Sashe 32
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kamar kullum yau ma Ustaz da kansa ya yi wa Ridayya wanka bayan ya naɗe ta da towel ya shirya ta cif cikin wasu sabbin kaya ƴan kanti daya siya mata, ya ɗaure tulin sumar da ribbon yana hakki, yana gamawa ya yi baya tare da kwanciya ta haye ruwan cikinsa tana dariya ta ce "Abbiye gajiya" Idanunsa rufe domin yanzu Ridayya ta zama ƴar lukuta saboda kulawar da yake bata. Ya yi murmushi ta ƙura masa ido, ganin kumatunsa ya loɓa _Beauty points_ ta danna yatsa a wajan ya ce "Shhhh, Shalale mu je ki yi bacci ko?" Ta maƙale kafaɗa ya rufe ido tana zaune bacci ya ɗauke shi da sauri ta fice ta nufi part ɗin iyayenta.
Lokacin data shiga ba kowa a parlour sai Mami wacce cikinta ya girma kawo yanzu kuma kowa ya san da zamansa hatta shi mai gayya da aiki Alhji Mansur Rano. Jin motsi ya saka Mami juyawa idanunta ya sauka akan Ridayya itama Mamin ta ke kallo. "Lafiya ke kuma?" Ridayya ta girgiza kai sai kuma ta juya zata fita aka ce "Daughter come back" Ammi ta faÉ—a cike da fara'a da sauri Ridayya ta juya tana murmushi don yanzu ta daina jin tsoran Ammi tunda ta fara nuna mata kulawa da soyayya.
"Yawwa Æ´ar baba mai iyaye maza biyu ta gaban goshin Abbiey É—inta Muhammad-Bilal Ustaz" Ridayya ta yi murmushi ta ce "Zauna na baki abin daÉ—i daughter na"
Mami dai ko motsi ba ta yi ba, Kwata-kwata bata damu da Ridayya ɗin ba, bata taɓa ɗaukar ta ba, tunda take a duniya bata taɓa hira da ita ba ki na seconds ba, sai magana sama-sama. Farfesun nama ta zubo mata hakan ya yi wa Ridayya daɗi tana son nama kuma gashi yanzu Ustaz ya saba mata kullum sai ya siya mata balango ko tsire ko kaza.
Ta cinye tas kana Ammi ta ce "To zo mu je na baki É—aya abin daÉ—in"
Hannunta ta kama suka nufi cikin bedroom ɗinta, a zuciyarta tana tsinewa Ridayya tana kuma jin daɗin yadda Mami ke nuna rashin kulawa a kan Ridayya ɗin. Maganin mayen da take bata a kullum, yanzu ma shi ta ɗauka. "Yawwa ungu wannan shanye tas kin ji ko?" Ridayya ta jinjina kai kana ta amsa ta shanye tas kusan cikin kwalba ɗin, kama hannunta ta yi ta ce "Kinga yadda nake son ki ko? Ko me kika ce ina miki haka ne? To Mami da kike gani ba ƙaunar ki take ba, cillar dake ta yi ta ce bata son ki ni kuma na ɗauke ki, ki daina ko gaishe ta kina ji?" Ridayya ta jinjina kai ta ce "Ai shi ne take mini haka...,"
Ta yi maganar tana yin harara da taɓe baki ta ce "Yaya sunan wannan abin Ammi?"Ammi ta ce "Yana nufin na tsane ki, kuma sai na kashe ki"
"Ta kashe ni na bar ganin Abbiey?" Ammi ta ɓata fuska ta ce "Abbiey kawai bani?" Ta yi shiru kan ta a ƙasa can ta ce "Ni ma na tsane ta, zan ɗauki wuƙa na caka mata"
BATSARI /KATSINA.
Yanayin duhun samaniyya da yadda daddaɗar iska ke kaɗawa, gari ya yi shiru sai kukan tsuntsaye da tashin ledoji zuwa sama zai tabbatar maka a tsakiyar watan Agusta ake. Yau ruwa gobe ruwa, hakan ya yi dab da shigowar watan azumin Ramadan. Yau ma kamar kullum garin ya yi baƙiƙƙirin gajimare sai gudu yake, ana wata kalar walƙiyya da iska mai ƙarfi dake tashi tana yaye gutsirarrun rufin saman wani gidan mai ƙarar kwana. Hankulan jama'ar ƙauyen Nahuta dake yankin ƙaramar hukumar Batsari, ya fara tashi ganin hadarin yau na musamman ne, wanda suke gonaki suka fara shirin dawowa gida, wanda suka fita bara suka fara tattaro tarkacansu suna ɗaukar hanyar gida, matan da suka fita garuwa suma duk suka yo hanyar gida, aka dinga kama awakai da shanu ana ɗaure su.
