Sashe 51
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke Hanne wannan yaron fa? Ina kika same shi?" Domin shi zaton shi ko jaririn da Khairy ta kawo ne ya yi masa kallon tsoro da farko? Wancan baƙi ne yanayin halittarsa har ta ɓaci sosai ga shimfiɗeɗen baki ƙaton goshi kamar irin yaran ruwan nan wannan kuma zaka iya cewa haihuwar Larabawa ne irin usul ɗin nan.
"Matarka ta haife shi yanzu fa Giɗaɗo, kaga da mun yi aure da tuni ni ce na haifa maka wannan kyakkawan babyn" Mamaki ya kusa kashe Zameer sai ya dake ya kama Ridayya ta yi saurin ƙwace hannunta da ƙyar ta buɗe baki ta ce
"Karka taɓa ni, Hanne kar ki kuskure ki bashi ɗa na don girman Allah"
Zameer ya ja tsaki sosai bai tsaya jiran me zata ƙara cewa ba ya sunkuce ta ya yi waje da ita zuwa can shargalan asibitin da suke da shi a gefen ƙauyen Batsari. Hanne ta rungume jaririn a ƙirjinta tana jin ƙaunar yaron na ratsa ta, dukda ta san zafin ciwo ya saka Ridayya cewa ta bar mata shi amma da gaske take ji inama ta bata shi? Amma ya za a yi mummuna kuma baƙar mace ta haifi wannan yaron?
"Ikon Allah" Hanne ta furta a fili. Ta juya ta kalli yaron da aka yasar a ƙasa yana ta tsala ihu da alama shima bai jima da zuwa duniya ba, ta juya ta kalli Iyatu ta ce
"Haba Iyatu kun bar yaro yana kuka a ƙasa? Akwai karara a gidan nan fa" a harzuƙe Iyatu ta ce
"Me ɗin zan taɓa? Wannan halittar Allah ya sauwaƙe, uwar Giɗaɗo ma bata taɓa shi ba sai ni da nake kishiyar uwarsa? Ai idan kin ganni a lahira wallahi kai ni a kai, gidan da kowa gashin kansa ya ke ji ya je can ya gama ta zubar ɗinsa a kawo shege ki ce na taɓa? Zunubin zan taɓa Hanne kema da zan ba ki shawara da kin haƙura haka nan kin yi auren ki, domin Giɗaɗo ba irin arziƙi bane tun yana ɗanƙaramin shi yake ƙoƙarin hakkewa yaran ƙauyen nan da gayya Malam ya kai shi bara ba? Ashe iskanci kawai yake zubawa a can birnin Kanon"
Wuff iya mahaifiyar Giɗaɗo ta fito daga ƴar bukka tana riƙe zani dake neman kuncewa ta ce "Baƙin ciki kike da ɗaukakar Giɗaɗo ya je birni ya yi ilimi na boko ya nemo mace mai ƙashin arziƙi ai ya bani labarin komai nan da ɗan ƙaramin lokaci jirgina zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki" Sai kumfar baki take yi ita ɗaya.
Iyatu ta buga cinya tana ajjiye abin kaɗin adudiga tare da yin shewa da tafi ta ce "Anzo wajan daidai wajan ma, ai ba girinrin ma ta yi ma, idan kuma kaga baƙin maciji ko baƙar leda ka gani ka shafawa hanyarka lafiya,ina ƙoda ina romansa?...," Wata shewa Iyatu ta sake yi tana juya ɗuwawu ta ce
"Riiiiiiii arziƙi kashi idan irin wannan arziƙin dana gani yau an kawo muku shi ne arziƙi to umma ta gaida assha, wai shi ɗan gidan mai dallla ne ko me?" Kafin ka ce me tuni sun hargitsa ɗan gidan nasu Hanne ta lallaɓa ta gudu da jaririn Ridayya zuwa gidansu domin ba zata iya da wannan azabar tasu ba, ko kunyarta sam basa ji.
