← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 118

Sashe 114

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Ghali Uba ya ce "Shazali kenan siyasa sai É—an siyasa, yanzu ka je ka yi bincike ka ji ko shi Khalid É—in ya bawa wani kwafin bidiyon, kuma ka ce ina kiran shi yama sunan shi yawwa MUTALLAB TAHHB"

"Da ƙirinka oga ai MUTALLAB ko appointment ka nema da shi baza ka samu ba, saboda shegan ƙaro ne, innalillahi wani aikin sai ɗan Amina oga shi fa TAHHB ɗan balaja'u ne ko a rukunninsa ba kowa ya san shi ba" da mamaki Dr Ghali Uba yake kallon Shazali a ran shi yana tambayar who is MUTALLAB TAHHB?

Mardiyya ta yi tsuru-tsuru lokacin da ƙawarta ta shigo gidan daman shirye-shiryen kai Ustaz koto take yadda ta ƙarfi za a mallaka masa yarinyar. Umma ta juya ta kalli wacce ta shigo haka Baba ƙarami da Junaid da sauran mutanen wajan "Baiwar ke fa?" Cewar Aliyu kafin ta yi magana Umma ta ce "Na san wannan fuskar ƙawar wannan ƴar iskar ce" cikin sauri Mardiyya ta ce "Laa ni ban santa ba, ban taɓa ganinta ba sai yau" da wani irin mamaki ƙawar ta ce "Idan ba ki ce haka ba ai ba ki cika cikakkiyar munafuka ba, ke har ni za ki kalla ki cewa haka? To bari ki ji I'm not coming for this ga uban yarinyar da kika haifa can waje yana jiranki" gaban Mardiyya ya faɗi ƙirjinta na dukan saba'in saba'in ta ce "Ban gane ba" ta ce "Oh bari na yi yadda za ki gane" ta juya ta kalli Ustaz ta ce "Sanda Mardiyya ta aureka tana da wanda take so, kuma maganar aure ya shiga tsakaninsu ma, tunda ta je gidan Ridayya suka samu saɓani ta ɗauki alwashin sai ta aureka, bayan an yi auren ta cigaba da mu'amala da Yaƙub suna haɗuwa a hotel kala-kala har mu'amala ta gitta tsakani ta samu cikin, hankalinta ya tashi domin a lokacin ta ji ta fara sakon ka gashi kana ƙoƙarin zama Gwamna, tana ta neman hanyar da za ku yi tarayyar aure saboda ta ɗauki bidiyo ya zama evidence na cewa cikinka ne, domin bata taɓa kawowa ranta zata haihu baka kasance ta ba, domin tabbatar da abinda nake faɗa ka je waje ai za kaga Yaƙub ɗin" Ustaz ya kasa cewa komai jin abinda yake kamar a littafan Hausa ko dram na film, ya juya tare da barin wajan. Mardiyya ta durƙushe a wajan tana rusa kuka bata taɓa ladamar abinda ta aikata ba sai yau, gashi wani irin mugun son Ustaz take kamar rai ji take kamar ta haɗeye shi ta hutawa ranta. Zuwan Hajia kenan ta ce "Amma dai kin watsa mini ƙasa a idanu Mardiyya, na yi bake bake raina bai huta ba sai dana ga kin auri yaron nan ashe tsatsa tuni ta cinye zuciyarki, to maza maza haɗa kayanki ki ɗauki ku yi gaba zuciyata har nunfashi take wajan ganin na ci miki mutunci" Inna ta ce "Ni dai daman zaman wanka na zo tunda abin ya zama haka ya lalace sai dai na ce Allah ya baku haƙuri amma tabbas anci mutuncin aure an kuma taɓa martabar aure" Tana kaiwa nan ta ja jakarta ko inda Mardiyya take bata kalla domin zata iya ci mata mutunci naƙin ƙarewa.

