Sashe 117
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi sai na zubar yarana watan su shida kawai sai a ganni da ciki? A saboda ba kai kake shiga cikin jama'a ba? Gashi ina tunanin ƙarasa karatuna" yadda take ɗaga masa murya ya fi komai bashi mamaki ya sake ta ya ce "Ridayya kenan, muddin ni na yi cikin nan wallahi tallahi kika zubar anan za ki san waye kike aure a nan za ki ɗaya fuskar tawa, ba maganar saki a tattare dani amma abinda zan miki sai kin gwammace kiɗa da karatu ni Muhammad Bilal Tahir zan ba ki mamaki" ya sauke numfashi yana jin kansa na sara masa ya ce "Idan kuma ke kikaiwa kanki cikin fine kina iya yin abinda kika ga dama" sosai suke cacar baki abinda basu taɓa yi ba, basu yi aune ba su kaga Little ya shigo cikin sauri Abbiey ya koma bayan Ridayya yana saita yanayinsa kana ya ɗan jawota jikinsa, Ridayya ta ɗan dake tana murmushi ta ce "Jarumi na ya akai? Shigowa ba sallama ba neman permission bana hana ba?" Little dai kallon su yake ya san dai ya yi sallama har babu adadi ya ce "Kuna ta faɗa Mimi da Abbiey"
"Faɗa kuma?" Ya ɗaga kai ya ce "Kuna ɗaga murya kinawa Abbiey haka" ya miƙar da yatsar shi yana pointing wani waje, Ridayya ta yi murmushi ta juya ta kalli Abbiey ta ce "Abbiey ka ji wai faɗa muke?"
Ustaz dai ya yi shiru don bai iya ƙarya ba idan muddin ya buɗe baki to e zai ce. Ta kalli little ta ce "Wani abu muke nunawa na Film, scane ɗin ya mini kyau na ce mu yi rihazal da Abbiey amma ba za mu kuma ba" cike da gamsuwa ya ɗaga kai ya ce "To malam ya ce idan an yi faɗa za a sasanta musabawa ake" ya kamo hannun Abbiey ya kamo na Ridayya ya haɗe, Abbiey ya damƙe hannunta dake cikin nasa yana shafawa ya zuba mata idanu, ya fahimci dole ya shiryawa wannan cikin domin ta tsiwa ya zo idan tana al'ada ta yi ƙunci taƙi magana yanzu kuma ciki ya zo mata da rigima dole ya tausasa zuciyarsa ya fahimtar da ita da kyau ya kuma iya controlling kansa ya ja numfashi ya sauke yana sake riƙe hannunta little ya ce "To ku gaisa"
"Assalamu Alaika Abbiey" shi dai kallon ta yaƙe yaƙi cewa komai ganin yadda little Bilal ya kafe shi da idanu ya saka shi cewa "Sannu Mimi" little ya dinga tsalle yaro ne mai shegen wayo da surutu ya ce "Second Mimi ta zo da wata" Ridayya ta ce "Ka cire second ɗin Just say Mimi, idan da amana kuma duniya da gaskiya ai wajan Zainura zaka zauna" ya maƙale kafaɗa ta ce "And this is the last time da zaka shigo bedroom ɗina da Abbiey ba a baka permission ba, a good person never do this ok?" Ya ɗaga mata kai Ustaz dai kallon su yake, little ya fara ƙoƙarin shigewa jikinta ta ce "A'a wallahi muje" sai da ta je bakin ƙofa bayan little ya fita ta juya ta kalli Ustaz ta ce "Kuma da kake maganar saki an faɗa maka ko ka sake ni zan tafi ne? Rayuwa da kai yanzu na fara saboda ina son ka" girgiza kawai ya yi a zuciyarsa yana "Allah ya yafe miki Ustaza" wato idan baka da mace ƴar drama ma da sauran ka, ko babu komai za a saka bakinka ya motsa da surutu.
A zaune ta samu Zainura da Zainab suka gaisa sosai nan da nan ta dafa musu taliya fara da mai da haÉ—in salad domin bata iya dafa komai. Ta kalli Zainura ta ce "Amarya bata lefi" Zainura ta ce "Sallama na zo miki zamu shige Lagos"
"Lagos ke da wa?"
"Da mijina mana yaya" Ridayya ta ce "Ikon Allah, to Allah ya tsare ya kai ku lafiya sai na tuna zuwana Lagos sai ki dage da sana'a garin neman kuÉ—i ne ba mugunta, ki fara business nima za kina turo mini da kaya" har compound ta raka Zainura sai a lokacin ta lura da Burhan tace "Kake ta zauna a mota? Ban san tare kuke ba"
"No ba komai yaya"
"To Allah ya tsare ya kiyaye" suna tsaye Ustaz dake balcony yana waya ya ƙarasu suka gaisa da Burhan kana ya musu fatan alheri ya yi Zainura faɗa sosai. A haka suka fice daga gidan "Baby lafiya naga ka ɓata rai?"
"Kin bar marayan Allah a waje shi ɗaya haba sweet" ta juya idanu tana shafo fuskarsa ta ce "A yi haƙuri mazaje ba za a kuma ba" ya juya ya kalleta ya ce "Zinu....." Sosai Zainaba ta yi wa Ridayya faɗa na wawtar da take shirin aikatawa ta bata shawarwari masu kyau, da Zainaba zata tafi Ridayya ta haɗa mata goma ta arziƙi kayan abinci da kayan miya suna nama da kuɗi dubu hamsin ta saka drive ya kaita gida.
That's how life is....
