaton sunan Allah da nufin neman taimako. Ga wani irin masifaffen yanayi da cikin ya saka ta, na buƙatar mace zuwa ga mijinta babu abinda take so irin kasancewa da Alhji Mansur da shaƙar ƙamshin turaren shi. Ta share hawayenta komai yaƙi ƙare wa kamar cin ƙwan makauniyya.
Washegari da sassafe ta kwashe komai nata, ta ce a zo a kwashe Alhji Mansur Rano wato Baffa da kansa ya kira yara suka kwashe tas, ya ce ita kuma a mayar mata da furnitures É—in Ammi ta ce ta gode. Kwana biyu da yin haka aka shigo da sabbin kaya Æ´an Turkiyya masu masifar kyau lokacin suna zaune a parlour Umma ta shigo.
Ammi ta dinga kallon zubin kayan da tunanin ko Baffa ne ya siya masa sabo fil tana girgiza ƙafa cike da taƙama ta ce "Kayan ne?" Wani matashin saurayi ne ya ce "E, Hajiya sune ina za a saka" Ya ce yana danne dariyar data kama shi
"Ok ku haura da su upstairs" cewar Ammi. Mami ta dinga murmushi kafin ta juya ta ce "Hilal har kun ƙarasu?" Ya ce "E Mami, Mimi na gaishe ki ma" Mami ta miƙe tana murmushi har lokacin ta ce
"Zan kira ta kam, amma kayan sun yi ma sha Allah". "Mami a wajan fa kaf babu irin su kin san kuɗin da Grandfather ya tura? Ai arziƙi ya yi idan kana da kuɗi ka shige duk wani raini da wulaƙanci wlh Mami"
Murmushi kawai Mami ta yi Hilal ya ce "Talk Mami, ai gaskiya ce duk wata mugunta a wajan ɗan talaka aka santa musamman idan ka samu gidan miji ba fus ba ass sai dai a shimfiɗa dugwayen ƙafafuwan na cin banza da damfara, ga mugun abu kamar haihuwar Katsinawa"
"Wallahi Allah ya shirya ka Hilal Yaya A'isha bata gasa maka baki ba halan?" Ya É—an kashe murya ya ce "Surprise....."
"What?" Ya mirgina kai ya ce "Na ba ki gari" Ta girgiza kai ta ce "I'm not good da cankar Surprise but i like surprises, just giss me" Hilal ya ce
"Aure zan yi" sai ya ɓata fuska ya ce "Mimi ta ce na yi ƙanƙanta don Allah mene abin ƙanƙanta a nan? Shi aure ai raya sunan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, kinga haihuwar fari sai na saka sunan Mamina" Mami ta ce "Kuma kana da gaskiya, amma auren RUƊIN ƘURUCIYA ne"
"Mami Ridayya fa?" A wannan lokacin ita kan ta Umma mahaifiyar Ustaz kallon Mami ta yi tana jira ta ji me za ta ce? Amma ta haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba, ganin hakan yasa Hilal yin shiru.
Ammi kunya ta kama ta ganin yadda ya kwafsa, a ranta tana mamakin kuÉ—i irin na mahaifin Hajja Fatima wato Mami.
Hilal suka fara gyara kaya, Mami kuma ta haɗa musu lunch. Hira suke sosai da Umma tana mata murnar kayan data siya ta ce "Hajja Fatima yaushe aka zuba miki kaya har kika sauya wasu?" Caraf Ammi ta ce "Lallai fa, cewa ta yi bata so tunda kinga ai haihuwa za ta yi shi ne Baffa ya ce ta bar mini su, da gudu na karɓa ina godiya" Girgiza kai kawai Mami ta yi tana jinjina munafurcin Alhji Mansur Rano. A ranta tana mamakin yadda Ammi ta gane tana da ciki domin kullum cikin hijab take a gidan, kamar wacce take duba?
Ustaz Bilal sai raba Idanu yake a harabar makarantar su Ridayya, a hankali ya dubi a gogon hannunsa ganin ai tuni lokacin tashi ya yi wasu sun jima a gida ma. Ya miƙe daga jinginen da yake a hankali cikin nutsuwa da kamala, tare da zallar haiba da nagartar dake siffanta ainahin Ustazancin shi, ya nufi office ɗin Headmaster a ransa yana ayyana rashin dacewar haɗa mata da maza a makaranta. Da fara'a Headmaster ɗin ya tarbi Ustaz Bilal.
