← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 118

Sashe 93

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sharri Ustaza"

Ya furta a hankali kuma a nutse yana matsawa daidai kanta inda take kukan wiwi. Ya dinga kallonta can ya ce

"Ki gasa jikinki"

Ta tattare duka duvet ɗin a jikinta ta fara ƙoƙarin sauka ya riƙe ta marairaice ta ce "Uhm ta ba zan wankan ba"

Ya sake ta yana ƙoƙarin tashi ta yi saurin shigewa toilet dukda ciwon da kwankwasonta ke yi mata hatta ƙirjinta a zabar zafi yake. Bayan ta shiga Ustaz ya tattare gadon ya gyara ya fito mata da wata blue ɗin riga iya qiwwa mai sauƙin nauyi a jiki. Fita ya yi zuwa sashinsa sai a lokacin ya ji gajiya ta saukar masa ainun shi kansa nasa kwankwason ciwo yake he wonder why? Maybe don ta amshi budurcinsa ne.

Wanka ya yi sosai ya shirya cikin English wear black colour suka ƙara fidda hasken fatarsa irin ta larabawa hannunsa rigar half damtsensa ya fito sosai wandon iya qiwwarsa gargasar jikinsa har ta yi yawa amma tai wa fatarsa kyau sosai da gaske ta yi kwance luf luf ya samu kansa da ɗaukan turaren daya siyo for the first time a rayuwarsa, ya dinga kallon turaren na ROJA DOVE AOUD a hankali ya dinga fesawa har su ƙasan wuyansa bayan kunne gashi kamshin na musamman ne, sai a lokacin yake duba price ɗin turaren lallai ya kashe kuɗi. Ya tattare sumarsa zuwa baya a karo na farko ya saka abu ya ɗaure dukda haka sai da wata ta kwanta gaban goshinsa ya dinga sakin murmushi shi kaɗai gabaɗaya wankansa na Ridayya yau. Ya kalli kansa sosai.

Sanda ya koma bedroom ɗinta ya sameta zaune a kan stool na gaban madubi tana ganinsa ta yi saurin ɓoye zuma da kwalaccar wajan Hajiya Nana. Ya buɗe idanunsa a bayanta dake ta glowing na baƙar fata. Gently a hankali ya ƙarasa ya ɗora hannunsa a kafaɗunta ta yi saurin ɗago kai ta cikin madubin suka haɗa idanu ta saki baki tana kallonsa wallahi idan ba magana Ustaz ya yi ba, ba zata taɓa cewa yana jin Hausa ba.

"Uhm cikakken Bahaushe ne mijinki bar tunani"

Ta yi mamakin yadda ya fahimta, ƙarasa shiryata ya yi kanta a ƙasa ya dakko kaya ta yi saurin cewa.

"Zan iya sawa fa"

"Are you sure?" Kin tabbata? Ta É—aga masa kai ta É—auki rigar zata saka ya yi saurin amsa ya É—age hannayenta ya zura mata ta yi baya kamar zata faÉ—i ya yi saurin jawota gefensa a kunne ya ce

"No more secret between us Baby "

Ita dai Ridayya yau ba Ustaz take gani ba, ba kuma Abbiey ba yau Yaa Bilal ne da kansa kuma Md na bankin Fidelity dake Lagos.

"Bacci zan yi ni"

"No, jikinki zai ciwo ki sha tea da paracetamol ko?"

Ta maƙale kafaɗa idanunta ya cicciko da hawaye te nemi rikice masa, sai ya kama hannunta a hankali ya jata wani ƙaramin parlorn da yake can gefe amma yana da sanyi saboda gabaɗaya taga da ƙofar na glasses ne hakan ya saka suke ɗaukan sanyi sosai duk snow a jikinsu, suna shiga ya kunna heater ta zafi.

Sanyin ya rasa Ridayya ta yi saurin maƙale wa a gefen shi tana juyar da fuskarta ya zaunar da ita a kujera mai tsayi, wayarsa ya fara danna ba jimawa door bell ya fara ƙara ya ajjiye wayar a cinyarta ya nufi ƙofa ta bi bayansa da kallo tana lumshe idanunta.

