← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 118

Sashe 48

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina ji" Ustaz ya faɗa yana ɗora ƙafarsa ɗaya saman table ɗin dake gabansa, can kuma ya miƙe ya nufi duguwar kujera ya kishin giɗa a kai. Baita ma ya tashi ya dawo kusa Ustaz, takaici ya saka Ustaz kasa magana domin ba zai iya da neman maganar Baita ɗin ba.

"Ina cases É—in da nake maka magana akai? Mun kusa yin nasara domin mun samu an yi tracking number É—aya daga cikin yaran" Ustaz ya jinjina kai sosai yake jin maganar amma idan aka kalle shi zaka É—auka bai ma san abinda Tajj Baita ke faÉ—a ba. "Na je Kano na yi kwana biyu gida a hanyata ta dawowa Legas na haÉ—u da wata"

"Maman Nadra za ka yi wa kishiya kenan?" Baita ya haÉ—e fuska ya ce

"Ka taɓa ganin an yi wa wanda baya raye kishiya?" Ustaz ya ɗaga kafaɗa tare da juyawa baya Baita ya ce

"Tana buƙatar taimako na tsaya, ka sanni bana ƙaunar ganin mace cikin wani hali ina da tausayi sosai a kan mace wallahi tunda na ganta na ji ina son taimakonta, zafa ka ɗauka tsohuwa ce irin sosai ɗin nan amma wallahi yarinya ce kasan ina da fahimtar abu ba a banza na shiga police ba, ina son taimaka mata"

"Ka yi mana"

"Ban san ina take ba, taƙi saurarata sam wallahi"

Tsaki Ustaz ya ja yana miƙewa tsaye a hankali ya ce "Yanzu ka zo ka faɗa mini naje na nemo maka ita ne? Tajj ka ɗan saurara mini ba ruwana da ita taimako ko ni zan iya taimakawa amma ka daina mini maganar ko wacce mace"

Baita ya riƙe baki ya ce "Wonderful! Ai wallahi sai na saka an yi maka aure da zarar ka san mece soyayya zaka riƙe mace hannu bibbiyu"

"Uhm soyayya, kune baƙin ta, daɗi da zafinta ba wanda ban sani ba" Ustaz na faɗin hakan ya fice daga office ɗin da sauri Baita ya bi bayansa yana cewa "Wait, tell me something about your first love kasa ka a kai wa ka taɓa so? Ka zama ragu a soyayya kenan?" Ustaz bai kula shi ba ya yi waje abinsa.

Tunda ta sulale ta suma a wajan bata san mene ya sake faruwa ba, bata san adadin data ɗauka ba a hakan balle kwanaki sautin muryar data tsana a rayuwarta fiye da komai ita ta firgitar da ita ta buɗe ido da ƙyar tana dafe kanta idanunta sun yi mata nauyi saboda kumburi da jimawa da ta yi da rufe su.
"Tashi mun ƙara su" Ya faɗa yana yin wani irin murmushi ganin hakan shi ne kawai damar data rage masa. Kafin ta sake buɗe idanunta ta ji ana faɗin

"Giɗaɗon ya zo Giɗaɗo ya zo, yee mijin Hanne ya dawo sannu da zuwa Giɗaɗo" Yaran da suka baibaiye motar suka shiga faɗa tsakar kuma basu taɓa ganin mota ba haka suke shafa ta ana leƙuwa tare da kallon Ridayya. "Waye kuma Giɗaɗo?" Ta tambaya a zuciyarta

"Ki fito" Ta ce
"Ina ne nan ɗin?" Kai tsaye ya ce "Katsina. Ƙauyen Nahutu dake yankin Batsari"

"Me za mu yi a Katsina mene ya kawo mu ƙauye"

"Saboda nan ne mahaifata cibiyata kuma daga yau zai zama garin mijinki" Ridayya ta girgiza kai bayan ta fito daga motar ta ce