Kamar yadda Hausawa ke yin lakabi da sunan “Katsinawan Dikko, kunya gare ku ba dai tsoro ba†Gefe guda kuma wasu su ce “Ta Dikko ɗakin kara" Hakan ɗin ce ta kasance a cikin wani fafakeken gida, wanda zubi da tsarin shi bashi da mara da gidan gandu. Gida ne mai rangwamen ƙarfi, ga tarin yara manya da ƙanana kasancewar mata huɗu ne a gidan, idan ka ɗauke surukansu da duk suke tare waje guda. A daidai sanda ruwan saman ya fara sauka a sannan ne ya fito daga ɗan ƙaramin ɗakin da take ciki mai kama da Bukkar Fulani mita take kamar ta ari baki
"Ni wannan masifa da bala'in na cikin gidan nan ya ishe ni, masifa kamar ana tuttula mata man fetir, hoɗijam!" Ta faɗa tana yin turken awakai tare da kama gudu wacce ta kifo mata da ƙazon data shanya,sai ta yi wa akuyar dokan kawo wuƙa kana ta ɗaure. Ta kalli sama ganin yadda cita ke ta gudu ta ce
"Ko a ina Gaaji ta samu gindin zama?" Kafin ta shige ɗaki yariyar ta shigo da gudu tana haki saboda ruwan daya fara dukan ta. Kallon tsaf ta yi mata kafin ta ce "Hala kin kwana turo? Hakin ga na lafiya?" Gaaji ta ce "Iya don ki ji Gidaɗo ya zo, ya dawo daga birni" A guje sauran yaran suka fito daga ɗaki suna murna yau za su ci abu mai daɗi da kyau. Iya ta ce "Ke ƙarya, Gidaɗo nawa? Yaushe ya zo babu labari"
"Yana bisa hanya" Rufe bakin Gaaji kenan ya faɗo gidan yana cin magani sai taɓe baki yake yana kakkabe jikinsa. Jikin Gaaji na rawa ta ce "Ina taimaka maka kawo jakar tafiyar" Tana zuwa ya saka hannu ya sakar mata ranƙwashi ya ce "Kina ƙara taɓa mini kaya sai na ci ubanki, ƴar ƙauyen banza" Da sauri ta matsa tana sosa kan ta. Iya ta ce "Sannu lale me ka zo mana da shi? Kawo jakar naga?" Ya haɗe fuska tamau ya ce "Ke Iya nan kamar kin bani ajjiya, wai karatu na je yi ne ko neman kuɗi?" Ta riƙe baki
"Kake faɗa mini haka Gidaɗo?" Ya ce "Gaskiya ce ai, ba ki ce Gidaɗo ya karatu ba sai me na zo da shi, ko tunanin na mutu a can bakwa yi kun kai ni gari kun zube babu mai zuwa, sai ni nima daga sallah sai sallah ko idan na yi wata ƙaryar"
"To zage ni ka huta Gidaɗo, ni dai bani burodi" Ya ƙara yin kicin-kicin da rai ya ce "Point of correction, biredi ake cewa Iya"
"Bari na je na faÉ—awa Hanne ka zo" Iya ta ce "Maza ki faÉ—a mata, a zo a yi maganar aurenku" GidaÉ—o ya kalli Gaaji ya ce "Wallahi kika fita kika gaya mata sai na yi miki shegen duka Æ´ar banza da baki kamar na aku" Haka daga shigowarsa suka fara yi da baki daman babu kowa namiji a gidan sai Jafar shekarar shi Bakwai shirin kai shi Maiduguri ake wajan sauran yayyensu da suke can.
"Ka je gona, lokacin girbi ya kusa za mu samu albakar noma na hatsi sosai" Gidaɗo ya miƙe ya ce "Ku za ku iya cin hantsi ni na yi hannun riga da shi, noma kuma a yanzu gaskiya Iya sai dai ku yi haƙuri na fi ƙarfinta" Kafin Iya ta yi magana an tsuge da ruwan saman, da gudu Gaaji ta fice daga cikin gidan ta nufi gidan su Hanne ta shaida mata Gidaɗo ya dawo.