Da ƙyar jinin ya tsaya aka ce za a ƙara mata wani dukda bata cikin hayyacinta furr cewa ta yi bata buƙatar jinin Zameer a jikinta bisa dole Dr ɗin ya haƙura akai mata allura ya bada magani kasancewar asibitin komai na masu haihuwa kyauta ne a haka bacci ya ɗauke ta. Dr ɗin ya dinga kallon Ridayya ko mutuminta ke bashi mamaki ko tsofan da ta yi shi kaɗai yasan abinda yake masa yawo a zuciya. Kwanan ta biyu cikin asibitin aka sallame ta ko inuwar Zameer bata marmarin kallo balle fuskarsa, sai yanzu kuma yadda ta samu Zameer ɗin shi da Khairy matsayin turmi da taɓarya ya dawo cikin tunaninta kamar mai cutar mantau haka abin ya kwanta a ranta sai dai wani irin zafi da ciwo da zuciyarta ke yi mata.
Tana shiga gidan sukai karo da Shatu, Shatu ta faɗi ƙasa tana birgima da ihu a gigice Iyatu ta fito daga ɗakinta ganin Shatu a kwance ga Ridayya a tsaye a gefe ta fasa kuka ta ce
"Ta kama mini yarinya mayya ta riƙe mini kurwar Shatu"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Shi ne abinda Ridayya ta faɗa a zuciyarta shin wacce kalar rayuwa take ciki ne? Me ya sa al'umma da mijinta da ƴan'uwanta suka kasa yi mata uzuri ne me ya sa har yanzu bata ganin daidai ne? Yaushe za ta yi farin ciki kamar kowa yaushe za ta samu ƴan'cin kanta ne yaushe zata bar wannan rikitaccen ƙauyen dake neman kashe da ranta da nasu kalar ƙazafin.
Iyatu ta finciko Ridayya ta ce "Wallahi sai kin sakar mini kurwar ɗiyata shegiya mayya baƙar muguwa mai baƙar aniyya" Ridayya ta kasa kuka ta kasa cewa komai sai kallon Iyatu take tamkar zautacciyya ta saka hannu ta tsinka mata mari ta ce
"Dai na kallona makira danginki ma sun guje ki balle mu? Mayya kawai"
"Wallahi ni ba mayya ce"
"Ƙarya kike ai mu da baƙin mutum muke gane maye" Sai a lokacin Iya ta fito hannunta ɗauke da Harazimi dake ta wangale baki yana tsala ihu Ridayya ta kalli yaron ta ce
"To kenan bani kaÉ—ai bace mayya ga wani nan ma" Iya ta ce "Jikina ba maye bane, ki ne mi can maye kuma ki zo ki faÉ—i uban É—an da kika haifa ni nafi zaton ma mu can muna surutu kikai mata sauyin yaro ko aljanu sukai muku musaya"
Zameer dake tsaye ya jingina da jikin garo ya ce "I was thinking the same thing Iya, Ridayya baƙa ce kuma mai muni kamar dai ɗan hannunki, ni kuma fari ne kyakkawa haka ma Khairiyya fara ce tas haka iyayenta to tayaya za mu haifi wannan ɗan? No way ki bata wannan Harazimi yake ko waye? Ki amshi farin ɗan wajanta domin babu yadda za a yi ta haifi ɗa kyakkawa"
"Amma ban taɓa ganin zalunci irin wannan ba, a kan idanuna ta haihu na yanke cibiyar kar ku rabata da yaronta wallahi zan tuna muku asiri" Ta fashe da kukan tausayin Ridayya kamar jininta.
Zameer ya dakawa Hanne tsawa tare da ƙwace ɗan daga hannunta ya ce "Ki dai na yi mini shisshigi cikin iyalaina Hannatou"
"Su waye iyalan naka? Ni da nake matarka ko fasiƙar da kuka haifi ɗa babu aure kuma ta hanyar zina? Ko kuma ita data kasance tana son ka kuma budurwar daka yaudara waye iyalin naka daga cikinmu Giɗaɗo?"
