← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 118

Sashe 88

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Azizat ta haɗiye yawo mai yauƙi daya tsaya mata can ciki ta ce "Matar me wayar ce, You can give the phone owner his phone?"

"Baya kusa yana kan......,"

"Hiiii stop this nonsense, mijina nake nema bake ba, and lemme warn you first; idan na sake kira kika É—aga mini waya I'll show you the other side of me, har ina ki bani mijina kina tsayawa yi mini rubbish? Who are you? How dare you eh?"

Faɗa sosai Hajiya Azizat ke yi daman mai haƙuri bai iya nuna ɓacin rai ba, ƙitt ta ji an kashe wayar. Tunani ya shiga kanta who is she? Mene haɗin ta da Professor? Har take ɗaukan wayarsa kai tsaye wacce ko ita bata da damar hakan?.

Ta miƙe tsaye ta fara kai kawo can wayarta ya fara ringing line ɗinsa ta gani ta ɗauki wayar tun kafin ta yi magana ta ji ya sauke ajjiyar zuciya mai nauyin gaske ya ce.

"Sorry wife wallahi wata....," Hajiya Azizat ta katse shi ta cewa "It's okay. I trust you ban taɓa saka zargi a aurenmu ba tsayin shekaru"

"But wife at least ki tsaya na miki explanation who is she to me?"

"Sweetheart bana buƙata ko wace na san bata da wani important a wajanka, kuma duk lalacewar abu matarka ai matarka ce" Ya sauke numfashi ta wayar ya ce "Haka ne that's why i always Madam, ya akai?"

"Ni da ɗanka Sadauki muna buƙatarka don Allah don Annabi don darajar iyayenka ka bamu lokacinka professor, muna da damuwa muna da matsala muna tsananin buƙatarka kusa damu amma kodayaushe kana nisanta kan ka damu why? Aiki ya fi mu ne? Sadauki na cikin matsala Prof na kasa jurewa kullum baya bacci yana jiran zuwanka amma kodayaushe baka dawowa kai ne meeting kai me secretary ya kira ka, kai ne Md ya nemanka ga shi ka cusa kanka a siyasa, ya kake so mu yi da ranmu? Bamu da abokin hira kai ba barina fita kake ba ko wajan ƴar'uwata da muke gari ɗaya you didn't allowed me to go? We need you dear..... Bama buƙatar kuɗi ko wani abu kai kawai muke so kusa damu ka yi mana wannan alfamar"

Ya yi shiru ya kasa magana, yana tsananin kishin matarsa da masifar son ta, yana jin tsoro ta fita wani ya ganta gani yake tamkar zata aikata abinda yake yi itama. Shi kansa bashi da wani dalili na tarayya da wasu matan, matarsa bata rage shi da komai ba ya ɗauki hakan matsayin babin ƙaddararsa, tsananin kunyar ta ya saka Prof kasa magana ta ce

"Can you? Za ka iya?"

A hankali ya ce "Ina kan hanya zan zo yanzu"

Kashe wayar ta yi, lokaci zuwa lokaci sai ta duba agogo ga Sadauki ya daina fita wajan aiki walwalarsa ta ragu baya magana duk barkwancinsa ya kaÉ—aita da kowa, tun yamma har aka yi magariba babu Prof. Number Tajj ta kira ta ce tana son ganinsa ya taho mata da Æ´ar wajansa yana dariya ya ce "to shikenan Anty, amma zuwa gobe"

"Ba damuwa, za mu yi ko chat ne Allah ya tsare ya taimaka" Ya amsa da

"Amin"

Har ƙarfe 2 na dare Prof bai dawo ba, ta sake nufar upstairs zuwa part ɗin Sadauki ta same shi a rufe wayarsa a kashe ta rasa yadda za ta yi tana sake kirab number Prof ta ji a kashe kawai ta durƙushe a wajan tare da fashewa da raunataccen kuka.