"Wallahi ƙarya kake ba zan taɓa zama a nan ba ina gidan Alhji Mahboon Dollar ɗin?" Sai kuma ta miƙe da sauri da sauri ta ce "Munafiki macuci azzalumi wanda baya tsoran Allah bambancinka da shaiɗan kaɗan ne"

A gigice Zameer ke kallonta koda wasa aka ce masa Ridayya zata ɗaga masa murya ba zai taɓa yarda ba, yau Ridayya shi take kallon cikin idanunsa babu tsoro balle shakka bata tunanin gargaɗinsa. Wani abu mai kama da faɗuwar gaba ya gitta masa ganin komai na yayewa a idanun Ridayya Mai son shi, babu son, babu tsoron, babu biyyar babu tattali da wannan tausayin nata zuwa gare shi lokacin na farko wani abu mai kama da fargaba ya matse zuciyarsa kar dai ta daina son shi? Ya girgiza kai da sauri a fili ya ce "Never!"

"Ridayya ni kike jefa da wannan maganganun?"

"Na faɗa waye kai banda MUNAFUKIN MIJI? Ka aure ni a caca ka ce kana so na saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, ka kwashe kayan ɗakina ka siyar ka ce kasuwanci za ka yi saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, ka ce a kano kake sai gamu a Katsina saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, mene laifina da zaka munafurci ni har haka? Laifi na kawai don na nuna maka soyayya? Ashe haramci ne nuna kana son mutum ka wulaƙanta ni ka wulaƙanta rayuwata ka gaggauta mayar dani Kano, wallahi ko zan kwana bola ban zama tare da kai"

"Idan kina da kuÉ—in mota ki koma tunda ai na san kin san hanya" Ya faÉ—a a dage amma zuciyarsa wani kalar tsinkewa take kar dai Ridayya ta sauya

"Gidaɗo ka zo ashe? Meke faruwa nan ne ake ta ɗaga haƙarƙari?"

"Gidaɗo? Wani munafurcin sunanka Giɗaɗo?" Ridayya ta ji gabaɗaya ta sare da al'amarin maza kuma da tsani ko wanne namiji gani take zai zama kamar Zameer ya kasance MUNAFUKIN MIJI. Da ƙyar aka rarrashe ta tana kuka sosai ganin kuma yadda yaran ƙauyen suka baibaiye ta kamar za su cinye harda masu leƙowa ta katanga babu ɗaurin ƙirji. Ta yi kuka mai isarta taƙi fitowa daga ɗaki komai aka bata bata ci bacci ya gagari idanunta ga wani irin ciwon kai kamar kanta zai rabe gida biyu da gaske bata da kowa bata da sauran gata ita fa dole Zameer Giɗaɗo ya saketa.

Cikin dare tana kwance ba bacci take ba sai juya kanta dake bala'in ciwo yake kuma ta dinga ganin Abbiey yana mata gizau yana kuka sosai sai taga wani ya zo ya janye shi.

Kamar daga sama ta ganshi ta yi masa banza ya ce "Hakƙina za ki bani na kasa jurewa na fahimci ke kaɗai nake samun nutsuwa a tare dake" Ridayya ta cije bakinta ta ce "To Bismillah" Ya yi watsi da suttura shi kamar dabba haka ya faɗo idan take ta yi saurin ta shi ya ce
"Ya haka ina jin kamar zan mutu" Ridayya ta waiga can ta hango fatanya ta ɗauka ta zage iya ƙarfinta ta maka masa akan abar........

Share and share and share as you can! Giɗaɗon Batsari da alama za mu je Nahutu jinya🤣🤣🤣

Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08119237616
*✿ MUNAFUKIN MIJI 24 ✿*
Mikiya Writers Ass....

BRIGHT PENS🤙🏼free batch
Nimcyluv

Mirgina wa ya yi gefe jikinsa na rawa yana ƙoƙarin kurma ihu ya ce "Akan hakƙina za ki nakasa ni? Ki cuce ni ki cuci kan ki?"