"Umma don Allah ki rufa mini asiri ka saka mijina ya mayar dani, wallahi na yi ladama ba zan kuma ba sharrin shaiɗan ne" Umma ta zare idanu ta ce "Wanne shaiɗan ɗin kuma? Ai kece shaiɗaniyyar kan ki wallahi kuma tsakanina dake Allah ya isa, ki yi gaggawar fito mini da takardar filin dana ba ki" ganin da gaske ta rabu da Ustaz rabuwa ta har abada ya saka Mardiyya miƙewa tana goge hawayen idanunta zuriyarta na yi mata wani irin zafi da ƙona ta ce "Ai fili na takwararki ne Hadiza, kamar yadda shaidu suka tabbatar tuni na siyar da shi na siya mata wata kadarar"

"Kika siyar mini dame? Dukiyar tawa akan ƴar zina?" Mardiyya ta ce "Bafa nina ce ki bani ba, da hannunki kika ɗakko tare da mallakawa cikina shi, da saka hannunki da komai, idan ba ki yarda ba kina iya kaiwa koto" tana kaiwa nan ta ɗauki yarinyarta tana cewa "Ga Hadiza ga takwarar Hadiza" Umma ta dinga tsinewa Mardiyya albarka duk irin cin mutuncin da takewa Ridayya bata taɓa yin tari ba balle tai mata kallon banza, yau wacce ta zaɓa ta fifita ita ke kiran sunanta haka tsirara. Baba ƙarami ya dinga murmushi daman wannan ranar yake jira gashi lokaci ya yi yana danne dariyarsa ya ce "Sai haƙuri,surikar so kuma surikar gwal da kika fifita ce akan zaɓin da ƙaddara taiwa ɗanki ce fa? Mardiyya fa? Haba Umma a dinga sara ana duban bakin gatari" Umma ta sake fashewa da kuka ta ce "Daman ai kana sani ka sawa shegiyar yarinyar suna Hadiza,kuma wallahi bani Hadizan ba" Ridayya na can part ɗin Mami bata san meke faruwa ba sai da Zainura ta shiga take bata labarin komai, ita kam ko a jikinta haushin Ustaz ɗin ma take ji.

A daren Ustaz ya saka Baffa a gaba akan ya yi haƙuri ya saka a saki Ammi haka nan tasha wahala da ƙyar ya shawo kan Baffa ya yi wa aka saki Ammi amma ya ce ba gidan shi ba, Junaid ya ɗauke ta zuwa gidan daya siya mata daman ya san zai wahala Baffa ya yafewa Ammi ta sauƙi. Ta dinga kuka tana bawa Junaid haƙuri da sauran yaran banda Yaya Zuhura ko wajanta ma bata je ba, domin ta ce ita ta sake uwa.

Prof na durƙushe gaban Hajja Azizat idanunsa sun ɗauka tare da yin jajur saboda damuwa da tashin hankali, abubuwa sun masa yawa ga matsalar takara daya samu domin tuni an sauke shi an bawa wani, ga matsalar Talatu ƙarin kunama data ke shirin tattare arziƙinsa saboda barazanar da take masa akan bidiyon data ɗauka duk ya fita hayyacinsa, ya yi gurfane kamar mai neman ɗauki ya ce "Me ya sa kika kasance mai taurin kai ne? Mara yafiya da duba baya?"

