Sashe 87
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa? Wai da gaske babban mutum ya saki Ridayya? Ku karanta mana takardar a fili mana" caraf Ammi ta karɓe zancen da faɗin "Wallahi Hajiya kema kya faɗa, su kawo takardar na karanta a fili kowa ya ji, ai saki ba kan Ridayya farau ba, ba kuma za a ƙare a kanta ba. Allah ya ƙaddara ita ɗin matar Burhan ce"
"Burhan kuma?"
Junaid ya furta da mamaki kwance a fuskarsa ita nata allon sai ya haska mata Burhan matsayin mijin Ridayya? Ai kowa da ƙaddara sam ba ta yi wa Ridha adalci ba, duk lalacewarta ta fi ƙarfin mashayi.
Ammi ta zarewa Junaid Idanu ta ce "To uwar mece da Burhan ɗin har kake maimaita sunansa, ai daman ya jima yana son ta, kawai babu yadda zai yi ne ni ce nake tanƙwara shi"
Kowa kallon Ammi yake banda Baffa da Mami, wacce ta yi kamar ruwa ya cinye ta wani irin zafi zuciyarta ke yi mata yaushe ne Ridayya za ta yi farinciki? Yaushe ne damuwarta za ta zo ƙarshe? Mene laifinta? Wani abu ya tukare maƙoshinta nan da nan abinda ke kwance a mararta ya motsa tare da tabbatar da lafiyarsa ras.
Baffa ya sauke numfashi bayan kammala karanta abin da takardar ta ƙunsa ya yi shiru domin bashi da wani abin cewa tsananin kunyar abinda ke zane a takardar shi ya addabi ransa ya kuma jin daɗin kalaman Ustaz har ransa, tantama da mamaki suka mamaye zuciyarsa at the same time kuna ya hasko irin zuri'ar da Ridayya da Ustaz za su samawa Rano families. Ya ɗaga kansa yana kallon Hajiya ya ce "To daman ba wani abu bane face.....,'
Abba ya yi saurin tarar numfashin Baffa yana me riƙe hannunsa ya ce
"Saki ne kamar yadda kowa ya ji sai fatan Allah ya daidai tsakani. Aure daman rai gare shi na wasu ya ɗore na wasu akasin hakan ƙaddara kuma yaɗo take idan an san farko babu wanda ya san ƙarshen ta, wata ƙarshen ya zo me kyau wata ba yadda muka yi tsammani ba, idan akwai rabo tsakanin Muhammmmd da Ridayya babu shakka wanda ke da tawaye da auren rabo zai yi ajalinsa kowa ya sassauta buri" saurin yin shiru ya yi jin Umma ta rangaɗa uwar buɗa da faɗin.
"Ayy yiri-yiriri. Na gode Allah na kuma ji daɗin wannan rana don murna kamar na zuba ruwa a ƙasa na sha haka nake ji, ina roƙan Allah ya ɗorawa muguwar ƴarku son ɗana wanda zai kwantar da ita har gadon asibiti ta ji irin abinda ya ji, kuma tsakaninta da shi sai kallo daga nesa Mardiyya ita ce matarsa ta nan gidan duniya da kuma lahira, na tsaneta bana ko ƙaunar buɗe idanu na ganta ina fata idan rabon ya tashi kisa ya kasheta ita" ta sake sakin dariya.
"Ahhayeee cas raina fari tas idan ma mata biyu yake so ni zan nema masa wata in sha Allah ko a cikin yaran Æ´an'uwana ne na Zamfara, kuma Muhammmmd dole ya dawo gida ya kuma bi umarnin uwarsa"
"To bari mu gani umarni uwa zai bi ko na mata? Ko kuma soyayya" Abba ya faÉ—a a fili ta ce "Me ka ce?"