MB USTAZ ya dubi baturen saurayin da yake masa magana cikin harshen turanci, Ustaz bai ce komai ba yana tsaye hannunsa zube a aljihu jin surutun mutumin ya yi wa ya saka Ustaz jan breakfast table ɗin tare da rufo ƙofar. Yana juyawa Ridayya ta yi saurin rufe idanu tana shassheƙar kuka ya ja table ya ajjiye tare da rage tsayin shi daidai su.

Ya kalleta murya ƙasa a taushashe cikin kulawa ya ce

"Ƴan mata ya dai?"

"Abbiey jikina ciwo, bayana,ƙafata, ƙirjina wayyo Abbiey na mutuwa zan yi"

Nan da nan ya rikice Ridayya ko tausayin Dattijon Abbiey ɗin nata ba ta yi daman haka soyayya take tsakanin yarinya da babba, kuka take sosai duk ta ɓata fuskarta hadda jinjigar zazzaɓin ƙarya.

BM USTAZ ya rikice duk da ƙoƙarin riƙe kansa da yake wajan ganin ya ja girmansa amma zuciyarsa ta yi masa gardama ya kama hannunta ya ce "Na bi Allah na biki Babyn baby ki bar ni haka nan Please"

Ta yi shiru ya matsa sosai yana rarrashinta

"I lost my words, i have no words wajan magana tunjiya ki bar nutsuwa ta ta dawo"

"To ni yunwa nake ji"

"Oopps" Tea ya haÉ—a mata mai kaurin gaske yana zafi ya zuba mata roman naman da aka dafa mai ruwa-ruwa ya saka cokali a shayin ya nufi bakinta ta É—auka kai tana kumbura fuska.

Ustaz a ransa yana jinjina shagwaɓar Ridayya dukda daman ya san halinta idan ta samu sake wajansa tun tana ƙarama

"What?"

Ta É—auke kai ta ce "Ni a bulunbuti nake so"

Da wani irin yanayi ya zaro idanu waje cike da tashin hankali da fargabar inda zai nemo wata bulunbuti.

A gida Nigeria Umma ce tsaye a kan Mardiyya ta gama kwara amai sosai take laulayi ta jigata ainun Umma kuma baki har kunne ta kusa samun jika sai kashe uban kuɗi take komai ta ɗauka ta ce Mardiyya matar Babana zata haifawa Bilalunta ɗa. Yanzu ma tana riƙe bowl wanda ta haɗa kwaɗon rama a ciki ya sha tumatur ta ce

"Oh ni Hadiza yanzu a yi ace komai mutum ya ci sai ya dawo da shi? Ki daure ki ci wannan"

"Umma wari abin hannunki yake zan yi amai"

Umma ta ce "Ikon Allah, shi ma bakya ci? To me kike so?" Mardiyya ta lumshe idanunta abubuwa da yawa ke mata yawo a rai babban burinta bai shiga Ustaz ya dawo ba. Ta sauke numfashi ta ce "Farfesun kai da ƙafa nake so, shi ma na ɗan taure irin me warin nan"

Umma ta tafe ƙirji ta ce "Wanne irin ɗan taure ina za a iya tantancewa ni Kubura" ita dai Mardiyya shiru ta yi Umma ta yi murmushi ta ce

"Ai shikenan duk ranar da mijin nan nawa ya zo duniya sai na dungure masa kai da hanci na wahalar daya saka ni, nasan fari jajur za ki haifo tunda ma sha Allah daga ke har Babban mutum farare ne tas a wanke kuke, Ubangiji ya ƙara nisanta shi da waccar munafukar mai baƙar fuska kamar zunubi, gwara da Allah ya raba wannan matsiyacin auren na ƙaddara da babu Makka duk ta haifa jama'a munana yara masu kalarta da ba zan taɓa amsar su matsayin jikokina ba"

