Sashe 15
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ridayya ta ce "Da farko dai...." Da sauri ta yi shiru zumbur kuma ta miƙe jikinta na rawa da ɓari ganin Zameer a kanta Zainaba ta ce "Ya zaka faɗo mini gida babu umarni kamar ana zaman bariki" Bai kula Zainaba ya finciki hannun Ridayya tana turjewa ya fara janta a ƙasa, maƙota duk suka fito har da mazajensu babu wanda ya iya dakatar da Zameer, Zainaba ta dinga ƙundumawa Meer zagi tana faɗin "Tsinanne haihuwar asara Allah ba zai bar ka ba, In sha Allah Ridayya ta kusa rabuwa da kai faƙirin banza cima zaune" Maganganun Zainaba kamar saukar dalma haka Ridayya take jinsu a zuciyarta, jin yar da take tsinewa mijinta da yadda take fatan aurenta ta mutu baƙin cikin haka ya saka Ridayya rushewa da kuka. Zameer ya rufe ƙofa baka jiyo sautin komai sai ihun Ridayya da saukar bulalar wayar caza "Iskancin banza da wufi ni za ki kawowa ɗan iska har gida, wato kema Idanunki ya buɗe abinda na gudu kenan na datse karatunki, shi ne za ki shigo mini da kwarto har cikin gidana?" Ridayya tuni numfashinta ya tsaya Khairy na tsaye ta ce "Shi ya sa ban taɓa faɗa maka ba ai wallahi kar ta ce sharri nake mata, yanzu ai ka gani da Idanunka" ran Zameer ya ɓaci domin baya wasa da duk wani abu daya shafi alaƙar gado tsakaninsa da Ridayya cikakkiyar gamsuwa a wajanta yake samu dukda bata tsinana masa da uwar komai, kamar ruwa haka take zama, she's not romantic at all. Amma baya jin zai iya sharing ɗinta da wani banza ya shige ɗaki Khairy ta bi bayansa suka rufe ƙofa Ridayya na shimfiɗe kamar gawa.
Hajiya da Mai ran ƙarfe ne suke jijjiga Ustaz amma ina ya jima da fita daga hayyacinsa, a gigice Bintalo ta shiga yayyafa masa ruwa amma ko motsi bai yi ba, Hajiya ta fara kuka wiwi don a duniya tana ƙaunar Ustaz ta jima bata taɓa ganin mutum mai zurfin cikinsa ba, taurin zuciya kafiya da na ci da kuma haƙuri da kawaici. Firfita take masa tana shafa kansa "Innalillahi! Mene shirin faruwa ne mun shiga uku" Mai ran ƙarfe ya ce "Maganin shiga uku Allah, ciwon Ustaz ne ya tashi yi ta yi masa firfita, Bintalo ci-gaba da zuba ruwa a kansa"
Gabaɗaya suka rufo akan Ustaz su shafe mintuna kafin ya sauke ajjiyar zuciya idanunsa rufe bakinsa na motsa wa shi kaɗai ya san me yake cewa "Bilalu lafiya,ina dalilin wannan ciwo naka?" Ya sake rufe idanu da tunani inama ya buɗe idanu yaga mafarki yake. Hajiya ta riƙo fuskarsa ta shiga girgiza shi ta ce "Yi magana Bilal buɗe Idanunka"
"Baffa, Abba, Mami, Amma, Junaid, Balkisa, Zuhura, Zainura, Aliyu, Usman, Umar, Abubakar...," Ya kasa ƙarasa maganar Hajiya ta ce "Mene ya same su? Suna ina yi mana bayani Ustaz" Nutsuwa ya tattaro ya aza bisa gangar jikinsa ya daure ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!"
"Ustaz wai mene haka?" A hankali yana fusgar numfashi ya ce "Ba a gansu ba, suna mace suna raye tsayin watanni..." Kafin ya ƙarasa faɗa Hajiya ta yanke jiki ta faɗi.