Gabaɗaya muryar Zameer rawa take ganin yadda har yanzu take riƙe da fatanyar idanunta sun yi jajur jikinta na wani irin ɓari kamar mai shirin tayar da aljanu. Ya dake ya ce

"Ki bi a hankali, ni mijinki ne kuma zan ci gaba amsa sunan hakan har gaban abada, idan kina tunanin wani abu saɓanin nawa kin yi kuskure"

Ridayya da ƙyar take riƙe kanta, ji take kamar za a wurgar da ita ne, duk da gabanta dake faɗuwa da kuma girman igiyar auren dake kanta bai hana ta nutsa idanunta cikin nasa ba ta ce

"GiÉ—aÉ—o"

"Giɗaɗo kuma? Ina kika ji sunan nan? Mene haɗina da Giɗaɗo?" Har lokacin yana damƙe da jikinsa da Ridayya bata samu damar idda nufinta akan shi ba sai gefen ƙafarsa data makawa.

Jikinta duka rawa yake gani take tamkar babban zunufi zata aikata faɗawa miji magana, mijin da a yanzu komai da take ji game da shi yake yayewa. Da ƙyar tana riƙe jikinta ta ce

"Giɗaɗo ba shi ne sunanka ba? Giɗaɗon ƙauyen nahutun batsari ko?" Ta girgiza kai ta ce

"Daga Almajiranci ka dawo Zameer?" Ta zube a kan ƙafafuwanta zuriyarta na yi mata wani irin zafi da tafasa ta haɗe hannayenta biyu ta ce

"Yau ɗaya ka faɗa mini laifina a gareka don Allah, soyayyar dana nuna maka? Zaɓarka da na yi na watsar Abbieyna? Ko fara furta maka kalmar Ina son ka? Ko kuma budurcina daka amsa kafin aure shi ne laifina? Ko kayan ɗakina daka kwashe ka siyar shi ne nawa laifin? Ciyar da kai da nake yi kullum, ko kuma fifitaka a kan iyayena shi ne laifina? Ka faɗa mini laifina dana cancanci irin wannan cin mutumcin wulaƙanci da ƙasƙanci a gidanka, me na aikata har haka daya dace ka zame mini MUNAFIKIN MIJI? ka faɗa mini mana"

Miƙewa ya yi ta yi saurin miƙewa dukda rashin ƙarfin jikinta ga ciki. Zameer bai bari kalaman Ridayya sun yi tasiri a zuciyarsa ba ya yi murmushi ya ce

"Wane ya faÉ—a miki haka? Wanne munafukin ne har haka Ridha tsakanina dake za a shiga?" Kallonsa kawai take da juyayyun idanunta ba tare da ta ce komai ba.

"Ridayya kar ki bari zuciyarki ta yaudare ki, ba ki da wani waje da yafi wajena, ba ki da wanda ya fini a yanzu dole ki yi mini biyayya domin Batsari kike ba Kano ba"

Ya nufi inda take domin baya jin zai iya rabuwa da ita, abubuwan da yake ji game da ita ƙara fusgarsa suke, a gare ta ɗinne kawai yake jin haka dukda wani irin tsoro da yake shirin ruskar shi a yanzu. Ya gyara tsaiwa ya ce

"Ni tamkar ƙadangaren bakin tulo ne, a gare ni a ɓata ruwa, a bar ni a ɓata ruwa, ni ɗin dai ya zame miki dole. Na tuna miki da babban murya iyayenki sun rasu baki da kowa a duniyar nan sai ni, kuma ki hanani abinda nake so ki gane Allah ɗaya ne"

Kallonsa kawai take duk yadda hawaye ke ƙoƙarin fita daga cikin idanunta ta kasa saboda kada ya gane a yanzu iyayenta sune rauninta da rashin gatan da take da shi. Hannu ya saka ya fusgota kamar yadda ya zama yi mata wanda hakan ya zama tamkar Sexual violence a gare ta ko shi mijinta ne idan ba da ra'ayinta bane to tamkar zalinci ne, CUTARWA ne.
Chapter 48 · 0% Book details