"Baya? Wanne bayan zan duba kenan Prof?" Hajja Azizat ta furta cikin yanayin mamaki dake cin zuriyarta lokaci guda kuma ta juya tare da zuba masa idanunta masu kaifi ya ce "Ki tuna ni ɗin mijinki ne zuri'a ta shiga tsakaninmu, karki duba kuskure na ki yafe mini ki dawo gidanki ƙarshen igiyar aurenki" ta cije baki tana girgiza ƙafarta ta kasa furta komai saboda yadda zuciyarta ke mata zafi, bata taɓa dana sanin auren Prof ba sai yanzu, ba shine irin mijin daya dace da ita ba, rabon Sadauki daya rantse shine ya ƙaddara auren nasu Sadauki ya rasu he is no more don haka dole auren ma ya rasu.
Ya miƙa hannu zai kamo ƙafarta ta yi saurin zamewa ya ce "Ki tausaya mini sharrin shaiɗan ne, wallahi ina matuƙar son ki da gaske i don't know what come over me nake aikata zunubin da bai dace ba, i love you i so much love you Azizat" Mother ta yi murmushi tana miƙewa tsaye ta ce "You know what Prof? Fita a parlon nan kafin zuciya ta ɗauke na faɗa maka abinda har ka mutu baka mance ba" ya miƙe tsaye idanunsa sun ƙara jirkicewa ya ce "Don girman Allah ki tausaya mini Azizat do you know how much I love you, kin san yadda nake son ki kowa? Me ya sa ba zaki yadda da ƙaddara ba? Eh?" Rai ɓace ta juya zata shige cikin gidan daman a parlon farko suke ya yi saurin kai hannu ya jawota, kafin ya zame hannunsa ta ɗaga hannu tare da sauke masa wani gigitaccen mari a kunci da yatsa ta ce "Kul! Ko da wasa don't even try to do, jikina ba irin na karyan matan da kake mu'amala da su bane Prof, a tsarkake nake kuma na gode da tsayin shekarun daka dinga tauye haƙƙina ashe hakan alheri ne a gare ni, wallahi tallahi na yi ladamar aurenka na ji inama ban taɓa aure ba" ta share hawayen idanunta don kar rauninta ya danne zafin zuciyar da take ciki ta ce "Me kake tunani dukiya shine aure da jin daɗi da kwanciyar hankali? An faɗa maka dukiya na kewa, ana yin aure ne domin raya sunnar ma'aiki, tare da tattali da soyayya da kulawa, haɗe da kare mutuncin juna da martabar aure, ban yi zaton soyayyar da kake nuna mini iya ta waje bace, baka san ka zauna da matarka ku yi hira ba, baka san ka sauke haƙƙina da ke kan ka ba, baka son ka zauna a gida cikin iyalanka, kai maƙaryaci ne you're a liar, cheater, hypocrite, adulterer, you're nothing but my destiny, you kill your own child saboda rashin kulawa da tsoran Allah irin naka" Prof ya dafe kunci ya ce "Ni kika mara Azizat? Ni kike zargi da kashe ɗana Sadauki?" Murmushi ta yi tears running down on her face tana girgiza kai she couldn't feel yadda take jin zuriyarta a lokacin.

"Zan iya yi maka abinda ya fi haka, wallahi na tsaneka kuma ka gaggauta rubuta mini sakina ba zan taɓa iya cigaba da zama da kai ba, daman can kasancewar mu tare zanen ƙaddara ne kuma yanzu ta sake rabawa" shi kansa Prof a sama yake jin maganganun nata, bai zacci girman son da ya kewa Azizat ya kai har haka ba sai yanzu da ƙaddara ke barazanar raba shi da ita, sakaci da son zuciyarsa sun takawa rawa wajan yin fatali da muradan zuciyarsa dana iyalansa ya duƙa saman ƙafafuwansa ya ce "Let by gone be by gone Hajja Azizat, wallahi ba zan ƙara bari mummunan zuciyata ta kwaɗaita mini wata sura ba face take, ki yafe mini na bi Allah na biki please ki yi komai zan ɗauka banda rabuwa da ke" kasa ce masa komai ta yi sai ta juya ya yi kamar zai bita ciki tana zuwa ƙofa ta ce "Mu haɗu a koto" Prof ya jingina da jikin bango yana dafe kansa ya bita da kallo har fa shige ciki. Tana shiga ɗaki ta ji kanta na sara mata ƙirjinta ya yi mata nauyi mutuwar Sadauki ya dawo mata sabuwa ta dinga kuka kamar ranta zai fita har bacci ya ɗauke ta.
Chapter 114 · 0% Book details