Professor bayan kammala wayarsa ya juya ya kalli Talatu ƙarin kunama ya ce "Sau nawa zan ce miki kar ki kuskura ki ɗauki wayata?"

"Au haba? Nima na yi maka warning idan ina tare da mutum bana buƙatar ya kula ko wacce mace" Ya ware idanu ya ce "Even my wife?"

"Ko ma wacece ai kasan da matar taka kake kula karuwa" da shock ya ce "Da kan ki kike kiran kan ki da karuwa?" Ta wani waskace ƙugu tana kaɗawa ta ce "Ba ka ji take na bane? Talatu ƙarin kunama? Ai guba ce ni idan na kafawa mutum ƙarina dole ya lalace ka bi a hankali kar ka ja na yi maka asarar kujerar ɗan majalisa ɗin da kake nema, kuma ba naga kana ruwan jiki ba muna tare dakai gabaɗaya weekend ɗin nan, da kake cewa ina kiran kai na karuwa ai ɗan'iska baya tsoran a kira shi da ɗan'iska mufa wannan harkar shi ne kasuwancinmu kune kuke ɓoye kan ku, but ni a yi shela a kira ni da Talatu karuwa ko a yatsana"

Nan da nan ta sauyawa Prof lissafi ya mance da batun Hajiya Azizat da ɗansa ɗaya tal a duniya daya kasa bashi lokacinsa har dare suna tare ƙarfe uku ya shige Dubai wajan Anita uwar shegu sai da gari ya waye ya haɗa haɗaɗɗan messages na ban haƙuri da kalamai masu sanyaya zuciya zuwa ga Hajiya Azizat cikin sa'a wayar hannunta ta gani sai ta ji tausayin mijin nata, komai ya ke yi saboda su ne yana yi don kyautata gobensu. A taƙaice ta masa reply da;

“Take care”

JAPAN....
A hankali ta juya tana sake shigewa cikin lallausan duvet ɗin saboda wani sanyi da yake ratsa mata jiki, kwanan su uku a ƙasar Japan ɗin amma ta kasa sabawa da weather ɗinsu kullum ƙasar cikin ruwan sama suke da zubar dusar ƙanƙara. Bata son ruwan sama hakan yasa kullum tana cikin bedroom dukda cewa gidan ko alamun saukar ruwan saman ba za ka ji ba, sai dai ka gani ta window, jin shigar sanyin ya tsananta gargasar jikinta na zubewa tana mimmiƙewa ya saka ta yaye duvet ɗin tare da yin miƙa bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, dim light ne hakan yasa ba sosai take gani ba, ta sakko da ƙafarta duba kayan baccin jikinta ta yi sai kuma ta yi baya tana lumshe idanunta da ƙanƙame jikinta a hankali ta ware laɓɓanta ta ce

"Uhm Abbiey"

Idan ta tuna kokawar da suka sha wajan sauya mata kayan har ta cije shi a wuya abin dariya yake bata, musamman yadda tana sane ta dinga bashi wahala. Wani flip flops slipper ta saka a hankali ta nufi parlour wanda ta ji ya ɗauki ɗumi tun daga nesa ta hango fararen ƙafafuwansa ya lanƙwasa su a saman glasses table zoom meeting yake don haka bai ji motsin fitowarta ba, Ridayya kuma haɗe rai ta yi ganin still jallabiyya ce ya kuma sakawa ita ta rasa dalilinsa na saka wata jallabiyya.

MB USTAZ idanunsa da suke lumshe ya buÉ—e yana sauraren mai maganar da yake cewa. "Kafin tsayawa takara dole ne ka ajjiye aikinka, domin ana da wata uku tsaida É—an takara ake ajjiye aiki, kuma har yanzu baka amsa cewar ka amsa ba ko aka sin haka"

Ustaz ya jinjina kai da gaske magana yake son yi da kuma bayani amma laɓɓansa sun yi nauyi ya rasa ta ina zai fara sai juya idanunsa yake yana datse leɓe ga gashin goshinsa dake reto a gaba.