"Ki daina ce mini Giɗaɗo ban so zan watsa miki tafi wallahi" Iya ta ce "Saurara ita kanti take ko kairi ai matarsa ce kamar yadda kike matarsa cewa ta yi dole sai an raba auren ba zata iya rayuwa a ƙauye ba shi ne yanzu data haihu ta kawo ɗan"
Ridayya ta kalli Zameer ya haÉ—e fuska ta kalli Iya ta ce "Ban yi mamaki ba tunda shi É—in Munafikin miji ne, amma wallahi ba matarsa bace"
Nan da nan Zameer ya sauya fuska ya ce "Sharri Ridha? Duk zafin kishin ne za ki haɗa ni da laifin aikata zina?" Ya zaro wayarsa ya shiga nunawa Iya pictures ɗinsu da Khairiyya wasu a kwance wasu suna rungume da juna wasu suna kiss abubuwa dai na ma'aurats ya ɗora da cewa "Wallahi matata ce sharri zata ƙulla mini"
Ridayya ta kasa magana Iya ta hau masifa tana cewa "Ke dai ba matar rufin asiri bace ki dinga aibata mijinki, ai ya faɗa miki komai da Allah da Annabi kika haɗa shi domin ya aureki kin rasa mijin aure to Allah yasa yana raye balle ki yi masa sharri, wannan tsinanen baƙin ɗan naki kowa ba lallai ya yi albarka ba kuma ba zan taɓa amsar shi matsayin jikina ba wallahi, gona ɗaya tal Malam yake da ita idan ya mutu ita Giɗaɗo zai mallaka ko Giɗaɗo ya mutu ki rubuta ki ajjiya bashi da gado, mai farar ƙafa"
Ta taga Iyatu ta leƙo ta ce "Tunda shi kaɗai Malam ya haifa dole ki ce gonar gantalallen ɗan ki zai mallake ta"
Faɗan ya koma tsakanin Iya da Iyatu Ridayya ta shige ɗaki wani abu ya tukare mata. Tun daga ranar bata da walwala damuwarta ta tsananta tsakaninta da ɗanta wanda har yanzu bata san sunan da aka saka masa ba sai kallo daga nesa ko kuma idan zata bashi nono, a ranta ta jima da bawa ɗan suna Muhammad-Bilal. Harazimi kowa yana ɗan girma muninsa na ƙara bayyana bisa dole take shayar da shi domin ba zata iya barinsa da yunwa ba. Watarana iya idan ta ɗauke shi sai ta daddoke mazaunansa ta tallaƙe masa ƙewa, tana ji za a dinga yi wa Little Bilal waƙa ana irin arziƙi irin albarka haihuwar farar mace ko da ka sha nonon baƙar mace sai ka ƙara fari gwanin ban sha'awa. Iye iye kamo mini shi nan. Irin wannan waƙen ya kan sanya Ridayya ɗan mursawa kaɗan. Har yanzu kuma tabon ƙonar da Zameer ya yi mata yana nan wani lokacin ya yi kamar zai tashi wani lokacin kuma ya addaba mata da ƙaiƙayi. Hanne ta ɗauki ragamar dafa mata zugala ta ci ta sha ruwan.
Tana zaune Zameer ya shigo hannunsa ɗauke da Little Bilal kamar ana ƙara masa girma sumar shi babu inda ta bar ta Ustaz yadda kasan Ustaz ne ya yi cikin ɗan ko kuma ya yi kaki ya tofar ba inda ya ɗauki kamar Ridayya sai ta Idanu, amma girma faɗi hanci baki dimple sumar kai da jerin yatsun hannu gabaɗaya irin na Abbiey ɗinta ne Muhammad-Bilal Tahir Rano. Ta ƙura wa yaron Idanu wanda yake ta kallonta gashi da ƙiriniyya hannunsa baya zama waje ɗaya duk sanda Zameer ya ɗauke shi ya dinga kuka kamar zai mutu.