Ta ja ƙwafa rai ɓace haka kawai ta tsani Ridayya Mardiyya ta ce "Umma amma Mai sunan sweetheart kyakkyawa ne kalli kama suke da Ustaz fa"

"Allah ya yi mini tsari Ridayya ta haifi mai kama da jinina can ta gwale mata wallahi, kune yaran zamani amma babu mamaki shi ma Bilal É—in data haifa shege ne bai yi kama da uwar ba, bai yi kama da mijin ba Zameer yake, wallahi ba mamaki shege ne suna can suna ta É—awainiyya da É—an haram Allah dai ya tuna mata asiri"

Mardiyya ta ɗan yi shiru ta ce "Umma yaushe Ustaz zai dawo duk na damu, kunya nake ji na yi ta zama kina ɗawainiyya dani,kuma a gida sai tambayarsa ake yi sai dai na yi ƙarya na ce tafiya ya yi wajan aiki. Bansan muhimmancina a wajan shi ba, wallahi ke na kewa biyayya"

Umma ta sauke ajjiyar zuciya a ɓoye ita kanta bata san inda Babban mutum yake ba. A zahiri ta ce "Ki kwantar da hankalinki, matsayi kuma ai kin sani karki manta cikin Bilal ne a jikinki, duk na mijin da ya ti tarayya da matarsa yana nufin ya aminta da ita kuma yana son ta. Kar ki saka haka komai a ranki ki raini cikinki kuma zan kula da ke Babban mutum kuma na miki alkawarin dawowarsa da wuri haka"

"Shikenan Umma na gode amma ko numbersa babu?"

"Zan bincika miki, bari na je a nemo kai da ƙafa"

Mardiyya ta yi saurin toshe hanci ta ce "Don Allah umma É—an matsa wari kike,ina nufin warin rama" kafin Umma ta yi magana ta fara kelawa amai a saman gadon ko tashi ba ta yi ba.

Umma da kanta ta dinga bulayin neman kai da ƙafa na ɗan taure. Bayan ta gama komai ta kawowa Mardiyya taƙi ce ta ce daman wurin ɗan tauren kawai take son ji. Baba ƙarami ya manta wayarsa a ƙaramin parlorn da yake sashinsa Umma na zuwa ta fara bincike cikin sa a ta samu wata sabuwar number da aka yi saved da Aboki. Ta san Babban mutum kawai baba ƙarami yake cewa.

"Me kike nema ne haka Hajiya Hadiza?"

"Ba komai, cewa na yi baka ce komai akan cikin Mardiyya ba?"

Ya kalleta ya yi murabus bai ce komai ta ce "To murmushin mene kake? Ina tunanin daman babban mutum rabonsa a tattare yake da Mardiyya ya kamata ka ce ya dawo gida haka, tunda ita muguwar mai baƙar aniyyar ba zata dawo ba saboda tana baƙin cikin ta ganshi tare da Karfi in sha Allah sai Ubangiji ya ɗorawa Ridayya soyayyar Ustaz kuma a banza ya mata nisa"

"Amin, hakan muke addu'a "

"Me? Yanzu dai ka faÉ—a masa"

"Ki faÉ—a masa da number da kika É—auka" yana faÉ—in hakan ya fice ya bar mata wajan.

Ammi abin duniya ya yi mata yawa Junaid ya kasa samun matar aure saboda matsalar Genotype, ga Balkisa ta dawo gida ba lafiya ga Yaya Zuhura miji ya yi mata dukan mutuwa har kwanciya ta yi a asibiti Mami ce ta kula da ita, ko kallonta ta lura Yaya Zuhura bata son yi yarinyar data fi karfin fiye da kowa a yaranta amma yanzu wai gaba da ita, kamar am musu farraƙu ta ɗauki alhakin hakan ta tattara akan Mami ita ce ta yi mata asiri. Gashi ta kwace gida abinda bata ƙauna kenan ga Baffa ya juya mata baya kwana biyu komai cuɗe mata. Ta juya ta kalli Burhan da baya cikin haiyacinsa ta ce
Chapter 93 · 0% Book details