← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 118

Sashe 102

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"No; kar ki damu da abinda za mu ci zan kula da wannan ki yi abinda kike so kawai" Ilhas ta jinjina kai domin bata jin daɗin jikin nata amma tabbas Ridayya na buƙatar kulawa ta musamman. Fita ta yi domin iyaka cin ta ƙaramin parlon gidan ganin hakan ya saka Ridayya miƙewa bayan ta kammala shan zumar ta nufi shashin da ta san gwarzonta na ciki, ƴar ƙaramar riga ce a jikinta silver mai sauƙin nauyi domin zafi jikinta ke yi mata dukda weather na ƙasar, rigar iya cinya jikinta duk a bayyane ga cikinta a gaba sumar kanta a tufke har baya gwanin sha'awa. Tura ƙofar ta yi sallama ta yi cikin siririyar muryarta mai cike da nutsuwa da tarin rauni tana shiga yana fitowa daga wanka murmushi ta yi ta ƙarasa bakin gado ta zauna tana miƙe ƙafa ta ce "Yau me ya samu Yaa Bilal ne?" Showel ɗin hannunsu ya miƙa mata ta gane me yake nufi ta maƙale kafaɗa ta ce

"Ni ma na ga ji fa"

"To tasar mini a ɗaki" Ta dinga dariya tana kallonsa ganin yadda ya kame fuska sam bata san fushin me yake ba, dukda bai nuna ba amma ta san dole akwai wani abu a ƙasa tana kallonsa ya gama shirya wa tas sai baza ƙamshi yake ya fito a cikakken mutum mai cikar zati gwarzon Ridayya mijin Ridayya yayan Ridayya jigon Ridayya ta ko wacce fuska, kusurwa ko wanne sashe. Jallabiya ya ɗakko zai saka yana sane ta yi saurin miƙe fuska a shagwaɓe ta ce "Abbiey Please na" Tana taɓa shi ya yi saurin damƙo hannunta ya haɗa ta da jikin wardrobe ta fara zazzare ido ya dinga kallonta ya ce

"Wana kama?"

"Ni ni.... A a bani ba"

Yanayinsa ya bayyana tuni shiyasa ko magana baya son yi ya sauke mata numfashi a ƙirjin "Ke kina tura mini stickers da emojis na kisses, a hall meeting"

"I am sorry"

"Nooo!!"

Magana za ta yi kawai ya kashe hasken ɗakin bisa sunna ya nufi bedroom....... Ƙafarta yake danna mata a hankali kumburin na sauka tana kwance gefensa karatun kur'ani suke saurara duka suna bi a hankali wayarta a hannunta ta shiga X tana rubutu can ta ji ya kashe karatun ya rungume ta very tight a jikinsa zuciyarsa na bugawa sun jima kana ta zuba masa ruwa mai sanyi ya kalli ruwan ya saka hannu ya amsa ya ajjiye ta ce "Kasha mana" "ban so"

"Me kake so"

"You!" Ta zuba masa ido yana ƙara riƙe ta a jikinsa "You Ustaza i want you Ridherh, I need u jaririya i want u always to be by my side I love you, I really really loves u Nisful hayaat" ya sumbaci kuncinta bayan ya gama maganar.

Gaban Ridayya ya faɗi akwai abubuwa da Abbiey ya kamata a ce ya sani amma ba zata taɓa iya faɗa masa ba, ba zata iya ba ita haka ƙaddararta take zama da MUNAFUKIN MIJI ya rusa dukkan wani jin ɗaɗinta ya taɓa career ta. Kallon juna sukai ta ce "About yesterday a makaranta" ya yi shiru ta ce "Sadauki Abbiey..." Ya yi saurin rufe mata baki da yatsu biyu ya ce "It's ok"

"Ya zo wajena....," ya watsa mata wani kallo jikinta ya yi sanyi calmly ya ce "I trust you ok"

Ta jinjina kai tana komawa jikinsa ta kwanta “I love you” da sauri ta miƙe tunawa da zata ɗora girki ga dare na yi ta kusa faɗuwa ya riƙe ta ya ce "Zauna"

"Abinci zan yi fa baka ci komai ba"

"Na sani, akwai maid za ta yi" ta maƙale kafaɗa ta ce "Bana son mai aiki ta yi maka salon ta barbaɗa wani abu"

"Kina tsoran snitching"

Gwalo ta yi masa har ta tafi ta dawo kamar zata ɗauki wani abu ta yi masa kiss ya girgiza kai kawai yana lumshe idanunsa. Ridayya taƙi komawa makaranta saboda tsoron gaminta da Sadauki sosai take jinsa a zuciyarta da shakkar haɗuwa da shi. Soyayya suke mai cike da kwanciyar hankali da fahimtar juna gashi kullum sai Ustaz ya bata magani ya kuma yi mata addu'a wani lokaci kuma ya sauya mata hira don ya fahimci aikin maganin, ya gujewa zuwa Nigeria yana buƙatar zama kusa da iyalinsa da bata kulawar daya dace ita da abinda ke cikinta. Suna da fahimtar juna amma hakan baya hana su samun saɓani wani lokacin Ridayya ta dinga kuka tana ita gida kawai zata koma shi kuma ya birus da ita idan ya gaji da jin kuka ya dafe kumatu ya ce "Oh ni mijin kwaila naga ta kaina, wanne zunubi ne wannan Ustaza?" bata yin komai sai girka musu abinci da wanke kayan Abbiey na sirri domin ta ce gajerun wandonansa sirrinta ne. MB USTAZ a zuciyarsa yake tsananin haɗuwa da Ubangiji akan hakkin Mardiyya ya kasa sauke nauyinta dake kansa har zuciyarsa kuma babu saki a tsarin rayuwarsa yana jin da zarar Ridayya ta sauka za su koma ya daidaita kan matansa ya yi addu'ar Allah ya bashi ikon kamanta adalci a tsakaninsu gashi daman an ɗaga zaɓe sai zuwa watanni bakwai masu zuwa...