"Irin wannan zuwan bazata haka? Fatan lafiya" Ustaz ya yi shiru yana haÉ—a kalaman da zai faÉ—a a gajarce. "Kamar kullum karatun Ridayya sai addu'a, domin tafi gane naka karatun fiye da na mu, babbar damuwar ma kullum cikin bacci take a aji, bata wasa da yara she feels uncomfortable" Ya fiddo da duka littafan ta na makaranta wanda ya amsa wajan class teacher É—in su, ya nuna wa Ustaz kana ya ce
"Za a Iya magance matsalar ta, ta hanyar cire mata tsoran dake addabar zuciyarta a saka son karatu da nuna mata itama ƴar ce kamar kowa mai gata da ƴan cin zama duk abinda take da buri a duniya, a nuna mata watarana ita uwa ce a nuna mata cewa Ubangiji ke yin halitta ba kuɗi ake bayar wa a kasuwa a siyi mutum ba, buwaya da ƙudirar Allah da girman zati da kaɗaitar shi ce, a nuna mata Ubangiji yana son duka bayinsa kuma babu mummuna a cikin halittun daya halitta, a saka mata ya ƙini da hope na cimma buri, a nuna mata cewa ko wanne mutum yana da nasa raunin cikakken mutum mai asalin kyau shi ne wanda ya yarda da Ubangiji ya kuma yar da ƙaddara. Dukda ba lallai ta gane yanzu ba, amma ya zama na wannan shi ne nata karatun kafin mu ga mai zai faru next"
"Yaa Rabb"
Ustaz ya furta a taushashe yana lumshe idanunsa, Headmaster baya iya tantance yanayin sauyin fuskar Ustaz Bilal don haka bai fahimci damuwa ko akasarin hakan ba ya ce "Karka damu fa, ina ji a jikina Ridayya zata zama wata a nan gidan duniya, yawanci yara irin wannan suna da baiwa ta musamman" Jinjina kai kawai Ustaz ya yi da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce "Ta na ina?" Da mamaki ya ce "Ai mun tashi, ka duba za ka ga babu students a compound" hankalinsu ya tashi a ka shiga neman Ridayya babu ita babu mai kama da ita, har class teacher ɗin su sai da aka kira.
A ɓangaren Ridayya sai rarraba manyan fararen idanunta take yi tana jin me suke faɗa.
"To ko dai Aljana ce ke ko kuma babanki kika gado a muni ko?" Ridayya ta kalli Nimra wacce ta kasance class mate É—inta a makarantar masu kuÉ—in dake nan unguwar Darmanawa.
ÆŠaya daga cikin students ta fashe da dariya ta ce
"Help me as Nimra, oh oh muni ko wahala?" Nimra ta yi fari da idanu tana riƙe maƙalallen ƙugu idanunta kamar ya fado cike da azaba ta ce
"Yapp, ga idanu kamar na mujiya gata daƙiƙiya sai tsinanen bacci kamar kasa, kullum sai ta yi mana fitsari a class"
"Ohh Goodness! Fitsari?"
Jidda ta faɗa a ruɗe. "Ai yawan sai na ci uwar ta wallahi, baƙa mummuna mai baƙin zunubi ji Idanu kila mayya ce" A sanyaye Ridayya ta ce "Ai dai ɗakin Allah ma baƙi ne"
Da sauri Nimra ta doke bakin Ridayya ta ce"Uban me kika sani? Ke ina kika taɓa ganin ɗakin Allah ɗin? Wannan dama gidan zoo aka kai ma da ita da sallah mu je mu ga daƙiƙiya" Idanun Ridayya ya yi rau rau sai ya fidda wani shiny.
"Ai dabbobi ake sawa a zoo road" Jidda tana dariya sosai ta ce
"To ke ɗin me ce? Wallahi dabba ce ki je ki tambayi Babanki ki ce a dabbobi da wacce kike kama zai faɗa miki" Suka haɗu sukai mata dukan tsiya da bulala wai ba za su saka hannu ba kar su shafi baƙin zunubi. Haka kurum suka tsane ta. Ridayya na son wasa da zarar ta nufe su idan an fita break sai kowa ya daka mata tsawa ya ce ta tafi, daga nan sai ta fi wajan bishiyoyin makarantar ta dinga wasa Ita ɗaya, a lokacin kuma sai ta dinga karatu ita ɗaya ita bata iya gani ta karanta muddin zaka takura mata ta yi karatu to ba zata iyi ba ko a exam ne. Idan ita kaɗai ce kuma sai ta dinga yi tiryen-tiryen a nutse take komai nata.
"Shalele" Da sauri ta ɗaga kai tana kallonsa dukda hawayen dake idanunta bai hana Ridayya sauke ajjiyar zuciya ba, ta nufi wajansa da gudu kafin ta ƙarasa ya ware hannayensa tana zuwa ya ɗauketa ya cira ta sama yana furta "Shalelen Abbiye, You scread me" Ta yi shiru. Jikinta ya ji zafi sosai yana ɗaga rigarta ya ga shatin bulala duka jikinta, ya kalleta tambayar duniya taƙi faɗa masa waɗanda suka dake ta.