Har gidan Ridayya Ammi ta je ta bata haƙuri Ridayya ta ce ba komai ƙaddara ce, ta nuna har zuciyarta komai ya shige. Umma ta yi ƙunci sosai kafin ta sakko Hajja Azizat ta nunawa baba ƙarami soyayya irin wacce ta yi masa tanadi tun suna samari, ya kuma sha mamaki ainun har wani fresh ya yi ya ajjiye tumbi ta ce Abba ya ce Zauja kullum kuma sai ta gai da Ammi bata da matsala hankalinta ya kwanta bata taɓa sanin haka zama yake daɗi idan ka samu caring husband ta ji ita kamar bata taɓa soyayya ba, bata san mene auren ba ta fara business sosai bai kuma hanata ba. Mami hankalinta kwance ita da mijinta Baffa sai junior babu abinda ta nema ta rasa a rayuwa, sosai take kula da su Aliyu Yaya Zuhura tana nan tana zuba zawarci abinta Balkisa ta samu suka daidaita da mijinta. Junaid ma lafiya suke zaune da Iklas hankali ya kwanta kowa ya amshi ƙaddara da Ubangiji ya jingina masa da rayuwa. Ridayya ta haƙura ta fara rainon ciki Mami kuma ta amsu yaran gabaɗaya abin mamaki kuma basu wani lalace ba girma suke sosai, a haka ta ce zata koma makaranta Abbiey ya ce ta bari ta haihuwa sun kusa komawa Japan ai ya mata settling komai a can ta yi masa godiya, sosai arziƙinsa yake ƙara yawa business yake sosai na motoci da da gidaje ya gina ya siyar ya buɗe babban shago a kantin kwari ya saka hannun jari ta ko'ina abubuwa sai addu'a da godiya ga Ubangiji a yadda ya ce Ridayya ce ƙashin arziƙinsa tunda ya same ta komai yake buɗe masa. Basu da matsala sai irin na samun saɓani da ko wanne ma'aurata suke samu a zamantakewa. Mardiyya ta auri Yaƙub babban gidana wajan sama da mutane ashirin tukunya ɗaya ake ɗorawa sosai ta rame ta zabge ta shiga damuwa amma bata da wata mafita data shige zaman gidan mijinta.
Prof komai ya ƙare a wajan Talatu ƙarin kunama ya zama bashi da komai komai ya lalace masa da ƙyar ya samu mace ya aura itama ƴar kanta yana fita take sakawa takalminta igiya ba ita zata dawo ba sai dare, tana dawowa ba maganar abinci za ta yi kwanciyarta idan ya tashe ta kan haƙƙinsa ta ce "wallahi kai kamar bunsuru haka kake, ba zan iya jaraba ba bacci nake ji" tana faɗin hakan take kwanciya abinta.
Bayan shekaru goma sha biyar.
Sosai Hanne ke kuka Zameer na tsaye a gefe ga tarin jama'ar da suka taro domin shaida auren ƴar wajan Zameer ɗin da Hanne ta haifa masa,bayan jama'a sun taro saurayin ya ce ya fasa auren a gaban bainar nasi koda aka buƙaci dalili ba kunya ya ce "Aje a tambaye ta" yana faɗin hakan ya ce a bashi sadakinsa aka bashi tun a lokacin ya bar garin gabaɗaya, a gida aka tsare yarinyar akan ta faɗi dalili ta fashe da kuka ta ce "Wai saboda likita ya ce masa ina da ciki"
"Ciki?" Hanne ta faɗa tana dafe ƙirji yarinyar ta ɗaga kai ta ce "E, kuma ai shi ne ya yi mini cikin ko kwanaki da aka nemi aka rasa ai ina shagonsa a can na kwana, kullum sai mun yi" Hanne "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun! Hakƙin Ridayya ke bibiyar rayuwar ƴata a dalilin zunubin daka aikata" kuka Hanne take kamar ranta zai fita ko Ridayya ƙaddara ce ta hau kanta da kuma sharrin MUNAFUKIN MIJI Zameer, kuma ba ta yi ciki ba amma gashi saboda an ce alhakii ɗan aike ne kan me shi yake bi ga abinda zunubinka ya ja nan, Allah ya isa wallahi ni dai na yi iya abinda zan iya da wanne ido zamu kalli jama'a? Ranar ɗaurin auren ƴarmu a gaban kowa miji ya ce ya fasa kuma ya ɗauke ƙafa ya gudu yanzu za mu yi da wannan cikin?" Gani sukai Zameer ya sulale tare da faɗuwa ƙasa babu numfashi, daidai nan Ƙaramin Alhaji ya shigo gidan wato Muhammad Bilal Zameer. wanda tuni an nuna masa cewa Zameer ne mahaifinsa tun bai yarda ba ya kuma yarda, Abbiey ya yi masa faɗa da nisiha sosai akan muhimmacin yarda da ƙaddara da yiwa iyaye biyayya hakan ya sa lokacin zuwa lokacin yake zuwa Katsina, kasancewar Alhaji ƙarami yana da garin jiki da shi da sadauki halinsu ɗaya kodayaushe fuska a kame ba walwala, idan ka ganshi zaka ɗakka wani babban mutum ne baya ɗaukan wargi hakan ya saka ƙannen shi suke shakkar shi, magana ɗaya yake baya biyu. Ya ɗaga labulan ɗakin yana daga bakin ƙofa ya dinga kallon yarinyar da kuma mahaifin nasu dake kwance ga Hanne dake kuka hannunsa ɗaya zube cikin aljihu ya ce "Ya akai?"