Umma na zaune a parlour look so worries tunanin inda za taga Babban mutum kawai take ta ji a ranta fushi ya yi saboda ta saka ya saki shegiyar yarinyar can wacce bata san wacce duniya take ciki ba, gashi abubuwan hannunta na neman gazawa ta yi siyayyar haihuwar Mardiyya gashi da sauran rina a kaba Diyya ta ce kayan fitar suna kala ashirin take buƙata, filin da ya yi saura wajan Umma ta mallakawa cikin Diyya ta saka sunan Mardiyya har da shaidu abin duniya ya fara yi mata zafi ita hakan duk bai dame ta ba ɗanta kawai take son gani, gashi har mujiyar yarinyar ba labarin su ta kalli Baba ƙarami ta ce "Ka yi wa Allah ka faɗa mini inda yarona yake ina so na ganshi ga matarsa na dab da haihuwa duk wasu responsibility nata yana kansa ka ji tsoron hakki Abba" "Responsibility?" Baba ƙarami ya maimaita ta ce "E, hakkina na uwa dana matata dana cikin dake jikinta nasan kasan inda yake duk duniya bashi da wacce ta fini wallahi"

"Hajiya Hadiza kenan ashe kin san ya sauke hakkinki na uwa ke kuma ba ki san ki sauke nasa ba ko? Ko a naki tauhidin babu haka halan? Ke da kan ki kika saka ya saki matarsa dukda kin fi kowa sanin irin son da yake mata, kika zana masa kashaidin zama da wacce kike ganin ta dace da shi, while ya miki abinda kike so shi ma soyayya ta saka ya yi abinda yake ganin daidai ne 50/50. Bari ki ji duk abinda ya faru ki kuka da kanki babu wanda ya ja miki sai ke, kin ɗauki son zuciya ki sawa ranki ki kasa yadda da ƙaddarar Ubangiji ki kasa tunanin dukkan abinda ya faru muƙaddari ne daga Indallahi, wallahi tallahi sai Allah ya tambaye ki hakƙin Muhammad domin raya kiwo ne a gare mu"

Cikin fusata ta ce "Na gaji Alhaji Tahir na gaji ni duk ba kaga irin baƙin cikin dana haɗiya ba? Wacce uwa ce zata zuba idanu ɗanta yana wahala akan abinda nake tunanin yafi ƙarfinsa? Ka duba ƙaunar daya nuna mata ya sadaukar da farincikinsa samartakarsa just because of her? Who is she in the whole world? Ƙiri-ƙiri ta kalli tsabar idanunsa ta ce masa Allah ya isa ta tsane shi saboda mijinta Zameer ta kalli idanunsa ta kira shi da sunan da ko ni shaƙar faɗa masa nake, tun tana zanin goyo yake ɗawainiyya da ita komai ya samu ita, sai yanzu da komai ya ƙare mata zata dawo wajansa don taka bashi da zuciya a kanta, to wallahi tallahi ba a haifi wacce zata wulaƙanta mini yaro ɗaya tal a duniya ba, kuma ina kan bakata bana son Ridayya bana ƙaunarta gwara da Allah ya raba su balle baƙin cikinta ya kar ni"

"Idan baƙin cikinta bai kashe ki ba, rabo zai kashe ki"

"Me kake nufi what do you mean by that eh?"

Ya miƙe tsaye ya ce "Kin ji ai, ki raba kanki da rabo ki ji tsoron rabo tun wuri ki amshi ƙaddara, daga ƙarshe ƙofar da kika saka a ɗakin babban mutum sam bai bata dace da ɗakin ba" Ta yi ƙwafa ta fice little ya shigo kenan ta saka hannu ta kwaɗe keyarsa ya juya da gudu yana kuka tare da yarda da chocolate ɗin hannunsa.

"Mimi mimi mimi" little ke faɗa a gigice yana fasa ihu sosai dukan ya shige shi daman ita da Mardiyya da Ammi ke zane shi idan ba idanun mutane har ya gane ya daina zuwa wajan su. Zainura ta matsa da sauri bayan ta gama ciwa Burhan mutunci ta ce "Sweetie kai da waye" Hanyar part ɗin Umma ya nuna mata ta gane sarai ta murguɗa baki a zuciya ta ce "Allah ya isa wallahi" Ta rarrashe shi da ƙyar ta juya kan Burhan dake cewa. "Ki dube ni na sauya sosai Zinu ba da niyyar soyayya na zo wajanki ba, amma na ji ina son ki wallahi auren ki zan yi"

"Kanbu! Ka raina mini wayo raguwar wiwi zan aura kenan? Allah ya suttura mini Zainura ta fi ƙarfin ka ta ko wacce siga"

Ya juya kai ya ce "Zan sauya yadda kike so Zinuna kuma ma ai na fara daina shan komai kuma ina sallah 5/daily"
Chapter 102 · 0% Book details