"Sir please ko dan al'umma ka ceci wannan jiha ta mu daga hannun Æ´an kama karya, domin ana mana kashin dankali ne, wahalar fetur, babu nepa, babu abinci, securities, abubuwa da yawa muna da tabbaci a kan ka ne"

"Allah subhanahu wata'ala shi ke da ikon ceto Jiharmu ba Ustaz ba, Allah ya yafe maka da kalamanka. Ba zan iya mulki ba, shugabanci yana bani tsoro ban san me zan cewa Ubangijina ba, ko shugabancin cikin gidana sai an tambaye ni balle na dubban al'umma ka yi....,"

Wanda suke meeting É—in da shi kai tsaye ne Ustaz yaga ya yi shiru ya kuma zubawa bayan Ustaz idanu, cikin sauri Ustaz ya rufe idanunsa sai yanzu ne ya ji bugun zuciyarsa ya sauya cikin sauri ya katse meeting É—in yana rufe laptop É—in.

Wani irin nauyi ƙirjinsa ya yi masa, ya ji wani abu mai tudu ya tukare masa ya dunƙule hannunsa waje guda waje guda karan hancinsa ya yi jajur. Bai juya ba sai a hankali ya yi baya tare da ɗaukan ruwa ya shanye tas. Ridayya kuma a hankali ta fara tafiya zata shige ɗaya part ɗin domin tunaninta bai ganta ba, shi ma ɗin ya rabo da ita ne yaga ƙarshenta ta yi sauri ta shige ya girgiza kai kawai, ya rasa dalilin wannan kunyar da ba haka take masa ba, tunda aka ce shi ne mijinta kuma ta yi accepted shikenan take jin kunyarsa addu'a ɗaya yake Ubangiji ya sa ba kallon uba take masa ba.

After 15 minutes ta fito sanye da riga body short da wani wando mai kauri iya qwiwa ta ɗora hula a kanta zanen ƙunshinta raɗau da shi, ta yi fresh baƙar fatarta ta sake fidda asalin kalarta wani irin baƙi ne mai masifar kyau. Ta ƙarasa wajansa ta zauna dab da ƙafafuwansa ta zubawa yatsun ƙafarsa idanu a hankali kuma tana danne nauyin kunyarta ta ɗaga kai suka haɗa Idanu ta yi saurin ɗauke nata ashe ita yake kallo ta miƙa hannunta na dama ta ce.

"Good morning Abbiey?"

Jin bai saka hannunsa sun yi musabaha kamar yadda suka saba ba ya saka ta turo baki tana shagwaɓe fuska ta ce.

"To ni me na yi maka ne? Ka yi haƙuri don Allah Abbiey"

Ya yi shiru ta juya gabaɗaya ta ga waya yake dannawa tunaninta ya bada ƙila Mardiyya ce suke chatting. _“Lovely, and sweetness”_

Da sauri ta miƙe tsaye tana fashewa da kuka, ya bi bayanta lallausan murmushi ya saki yana miƙewa tsaye tare da bin bayanta ya same ta sai sharɓar kuka take tana tsaye gaban madubi, gently ya ƙarasa inda take ya tsaya zata gudu ya yi saurin riƙo ƙugunta da tafin hannayensa ya jawota tare da haɗe bayanta da ƙirjinsa ya riƙe ta a jikinsa tare da rungumota tsam a ƙirjinsa, murya can ƙasa yana goga mata sajensa da hancinsa ya ce

"Allah ya yafe miki Ustaza, wake fushi da miji?"

"Uhm a'a um'um ni"

"Kuma haka ake gaisuwa? Kina neman rabauta a ƙarƙashina?"

"To ba kai ne ba" ya juyo da ita, tare da zuba mata idanu ya dinga kallon ta sai kawai ya É—aga ta ya É—ora saman madubin ya shiga dudduba mayukan wajan ta ce

"Me kake nema?"
Chapter 88 · 0% Book details