Zameer na zaune shi da Gaza ya ce "Zameer baka son yarinyar nan ka sakar musu Æ´arsu?" Wani irin murmushi ya yi ya ce "Hauka ma kenan"
"Kamarya Hauka mene fa'idar zamanku aure ba soyayya ba kulawa" Zameer ya gyara zama ya ce "Tunda nake a rayuwa ko da second guda ban taɓa jin son Ridha ya gitta ta zuciyata ba, ban taɓa ji ba"
"Than, you have to divorce her" Ya É—aga kafaÉ—a ya ce "Shi ne ba zai iya ba, domin akwai amfaninta yana nan zuwa musamman yanzu dana fahimci ciki gare ta" Gaza ya ce "Ikon Allah, mene shirinka sanar dani please" Murmushi kawai ya yi ya ce "Babar Ridayya na da kuÉ—i sosai da wanda aka bar mata gado da wanda ta mallaka nata na kanta, na saka an duba mini wajan ÆŠAN GADO, Malamin ya iya aiki"
"Kenan asiri ka yi wa ƴar mutane" Ya girgiza kai ya ce "Ko kaɗan wallahi ban taɓa yi wa Ridayya asiri ba, ai ba zan ɓoye maka komai ba nasan dai ina zuwa ana yi mini duba, plan ɗina shi ne da zarar iyayenta sun baza zata mallaki kadara nai yawan gaske, zan buƙaci ta bani na juya mata amma ko wanne ta yi sa hannu da sunana" Dariya Gaza ya yi sosai ya ce
"Saboda ita bata da ilimi" kai tsaye ya ce "Ina ta ganshi, ai dabara na yi na datse mata karatu saboda karma idanunta ya buÉ—e ta ce zata iya juya kadarorinta, tana gama secondary a ajinta na farko na jam'i na datse karatun idan ina raye ai ba zan bar Ridayya ta yi ilimi ba balle ta mallaki wani abu nata na kanta, soon rabata da garin nan"
"But You don't love" Ya É—aga kafaÉ—a ya ce "Ita ai tana so na, zata iya mutuwa saboda ni soyayyarta a gare ni ita ce rauninta na fahimta, yanzu ma goga take mini" Sallama sukai yi tare nufar gida.
Kasancewar bata samun bacci sosai ya sa tana tsaka da goga bacci ya ɗauketa. Hayaƙi ya cika ɗakin da sauri Zameer ya shigo gani ya yi sabuwar shaddar shi ta babbake Allah ya sa dutsen bai buga ba. Ya kalli Ridayya ya kalli kayan cikin ɓacin rai dutsen da ya yi jajur da wuta ya ɗauka ya manna mata shi a fuska. Ihun a zaba ta saki da sauri ta shafa fuskarta sai fata ta biyo hannunta rabin fuskar ya kwailaye kafin ta dawo hayyacinta ya yi ball ta ita ya taka mata ruwan ciki azaba ta saka ta saki fitsari da tusa a wajan ya juya ya fice daga cikin gidan, kuka ta kasa ta riƙe cikinta sai birgima take a wajan har gari ya waye tuni kamanninta suka sauya. Ta fito da ƙyar zata shiga banɗaki ta ji Khairy na waya tana cewa "Na je likita ya tabbatar mini ciki ne dani" Ridayya ta nemi ciwo ta rasa ta saki butar hannunta ta nufi kitchen wata sharɓeɓiyyar wuƙa ta ɗakko kai tsaye ta nufi ɗakin Khairy da wuƙar a hannunta....
Idan naga comment gobe kuga posting da wuri.
Muna godiya da zaÉ“ar BRIGHT PENS🫶ðŸ¼ðŸ¤™ðŸ¼
*✿ MUNAFUKIN MIJI ✿*
Nimcyluv@Arewabooks
Page 9
BRIGHT PENS🤙🼠free batch
*HAUSA AFFILIATE MARKETING🥰👇ðŸ¼*
https://chat.whatsapp.com/LvflCjMI3U5IfUHobHzudk
Khairy na kwance akan gado daga ita sai gajeren wandon Zameer, tana danna waya tare da ƙyaƙyacewa da dariya. Kamar daga sama taga Ridayya ta faɗo cikin ɗakin tana huci kamar wata mahaukaciya, jiri sai neman ka da ita yake neman yi amma ta turje.