"Cewa na yi ki saurin nema masa matar auren nima zan fi son hakan, kuma ki dinga sara kina duban gatari ki buɗe kunne da idanun zuciyarki kuma ki tuna cewa ɗanki nakasashe ne banga lafiyayyiyar yarinyar da zata zauna da shi baya amfana mata da komai ba, musamman yaran zamani da idanunsu yake a buɗe. Babban dalili babu iyayen da za su amince su bawa Muhammmmd auren ƴarsu bayan sun san ba zai taɓa haihuwa ba. Itama Mardiyya zan nemi makusanta na labarta musu komai"
Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da barin parlourn ransa babu daɗi, ana zaton wuta a maƙera sai gata a masaƙa bai yi zaton Hajiya Hadiza zata kawo masa tsaiko ba. Mami ma miƙewa ta yi ta nufi part ɗinta zuciyarta tuni ta raunata ainun.
Hajiya ta ce "Allah shi daidaita al'amarin nan duk auren da ake tsiya haka fa ya fi tsayin rai, mutane suyi ta ƙoƙarin kashe aure kamar sune suka halacce shi, Ubangiji ya kawo musu da sauƙi"
"Amin" Anty Zuhura ta ce Ammi ta watsa mata muguwar harara tana ƙwafa.
Baffa ya miƙe Ammi ta yi saurin cewa "Baffa idan ba damuwa ina son magana da kai" ya dube ta can ya ce "Ina ji"
"Kamarya kana ji nemi waje ka zauna" da wani irin expression Baffa ya juya gabaɗaya yana kallon Ammi a kasashe ya ce "Maryama kin haife ni ne? Yaushe muka saba haka dake? Ko Junaid kya faɗawa haka balle ni ubansa kuma mijinki?" Ta yi shiru domin ta kwafsa wai tana gwada aikin sabon malamin data samu ne sai dai taga har yanzu da saura. Rai ɓace ya juya ya nufi ɓangaren Mami dukda cewa girkin Ammi ne.
"Uhm ka yi lokacinki na, ka mure shi ina nan zuwa daga kai har Fatima za ku gane shayi ruwa ne" Junaid ya kalli Ammi ya ce "Ammi wai meke faruwa ne?" A tsawa ce ta ce "Ubanka da uwarka sune suke faruwa, ka fita daga sabgata Junaid kuma wallahi ko ka fito da matar aure ko na zaɓa maka duk wacce ta yi mini"
Ya miƙe zai fice ta ce "Ina magana kana mini banza? Do i look like an idiot to you?"
Ya girgiza kai ya ce
"Me zan ce Ammi? Kin san matsalata genotype ɗina AS ne duk wacce na gani ina so da zarar mun je gwaji sai itama aga AS ne dole aure ba zai yiwu ba" tausayin Junaid ya kama anty Zuhura amma Ammi ta saka ƙafa ta shure ta ce "Duk fa ƙarya ce kawai irin ta likitoci ba wani ciwon sikila da sanda ake auren uwar wa ya samu mutane? Sai yanzu to ni zan nema maka mata kuma dole ka aura tunda kai baka ganin me nake faɗa maka, bari su Aliyu, Abubakar, da Khaliperh su shigo suma"
Junaid dai bai ce komai yana fice daga gidan bakiÉ—aya.
Baffa ya samu Mami tsaye a baƙin ƙofa ta yi shiru ya shiga yana murmushi ya ce "Waya ɓata mini ran Sahiba? Shi ma yanzu nasa ya ɓaci" Ta juya gabaɗaya hakan ya bawa hawayen idanunta damar sakkowa zuwa saman kumatunta. Muryarta na rawa ta ce "Baffa da gaske ne Babban mutum ya saki Ridayya?"
Ya yi shiru yana kallonta sai kuma ya saki dariya ta kwaɓe fuska tana dire ƙafa ta ce "Ba maganar wasa bace hankalina duk ya tashi, tsoran sanin gaskiyar abin ya addabi zuciyata"
"Yaushe na yi miki ciki Batool? Ciki nake gani a jikinki fa?" GabaÉ—aya hankalinsa yana kan cikin ta yi saurin juyawa ya kamota ya saka hannu a cikin muryarsa na fidda sauti na farinciki ya ce
"This is serious, please when?"
"I have no idea, ni ba maganar ciki nake yi ba"
"Ni kuma ita nake so mu yi Zarana É—a za ki haifa mini wannan karan. Allahamdulillah" gabaÉ—aya ya kamota jikinsa ta yi shiru can ta ce "ina son Ridayya ta rayu da Ustaz Baffa ina son haka shi kaÉ—ai na aminta da shi, bana son ta sake shan wahala a rayuwarta"
"In sha Allah,ki kwantar da hankali ba wani saki fa? Bai sake ta ba kawai muna pretending ne zuwa sanda ƙaddara zata sauya komai, ya isa kin ji?" Ta jinjina kai... Yana shafa cikin ya ce "Mu je ki ji akwai batu fa ƴar nan" ya ce yana raɗa mata a kunne.
*****
Numfashi ya sauke a karo na biyu yana sake ware idanunsa da nutsa su cikin photon da kyau "why? You have been far away from me and you have tortured my heart a lot?" Ya cije bakinsa tare datse bottom lip yana jiwa kansa ciwo, zafin da zuciyarsa ke masa tamkar ciwon daya ruski mace mai ciki.
“Ban taɓa ganin inda so ya zama aibu ba, I love you, i just loves you kina yi kamar ba ki san komai ba, kina wasa da feelings ɗina, I don't care what will happen, I don't care what you will say, I only know myself and my heart, dole na raba ki da ko wanne namiji na kasance dake, ba zan yafe miki ba muddin kika saka bakin almakashi wajan datse alƙawarin zuciyoyinmu, dole; tabbas ne hakan"
"Sadauki what is this? Mene haka Sadauki kana cikin nutsuwarka kowa?"
Ya juya da jajayen idanunsa ya kalli Mother laɓɓansa sai rawa suke ya kasa furta komai har ƙanƙance Idanu yake, ganin yanayinsa ya saka Mother juyawa zuwa wajan fridge ta ɗauki ruwan gora mai sanyi tare da tsiyayawa a farin cup ta ƙarasa kusa da Sadauki tana cewa
"Drink, sha Sadauki"
Bai yi magana ba sai tsare Mother da kallo da ya yi, a hankali ta kama hannunsa tare da saka masa glasses cup ɗin hannu, ya amsa still he looks at into her eyes ya matse hannunsa cup ɗin ya yi ƙara tare da fashewa a hannunsa jini ya fara zuba hankali tashe Mother ta ce "A kan mace kake neman kashe kan ka Hamza? Baka tunanin ni da kuma Prof?"
Murmushi kawai ya yi mata idanunsa na Æ™ara rinewa a hankali kuma underneath his breath ya maimaita sunan “Prof.....â€
Irin bai gane ɗin nan ba can ta ce "Baka tunanin halin da za mu shiga ni da mahaifinka? Kai kaɗai muke da shi fa" ya yi baya yana tura hannunsa cikin suma har yanzu jikinsa rawa yake musamman tsokar ƙirjinsa ta cikin zuciyarsa
"Oh your husband?"
"What?" Sai kawai ya girgiza kai ya juya baya yana ɗaga kansa sama tare da ƙurawa waje guda kallo. Tsoro ya kama Mother kar wani abu ya taɓa tunanin Sadauki ta sakko daga upstairs da sauri tare da ɗaukan wayarta.
3 miss calls ta yi Prof amma ba a ɗagawa ana huɗu ta samu aka yi picking muryar da ta ji ya saka ta yin baya tare da neman waje ta zauna bisa tilas, wani irin bugawa ƙirjinta ke yi ta kasa furta komai sai da aka ce.
"Hello who is on the line?"