Tsirarar wuƙar ta nunawa Khairy tana nufar wuyanta da ita, idanunta jajur hawayen baƙin ciki na zuba daga cikin idanunta, na tsananin kishi da soyayyar Zameer, imagining take ita cikin ya tabbata yana da kusanci da Zameer, to; a cikin biyu za a yi ɗaya, ko dai ta kashe Khairy ko kuma ta kashe kanta ta huta.
"Kar ki mini ihu a ɗakin nan, daga ni sai ke ba ki da wani mataimaki" Ridayya ta furta tana sake nunawa Khairy wuƙar. Ganin haka yasa Khairy rikicewa tsoro ya ɗarsu a zuciyarta. Bakinta na rawa da ɓari ta ce "Na shiga uku me na yi miki da zafi haka Anty Ridayya? Me ya sa kika tsane ni?"
"Riƙe kalamanki marasa daraja a wajena Khairy, bana buƙatar duk wasu shaci faɗe naki, idan yau ki kaga ban kashe ki ba, to wallahi gaskiya kika faɗa mini" Ganin al'amarin Ridayya da gaske ne domin ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta, maganganun fitar da kansu kawai suke ba tare data shirya ba ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Kisa kuma? Kashe ni za ki yi, me na yi miki kina cikin hankalinki kowa?" Ridayya ta yi dariya sosai dukda cewa bakinta a waskace yake, fuskar ta tattare saboda ƙona ta da Zameer ya yi, muninta ya sake bayyana ƙarara idan ka kalli fuskar Ridayya ba za ka so ka sake kallo ba.
Ridayya ta ce "Idan na yi miki lahani, na saɓa miki kamanni tare da ji miki rauni na kashe ki za ki gane ban haɗa hanya da dawanau ba balle a laƙaba mini sunan mahaukaciya, Khairiyya ki faɗa mini cikin waye a jikinki, mene ya haɗaki zama da ɗakin mijina bayan ga naki can? Ina dalilin sanya sutturar mijina bayan ta haramta a gare ki, gajeren wandonsa, tsaraicinsa ne" Lallai daman an ce; mai haƙuri bai iya fushi da tara mutum ba. Khairy ta rikice ta rasa da wanne kalamai za ta yi amfani da su wajan shimfiɗa ƙaryar da zata tseratar da ita, daga haukan Ridayya domin ta gama tattarawa tare da azata a gurbin sabbin masu taɓin hankali.
"Ci...ci...ciki kuma? Ni mene haɗina da ciki? Wallahi....," Kafin ta ƙarasa maganar Ridayya ta sauke mata wuƙa a gefen hannunta, nan take wajan ya dare jini ya fara zuba. Khairy ta zunduma ihu tare da faɗin.
"Wayyo Allah, mahaukaciya ce wallahi mahaukaciya ce jama'a a kawo mini ɗauki" Ridayya ta sake sheƙewa da dariya ta ce "Ai na faɗa miki, kashe ki zan yi muddin ba ki faɗa mini cikin waye a jikinki ba"
Suka shiga zagaye ɗakin, Khairy na riƙe da hannunta tana ihu a kawo mata ɗauki, amma tsit kake ji, tamkar malam ya ci shirwa. "Khairiyya kenan ki daina ɗauka ban san me nake ba, na sani ni yarinya ce, you're smarter than me, tunaninki da nawa ba ɗaya bane ba komai nake ganewa ba idan, idanuna suka makance, wallahi a yau ko za a kashe ni, ko zan tafi gidan yari sai kin faɗa mini gaskiya ko na kashe ki a nan, idan ya so a yi jana'izarmu tare Ubangiji ya yi mana hisabi ya kuma tantance mai gaskiya" Khairiyya na kuka sosai, bawai don Ridayya ta fi ƙarfinta ba, saboda makamin dake hannunta ba a wasa da mai wuƙa.
"Bani da ciki, mene zai haÉ—ani da ciki kuma? Ki yi mini rai ni gidanki ma zan zo na tattara na bar miki, idan hakan zai zama farin giki a gare ki, da nutsuwar zuciyarki"